Showing 27001 words to 30000 words out of 59965 words
Chapter 10 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt
MAZAJEN DUNIYA Bayin Mata.
Lokacin Da Nashmira Ta Ga Ta Cika Kyakkyawar Budurwa kuma Basadaukiya Sai Ta Ziyarci Wani Boka A Birnin Kisra Mai Suna Shahamar Ibn Ubaidah.
Lokacin Da Nashmira Ta Kaɗaita Da Boka Shahamar Sai Ta Buɗi Baki Da Nufin Ta Bayyana Mashi Abin Da Je Tafe Da Ita.
Kafin Ta kaiGa Hakan Boka Shahamar Ya Dakatar Da Ita Ta Hanyar Ɗaga Mata Hannu Yana Mai Nuna Tayi Shiru, Sannan Ya Sanya Hannunshi Na Hagu Ya Shafi Dogon Gemunshi Fari Sol, Kana Ya Bude ta Da Jajayen Idanuwanshi Masu kama Da Garwashi, Ya Buɗi Baki Cikin Kakkausar Murya Mai Kama Da Haniniyar Doki Yace "Yake JARUMAR JARUMAI Shin Mene ne Dalilin Da Ya Sanya Zaki Wahalar Da Kanki Wajen Sanar Dani Buƙatar Dake Tafe Dake, Ki Sani Cewa Fiye Da Shekaru Arba'in Nasan Da Zuwan ki Nan, Abin Da Ke Tafe Dake Ɗin Shi ne Ki Na So Ki Maishar Da Dukkan Mazajen Duniya Bayin Mata Ko Ba haka Bane?.
Cike Da Matuƙar Mamaki Nashmira Ta Ce "Tabbas Zancen ka Dutse Ya Madubin Bokaye".
Shahamar Yayi Gyaran Murya Karo Na Biyu Yace "Yake Nashmira kiyi Sani Cewa wannan Buƙata Taki Dai-dai Take Siyen Ajalinki Da Kuɗinki, Haƙiƙa Kin Ɗebo Ruwan Dafa Kanki, I na Mai Baki Shawara Da ki Janye Wannan Ƙudiri Baki, Domin Ta Yaya Maza Zasu Zamo Bayin Mata, Shekarun Da Su ka Gabata An Samu Mata Masu Irin Wannan Mummunar Aƙida Taki Amma Basa Kai Ga Cika Burin Su Ajali Ke Riskar Su.
Tun wanzuwar Duniyar Nan fa Maza Ne Ke Mulkin Duniya, Kuma Haka Ne Zai Cigaba Da Tabbata Ƙarni Bayan Ƙarni.
Ko da Jin Wannan Batu Sai Nashmira Ta Fusata Ainun Ta Dakawa Shahamar Tsawa Cikin Matuƙar Fushi Tace" Zancen Banza Ke Nan Ya kai Shahamar Kayi Sani Cewa Ban Kowa Maka Ziyara Domin Ka Bani Shawara ba, Abin da Nake Buƙata Kawai Shi ne Ka Bayyana Mini Hanyar Da Zan Cimma Burina, Idan Kuwa Kayi Wani Ganganci To Kai ne Namiji Na Farko Da Zan Fara Hallakawa.
Da Jin Wannan Batu Sai Dariya Ta Suɓucewa Boka Shahamar Mai Kama Da Haniniyar Doki Wacce Ta Ƙarawa Fuskarshi Muni Ya Dubi Nashmira Yace "Haƙiƙa Yaro Man kaza Ne Bai San Wuta ba Sai Ta Narka shi, kuma Duk Tsuntsun Da Yaja Ruwa Shi Ruwa Ke Doka.
Kuma Masu Iya Magana Dai Na Cewa Ba'a Ƙwacewa Yaro Garma.
"Yake Nashmira kiyi Sani Matukar Kina So ki Maishar Da Dukkan Mazajen Duniya Bayin Mata, Wajibi Ne Ki Nemo Waɗansu Abubuwa Da Mallakar Su Dai-dai Ya ke Da Buɗe Taskar ANNOBA ƊARI.
Da Farko Wajibi Be ki Nemo Waɗansu ZARATAN JARUMAI Mata Waɗanda Shekarunku Da Kamanninku Suka Zo Ɗaya Sak Tamakar An Tsaga Kara.
