Showing 9001 words to 12000 words out of 59965 words
Chapter 4 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt
komai naka zuwa gare ni, idan kuwa ka yi girman kai ma'ana ka saɓawa umarnina, to ba makawa da zan shafe ka da jama'arka daga doron ƙasa kamar yadda na saba yi ga ƙananan Sarakuna masu taurin kai irin ka.
Ka sani cewa bakin rijiya ba gurin wasan makaho ba ne, tabbas idan kunne ya ji jiki ya tsira.
Lokacin da magatakarda ya zo nan a karatun wasikar sai Sarki Huraisu ya mike tsaye daga kan karagarshi ya tako da kafafunshi har inda ɗan aiken Sarki Baddadul Arus yake ya shammace shi ya dunkule hannayenshi biyu ya gabza masa naushi a a wuya, nan take wuyanshi ya karye ji kake rukus. Take ya faɗi ƙasa matacce ko shurawa bai yi ba, kawai sai Sarki Huraisu ya yi umarni a dauke gawar ɗan aiken aka goge jinin da ya zuba da wani farin kylle.
Sarki Huraisu ya kalli gaba ɗaya mutanen fadar a cikin matuƙar fushin da bai taɓa yin kamarshi ba ya buɗi baki cikin maɗaukakiyar muryar ya ce: "Ya ku mutanen fada mai albarka ku sani cewa, wannan yaƙi babu gudu babu ja da baya, kuma ban ɗaukewa kowa ba babba da yaro. "
Koda gama faɗin haka sai Sarki ya juya ya nufi wata 'yar siririyar hanya da za ta sada shi da gidan sarauta, wasu ZARATAN DAKARU ma'abota bakaken tufafi suka mara mashi baya har suka kule da zuwa gidan sarautar.
Koda ficewar Sarki sai fadar ta hargitse, mutane zasu dinga zuwa gudaddajin su suna shigar yaƙi domin tunkarar abinda zai kawo karshensu.
****
Lokacin da Sarki Baddadul-Arus suka ga an shafe tsawon sa'a ba a ga ɗan aikensu ya dawo ba, sai kawai Baddadul- Arus ya ba da Umarnin da a afkawa birnin a karya kofa ya shiga. Kawai sai aka jiyo an busa ƙahon yaƙi daga cikin birnin Jarul-Iman sai ga kofar ta ta buɗe mayaƙa suna tururuwar fitowa.
Lokacin da mayaƙan suka gama fitowa sai aka fara kallon-kallo tsakanin ɓangarorin biyu har ya zamana an shafe wasu 'yan daƙiƙu.
Kawai sai Sarki Baddadul-Arus da Uzaima suka saki linzamin dawakansu suka durfafi in da tawagar Sarki Huraisu take.
Koda ganin haka sai shi ma Huraisu da sarkin yaƙinshi mai suna Bilar su ka sakarwa dawakansu linzami don tarar juna, yayin da a ka zo daf da juna sai suka tsaya cak!.
Aka sa ke yin kallon-kallo a karo na biyu sannan Sarki Baddul Arus ya ce "Ya kai wannan Sarki Ma'abocin taurin kai a garemu ka sani cewa ko ba a gwada ba ka san cewa linzami yafi karfin
bakin kaza haƙiƙa runduna ta Ninka taka a yawa da karfi.
Ni sarki Badaddul-Arus mai burin zamowa shugaban nahiyar Mufrad baki ɗaya na zo ni da 'ya Uzaima lallai ba zan koma ƙasata ba face na baje birnin ka daga doron ƙasa domin hakan ya zama darasi ga ' yan tsakin sarakuna irinka. Koda jin wannan batun sai Sarki Huraisu bushe da dariya kamar bazai daina ba.
Al'amarin da ya yi mutuƙar ba wa Badaddul-Arus da Uzaima mamaki kenan kuma ya ya fusata su ainun.
Bisa ganin cewa duk kasaitarsu amma yau wani mahaluƙi ya wanzu a gabansu ya na neman ƙasƙantar da Darajarsu. Sarki Huraisu ya haɗe rai sannan ya ƙurawa Uzaima idanu ko ƙiftawa ba ya yi, sannan ya juya ya dubi Badaddul Arus ya ce.
