Showing 3001 words to 6000 words out of 59965 words

Chapter 2 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt

09 Dec 2024

9381

Shi kuwa yarima sai ya kura kyakkyawar budurwar idanu batare da yayi yunƙurin komai ba, kawai sai a ka ga budurwar ta tsaya cak sannan ta waigo tare da yiwa junan su lallausan murmushi a lokaci guda su duka biyun su kaji sun kamu da matuƙar soyayyar junan su.
kyakkyawar budurwar ta ɗauke dubanta daga na yarima su ka ci gaba da tafiya sai dai su yarima su ka daina hango su.
jiki a sanyaye yarima ya je ya kama linzamin dokinshi yayi gaba, Sauran dakarun su ka mara ma shi baya suna masu zaburar dawakansu.
Tun da aka fara wannan tafiya har aka iso gidan sarauta yarima bai ce kalaba.


*****


Fada ce ƙasaitacciya da aka ƙawata ta da kayan alatun jin dadin rayuwar duniya, Duk isar BASARAKE ko attajiri idan ya tsinci kanshi a cikin wannan fada dola ne ya zamo cikekken ɗan kauye kuma ya rai na kanshi.
Zaune a bisa karagar mulkin, sarki Baddadul-arus ne.
Sarki Baddadul-arus yakasance garjejen kato mai kama da giwa yana da ɗan mitsitsin kai da katon ciki tamkar an kifa ƙwarya a habarshi yana da ɗan mitsitsin gemu fari rol! da tsawon shi bai huce kamu ɗaya ba.
A gefen hannunshi na dama gimbiya uzaima ce, zaune a bisa wata kayatacciyar kujera ta alfarma ta na sanye da tsaleliyar alkyabba mai fatsi-fatsi, shigar tayi matukar fito da kyawun surar jikin ta.
Haƙiƙa duk inda kyawu yake gimbiya uzaima ta cika kyakkyawa domin ko gasar kyau Za ayi zata iya zamowa ta daya.
A wannan lokaci gaba ɗaya mutanen fadar babu abinda su ke kallo face satar kallon gimbiya uzaima, kai bama maza hatta 'yan uwanta mata idan su kayi arba da ita sai kaga sun wan game bakunan su suna dalalar da yawu, saboda yadda kyawun ta ya burgesu.
Gaba ɗaya fadar tayi tsit! tamkar mutuwa ta gifta, Daga can sai gimbiya ta katse shirun daya wanzu ta dubi mahaifinta sannan ta buɗi baki cikin zazzaƙar murya mai daɗi tamkar sarewa tace
"ya Abbana wai yaushe ne zamu tafiya nemo abubuwa guda uku domin mallakar TAKOBIN SIHIRI ?, Tabbas na ƙagu naga anyi wannan tafiya domin na sake yin ido biyu da abokin gaba ta yarima muzaifar domin ayi ta takare.
Koda jin wannan tambaya daga bakin uzaima sai sarki Baddadul-arus ya bushe da dariyar mugunta har da kyakyatawa sannan daga bisani ya dubi uzaima yace
"ya yata mafi soyuwa agareni kiyi sani cewa bakomai ne ya hanamu tafiya nemo abubuwa uku ba domin mallakar TAKOBIN SIHIRI ba sai domin akwai wani sauran birni guda daya da nake so na cinye shi da yaƙi, dazarar na kammala zamu fara shirye -shiryen tafiya, ina fatan kin gamsu da wannan bayani. Uzaima ta gyaɗa kai alamar gamsuwa sannan ta buɗi baki a karo na biyu tace,
"ya Abbana a sanina babu wata ƙasa da tarage a yankinmu da bamu cinye ta da yaki ba.
kafin uzaima ta ƙarashe maganar ta sarki Baddadul-Arus ya tari numfashin ta yace.
"wannan birni dazan kai farmaki baya iyaka da ƙasata na gano boyayyen birnin ne a lokacin da nake gudanar da bincike bisa halarar tsafi na.
Gama fadin hakan keda wuya sai sarki Baddadul-arus ya haɗe hannayenshu biyu ya karanto wadansu dalasiman tsafi jim kadan sai ga hoton wani kasaitaccen birni ya bayyana akan tafukan nashi.
Gine-ginen birnin sun kasancce cikin tsari, hatta tufafin su abin sha'awa ne.
Nan take uzaima taji birnin ya burge ta sannu A hankali hoton yana canza launi har ya bayyana hoton wani kyakkyawan saurayi yana sanye da kayan ado na sarauta.
Tun da gimbiya uzaima tazo duniya ba ta taɓa gani ko jin labarin da namijin da yakai saurayin kyawu ba.
Nan fa uzaima ta ƙurawa saurayin idanu tana nazarin shi, koda sarki Baddadul-Arus ya lura da halin 'yar tashi shiga sai ya karanto ɗalasiman tsafi ya tofa akan hannunshi, Faruwar hakan keda wuya sai hoton ya bace bat!,
Tamkar bai taɓa wanzuwa ba.
A sannanne uzaima ta dawo hayyacinta tana mai sauke ajiyar zuciya,
sarki Baddadul-arus yayi gyaran murya ya dubi uzaima yace"wannan birni dazan kai farmaki ana kiransa da suna JARUL-IMAN.
Yaushe ne zamu kai MAMAYAR BAZATO birnin?.
Uzaima ta tambaya a kagauce.
Baddadul-arus ya bushe da dariya sannan yace "Haba 'yata mai ki ke ci na baka na zuba ai saura kwanaki kaɗan mu kai wannan farmaki, ke dai kawai ki yi tanadi kafin ranar.
Ko da jin wannan batu sai uzaima ta cika da matukar farin ciki maral-musaltuwa.
koda gama fadin hakan sai sarki Baddadul-arus ya rike hannunta suka miƙe tsaye daga kan kujerunsu su ka nufi wata yar siririyar hanya dazata sadasu da gidan sarauta.