Ta Farko Ita Ce Jaruma Siyasar Bintu Sha'aban, Sai Shuraiba 'Yar Ƙaura Hubbaru Na Birnin Sin.
Abu Na Biyu Shi Ne Wani Mashi Da Garkuwa Dake Ajiye A Cikin KOGON TSAFI kafin Mutum Ya Isa Inda Kogon Yake Sai Ya Ƙetare Waɗansu Miyagun Dazuzzuka Guda Sha Biyu A Yanzu Da Nan Gaba Babu Wani Mahaluƙi Da Ya Isa Ya Gano Adadin Musibun Dake Tattare Da Dazuzzukan.
Abu Na Uku Shi Wani Sihirtaccen ƙwai Dake Ajiye A Cikin Tekun Bahar Maliya Wanda Shugaban Tsuntsayen Ta Tsare Shi Ta Ciro Shi Daga Cikin ta Kafin Ya ƘyanƘyashe Kanshi,Fiye Da Shekaru Dubu Shugabar Kifayen Na Matuƙar Buƙatar Haihuwa.
Na Huɗu Shi Ne Waɗansu Kayan Yaƙi Riga Da Wando Dake Ajiye A Fadar Uwar Mayu.
Abu Na Ƙarshe Shi Ne ƊAMARAR SIHIRI Ta Sarkin Matsafan Aljanun Duniya Matsafi Kashmil.
Waɗancan Jarumai Biyu Mata Zasu Taimaka Miki Ne Wajen Cimma Burinki Kuma Su Taimaka Miki Waɗancan Abubuwan, Sihirtaccen Mashi Da Garkuwa Kuwa Sune Makaman Da Babu Kamar Su A Duniya Kuma Suna Dauke Da Muhimman Sirrika Kamar Haka.
Sirri Na Farko Shi Ne Matukar Kana Tare Dasu Babu Wani Abu Da Zaka Sa A Gaba Face Ka Cimma Nasara, Dole Kowa ce Halitta Tayi Biyayya A Gareka, Komai Tsananin Rundunar Abokan Gaba Idan Ya Tunkare Su Zai Iya Hallaka Su Domin A Cikin Abin da Bai Huce Daƙiƙa Goma Yana Kashe Mutum Dubu, Sirri Na Ƙarshe Shi Ne Daga Inda Mutum Yake Yana Iya Tura Makaman Su Hallaka Mashi wanda Yale So Batare Da Shan Wata wahala ba.
Kwai Na Sihirin Kuwa Za'a Yi Amfani Da Shi Ne A lokacin Da Za'a Shiga Kogon Tsafi, Ɗamarar Sihiri Kuwa Da Makaman Yaƙi Da Zarar Kin Sanya A Jikin ki Za ki Mallaki Rabin Sirrikan Tsafin Duniya Dake Jikin Ɗamarar Da Kayan Yaƙin, A Sanne Zaki Zamo Babu Wata Halitta Da Ta Kai ki Karfin Damtse Walau Mutum ko Aljan.
Waɗannan Sune Abubuwan Da Zaki Mallako Domin Cika Burinki Bautar Da Mazajen Duniya.
Sa'adda Jaruma Nashmira Taji Dukkan wadannan Jawabi Daga Bakin Boka Shahamar Sai Hankalinta Ya Ɗugunzuma Ainun Taji Tamkar Ta Janye Ƙudirinta Na Mayar Da Dukkanin MAZAJEN DUNIYA Bayin Mata, Amma Koda Ta Tuna Halin Da Mahaifiyarta Ta Rasu Akai Sai Kawai Ta Zurfafa Cikin Kogin Tunani Daga Can Sai Ta Dubi Boka Shahamar Ciki Tattausar Murya Tace "Ya Dodon Bokaye Ka Sanar Dani Sunayen Jaruman Da zasu Kasance Abokan Tafiyata Amma Baka Sanar Dani In da Zan Same Su ba.
Ko da Jin Wannan Tambaya Sai Shahamar Ya Buɗi Baki Cikin Kakkausar Murya Yace" Ai Jaruma Siyamat Na Zaune A wani Ɗan Karamin Gari Da Ake Kira Da Latul-Habrus Dake Arewacin Birnin Hindu.
Jaruma Shuraiba Kuwa Na Birnin Sin Kamar Yadda Na Sanar Dake, Da Wannan Nake Ya Maki Fatan Samun Nasara.
