Showing 33001 words to 36000 words out of 59965 words

Chapter 12 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt

09 Dec 2024

9383

Sai Ya Tura mashi Ƙanƙara Idan Suka Haɗu Da juna Sai Kaji sunyi Bindiga Tamkar Saukar Aradu.
Haka dai Zaratan Jaruman biyu Yazamana Cewa sun turawa Juna Miyagun Abubuwan Sihiri Fiye Da Kala Saba'in Amma Basu Nasarar Lakutar Jikin juna ba.
Wohoho! Haƙiƙa KARON MAZA Abin Tsoro ne Babu Abinda Zai Ɗimauta Zuciyar Mutum Face yadda GWARAZAN MAYAKAN Ke Yakin Cikin Matuƙar Zafin Nama JURIYA DA BAJINTA Tamakar Waɗansu Fusattun Zakoki Da suka Shafe mako guda basu yi kalaci ba Suka yi Arba Da Barewa Guda Ɗaya.
Ana Cikin Wannan Guguntsumin Artabu ne Sarki Baddadul-arus Ya Shammaci Sarki Himras Ya Gabza Mashi Naushi a Haƙarƙarinshi Na Dama, Saboda ƙarfin Naushin Sai Da Yayi Katantanwa A sama Sau uku Sannan ya faɗo Ƙasa Tim Yana Mai Tsandara Ihu Sarƙar Tsafin dake Hannunshi Ta faɗi Can Gefe Guda.
Kafin Sarki Himras Yayi Wani Yunƙuri Baddadul-arus Ya Karanto Waɗansu Ɗalasiman Tsafi Ya Face Ɓat Tamkar Bai Wanzuwa ba Yana Mai Ƙyalƙyala Mashi Dariyar Mugunta.
Cikin Matuƙar Fushi Mara Misaltuwa Sarki Himras Ya Miƙe Tsaye Zumbur Yana Mai kai dubanshi Izuwa inda Sarkar Tsafinshi Ta faɗi Aikuwa Sai Yaga wayam Babu ita, kawai Sai Ya Taƙarƙare Ya Kurma Wawan ihu, kawai Sai Ya Shafi Gurun tsafin Ya Shafe shi Da hannun shi Na hagu Take Ya ɓace ɓat Tamkar Baitaɓa wanzuwa ba.
Bai Bayyana A ko ina ba Sai A Filin Yaƙi Sai Ya Cika Da Matuƙar Takaici Da Baƙin Ciki, Bakomai Ya Gani ba face Babu sarki Baddadul-Arus Da Dukkanin Tawagarshi.
Cikin Matuƙar Fushi Ya Zira Hannunshi A Aljihunshi ya Ɗauko Madubin Tsafin Ya Shafe shi Da hannunshi Na Hagu Take Aljanu Zamzaru ya Bayyana Ɗauke Dasu Sarki Baddadul-arus A Gadon Bayanshi Yana Tsala Gudu A Sararin Samaniya.
Ko da Ganin Hakan Sai Sarki Himras Ya Falfala da Azababban Gudu yana nufi inda Aljani Narguz Yake Yana banke dakarun Dake Gabanshi Yana Samarwa Da Kanshi Hanya Ta ƙarfin Tsiya, Yana Isa Ya Daga Tsalle Ya Haye Gadon Bayan Nargzu Yana Mai Cewa Da shi " Ya Hanzari Ka Ɗauko Yarima Da Abokan Tafiyarmu Ka bi Sahun su Aljani Zamzaru.
Da jin Wannan Umarni Sai Narguz Yayi Wuf! Cikin Baƙin Zafin Nama ya Sanya Hannunshi Ɗaya Ya Ɗauko Yarima Muzaifar, Jaruma Sharilat da Tsoho kuhairu Ya Ɗora su bisa Gadon Bayanshi Ya Buɗe Fuka-fukanshi Ya Luluƙa Cikin Gajimare Cikin Matuƙar Gudu Tamkar Giftawar Tauraruwa Mai Wutsiya.