****
Al’amarin wannan kyakkywar budurwa da mahaifinta kuwa,
lokacin da suka kammala fafatawar yaƙi da yarima muzaifar sai suka ci gaba da tafiya babu sassauci, duk sa’ada su zo giftawa ta wani waje sai ka ga mutane sun tarwatse sun basu hanya sannan su bisu da kallo,
Al'amarin daya sa su duka biyun su ka cika da mamaki ke nan.
Haka kuma suka ci gaba da tafiya har ya zamana sun shafe tsawan sa'a uku suna wannan tafiya har suka fice daga cikin kasar suka shiga cikin dajin dake arewa da kasar. Tafiyar sa'a huɗu da daƙiƙa talatin kadai su ka yi suka isa wani madaidaicin gida a dajin.
shi dai wannan gida angina shi ne da zallar duwatsun wuta manya manya yana da tagogi guda shida da kofa guda ɗaya jal!.
Kofar an yi tane da zallar mulmulallen bakin karfe tsawanta ya kai kamu goma inda za'a sanya karti majiya karfi tsakanin ashirin ba zasu iya bangaje kofar ba.
Kai tsaye kyakyawar budurwa ta je bakin gidan sannan ta sanya hannunta ɗaya ta tura kofar ta bude.
Nan take ita da Dattijon suka kunna kai ciki budurwar na gaba dattijon na biye da ita.
Daga ciki gidan ya kasance yana ɗauke da manyan dakuna uku,Daga ɓangaren yamma akwai banɗaki guda biyu da kuma wani dan fili da aka yi rumfa domin shaƙatawa.
Kai tsaye suka shiga izuwa ɗakin dake yamma, sannan budurwar ta ta fice daga cikin dakin.
jim kaɗan sai gata ta dawo ɗauke da akusuhi da salkar ruwa ta ajiye gaban mahaifinanata ta sanya hannunta ta bude akushin ta shiga ɗibar abincin dake ciki tana bawa mahaifinnata a baki.
Sai da ta tabbatar ya ƙoshi sannan ta ɗauki salkar ruwa ta kafa mashi a baki ya sha ya ƙoshi.
A sannane ita ma Kyakyawar budurwa ta sanya abincin a gaba domin ta fara ci amma sai hakan ya gagara, Ba komai ne ya hanata cin abinci ba sai saboda tunanin Yarima Muzaifar.
Shiru ne ya wanzu a a tsakaninsu na tsawo lokaci
can sai mahaifinnata ya yi gyaran murya sannan ya buɗe baki ya ce.
"Ya 'yata shin ina dalilin rashin cin wannan abincin naki?".
Ko da jin wannan tambaya sai Sharilat ta dubi mahaifinnata ta ce.
"Ya Abbana ka yi sani cewa ba komai bane ya sanya ni cikin wannan hali ba face tunanin yadda rayuwarmu ta kasance cikin kunci da talauci.
Koda jin hakan sai tsoho Kuhairu ya yi murmushi ya dube ta ya ce.
"Haba 'yata shin me ya sanya zaki ɓoye mini gaskiyar al'amari, ki sani cewa ina da yaƙinin ba wannan abu ne yake damun ki ba dubu da yanayin yadda fuskarki ta nuna.
Koda jin haka sai Sharilat ta sunkuyar da kanta ta ce.
" ka gafarceni ya abbana Tabbas na ɓoye maka Gaskiyar abinda yake damuna.
Tsohon Kuhairu ya yi murmushi sannan ya dafa kafaɗun Sharilat ya dubeta ya co.
"Kar ki damu ya 'yata ki sani cewa ke kaɗaice ki ka rage mini daga cikin zuri'ata ya zama dole ki gaya mini abin da ke damunki.
Domin baki da wanda ya fini, ni nasan abinda yake damunki shi ne, kin kamu da soyayyar Yarima Muzaifar Jarumin da ki ka fafata yaki da shi ko ba haka bane.?