Ko da Gama Faɗin Hakan Sai Ya Shafi Wani Gurun Tsafi A Damtsenshi Take Ya Ɓace Ɓat Tamkar Bai Taɓa Wanzuwa Ba.
Kawai Sai Nashmira Ta Miƙe Tsaye Tsam Daga Kan Kujerar Da Take Zaune, Ta Fice Daga Ɗakin Bakwai Tsafin Tana Fita Ta Kama Dokinta Ta Haye Ta Sakar Mashi Linzami Ta Fara Falfala Azababban Gudu.
Sai Da Ta Shafe Tsawon Zango Ɗaya Tana Tafiya, Tana Cikin Wannan Hali ne Kwatsam Sai Taga Wani Mahayi Yayi Fitar Burgu Daga Cikin Duhuwar Bishiyoyin Dake Dajin.
Shi Zai Mahayin Yakasance Zabgegen Saurayi Kyakkyawa Na Gaban Kwatance Dogon Gashin kanshi Ya Zuba Akan kafaɗunshi, Yana Sanye Da Kayan Fata Riga Da Wando Da Akayi Su Da Fatar Damisa, A Gadon Bayanshi Yana Rataye Da Wani Rantsatstsen KWARI DA BAKA, Kuma Yana Zaune Bisa ingarman Doki Fari Sol, Kallo Ɗaya Zaka Yiwa Jarumin Ka Fahimci Cewa Ya Cika GWARZON MAYAKI Saboda Yadda Ya Tara Ƙwanji.
Babu Wata 'ya Mace Mai Hankali Da Zata Yi Arba Da Wannan Kyakkyawan Saurayi Face ta Kamu da matuƙar ƙaunar shi.
Sa'adda Jaruma Nashmira Tayi arba da mahayin sai ta ji linzamin dokin ta ta tsaya cak!, Aka fara Kallon-Kallo tsakaninsu na wani Lokaci.
Daga bisani Nashmira Ta Katse Shirun Da Ya Wanzu Ta Hanyar Dakawa Mahayin Tsawa Cikin Matuƙar Fushi Tace Da Shi "Shin Wane Ne Kai Da Zaka Tsare Mini Hanya, Hanzarta Amsa Mini Wannan Tambaya Kafin Na Yanke Maka Hukunci Bisa Laifin Da ka Aikata Mini.
Ko da Jin Wannan Batu Daga Bakin Nashmira Sai Mahayin Ya Bushe Da Dariyar Mugunta, Lokaci Guda Ya Turɓune Fuska Tamkar An Aiko Mashi Da Wasiƙar MUTUWA Ya Dube ta Cikin Gadara Ya Buɗi Baki Yace "Ai ke Ce Yafi Cancanta Ki Bani Amsar Wannan Tambayoyi Da Kika Yi Mini.
Da Jin wannan Batu Sai Nashmira Ta Fusata Ainun Ta Sake Dakawa Mahayin Tsawa A Karo Na Biyu Tace Yakai Wannan Jarumi Ma'abocin GAJEREN KWANA, Haƙiƙa Ka Taɓo Tsiliyar Dodo, Kuma Ka Jefa Kanka Cikin Taskar ANNOBA ƊARI Mai Wuyar Fita, Sai Ka Shirya Ga Maza Nan Bisa Kanka.
Tana Gama Faɗin Hakan Sai Ta Zaburi Dokinta Tayi Ɗauki Kanshi Gami Da Dunkule Hannayenta Tare Da Kai Mashi Naushi Domin Hanɓaroshi Daga Kan Dokin Shi.
Cikin Ɓakin Zafin Nama Mahayin Ya Sunkuyar Da Kanshi Ƙasa Hannun Nashmira Ya Naushi Iska.
Nan Take Suka Ruguntsume Da Azababban Yaƙi Mai Matuƙar Kwarjini, Muni, Daban Al'ajabi, Suka Wanzu Suna Kaiwa Juna Sara Da Suka Cikin Matuƙar Zafin Nama JURIYA DA BAJINTA Ta Gaban Kwatance.
Wohoho! Haƙiƙa Artabun Gwanaye Daban Yake Dana Ƙananan Ƙari, Idan Basadaukiya Ta Haɗu Da GWARZON MAYAKI Dole Gumurzu Ya Zamo Tashin Hankali, Kuka kuma Ranar Bikin Gwanaye Sai Wance Da Wance Ne kaɗai Ke Fitowa Su Taka Rawa.
