Showing 6001 words to 9000 words out of 59965 words

Chapter 3 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt

09 Dec 2024

9379

ya kuma kai mata saran a kafaɗa.
Shirilat ta wurkila ta zamewa Saran addarshi ta nutse cikin ƙasa.
Kafin ya zare ta cikin ƙarƙashin ƙasa tuni Sharilat ta shammace shi ta soka masa mashi a kirji.
Nan take jini ya fantsama a kirjin ya kwalla ƙara cikin karfin hali da juriya ya shammaci Sharilat ya dunƙule hannayenshi biyu ya gabza mata naushi a maƙogaronta Nan take su duka biyun suka zube ƙasa magashiyan.


****


Kamar yadda Sarki Baddadul-Arus Arus ya faɗawa 'yarshi Uzaima haka al'amarin ya kasance.
sai da mako guda ya shuɗe da yin maganarsu Baddadul-Arus.
Sannan suka fara shirye-shirye shiryen tafiya birnin Jarul iman.
Shi dai birni na Jarul- iman ya kasance mai tattare da albarkatun ƙasa.
Sarkin dake mulkin jarul Iman ɗin ana yi masa lakabi da Huraisul-Zaman.
Sarki Huraisu yakasance kyakkyawa nagaban kwatance mai shekaru ashirin da huɗu, yana da karfi na Allah ya isa.
A rayuwar Sarki Huraisu baya tsafi kuma baya tasiri a kan shi, Babu wani al'amari da zai sanya gaba gaba face ya cimma nasara akan shi.
Allah (S.W T) ya azurtashi da wata baiwa guda daya. Baiwar kuwa ita ce hikima, komai hikımar mutum da fasahar shi idan ya zo gaban Huraisu sai ya zamo daƙiƙi tamkar bai taɓa sanin komai ba.
Baiwa ta biyu kuwa ita ce, Babu wa musiba ko annoba da zata afku face ya gano hanyar da za'a magance ta komai daɗewarta.
Bakoyen duniya na wannan zamani sun labarta cewa, Asalin Sarki Huraisu ya kasance jinin jarumi Usmairu wanda shi ne ya taɓa shiga taskar boka Shuyudan wato Taskar ANNOBA DARI, kuma ya fito a raye.
Sarki Huraisu bai yarda ya bautawa wani ubangiji ba face kawai yana dogaro ne da baiwar da yake da ita, saboda haka ne kowane mutum a birninshu yake bautawa abinda yake so.
'ya'yan Sarakuna daga biranan duniya, suna aiko da wasikar soyayyar su zuwa ga sarki Huraisu akan ya amince ya aure su amma sai ya ƙi amincewa da yawa daga cikin su sun mutu, sanadin kamuwa da soyayyar shi.
Bakomai ya sanya Huraisu baya amincewa da soyayyar su ba, Burinshi shi ne ba zai auri kowa ce ya mace ba face ya samu macen da ta ɗara shi a yawan baiwa kuma wadda tai mu'amala da shi har sa'a ɗaya amma bata kamu da son shi ba duk irin kyawun surar shi.
Gaba ɗaya jama'ar birin Jarul Iman suna mutuƙar kaunar Haraisu kamar ɗan cikinsu, saboda yadda yake tafiyar da mulkinshi babu kama karya.
Wannan shi ne taƙaitaccen labarin Sarki Huraisu na birnin Jarul Iman.
Tun da duku-dukun safiya mayaƙa suka yi sahu-sahu a kofar gidan sarautar Sarki Baddadul-Arus, wasu suna zaune a bisa dawakai, rakuma wasu a ƙafa, makaman yaƙinsu kuwa gasu nan birjik bila adadin.
Jim kaɗan sai ga sarki Baddadul Arus da 'yarshi Uzaima, sun fito daga gidan sarauta cikin gagarumar shigar yaki mai mutukar kwarjini, shigar baƙaƙen tufafi su ka yi hatta takalman ƙafarsu bakake ne.
jikinsu kuwa suna sanye da makaman yaƙi sama da kala arba'in, kuma suna zauna ne akan bakaken dawakai ingarmu.
Ko da fitowar Sarki Baddadul Arus da Uzaima sai miliyoyin Mayaƙan su ka risina da kawunansu domin girmamawa a gareshi.
Kai tsaye Badaddul-Arus da Uzaima suka durfafi kofar suna fira cikin nishaɗi da annashiwa.
A sannane miliyoyin mayaƙan su ka ɗago da kawunansu suka zaburi dawakansu da gudu suka mara musu baya.
Da isarsu bakin kofa waɗansu Girɗa- Girdan dakaru masu kirar samudawa suka yi hanzarin wangame kofa suna masu sunkuyar da kansu kas, Domin girmamawa a garesu. Sai da Badaddul Arus da Uzaima suka yi nisa da su sannan suka dago kawunansu suna masu karewa sauran mayaƙan kallon,Da fitarsu sai suka shiga cikin daji aka ci gaba da gudu babu sassauci ana cikin wannan tafiya Uzaima ta dubi Mahaifinta ta ce "Ya Abbana ina da wata tambaya?"
Ko da jin hakan hakan sai Badddaul-Arus ya ce, "Fari tambayarki ya 'ya ta."
Uzaima ta yi ajiyar zuciya gami "da gyaran murya ta ce," Ya Abbana wai shin me ya sanya wannan karon mu ka taho da mayaƙa, alhalin idan Za'a kai YAKIN BAZATO ni da kai kaɗai muke zuwa.? "
Ko da jin wannan batu sai Baddadul Arus ya bushe da dariya mai ka ma da kukan Jaki ya ce.
"Da sannu za ki ga amfanin wadannan mayaƙa ina mai tabbatar miki da cewa wannan yaƙi da za mu yi bamu taɓa yin kamar shi ba lallai za ki sha kallo.
Ko da gama fadin hakan sai Uzaima ta yi murmushi wanda ya tona asirin kyawun ta, Daga bisani da gaba da tafiya batare da dayansu ya ce uffan ba.
wanan shi ne abinda ya faru ga Sarki Baddadul-Arus da 'yar shi Uzaima a lokacin da zasu kai farmaki birnin Jarul-Iman.