******


Sa'adda Sarki Usulul-Haibar, Gimbiya Hulaifa da Boka Hushaib Suka ga Irin Gagarumar Ɓarnar Da Da su Sarki Himras suka yi masu Sai Suka Cika Da Matuƙar Baƙin Ciki Maral-Musaltuwa.
Cikin Hanzari Boka Hushaib Ya Ɗauko Madubin Tsafin shi Ya Shafe shi Da hannunshi Na Hagu Ya Shiga Gudanar Da Bincike, Amma Sai Madubin Yayi Bindiga Ya Tarwatse.
Koda Ganin Wannan Al'amari Sai Sarki Usulul-Haibar Ya yanke Jiki Ya Faɗi Ƙasa Sumamme Cikin Figici Boka Hushaib Ya ƙwallawa Masu Magani kira Suka Ɗauki Usulul-Haibar bisa Wani Ƙayataccen Gado Suka Ruga dashi zuwa Cikin gidan Sarauta Domin Ceto Rayuwar shi.
A Sannanne Jiri ya fara Ɗibar Gimbiya Hulaifa Da Boka Hushaib sakamakon jinin Dake Zuba A Jikin su, Cikin Hanzari Aka Ɗauke Su A Cikin Wani Ƙasaitaccen Keken Doki Aka nufi Gidan Sarauta masu magani Suka Shiga Basu Taimakon Gaggawa.
A Dai-dai Wannan Lokaci Ne Dakaru Suka shiga Kwashe Gawarwakin waɗanda suka Rasa Rayukansu, Waɗanda Suka Samu Miyagun Raunuka Kuwa Aka Shiga Basu Taimakon Gaggawa.
Nan fa Gaba Ɗaya Birnin Rum Ya Kaure Da koke-koken Jama'a Yara,mata da tsofaffi wasu na kuka ne bisa Rasa Masoyansu Da iyayensu.
A iya Tsawon Wanzuwar Birnin Rum Basu taɓa Ganin Tashin Hankali kamar Na Wannan Rana ba, Domin babu wani Mutum Da bai Rasa Ɗan Uwanshi Na Jini ba.
Babu Abinda Zai Jefa Tausayi A Zuciyar Mutum kuma Ya Sanya shi Zubar Da Hawaye Face idan Yaga Yadda Ƙananan yara ke Rungume Gwarwakin Mahaifansu Suna Rusa kuka abin Ban Tausayi Tamkar Ransu Zai Fita.
Wannan Shi ne Abinda Yafaru A birnin Rum Bayan Sarki Baddadul-arus Ya Sami Nasarar Ɗaukar Tsafi Dake Ajiye A Cikin Tsohon ƙabarin Boka Aulad.


