Showing 12001 words to 15000 words out of 59965 words
Chapter 5 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt
mutukar kaunar Sarki Sariful saboda gudanar da mulkinshi bisa adalci babu cutarwa.
Hatta Sarakunan dake maƙwaftaka da kasarshi suna jin dadin mu'amala da shi, domin ko wani sarki ya yi niyyar zaluntar wani, sai Sarki Sarifu yana kai ma shi ɗauki.
Wannan dalili ya zaman lafiya da kwanciyar hankali hankali suka mamaye.
Masana tarihin duniya ke kiran Nahiyar da suna Mufrad, ma'ana ƙasashen sun zama bisa turba ɗaya.
Yarima Himras da Kuhairu sun ta so cikin jarumtaka ta ban mamaki domin tun suna yara koda 'yan tsirarun abokan gaba suka kawo farmaki suke tarar su su gwabza yaƙi samu nasara a kansu. Kasancewar Sarki Sarifu shekarunsa sun ja tsufa ya fara riskarshi ba zai iya bawa su Yarima horon yaƙi ba, Sai Ya tura su wani babban birni da ake horar da mayaƙa sai da suka shekara a shirin sannan suka dawo gida. A wannan lokaei sai ya zamana sun cika ZARATAN MAYAKA da babu kamarsu.
Domin akwai wata rana da wani hatsabibin Sarki da ya zo kasar domin ya raba Sarki Saruful-uzwar da karagarshi, Yarima Kuhairu da Himras kaɗai suka yaƙi Sarkin da rundunar shi basu bar mutum ɗaya ya tsira da rayuwarsa ba.
Lokacin da Sarki Sarifu ya ga cewa shekarun shi sun ja tabbas ajali zai iya zuwa masa akowanne lokaci sai ya karkata ga Yarima
Kuhairu a matsayin mai jiran gado.
Lokacin da Yarima Himras ya ga cewa mahaifinsu ya zaɓi ɗan uwanshi Yarima Kuhairu a matsayin mai jiran gado sai baƙin ciki da ƙyasi suka mamaye zuciyarshi, Amma sai ya bar abin a ranshi bai bayyana ba. Amma kullum sai ya yi kukan baƙin ciki kuma ya ƙudiri aniyar in dai ya na numfashi a doron ƙasa, ba zai bar ɗan uwanshi Kuhairu ya gaji mahaifinsu ba.
Bayan shekara ɗaya da dawowar su yarima Himras sai Sarki Sarifu ya kamu da matsananciyar rashin lafiya ya zamana sai an kwantar an tayar,
Sai hankalin Yarima da mahaifiyarsu ya Ɗugunzuma bisa ganin halin da mahaifinsu yake ciki, nan fa suka bazama nemo masa magani amma kullum cuta ƙara gaba ake yi.
Wata rana Yarima Kuhairu da Himras suna zaune a gaban mahaifinsu a cikin turakarshi suna kallon shi suna masu zubar da hawayen.
A na cikin wannan hali ne sai suka ji mahaifinsu ya yi gyaran murya ya ce, "Ya ku 'ya'yana ku matso kusa gare ni.
Koda jin hakan sai duk su biyun suka cika da matuƙar mamaki domin a iya saninsu rabon da Sarki ya buɗi baki ya yi magana yau tsawon wata uku ke nan ko wani abu yake son faɗa sai dai ya yi nuni da hannu ko da baki.
Himras da Kuhairu suka matsa kusa da mahaifinsu wanda ke kwance bisa kan gadon sarautar ta yadda suna iya jin numfashin juna domin su ji abinda zai sanar da su.
Sarki Sarifu ya yi gyaran murya a karo na biyu sannan ya buɗi baki da ƙyar ya na duban Kuhairu, Himras ya ce.
"Ya ku 'ya'ya na abin alfaharina ku yi sani cewa na ji ajikina wannan cuta tawa da ta same ni bata ta shi ba ce, kai Kuhairu kai ne babba dole kai zaka gaji KAMBUN MULKI na domin bisa al'adar wannan ƙasa babban ɗa shi ne ke gadar mahaifinshi.
Sa'adda sarki Sarifu ya zo nan a Zancenshi sai tari ya turnukeshi da ƙyar ya samu tarin ya tsaya ya ci gaba da ce wa.