*****


Lokacin da Sarki Himras ya rabu da Yarima Muzaifar akan gobe zai shiga cikin halarar tsafin shi domin ya gano sunan ɓakuwar jaruma da na mahaifinta.
Ko da Sarki Himras ya kaɗaita a cikin turakarshi sai barcı ya gagareshi kuma zuciyarshu ta kama tafarfasa tamkar zata faso kirjinshi ta fito waje.
Ba komai ne ya hana Sarki Himras ya kasa rintsawa ba fa ce Jarumar da ta fafata yaƙi da Yarima 'ya ce ga ɗan uwanshi sarki Kuhairu.
Abu na farko daya faɗo mashi a rai shi ne yaya aka yi aka samu wani mahaluki daya iya horon yaƙi irin nashi ya san cewa shi da ɗan uwanshi Kuhairu ne kaɗai suke da irin shi, ya aka yi Kuhairi ya rayu shi da matar bayan cewa ya yi kisan da ba za su ƙara ba dai-dai da daƙiƙa ɗaya a duniya ba.
Ya yinda Sarki Himras ya zo nan a tunanin shi sai ya cika da baƙın ciki maral- musultuwa har ta kai kwallar takaici ta zubo ma shi. Babban abinda ya hana Sarki Himras gudanar da binciken akan wannan al'amarı shi ne.
Matsawar ya tabbata cewar jaruma sharilat 'ya ce ga Ɗan uwanshi Kuhairu a aka yi rashinsa'a to nan take Zai yi Dukkan sirrikan tsafinshi zasu lalace, bisa ƙa'idar tsafin baya tasiri akan junansu.
Sa'adda Sarki Himras ya zo nan a tunanin shi sai ya taƙarƙare ya kwarara uban ihu wanda ya haddasa girgizar gidan sarautar baki daya. Al'amarin daya firgita gaba ɗaya dakarun gidan ke na, suka ɗebo makamansu suka rugu izuwa ɓangaren Sarki domin rabon su da Sarki Himras ya yi wannan kururuwa yau shekara biyu tun ranar mutuwar matarshi.
Su kansu kuyangun da bayin gidan da yawansu sai da suka farka daga barcinsu saboda jin wannan ihu, Domin su san duk sa'adda suka ji wannan ihu.
Wannan shi ne abinda ya faru ga Sarki Himras bayan ya rabu da Yarıma Muzaifar ya kaɗaita a cikin turakarshi.




