Showing 15001 words to 18000 words out of 59965 words

Chapter 6 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt

09 Dec 2024

9385

tana da dara-daran idanu farare ƙal, tamkar tacecciyar Madarar shanu ƙwayar cikin su sun yakance baƙaƙe siɗik, masu ɗaukar hankalin duk ɗa namiji mai hankali, Batun diri da ƙira kuwa tamkar ita ce ta tsara kanta yadda take buƙata,
Ba wata ba ce wannan kyakkyawar halitta ba face gimbiya sharzila'ya ga waziri Zuraisu.
Bayan shiru da wanzu a tsakanin su na ɗan wani lokaci sai waziri ya buɗi baki ya dubi yarima yace "ya sarkin ƙasar Darul-kushur na gobe shin wane labari kake tafe da shi?, Daga yadda fuskarka ta bayyana akwai bayani mai kyau, kasan masu iya magana na cewa labarin zuciya a tambayi fuska".
Yarima yayi gyaran murya yace " Ya waziri kayi sani cewa Haƙiƙa haƙanmu ya kusa cimma ruwa, Nan da lokaci ƙafan idan na samu goyan baya daga gareku, Ya sirikina kayi sani cewa a daren jiya na gana da ɗan uwana, kuma na amince mashi ya auri masoyiyata sharzila.
Cikin alamun fushi waziri ya dubi yarima yace"Wannan wace irin maganar banza ce ka ke yi?
Da jin hakan sai Yarima ya bushe da dariya.
Al'amarin da yayi matuƙar bawa waziri da gimbiya mamaki kenan suka ƙura ma shi idanu, domin su ga iya gudun ruwan shi.
Lokaci guda yarima ya haɗe rai sannan yace"ya sirikina kayi sani cewa tun lokacin da mahaifinmu ya rasu mun mallaki dukkan sirrikan tsafinshi, Bisa binciken da na gudanar a halarar tsafina na gano cewa babu wata hanya da zan bi domin kawar da ɗan uwana face ta hanyar makirci.
Bisa wannan dalili ya sanya na nuna goyon bayana akan ya auri masoyiyata sharzila, domin da ita ce kaɗai zata iya samun nasarar sato mini gurin tsafin sarauta wanda babu wani mahaluki da zai mallake shi face duk wata halitta dake wannan birni tayi biyayya a gare shi, Ya waziri kayi sani cewa da yawa daga cikin sarakunan duniya ƙarfin rundunar mayaƙa, shirin tsafi ba ya kawar dasu face ta hanyar shirya musu makirci da matayen auren su, Abinda nake muradi kawai shine masoyiyata sharzila ta so ɗan uwana Kuhairu so mai tsanani domin samun nasara akan Abinda mu ka sanya a gaba.
Kaga kenan da zarar sharzila ta auri Kuhairu Nan da wata guda zan zamo sabon Sarkin birnin Darul-Kushur tare da ɗaurin aurena da gimbiya sharzila.
Sa'adda yarima yazo nan zancenshi sai waziri da gimbiya suka cika da matuƙar mamaki gami da farin ciki maral misaltuwa, Batare da wani jinkiri ba su ka rabu akan cewa gobe yarima zai sake bayyana ya sanar da su abinda yake wakana.
Bayan kammala hakan sai Yarima ya sake rikiɗa Izuwa wannan kyakkyawan tsuntsu ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa.