"Ya ku 'ya'yana ina mai neman alfarma a wajenku da ku ci gaba da tafiyar da wannan ƙasa bisa adalci da tausayawa ku kasance masu kyautatawa mu'amala tsakanin ku, ka da kwaɗayin mulki da na dukiya ya sanya gaba a tsakaninku, kai kuma Himras ina so ka zama mai biyayya ga ɗan uwanka domin rayuwarku ta kasance mai kyau.
A yanzu zan baku dukkanin sirrikan tsafina domin su zame muku kariya.
Gama faɗin hakan ke da wuya sai Sarki ya sanya hannunshi na dama a na Yarima Kuhairu na hagun a na Himras suka ƙanƙame juna.
Faruwar hakan ke da wuya sai wani irin farin haske ya dunga fita daga sarkin Sarifu yans shiga hannayensu yarima.
ko da hasken ya kammala shiga jikinsu yarima sai Sarki Sarifu yana kama kakarin mutuwa.
jini ya dunga fita daga bakinshi, Nan take gagarumin karfi mai karfi ya shige su tamkar za su iya iya tunkarar Mayaƙan duniya.
Faruwar hakan ke da wuya sai jikin Sarki ya sandare, komai na ya daina motsi kuma idanunshi suka ƙafe alamar rai ya yi halin shi. Koda ganin hakan sai su Yarima Kuhairu suka fashe da kukan baƙin ciki su na masu rungume gawar mahaifinsu.
A dai dai wannan lokaci ne mahaifiyarsu ta rugo izuwa cikin turakar a dimauce bisa jin kuka da ta yi, Ya yin da ta isa inda su Yarima suke ta ga halin da suke ciki, sai ita ma ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.
Su ukun suka ci gaba da rusa kuka kamar ba za su daina ba. Al'amarin da ya haddasa hargitsewar gidan sarautar ke nan mutane su ka dunga guje guje-guje da ifice-ifice cikin tashin hankali, a wannan rana gaba ɗaya mutanen kasar Darul-Kushur sun kasance cikin tsananin baƙin ciki da jimamin mutuwar Sarki Sariful-Uzwar Su kansu manyan da kana nan sarakuna dake makwabtaka da shi sun shiga cikin tararrabi, Domin suna ganin sun yi babbar hasara.
Kuma gaba ɗayansu sun halarci bikin binne Sarki Sarifun.
Bisa al'adun kasar Darul-Kushur, Ranar da Sarki ya mutu kashe gari ake bikin naɗin sabon sarki."
Hakanne ya sanya tun a daren da Sarki Sarifu ya mutu bayan binne shi a ka yi shela izuwa ƙasashe da birane na naɗin sarautar Yarima Kuhairu.
Kashe gari da sassafe a ka ta shi da shiryen nadin sarauta Yarima Kuhairu, nan fa birnin ya cika ya batse da baki manya da ƙanana a Attajirai da sarakuna. Bayan an gama shiri tsaf fada ta cika maƙil da jama'a sai ga Yarima Himras da Kuhairu sun shigo fadar, suna sanye da suturu iri daya sak hatta takalmi da hulunan dake kansu iri ɗaya ne, kuma su na riƙe da wata sanda da ka yi mariƙinta ta siffar damisa.
A wannan lokaci fusakunsu cike da annuri suna fira a cikin Nishaɗi.
koda shigowarsu sai fadar ta rude da hayaniya kowa na faɗin albarkacin bakin shi, ba a samu damar yin shiru ba har sai da su Yarima suka zauna a kan kujerun da a ka tanadar musu.
Shiru ne ya mamaye fadar tamkar an yi ruwa an ɗauke daga can sai yarima Kuhairu miƙe tsaye ya fuskanci jama'a ya yi gyaran murya ya ce.
"Da farko dai ina yiwa dukkannin mutanen da suka halarci wannan fada mai albarka, na yi mutukar jin daɗi bisa gani yadda manyan sarakuna, attajirai, talakawa da sauran mutanen gari su ka halarci wannan naɗin sarauta tawa.
Sannan daga bisa ni ina mai taya ' yan uwa jimamin mutuwar mahaifin mu Sarki Sarifu, ina fatan mutanen wannan fada suna mutuƙar kwaɗayin kasancewa sabon sarkinsu a yau.