Cikin alamun jin kunya sharilat ta sunkuyar da kanta kas! Kamar mai tunanin wani abu.
Ba ta yi mamakin don mahaifinnata ya san abinda ke damunta ba, Domin ba baƙn al'amarin ne a wajen ta ba. Cikin alamun takaicin tsoho kuhairu ya dubi sharilat ya ce, " ya 'ya ta ki yi sani cewa da kin san abin da zai faru da kin gaggauta cire soyayyar Yarima daga zuciyarki, Domin gudun matsalar da zata faru.
Cikin kaɗuwa Shirilat ta dubi mahaifinta ta ce da shi "Ya abbana shin wace irin Matsalar zan fuskanta na kamuwa da soyayyar Yarima?".
Tsoho Kushairu ya ce " A yanzu bai kamata ba ki san matsalar ba, Domin sanin ta a yanzu ba shi da amfani,Tabbas anan gaba zaki gasgata batuna."
Koda jin hakan sai ta yi shiru tana mai zurfafa cikin kogin tunani.
Abu na farko da ya faɗo mata a rai shi ne ta yaya zata iya cire son Yarima a zuciyarta?.
Shin yanzu idan taki cire son na shi matsalar da mahaifina ya faɗa zata faru kuwa?.
Abu biyu shi ne ya aka yi mahaifinta ya gano sunan Yarima, Bayan cewa tunda suke basu taɓa gani ko jin labarin shi ba.
"Babban abinda hankalinta shi ne da ta yi nazari sosai a ɗazu, Irin kallon da yarima yake yi mata iri ɗaya ne sak! da na mahaifinta,
duk dacewar mahaifin nata ya tsufa amma yana ɗaukar kamanni da Yarima, A yanayin fuska da kirar jiki.
Har Sharilat ta buɗi baki zata ce wani abu sai suka jiyo ihu da kururuwa a can waje.
Al'amarin da ya sanya gaba ɗayan su suka miƙe tsaye zumbur!.
Tsoho Kushairu na rike da sandarsa ita kuma Sharilat tana rike da wani mashi suka ruga waje da gudu.
Aikuwa koda fitowarsu sai suka yi arba da waɗansu girɗa-girdan dakaru shirye-shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai tsananin kwarjini da ban tsoro.
Gaba ɗayan su suna zaune akan dawakai, a hannayensu suna ɗauke da makamai daban-daban irinsu gatari, da al'amudi.
Tabbas wadannan Dakaru sun zama abin tsoro, Domin komai dakewar zuciyar mutum baza iya kare musu kallo ba, face JARUMIN KWARAI, mai dakakkiyar zuciya.
A ƙalla adadin su ya kai guda ɗari tara.
Lokacin da dakarun suka yi arba da Sharilat da tsoho Kushairu sai aka fara kallon kallo, Sharilat tsoho da Kushairu suna masu gyara tsayuwarsu.
Sai da aka shafe tsawon lokaci ana kallon kallo.
Sai daga bisani ne wani garjejen kato mai jajayen idanu daga cikinsu, wanda yafi sauran munin siffa ya fito daga cikin mayaƙan yana mai zaburo dokinshi ya nufo inda Sharilat take tsaye.
Koda ya rage saura taku biyar a tsakanin su ba sai shugaban dakarun ya ja linzamin dokinshi ya tsaya ya karewa Sharilat da tsoho Kuhairu kallo tunda daga ƙasa har sama, kawai sai ya bushe da dariya mugunta sai da ya yi ta ishe shi sannan ya murtuke fuska kamar an aiko masa SAKON MUTUWA ya dubi Sharilat a cikin kallo na kaskanci da wulakanci, sannan ya fara magana da muryarshi mai kama da gurnanin damisa ya ce.
"Ya Sharilat ki yi sani cewa yau nazo gareki cikin gagarumin shirin daban taɓa yin kamar shi ba.
Ki sani cewa yau ba zaki kuɓuta daga tsananin ukubata ba …!