*****


Lokacin da Aljani Narguz Yabi Sawun su Sarki Baddadul-arus A Gadon Bayanshi Yana Ɗauke Da Sarki Himras, Yarima Muzaifar,Tsoho Kuhairu Da Jaruma Sharilat, Sai Ya wanzu yana keta Gajimare .
Sai da Akan Shafe Rabin Sa'a ba'a ji koda Ɗuriyar su Sarki Baddadul-arus ba,
Al'amarin Daya Ɗugunzuma Hankalin kowa Kenna musamman Sarki Himras Ya Zira Hannunshi A Aljihunshi Ya Ɗauko Madubin Tsafin shi ya Shiga Gudanar Da Bincike Domin Gano inda su Sarki Baddadul-arus suke, Daƙyar da Siɗin Goshi Ya Gano dalilin Daya Sanya ya kasa Ganosun Dalilin Hakan kuwa Shine, Matsawar Suna Riƙe Da Wannan Sarkar Tsafi Babu wani sihiri Da zai yi tasiri a kansu.
Sa'adda Sarki Himras yaga Wannan Al'amari Sai Ya Cika Da Matuƙar Baƙin Ciki Har Kwallar Takaici Ta Zubo Daga Idanuwanshi.
Al'amarin Daya Sanya Yarima Muzaifar Dake Zaune A gafen shi Ya Shiga Damuwa Kenan Ya Dubeshi Yace " Ya Abbana Shin ina Dalilin Wannan Ƙwalla taka?.
Ko da jin Wannan Tambaya Sai sarki Himras Ya share Hawayen dake Fuskarshi Ya Dubeshi Yace " Ya Abin Alfaharina kayi Sani binciken da na Gudanar A Halarar Tsafina Na gano cewa Matsawar Su Sarki Baddadul-arus suna Tare Da wannan Sarƙar Tsafi Bazamu iya Samun Nasara Akan su ba.
Don haka akwai bukatar mu yada zango Domin Mu Tattauna, Sanin kankane Cewa Babu Wanda Ya Isa Ya mallaki TAKOBIN SIHIRI Face Ya Tashi Boka Sharubu Daga KUSHEWAR shi Domin Shine Kaɗai Yasan Ƙa'idojin Tafiyar.
Ko da jin Wannan Bayani Sai Yarima Muzaifar Ya Shiga Cikin Matukar Damuwa, Batare Da wani Ɓata lokaci ba Sarki Himras Ya Dubi Aljani Narguz Dashi "Yakai Narguz Ina So Mu Yada Zango Anan.
Da Jin Wannan Batu Sai Nargzu Yace "Ya Shugabana Shin Mun Haƙura ne Da bin sawun abokan gaba ne.
Ko da jin hakan Sai Himras Ya Fusata Ainun Ya Dakawa Narguz Tsawa wacce Ta Sanya Hantar Cikinshi Ta Kaɗa Tsaro Ya Kamashi, Ya Dube shi Cikin Fushi Yace " Zancen Banza kenan, Yakai Narguz kayi Sani Cewa Duk Abinda Na Faɗa Umarni nake Baka bawai Neman Shawara Nake ba.
Sa'adda Narguz yaji wannan batu sai Jikin shi yakama Tsuma Yana Kyarma, Bakinshi Na Kyarma Yace "An Gama ya Shugabana Tuba nake yi, Yana Gama Faɗin Hakan Ya saki Manyan Fuka-fukanshi Yayi Ƙasa Luuu! Ya Sauka A Turba.
Inda Ya aka Sauka Yakasance Waje Mai Tattare Da Bishiyu, Duwatsu,koramu Wata irin Ni'imtacciyar Iska Na kaɗawa Rassan Bishiyu Nayin Rangaji, Waɗansu Tsuntse Masu Ƙyawun launi Na Shawagi A Sararin Samaniya Suna Fitar Da wani Sautin Kuka Mai Ɗankaran Daɗi.
Tabbas Wannan Waje Ya Cika Mai Matuƙar Abin Sha'awa, Babu Wani Bil'adama Da Zai Arba Da shi Face Ya kwaɗitu Ya Rayu A Wajen.
Batare da ɓata lokaci ba kowa ya Shiga Tsaftace Jikin shi Da Ruwan Korama, Sannan Aka Kafa Ta tuna, Yarima Tare Da sarki Sharilat Da Tsoho kuhairu, Shi kuwa Aljanu Narguz Sai Ya Zare Wata Rantsattsiyar Takobi A Damtsenshi Ya Shiga Yin Rangadi Domin Tabbatar Da Tsaro A Tsakanin Tantunan Kasancewar Duhun Dare Yafara kawo Kai.
Lokacin Da Yarima Muzaifar Da Sarki Suka Samu Nutsuwa Sai Suka Ɗauko Abin Guzurinsu Suka Shiga Kimtsa Cikin su.
Bayan An Kammala ne Sai yarima ya Dubi Sarki Yace Ya Abbana Shin Baka ƙara sa bani labarin jaruma Nashmira ba wacce take burin Bautar Da Mazajen Duniya?
Ko da Jin Wannan Tambaya Sai Sarki Yayi Shiru Sannan Ya ce "Ya Ɗana Duk da cewar A halin yanzu ina Cikin Damuwa bisa Suɓucewar Sarkar Tsafi Amma zan baka cigaban Hikayar Nashmira a kaƙaice, Sai ka saka kunne kaji yadda Takasance.