Ya yin da Yarima Kuhairu ya zo dai dai nan a Zancenshi sai fadar ta sake ruɗewa da suratai karo na biyu mutane Suna masu nuna goyan bayansu a kan Kuhairu ya zamo Sarkinsu.
Koda Yarima Himras ya ga yadda jama'ar fadar ke nuna tsananin kaunar ɗan uwanshi ya zamo Sarkin su, sai zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata ƙone yaji tamkar ya zare takobi ya afkawa Kuhairu da yaƙi.
Kuhairu ya ɗaga hannunshi sama mutane suka yi shiru sannan ya koma bisa kujerarshi ya zauna.
Faruwar hakan ke da wuya sai ma'ajin sarauta ya gabato da alƙyabba da kambun sarauta na Sarki, Domin bisa al'ada dazarar Sarki ya mutu za a cire kayan sarautar shi a damƙa a hannun ma'ajin sarauta, sai ranar da za a yi naɗin sarauta sannan ma'aji ya kawo su fada.
Ba tare da ɓata lokaci ba Yarima Kuhair ya sake miƙewa tsaye waziri ya ƙarɓi kayan dake wajen Ma’aji sannan ya sanya Yarima alkyabbar ganin da KAMBUN Mulkin, Nan take Yarima ta taka da kafafunsa har inda karagar Sarki take ya hau ya Hakimce.
Faruwar hakan ke da wuya sai 'yan majalisar kasar su sha biyu suka durƙusa ƙasa su na masu sunkuyar da kawunansu a gaban yarima Kuhairu.
Nan take jama'ar fadar suka kaure da shewa gami da yiwa Yarima Kuhairu jinjina, Nan take zuciyar Yarima Himras ke zaune a gefe guda ta ci gaba da tafarfasa tamkar Zata ƙone, kuma ya cika da mutukar baƙin ciki mara mara Misaltuwa, amma saboda gudun kada mutane su lura da halin da yake ciki sai ya saki fuskarshi ya dunga shewa da tafi ga Kuhairu. Bayan kammala naɗin sarauta sai kuma a ka shiga hidimar ciye- ciyen abinci da abin sha amma da a ka fara wannan walima sai Yarima Kuhairu ya miƙe tsaye daga kan karagar mulkinshi, ya taka da kafafunshi har inda Yarima Himras ke zaune ya rike kafaɗunshi ya tashe shi ya riƙe hannun shi har inda kujerar mulkin take suka zauna tare sannan a kawo musu abinci da abin sha suka ci tare suna Firarsu cikin nishaɗi.
A wannan rana dai haka aka yi gagarumar walimar naɗin sarautar Yarima.
Mutane ba su bar fada ba sai da Sarki Kuhairu da Yarima Himras suka yi suka shiga gidan sarauta sannan mutane suka bar fadar.
Sarakunan da suka halarci bikin Suka fara shirin tafiya izuwa biranen su.
***
Ƙayataccen lambu ne da aka ƙawata shi da nau'ikan kayan marmari da furanni, Wata irin Daddaɗar iska na kaɗawa tsirrai da bishiyu na yin rangaji abin gwanin ban sha'awa.
Idan mai mai kallo ya kai duban shi ga ɓangaren yamma a lambun zai yi ido biyu da waɗansu ƙayatattun kujeru, a tsakiyar su an ajiye wani madaidaicin teburi na azurfa mai ɗauke da kofunan zinare, Zaune akan kujerun waɗansu zaratan samari ne guda Biyu, Suna sanye da tufafi na ma'abota sarauta.
Duk irin duhun dare, da na bishiyun lambun, Kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci cewa sun kasance ZARATAN MAYAƘA masu dakakkiyar zuciya.
Ba waɗansu ba ne samarin ba face sarki Kuhairu da Yarima Himras, Kuhairu ya ɗauki dogon kofin dake kan teburin ya tsiyaya ruwan inibin a cikin ƙananan kofuna guda biyu ya ɗauki ɗaya ya miƙawa ɗan uwanshi Himras, ya ɗauki ɗayan, A lokaci guda suka kai kofunan Izuwa bakunan suka shanye ruwan inibin.