Babu Abinda Zai Burge Mutum Kuma Ya Bashi Sha'awa Fiye Da Yadda Jaruman Ke Yaƙar Juna Ta Hanyar Bugu Da Naushi Tamkar Jikkunansu Basu Kasance Na Jini Da Tsoka ba.
Sai Da Suka Shafe Tsawon Rabin Sa'a Suna Wannan Ɗauki Badaɗi, Hatta Dawakansu Kaiwa Juna Hari Da Ƙafa Suke Yi Suna Turmutsutsu Kofatunsu Na Kartar Ƙasa Suna Tayar Da Ƙura.
Sa'adda Jaruma Biyu Suka Ga Sun Shafe Tsawon lokaci Batare Da Ɗayansu Ya Samu Nasarar Koda Lakutar Jikin Abokin Gwaminshi ba Sai Suka Fusata Ainun Suka Faɗa Izuwa Kogin Tunani.
Abu Na Farko Daya Faɗowa Nashmira A Rai Shi ne Ta Yaya Za'a Ce Wani Jarumi Ya Gagareta Duk Da Kasancewarta Jaruma Mafi Karfin Damtse Akaf Nahiyar Anya Kuwa Wannan Saurayi Bil'adama Ne.
Aɓangaren Mahayin Kuwa Abun da Ya Faɗo Mashi A Rai Shi Ne Taya Za'a Ce Ya Kasa Samun Nasara Akan 'Ya Mace, Shin Ko Bokanshi Ya Yaudare Shi Ne Daya Faɗa Mashi Cewa Shine Jarumi Mafi Karfin Damtse A Nahiyarsu.
Ko da Jaruman Biyu Su kazo Nan A Tunanin Su Sai Suka Ja Da Baya Suka Canza Tsayuwa, A Lokaci Guda Tamkar Haɗin Baki Suka Zaburi Dawakansu Suka Sake Afkawa Juna Suna Masu Canza Salon Faɗansu.
Wohoho! Haƙiƙa Masu Iya Magana Sun Yi Gaskiya Da Suka Ce Idan Kiɗa Ya Canza Dole Ne Rawa Ta Canza, Faruwar Hakan Keda Wuya Sai Jaruman Suka Fara Galabaitar Da Juna, Suna Haɗawa Juna Jini Da Majina Suna Layi Jiri Na Ɗibar Su Tamkar Sun Sha Barasa Sun Bugu.
Ana Cikin Wannan Artabu ne Mahayin Ya Shammaci Nashmira Ya Kirɓa Mata Naushi A Fuska, Saboda Ƙarfin Naushin Sai Da Tayi Sama Tamkar An Janye Ta Da Ƙungiya, Sannan Ta Faɗo Ƙasa Tim! A Matuƙar Galabaice.
*****
Sa'adda Sarki Himras Yazo Dai-dai Nan A Labarin Da Yake Bawa Yarima Muzaifar Sai Ya Juya Ya Dubi Yarima Dake Gefanshi Aikuwa Sai Yaga Fuskarshi Cike Da Alamun Damuwa.
Yarima Ya Buɗi Baki Cikin Damuwa Yace "Ya Abbana Shin Ina Dalilin Tsayar Da Wannan Labari, Haƙiƙa ina So Naji Shin Wane ne Wannan Mahayi, Nashmira Na kuɓuta Daga Hannun Sa Har Ta Tafi FARAUTAR 'Yan Mata Biyu, Tana Burinta Na Mayar Da Dukkanin MAZAJEN DUNIYA Bayin Mata?.
Ko da Jin Wannan Tambayoyi Daga Bakin Yarima Muzaifar Sai Sarki Himras Ya Dube Shi Cikin Murmushi Mai Taushi Yace " Ya Farin Cikina Duba Can Ka Gani Ai Mun iso Izuwa Birnin Rum, Ina Mai Tabbatar Maka Dacewa Bayan Mun Samu Nasarar Ɗauko Sarƙar Tsafi Zan Cigaba Da Baka Wannan Hikaya, Idan Hakan Bai Samu Ba Kuwa Sai Dai Ka Nemi Littafin MAZAJEN DUNIYA Wanda Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaƙi Ya Wallafa Domin Cigaban Hikayar Nashmira.