*****
Cikin tsananin JURIYA DA BAJINTA a lokaci guda su duka biyun suka miƙe tsaye zumbur suka ci gaba da kaiwai junansu hare-hare da zummar halaka juna a duk lokacin da makamansu suka haɗu da juna sai ka ga sun haddasa tartsatsin wuta gami da ƙara marar daɗin sauraro.
Al'amarin daya ƙara fusata jaruman biyu ke nan suka zage damtse suna kawai junan hare hare-hare na ban al'ajabi.
A ɓangaren tsoho Kuhairu kuwa ya zamo kamar shaidɗani a tsakiyar dakarun ya wanzu yana kare harin da suke kawo mashi na sara da suka.
ya wanzu yana tsire su da mako su ƙasa suna zubewa kasa matattu.
A wasu lokutan ma sai ka ga dakaru sama da shirin sun yanyayame shi suna neman su kaishi ƙas, Amma sai ka ga ya tarwatsa su ko ka ga ya yi katantanwa a Ƙasan su ya doki kafafuwan su da dawakansu sun zube kasa.
Kaicol Tabbas idan TSANANIN DA UKUBA a yaƙi suka tsananta, Hanyoyin tsira su toshe, sai ga ZARATAN MAYAKA suna neman su cika wandonsu da iska domin su TSIRA DA RAYUKANSU.
Hakanne ya faru ga yaran Huzlan, Domin koda suka ga irin kisan gillar da Kuhairu ke yi masu sai da yawa daga cikin su suka yunkura zasu gudu, Amma kafin su kai ga hakan tsoho Kuhairu ya afka musu ya hana su sakat!.
Ana cikin wannan yaƙi ne Huzlan ya shammaci Sharilat ya sareta a cinya ya yi mata wani lafcecen rauni jini ya yi tsartuwa duk irin tsananin jarumtakar Sharilat sai da ta kwalla ƙara bisa tsananin zafi da zugi da ta ji.
Cikin gwaninta da juriya Sharilat ta shammaci sadauki Huzlan ta soka ma shi mashi a cinya, nan take inda ta suken shi ya haddasa wani katon rauni, tamkar an saka ɗan buda a wuta sannan aka cakamashi a cinyar, Huzlan ya taƙarƙare ya kwarara uban ihu saboda yadda yaji raɗaɗi .
Kafın cıkar rabin sa'a sun yiwa junansu raunuka fiye da sha biyar.
Al'amarin da ya sanya su duka biyun suka galabaita ainun, saboda yadda jini ke zuba ajikinsu, Amma a hakan suka ci gaba da yaƙin.
Gaskiyar masu masu iya magana da suke ce kyan faɗa a kwana ana yi kuma tabbas idan ka ji ana ga ƙi gudu, To sa gudu ne bai zo ba".
Sai da aka shafe tsawon sa'a daya ana wannan gurmurzu babu sassauci, a dai- dai wannan lokaci ne fa duhun dare ya fara kawo kai, koda fahimtar hakan sai Sadauki Hazlan ya shammaci Sharilat ya kirɓa ma ta naushi a fuska.
Saboda ƙarfi naushin sai da sharilat ta yi sama tamkar an janye ta da ƙugiya sannan ta bugu da wata bishiya kanta ya tsage jini ya yi tsartuwa baje a ƙasa magashiyan numfashinta na fita sama sama Koda samun wannan nasara sai Huzlan ya bushe da dariyar farin ciki kawai sai yaje inda Sharilat take ya raba kafafunshi akanta.
sannan ya ɗora kaifin Addarshi akan wuyan sharilat yana mai yi ma ta murmushi mugunta.
Kwatsam! ba zato babu tsammani sai aka ga jaruma Sharilat ta gabzawa Sadauki Huzlan wawan naushi a maƙogaronshi, saboda ƙarfin naushin sai da Huzlan ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya sannan ya faɗo ƙasa a matuƙar galabaice Numfashinshi na fita sama-sama.
Kafin ya yi wani yunƙuri Sharilat ta miƙe tsaye zumbur! suri mashinta ta caka ma shi a kirjinshi, take ya fasa kijinshi ya billo ta gadon bayansa, jini ya dunga kwaranya ya na tsartuwa sama.
Kaino! Tabbas gaskyar masu iya Magana da suka ce idan TSANANIN DA UKUBA a yaƙi suka tsananta wuya ta yi wuya sai ka ga ZARATAN MAYAKA suna neman cika wandonsu da iska domin su TSIRA DA RAYUKAnsu Hakanne ya fatu ga sauran mutanen Huzlan domin koda suka yi arba da gawar Huzlan kwance sai suka yunƙura da nufin tserewa, Amma sai tsoho Kuhairu ya dunga ƙure musu gudu yana makosu daga kan dawakansu suna yin MUGUWAR HALLAKA.
Kafin cikae daƙiƙa ashirin Kuhairu ya hallaka mayaƙan ɗayansu bai tsira da rayuwarsa ba, cikin mutukar farin ciki mara misaltuwa Sharilat ta ruga da gudu ta je ta rungume mahaifinta, Tsawon lokaci a rungume da juna, sannan daga baya Sharilat ta janye jikinta daga na abbanta su ka sake juyawa su ka shigo cikin wannan gida, suka bar gawar Huzlan da jama'arshi kwance cikin jini.
Bakomai ne ya haddasa gaba tsakanin Huzlan da su Sharilat ba face rigima a kan wannan daji da suke ciki, asalin dajin na wani tsohon mafarauci ne da ya taimaki tsoho Kuhairu da matarshi Hasmila. Bayan mutuwar mafarauci Kamzil ne sadauki Huzlan ya ƙudiri aniyar kwace dajin saboda irin arbarkatun dake tattare da dajin. Babban burin Huzlan a duniya shi ne da zarar ya mallaki dajin zai gina wani katafaren birni wanda yake ababu kamarsa,Kasancewar Huzlan mashahurin attajiri, Saboda sana'ar fashi da makami da yake yi.
A ƙalla Huzlan da su tsoho Kuhairu sun yaƙi junansu sau ashirin da huɗu amma babu wanda yake samun nasara sai dai ayi ragas.
wannan shi ne dalilin kulluwar gaba a tsakanin su.