"Ya kai Badaddul-Arus kayi sani cewa na daɗe ina jiran wannan rana mai cike da farin ciki domin a wannan rana. ne na taba fita yaƙi a rayuwata, A iya tsawon rayuwata tun da nake ban taɓa sanya wani al'amari a gabana ba face na cimma nasara akanshi, Ina mai tabbatar maka da cewa yawan mayaƙan ba zai bani tsoro ba, Domin Ni kaɗai zan iya ja da su na kawar da su cikin 'yan daƙiƙu. "
Sa'adda Sarki Huraisu ya zo nan a Zancenshi sai Sarki Baddadul-Arus da 'yarshi Uzaima su ka tuntsire da dariya, Domin suna ganin cewa Huraisu ya yi wauta, kafin dayansu ya kara cewa wani abu Badaddul Arus da' yarshi Uzaima sun zaro makamansu suka sakarwa dawakansu linzami su ka yunƙura kan Sarki Huraisu.
Ko da ganin hakan sai shi ma Sarki Huraisu ya zaburo dokinshi ya durfafi su Badadul Arus ya na mai ya dakatar da Sarkin yakin shi da hannu yana nuna ya dakata.
Koda Sarki Badaddul-Arus da Uzaima su ka yi arba da Sarki Huraisu ya durfafo inda suke batare da riƙe wani makami ba, sai suka cika da mamaki amma sai su ka raya a zuciyarsu, cewa lallai Sarki Huraisu ya zama wawa marar tunani to amma masu iya magana na cewa "idan ka ji makaho ya ce a yi wasan jifa to ji ya yi ya taka dutse.
Lallai akwai wani abu da Huiraisu ke takama da shi.
Koda gwarazan jaruman uku suka haɗu sai a ka kacame da masifaffan yaƙi, su ka wanzu suna kaiwa junansu hare-hare cikin mutuƙar zafin nama da JURIYA DA BAJINTA. Sarki Huraisu ya wanzu ya na kare hare-haren Badaddul-Arus da Uzaima kawai batare da ya yi yunƙurin zare makami ba.
wannan shi ne abinda ya faru ga Sarki Badaddul-Arus da gimbiya Uzama a birnin Jarul-Iman domin su kawar da Sarki Huraisu.
***
Gari na wayewa tunda dukun-dukun safiya Yarima Muzaifar ya kammala shiri tsaf, sannan ya ɗebi dakaru suka shiga cikin gari bisa dawakai amma wannan karon su Yarima ya ƙi sanya kayan yaƙi ajikinshi kuma ya rufe fuskarshi da rawani ta yadda babu wanda zai iya shaida shi.
Lokacin da su ka ci gaba da tafiya a cikin birnin sai ya zamana sa'a biyar ta shuɗe batare da Yarima ya ji duriyar bakuwar jaruma ba. Al'amarin da ya Ɗugunzuma hankalin Yarima Muzaifar kenan ya shiga damuwa ainun.
Lokacin da dakarun suka ga Yarima bai samu baƙuwar jaruma sai suka shiga kasuwa suka shiga bincike jama'a.
Koda buhun hatsi mutum yazo dashi sai an bincika, rumfuna da saƙo da lungu.
Tabbas gaskiyar masu iya magana da suka, "idan Raƙumin ka ya ɓata ko akurki ka gani sai ka leƙa.
Nan fa gaba ɗaya su Yarima su ka hargitse kasuwar mutane suka shiga guje - guje gami da iface- ifacen tamkar sun ga mutuwar su, masu karfi suka dinga ta ke masu rauni suna suna Faɗuwa ƙasa ana tattake su, sai da yarima da dakarun su ka shafe tsawon Sa'a biyar suna tafiya a cikin babban birnin Darul-Kushur ba su ji labari ko Ɗuriyar bakuwar jaruma ba. Al'amarin da ya sanya zuciyar Yarima ta karaya kenan ya shiga damuwa kamar zai fashe da kuka ga yunwa da kishi sun addabe shi, tare soyayyar Almajirar dake Addabarshi a zuciya.
Abin da Yarima bai sani ba shi ne, ita ma baƙuwar jarumar tunda duku-dukun safiya ta shigo cikin gari domin ta sadu dashi.
Sa'adda baƙuwar jarumar ta ga har yamma tayi bata ga inda su yarima suke ba sai ta yanke shawarar ta ɗan huta a ƙasan wata bishiya sannan ta fice daga birnin.
A na cikin wannan hali ne sai ga Yarima da dakarunshi sun zo giftawa ta wajen, ko da Yarima ya yi arba da jarumar sai ya ja linzamin dokinshi ya tsaya sannan ya taka da kafafunshi har inda take, tare da yiwa junansu murmushi ba.