******
Ko da samun wannan nasara sai baƙon Mahayin ya sauko daga kan dokin shi ya zare wata Sharɓeɓiyar takobi a Damtsenshi yana mai bushewa da dariyar mugunta, ya taka Ƙafafuwanshi har zuwa in da Nashmira ke Kwance babu alamun numfashi a tare da ita.
Ko da ya rage rage bai wuce taku ɗaya tsakanin su ba sai sai kawai ya ɗaga takobin domin ya datse mata wuya.
Kwatsam bazato babu tsammani sai ya ga Nashmira taja Gwauron numfashin Idanuwanta sun buɗe, cikin zafin nama ta wurƙila gefe guda takobin ta nutse a cikin ƙarƙashin ƙasa.
Cikin zafin nama ya sa ke zare takobin ya kaiwa mata sara a karo na biyu, ta kaucewa harin a karo na biyu, sannan ta sanya ƙafafuwanta biyu ta bugi Ƙafafun shi take ya faɗi ƙasa rikica! takobin shi ta faɗi can gefe guda.
Cikin Gwaninta Nashmira ta yi wuf ta mike tsaye ta ɗauki takobin Mahayin ta sanya tsininta akan wuyan shi, har tsinin ya yanke shi jini ya zuba kaɗan, ta ƙura ma shi idanu.
Sannan daga bisani ta ɗauke takobin ta jefer da ita Sannan ta taka da ƙafafuwanta ta nufi inda dokin ta yake takama ta haye ta sakar mashi linzami, amma sai ta taga mahayin yasha gabanta Fuskarshi cike da annuri ya dube ta ya ce "ya JARUMAR JARUMAI kiyi sani cewa iya tsawon rayuwata bantaɓa yin Artabu da wata jaruma da tayi nasara akai na ba sai ke, lokacin da mahaifina ke raye ya taɓa faɗa mani cewa har abada bazan taɓa cika burina na zamowa SARKIN SADAUKAI ba face na haɗu da Jarumar da na fafata yaƙi da ita ta yi rinjaye a kai na.
Saboda haka ina roƙon ki ki sanar da ni labarin rayuwar ki domin na gasgata wasiyyar abbana.
Ko da jin Wannan batu daga bakin mahayin sai Nashmira ta bushe da dariya daga bisani ta ƙura mashi idanu tana yi mashi wani kallo mai ɗauke da alamar tambaya, sannan tayi gyaran murya tace "yakai wannan jarumi kayi Sani cewa ni ma kai ne jarumi na farko a rayuwata da ya taɓa samun nasara a kai na, amma ina mai baka shawara da ka janye niyyar ka na jin labarin rayuwata, domin babu abinda zai jefa ka face wasu musibun.
Koda Jin wannan batu sai mahayin ya cika da matuƙar mamaki ya ce "ya Ma'abociyar kyawu shin mene ne ke tattare da labarinna ki?.
Da jin wannan tambaya sai murmushi ya suɓucewa Nashmira ta ce "yakai wannan jarumi ka yi sani cewa a rayuwata babu abinda na tsana fiye da 'ya'ya maza, burina shine na mallaki waɗansu abubuwa da zasu kai ni ga waccan matsayi na mayar da dukkan MAZAJEN DUNIYA bayin Mata, ina so Yazamo cewa 'ya'ya mata ne ke riƙe da Sarautar ƙasashen duniya.
Da jin amsar wannan tambaya sai Mahayin ya cika da matuƙar mamaki maral-misaltuwa, ya yi shiru ya na mai Sunkuyar da kanshi ƙasa yana zurfafa cikin Kogin tunani.
Daga can sai ya ɗago da kanshi ya dube ta cikin tattausar murmushi ya ce “ Ya ke sarauniyar kyawawa a sani na tun wanzuwar Duniyar maza ke riƙe da Sarautar duniya.