Bayan Shirun da ya wanzu a tsakanin su sai sarki Kuhairu yayi gyaran murya sannan yace"Yakai Himras kayi sani cewa Haƙiƙa har abada kai ɗan uwana ne na jini, Yanzu Gashi an naɗani a matsayin halifan Mahaifinmu, Shin wace shawara za ka bani domin ganin nayi jagorancin wannan ƙasa tamu mai albarka?.
Koda jin wannan jawabi daga bakin Kuhairu sai Himras ya yi shiru yana mai sunkuyar da kanshi ƙasa tamkar mai tunani wani abu, Daga bisani kuma sai ya ɗago da kanshi sama ya dubi Ɗan uwanshi yace.
"Ya ɗan uwana ina mai matuƙar farin ciki bisa zamowarka matsayin halifan Mahaifinmu, Shawara ta Farko da zan ba ka ita ce, Wajibi ne a hukunta dukkan mai laifi tsakanin talakawa da Attajirai, shawara ta biyu bawa mayaƙa horon yaƙi, tare da sabunta makaman yaƙi, Domin tunkarar HARIN BAZATO.
Karɓar Haraji a hannun 'yan kasuwa domin gudanar da aiyukan cigaban al'umma,
Abu na ƙarshe shine aure,
Aure shine cikar darajar kowane BASARAKE.
Koda jin waɗannan shawarwari sai sarki Kuhairu ya cika da matuƙar farin ciki maral misaltuwa, ya dubi Himras cikin Tattausan murmushi yace"Haba ɗan uwana ko ka manta ne cewa a rayuwata ban taɓa yin budurwa ba, Hasalima bana shiga sabgar mata, taya zan iya gano macen da ta dace na aura.
Himras ya bushe da 'yar ƙaramar dariya sannan yace"Kwantar da hankalin ka yakai ɗan uwana na amince maka ka auri masoyiyata na tabbata cewa zata soka fiye dani kuma idan ku kayi aure za'a samu zuri'a mai inganci.
Cike da matuƙar mamaki maral misaltuwa Kuhairu ya dubi yarima yace " kana so ka ce mini ka Amince na auri masoyiyarka sharzila 'ya ga waziri Zuraisu, wacce ku ke soyyayya tun kuna yara ƙanana?.
Himras ya gyaɗa kai yace " ƙwarai kuwa haka nake nufi, ya ɗan uwana kayi sani cewa babu wani abu da na mallaka a wannan duniya face na baka shi, Ni da kai duk abu ɗaya ne, Domin uwa ɗaya uba ɗaya yafi ƙarfin wasa.
Sa'add yarima yazo Nan zancenshi sai sarki Kuhairu ya cika da matuƙar farin ciki maral misaltuwa, bai san sa'adda ya tashi daga kan kujerarshi ba yaje ya rungume yarima, su duka biyun suka fashe da kukan farin ciki, Tsawon daƙiƙa goma suna rungume da juna sai daga bisani ne Kuhairu ya janye jikinshi daga na Yarima ya riƙe hannun shi suka nufi hanyar da zata fitar dasu daga lambun, sai da su ka zo wata mararraba sannan kowanne yayi nashi ɓangaren.
Lokacin da yarima Himras ya kaɗaita a cikin turakarshi sai kawai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta.
Sai da yayi dariyar ta isheshi sannan daga bisani ya tsuke bakinshi ya karanto waɗansu Ɗalasiman tsafi, ya rikiɗa Izuwa wani kyakkyawan tsuntsu ya ratsa rufin turakar tamkar yadda danshi ke ratsa ƙasa ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba.
A cikin wani ƙayateccen lambu ya bayyana yana mai fitar da sautin wani kuka mai Daɗin saurare, jim ƙaɗan da aiwatar da hakan sai ga wani Dattijo ya riƙo hannun wata kyakkyawar budurwa sun shigo lambun da zuwa suka samu waɗansu ƙayatattun kujeru suka Hakimce, kyakkyawan tsuntsun ya rikiɗa izuwa surar yarima Himras yaje ya zauna abinda kujerar dake fuskantar mutane biyu.
Kyakkyawan murmushi yarima ya sakarwa budurwar ita ta mayar mashi da martani.
Ita dai kyakkyawar budurwar ta kasance mai matsakaicin tsawo da kauri,