Da isowarshi ya tsugunna a gabanta ya dubeta fuskarshi cike da Annuri ya ce.
"Marhaban da sake saduwa da tauraruwar Abar haskawa, sarauniyar matayen duniya.
Ya ke jaruma ma'abociyar kyawu ki yi sani cewa tun ranar da mu ka fafata yaƙi a junanmu na ji na kamu da mutuƙar kaunarki, ina fatan za ki ba ni kujerar zama a fadar sonki.? " Baƙuwar jarumar dubi Muzaifar cikin murmushi mai taushi ta ce "Ya kai Muzaifar ka yi sani cewa tun ranar da muka haɗu ni ma na ji
na kamu da kaunarka, bisa wannan dalili ya sanya na fito neman ka domin zuciyata taƙi hakura ta danne soyayyarka face na yi arba da kai.
Lokacin da baƙuwar jaruma ta zo nan a zancenta sai su duka biyu suka kurawa junansu idanu suna yiwa juna tattausan murmushin mai mai tattare da tsantsar soyayya.
Cikin nutsuwa yarima ya yi ajiyar zuciya ya dubi jarumar ya ce, "Ya abar kaunata idan ba zaki damu ba ina buƙatar nayi miki waɗansu tambayoyi."
Ko da jin haka sai Jaruman ta ce , "Fadi tambayarka ya masoyi ina mai sauraren ka. Yarima ya yi ajiyar zuciya sannan ya kawo gwauron numfashi ya ajiye ya ce, "Menene sunanki da na mahaifinki.? Kuma menene labarin rayuwarki."
Koda jin waɗannan tambayoyin sai jarumar ta runkui da kanta ƙas batare da ta ce uffan ba, duk Wannan abu dake waka a tsakanin yarima da jarumar, Dakarun Yarima na tsaye a gefe guda Suna kallon abinda ke faruwa.
Koda su ka ga abin da ke wakana sai suka cika da matuƙar mamaki domin a iya sanin su tunda suke ba su tuba ganin Yarima ya kula wata 'ya mace ba, duk irin tsananin kyawunta.
Amma sai zukatan su suka shiga cikin wasi-wasi domin gaza gane wannan jaruma, a da sun yi tsammanin gimbiya Uzaima ce 'yar Sarki Badaddul-Arus ce ta yi ɓadda kama, amma a yanzu abin ba baka yake ba.
Jarumar ta ɗago da kanta ta yi murmushi ga Yarima mai ɗimauta zuciyar duk wani da namiji mai hankali sannan ta buɗe baki ta ce. "Da farko dai ni sunana Sharilat Bintu Kuhairu game da tambayarka ta biyu kuwa labari ne mai tsawo wanda da zamu kwana ba zan iya kawo karashe shi ba.
Saboda haka ka yi mini uzuri wannan tambaya na yi maka alkawari idan mun sa ke saduwa zan sanar da kai labarin rayuwarta.
Da jin wannan jawabi sai Yarima ya ce, "Babu damuwa ya masoyiyata idan mun sake Haɗuwa sai ki bani tarihin rayuwarki ni ma in ba ki tawa.
Koda gama faɗin hakan sai Sharilat ta miƙe tsaye ta juya ta nufi kofar fita gari, ta na mai waigen yarima su na yi juna murmushi mai tattare da santsar so da kauna.
Sai da Sharilat ta yi nisa cikin tafiyar har ta ɓace Yarima ya daina hangota, sannan yarima yaje ya kama dokinshi ya hau sannan ya sakarmashi linzami ya yi gaba dakarun shi su ka mara ma shi baya, zuciyar Muzaifar cike da farin ciki ciki mara misaltuwa.
ko da su yarima suka iso gidan sarauta sai ya huce kai tsaye izuwa cikin turakarshi ya shiga kewaye ya tsala wanka, ya ci abinci sannan ya fice ya nufi tukarar mahaifinshi.
Tun kafin yarima ya isa su ka haɗu da sarki Himras shi ma ya na shirin zuwa wajenshi koda budurwar ta su sai suka garzaya wani ƙasaitaccen lambu dake nesa kadan da turakar Sarki.
Bayan sun zauna a bisa waɗansu ƙayatattun kujeru na azurfa, sai shiru ya wanzu a tsakanin su na ɗan wani lokaci.
Daga can sai yarima ya yi gyaran murya ya dubi mahaifinshi ya ce,"Ya Abbana ka yi sani Cewa a yau ne na sadu da wannan jaruma kuma ta sanar da ni sunanta dana mahaifinta.