Da Jin Amsar Wannan Tambayoyi Sai Yarima Muzaifar Ya Sunkuyar Da Kanshi Ƙasa Aikuwa Sai Yayi Arba Da Dogayen Gine-Ginen Birnin Rum.
Sarki Himras Ya Dubi Aljani Narguz Yace "Yakai Narguz Sai Ka Sauke Mu A Turba Domin Mun Iso Birnin Rum.
Kafin Hirmas Ya Gama Rufe Bakinshi Narguz Ya Saki Fuka-fukanshi Yayi Ƙasa Luuu! Ya Sauka A Turba, Aikuwa Koda Sakarsu Sai Suka Yi Turus !, Bawani Abu Suka Ga Ya Basu Mamaki ba Face Wata Ƙasaitacciyar Runduna Cikin Shirin Kota Kwana, Zaune A bisa Dawakai, Wasu A Giwaye Wasu A Raƙuma Wasu A Ƙafa, Makaman Yaƙinsu Kuwa Gasu Nan Birjik Marasa Adadi, A Gefe Guda Sarki Baddadul-Arus Ne Tare Gimbiya Uzaima,Sarki Huraisu Tare Da Hadimi Shaibat Zaune A Bisa Kan Aljani Zamzaru Shirye Cikin Gagarumar Shigar Yaƙi Ta GWARAZAN JIYA.
Sa'adda Su Sarki Baddadul-arus Suka yi Arba Dasu Sarki Himras Sai Suka juya Daga Fuskantar wannan Runduna Aka Shiga Yin Kallon-Kallo Tsakaninsu Cikin Ƙiyayya Gami Da Mugun Tanadi.
Sai Da Aka Shafe Tsawon Daƙiƙa Talatin A Cikin wannan Hali, Sannan Kowane Ɓangare Suka Tawo Domin Tarar Juna Batare Da Sun Sauka Daga Kan Abin Hawan Su ba, Lokacin Da Yage Saura kamar Taku Goma A Tsakani Sai Kowannen su Yaja Ya Tsaya, Aka Sake Yin Sabon Kallon-Kallo Na Ɗan lokaci.
Sarki Baddadul-Arus Ya Ƙatse Shirun Daya Wanzu Ta Hanyar Budar Baki Cikin Kakkausar Murya Fuskarshi A Murtuke Yace "Yaku Abokan Gaba Na Har Abada Ku Sani Cewa A yaune Za'a Tantance Tsakanin Aya Da Tsakuwa, Naso Ace Na Isa Inda Sarƙar Tsafi Na Mallaketa Sannan Na Kawar Daku Baki Ɗaya.
Caraf Sarki Himras Ya Tafi Numfashin shi yace " Kai Tsohon Maƙiyi Na Har Abada Kayi Sani Cewa Yaushe Ranar ka Ta Ƙarshe Kai Da 'Yarka Uzaima Domin Nazo Da Gagarumin Shirin Da Bantaɓa Yin Kamarshi ba.
Baddadul-arus Ya Bushe Da Dariyar Mugunta Sannan Yace "Ai Yaƙi Tsakanin Mu Ɓata Lokacine, Domin Dai Dole Ne Sai Dayanmu Ya Kawar Da Rundunar Dake Gabanmu Sanna Zai Samu Nasarar Kutsawa Cikin Birnin Rum, Yanzu Dai Shawara Ta Rage Ga Mai Shiga Rijiya, Duk Wanda Ya kawar Da Rundunar Shine Ke Da Nasara.
Ko da Gama Faɗin Hakan Sai Sarki Baddadul-arus Ya Zare Wata Rantsattsiyar Takobi A Damtsenshi Mai Matukar Faɗi Tsawo Gami Da kaifin Tsiya, ko da Ganin Hakan Sai Gimbiya Uzaima, Sarki Huraisu Da Hadimi Shaibat Suka yi Koyi Dashi Suna Masu Zare Nasu Makaman, Take Aljanu Zamzaru Ya Yunƙura Izuwa kan Abokan Gaba Yana ihu Da Kururuwa Mai Firgitarwa.
Ko da Ganin Hakan
Sai Sarki Himras, Yarima Muzaifar, Jaruma Sharilat, Tsoho kuhairu Suka Zare Makamansu, Cikin Matuƙar Zafin Nama Aljani Narguz Ya Yunƙura Izuwa kan