Shin ta ya za a ce maza su zama bayin Mata, Amma masu iya magana na cewa ba a ƙwacewa yaro garma Kuma tabbas duk Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan daka.
Da farko dai suna na Hufairu Ibn shaddad mahaifina mashahurin Matsafin ne kuma maƙeri da ya yi shura a nahiyar mu.
Kasancewar ni da mahaifina muna rayuwa ne a daji babu abin da ke rabu mu ko da kwanciyar barci haka ne ya sanya mu ka shaƙu ainun da juna.
Tun ina da shekara sha biyar a duniya na ke shiga daji na farauto muguwar dabba, Akwai wata rana da ‘yan fashi tsautsayi ya kawo dajin mu, Ni kaɗai na afka ma su da yaƙi na hallaka su baki ɗaya.
Cikin Matuƙar farin ciki mahaifina ya rugo Izuwa inda nake ya rungume ni a ƙirjinshi.
Yana mai cewa haƙiƙa ɗana ka gajeni a sadaukantaka ɗari-bisa-dari sai dai ina so ka zamo mai cika babban burina.
Cikin matuƙar mamaki na dubi Abbana na ce “Ya Abbana shin yanzu akwai wani burinka da ya huce na gaje ka a jarumtaka?
Mahaifina ya yi Murmushi mai taushi ya dafa kafaɗuna bayan ya janye jikin shi daga nawa sai ya dube ni a karo na biyu ya ce “Ya farin Cikin Zuciyata kayi Sani cewa babban burin da na ke so ka cika mini a duniya shine ka mallaki wata Sihirtacciyar Ɗamara.
Shekaru ɗari da suka gabata na taɓa ƙera wata ɗamara a lokacin ina bauta a ƙarƙashin wani mashahurin sarki mai suna Hafzul-Masnur.
Hafzul-Masnur yakasance mashahurin Matsafin attajiri kuma Gwarzon mayaƙi a filin fama.
Bisa wannan dalili ne ya sanya ya yi fice Kuma ya zamo gagarabadau a nahiyar.
Wata rana Hafzul-Masnur yana gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi sai ya gano cewa na sa’anta wata ɗamara wacce ni kai na bansan amfanin ta ba,
Ya gano cewa ɗamarar tana ɗauke da waɗansu muhimman sirrikan tsafi guda miliyan biyu, Domin na ƙera ɗamarar ne da karfen zoben tsafin sarkin bokaye Aljanu.
Babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai mallaki Ɗamarar face yazamo ANNOBA ƊARI ga Duniya kuma SARKIN SADAUKAI.
Bisa wannan dalili ne yasanya sarki Hafzul-Masnur ya buƙaci na ba shi ɗamarar ni kuma na ƙi ba shi goyon baya.
Saboda hakan ya yi ta gana mani azaba iri daban daban.
Da na fahimci cewa idan ban bashi ɗamarar ba zan iya rasa rayuwata sai kawai na yanke shawarar na na shi.
Bayan na mallaka ma shi ne wani hatsabibin boka ya sace ɗamarar domin ya mallaki sirrina tsafin da ke jikin ta.
Amma Sai ajali ya riske shi bai cika wancan burina shi ba.
Ya ɗana kayi sani cewa ba zaka iya cika mani wannan burina wa ba face na ka haɗa kai da wata hatsabibiyar jaruma da binciken halarar tsafi ya tabbatar da cewa ba zai yiwu na iya ganin siffofin Jarumar ba.
Kawai dai alama ta farko da za ka gane Jarumar shi ne idan ka fafata yaƙi da ita za ta yi nasara a kan ka, Alama ta ƙarshe ita ce tana da wani ƙazamin ƙudiri na ta na mayar da dukkan MAZAJEN DUNIYA bayin mata.
Wannan shi ne taƙaitaccen tarihin rayuwata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login