Abin da ta gaya min shi ne sunanta Sharilat sunan mahaifinta Kuhairu, na yi iyakar ƙokarin sanin labarin rayuwarta sai dai hakan bai samu ba.
Sa'adda Sarki Himras ya ji wannan batun daga bakin Yarima sai zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata zata ƙone kuma ya cika da matuƙar baƙin ciki da takaici mara misaltuwa. Amma saboda kada yarima ya gane halin da ya ne ciki sai ya bar abin a ranshi, ya sa ki tattausan murnmushi ga Yarima mai kama da yaƙe ya ce, "Babu damuwa ba dole ba ne sai na ji tarihin rayuwar jarumar tabbas na gamsu da bayaninka. a yau da safe na gudanar da bincike a bisa halarar tsafina nagano dukkan abin da ke faruwa tsafin ya Bayyana mini cewa, lallai Sharilat da mahaifinta za su ba mu gagarumar gudunmowa a tafiyarmu ta ɗauko TAKOBIN SIHIRI.
"Ya na da kyau a cikin daren nan na gana da Sharilat da mahaifinta domin na nemi goyan bayansu domin tafiya neman abubuwa uku wato sarkar tsafi dake ajiye a tsahon ƙabari a
Birnin Rum.
SIHIRATACCEN KUNDI dake ajiye a fadar Boka Zammar domin Ɗauki TAKOƁIN SIHIRI.
Ya yin da Yarima ya ji Wannan bayani sai ya dubi mahaifinshi ya ce.
"Ya Abbana shin ban ji ka min bayani ba akan yadda Sharilat da mahaifinta suke da horon yaki irin na mu ba.
Koda jin wannan tambaya sai Himras ya bushe da dariya sannan ya dubi Yanma ya ce " In banda abinka ai ranar da zan ziyarci su Sharilat zan gane gaskıyar wannan al'amari, kai dai kawai ka je ka kwanta domin huce gajiyar dake tattare da kai, tunda a yanzu duhun dare ya kawo kai ni zan ɗan shaƙata a nan.
Koda jin hakan sai yarima Muzairaf ya miƙa tsaye tsam! Ya taka da kafafunshi ya nufi kofar fita daga lambun ya ną mai waigen mahaifinshi. Koda ficewar shi Ysai Sarki ya mike tsaye zumbur! Ya dunga kai komo a cikin lambun cikin matuƙar tashin hankali tamkar zai fashe da kuka.
Bakomai ne ya sanya Himras ya shiga damuwa a lokacin da yarima Muzaifar ya sanar da shi sunan wannan Jarumar da mahfinta ba, Fa ce a yanzu ya gano cewa Kuhairu ɗan uwanshi ne wanda ya sanya a ka kashe ya ɗare kan karagar mulkin shi. Abin tambaya a nan shi ne ya aka yi Kuhairu da matar Hashmilat suka rayu har suka samu Haihuwa bayan cewa ya tabbatar an yi musu kisan da baza su iya ci gaba da rayuwa ba.
Abu na farko da ya faɗo Himras a rai shi ne tabbas idan a ka yi sakaci har Yarima ya gano ɓoyayyen sirrin dake tsakaninsa da tsoho Kuhairu lallai za a samu babbar matsala, ya zamana dole ka gana da Kuhairu a wannan dare. Sa'adda Sarki Himras ya zo nan a tunaninshi sai ya runtse idanunshi ya karanta Ɗalasiman tsafi faruwar hakan ke da wuya sai ya ɓace ɓat daga lambun tamkar bai taɓa wanzuwa ba.
*****
Dalilin ƙulluwar gaba tsakanin Sarki Himras da tsoho Kuhairu kuwa shi ne.
Sarki saruful-uzwar ya kasance ƙasaitaccen Sarki ya shara asanin dalisiman tsafi ya na da tarin dukiya dangin lu'ulu'u u dadin daɗawa kuma ya kasance sadauki mai tarwatsa maza a filin daga.
Ya na da matar aure mai suna Muzaira ta haifa masa 'ya'ya guda biyu Yarima Kuhairu shi ne babba sannan a ka haifo Yarima Himras a rayuwar Sarki Saruful-uzwar babu abinda yake so sama da waɗannan ' ya'ya na shi kasancewar ya na ganin cewa su kaɗai ne suka rage ma shi a cikin zuri'arshi.
Mutanen ƙasar Darul-kushur suna