Kafin shugaban ya ƙarashe zancenshi Sharilat ta tari numfashin shi ta na mai daka masa tsawa ta ce, "Kaiconka ya kai Huzlan tabbas ka tafka babban kuskure da har kake ganin cewa zaka samu nasara akaina.
Lallai yau zan yi maka kisa mafi muni ka yi MUGUWAR HALLAKA domin hakan ya zama darasi ga masu muguwar ɗabi'a irin taka. Haƙiƙa zalunci da azzalumai basa ɗorewa aban ƙasa face an samu abu biyu ya kawar dasu, walau dai mutuwa ko kuwa wata haitta ta kawar dashi aban ƙasa.
Koda jin wannan batu sai Shugaba Huzlan ya kuma bushewa da dariya a karo na biyu a wannan karon sai ya kusa suɓutowa daga kan dokinshi saboda da dariyar,
Sannan ya tsagaita ya dubi Sharilat ya ce.
"Haba yarinya ki sani cewa ai karo dani a yau dai dai-dai yake da buɗe taskar ANNOBA DARI.
Domin a yau na zo da gagarumin shirin da ban taba yin kamar shi ba, ki sani cewa wannan gafalallen tsohon na ki ba zai hanani cimma buri na ba.
Yau shekaru shida ke nan muna gwabza yaƙi dake, Babu wanda ke samun nasara amma a yau za'a yi ta ta ƙare.
Koda gama fadin hakan sai Huzlan ya zaro wata zabgegiyar adda dake rataye a gadon bayanshi.
Sannan ya wangame bakinshi ya kwarara ihu ya dako tsalle daga kan dokinshi, kai ka ce ba ya jin nauyin jikinshi ya afkawa Sharilat da dukkan karfinshi.
Su duka biyun suka kaceme da azababben yaki, su ka wanzu suna kawai junansu mugggun hare hare cikin zafin nama.
Koda ganin hakan sai tsoho Kuhairu ya kwarara uban ihu ya falfala da azababben gudu kan dakarun Huzlan hannun shi na hagu rike da wannan sanda, koda ya rage baifi saura taku huɗu tsakaninsu ba, sai sandar ta rikiɗa izuwa dogon mashi iri ɗaya sak da na hannun Sharilat.
In da ace mutum zai ga yadda tsohon Kuhairu ya tari waɗannan Ɗaruruwan mayaƙa dole ne ya jinjina ma shi ya san cewa ya cika tsoho mai ran karfe kuma.
Ana haɗuwa aka yamutse da azababban yaƙi, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya saboda yadda dawakai ke yin dudufniya suna turmutsustsu,ƙarar HADUWAR TAKUBBA ta cika dodon kunne, ƙiri-ƙiri gashi dai dakarun sun fi Kuhairu karfin damtse amma sai ya zamana ya zame musu kaifin takobi ya wanzu ya aika rayukan su barzahu, Ta hanyar tsire su da mashi, A wasu lokutan sai kaga ya mako badakare ya bazar da shi a kas.
Nan fa waje ya cika ihu mazaje suka dunga yin muguwar hallaka, jini ya dunga kwaranya, fantsama da tsartuwa.
Kafin cikar daƙiƙa arba'in Kuhairu ya samu nasarar kashe dakaru sama da saba'in.
Al'amarin daya yi mutuƙar dugunzuma hankalin dakarun
ke nan kuma suka harzuƙa ainun suka ƙara afka ma shi da yaƙi yafi muni.
A ɓangaren Sharilat da Sadauki Huzlan kuwa sun wanzu suna kawai junansu sara da suka cikin zafin nama JURIYA BAJINTA ta ban al'ajabi.
A na wannan yaƙi ne cikin shammace Huzlan ya kawai Sharilat wani wasan sara da zabgegiyar addarshi domin tsinke mata wuya.
Cikin zafin nama ta sunkuya addar ta sari iska, cikin Fushi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login