****
Lokacin da Sarki Badaddul-Arus da 'yarshi Uzaima su ka ci gaba da jagorantar miliyoyin DAKARUN YAKInsu sai su kaci gaba da ratsa dazuzzuka da bira ne sai suka shafe tsawon sa'a tara suna tafiya babu sassauci.
Sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba sai ga shi Sarki Badaddul-Arus da jama'arshi sun shafe tsawon kwanaki biyar suna tafiya, a iya tsawon tafiyar babu abin da ke tsaida su face idan gimbiya ko Sarki sun yi buƙaci da dakatar da tafiyar.
A kwana na shida ne a lokacin da rana ta zo tsakiya Sarki Badaddul Arus da jama'arshi suka iso birnin Jarul Iman, koda isowarsu sai Badaddul-Arus ya umarci magatakarda ya rubuta wasika sannan ya shi manzo ya tura shi izuwa birnin.
Lokacin da jakadan ya isa fadar birni sai ya tarar da fadar ta cika ta batse da jama'a a wannan lokaci Sarki Huraisu na zaune a kan karagar mulkin wcce aka sana'anta ta da zallar zinare a ka yi mata feshi da ruwan rukut, Ya na sanye da doguwar shuɗiyar alkyabba da a ka yi mata cin baki da zaren lu'u-lu'u takalmin dake kafarshi an yi mashi ado da gashin ɗawisu sanye a kanshi akwai KAMBUN MULKI da a yi shi da zallar zinare ya na ta walwali da daukar ido. Tabbas wannan shiga da Sarki Huraisu ya yi ta mutukar fito da kyakkyawar surarshi babu wata 'ya mace da zata yi wannan arba da shi face ta kamu da matuƙar kaunarshi a zuciyarta.
A gefe guda kuwa yan majalissa ne a zazzaune bisa shimfiɗu na alfarma, dakaru kuwa sun yiwa fadar kawanya su na ta kai komo dan tabbatar da cikakken tsoro.
A wannan lokaci gaba daya mutanen dake fadar su kuma satar kallon Sarki Huraisu suke yi kuma a na fira cikin nishaɗi da walwala.
jakadan ya shigo fadar da zuwan shi ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa sannan ya gabatar da wasika.
Sarki Huraisu ya umarci magatakardar da ya karbi wasikar dake hanun badakaren ya warwareta sannan ya fara karanta abin da ke cikin fili kowa ya na sauraro. Takarda daga dodon Sarakuna Sarki Baddadul Arus.
Zuwa ga ɗan tatsitsin sarki a cikin sarakuna Sarki Huraisu.
Ya kai wannan kaskantaccen Sarki ka yi sani cewa bai rubuto wannan wasika ba sai domin baka umarni.
Ina so ka mallaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login