***
Kamar yadda yarima Himras ya faɗa haka al'amarin yakasance, A cikin Abin da bai gaza mako huɗu ba, soyyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin sarki Kuhairu da gimbiya sharzila, Har yazamana cewa an sanya ranar da za'a ɗaura musu aure.
A iya tsawon waɗannan kwanaki a kowane dare sai Yarima ya bayyana a lambun shaƙawar waziri da 'yarshi sharzila, sun tattauna akan abubuwan da zasu aikata.
Lokacin da labarin soyyayyar sarki Kuhairu da gimbiya sharzila ya watsu a gari, sai jama'a suka cika da matuƙar mamaki, su na masu tambayar kansu cewa, Shi ya akayi sharzila ta koma soyyayya da Kuhairu alhalin tun suna yara ƙanana suke matuƙar juna ita da yarima Himras, Shin ko kwaɗayin mulki ne yasanya ta aikata hakan, Amma da su ka ga Yarima Himras bai nuna damuwa ba sai ma farin ciki, sai suka cire dukkan shakku daga zukatansu.
A cikin kwanaki biyar kacal sarki Kuhairu ya aika jakadu Izuwa ƙasashen dake nahiyar, akan yana gayyatar su ɗaurin auren shi.
A ranar ɗaurin aure kuwa, ƙasar Darul-kushur ta cika ta batse da jama'a babu masaka tsinke, saboda matuƙar yawa wasu ma a bayan gari suka tsaya, basu samu damar shigowa wajen ɗaurin auren ba.
A wannan rana anyi shagalin bikin da ba'a taɓa yin kamar shi ba tsawon wanzuwar ƙasar Darul-kushur, saboda mutum koda ruwa ya ƙasa sai ya samu arziƙi.
Sarki Kuhairu da Yarima Himras kuwa sai su dunga rabon dukiya da suturu ga talakawansu, bayan an kammala shagalin biki, kowa ya koma gidan shi Lafiya cikin farin ciki saboda arziƙin da ya wadata.
Sarki Kuhairu da Amaryarshi sharzila suka tare cikin farin ciki, Tun daga wannan rana sarki Kuhairu ya cigaba da gudanar da mulkinshi cikin kwanciyar hankali da annashiwa, Sannu-Sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba'a je ba, sai gashi sarki Kuhairu ya cika shekaru gida batere da Amaryarshi ta samu Haihuwa ba, Al'amarin da yayi matuƙar jefa shi cikin damuwa kenan, kuma ya yanke shawarar ƙara aure.
Abin da Kuhairu bai sa ni ba shine, A duk lokacin da zai Kusanci sharzila, sai Yarima Kuhairu ya bayyana cikin siffar duhu ya samar da wata mace ta sihiri mai matuƙar kama da sharzila sannan ya ɗauke sharzila suje su sheƙe ayarsu, shi kuwa yana saduwa ne da wannan mace ta sihiri.
Abin da yasanya Kuhairu bai gano hakan ba shine saboda bisa ƙa'idar tsafin su, ɗayansu ba shi da ikon gudanar da bincike a kan ɗan uwanshi.
Lokacin da Sarki Kuhairu ya buƙaci ƙara aure, sai wani daga cikin fadawanshi ya amince ma shi ya auri 'yar shi Hashmila.
Bayan mako guda da ɗaura auren, sarki Kuhairu na zaune da uwar gidanshi sharzila, sharzila ta ɗora hannunta akan ƙafafun mai gidan ta ta ƙura ma shi idanu sannan ta dubeshi cikin alamun damuwa tace"Ya uban 'yayana shin yaushe ne burinmu zai cika na samun magaji, zan fi kowa farin ciki idan aka ce yau jinana ne ke mulkin kasar Darul-Kushur?.
Koda jin wannan batu sai idanun sarki Kuhairu ya cika da matuƙar damuwa ainun ya buɗi baki yace"ya mafi soyuwa agareni kiyi sani cewa haƙiƙa na fiki damuwa akan wannan hali da muke ciki, Babban abinda ke Ɗugunzuma hankalina shine halarar tsafina ta gaza bayyana mini mafita.
Koda jin wannan batu daga bakin Kuhairu sai sharzila ta dubeshi cike da damuwa ƙarara tace" ya sanyin idaniyata zan kasance mai roƙon abin bauta gunki sabrat akan ya cika burinmu. Yanzu abinda ya kamata shine ka shiga kewaye kayi wanka ka huce gajiyar dake tare da kai, sannan kayi kalaci.
Koda jin hakan sai sarki Kuhairu ya miƙe tsaye ya cire alƙyabbarshi ya nufi kewayen wanka yana mai waigen sharzila suna yi wa suna murmushi mai tattare da alamar tsantsar so da ƙauna.
Koda shigewar sarki Kuhairu izuwa kewayen,sai sharzila ta miƙe tsaye zumbur ta sanya hannun a cikin alƙyabbar sarki ta ɗauko wani gurin tsafi, A dai-dai wannan lokaci ne Yarima Himras ya bayyana a turakar ya riƙe hannunta su ka ɓace bat!. tamkar basu taɓa wanzuwa ba.
A cikin lambun shaƙawar waziri suka bayyana, batare da ɓata lokaci ba sharzila ta ɗauko wannan gurin tsafi na sarki Kuhairu ta miƙawa Himras ya ƙarɓa ya saka a damtsen hannunshi na hagu, Faruwar hakan ke da wuya sai alƙyabba,kambu gami da kwagiri suka bayyana a jikinshi.
Nan take sharzila da yarima suka bushe da dariyar mugunta tamkar ba zasu daina ba, sai daga bisani ne Yarima Himras ya buɗe baki ya ƙwallawa waɗansu dakaru kira,Dakarun suka bayyana gareshi suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa.
Yarima ya dubi wani garjejen ƙato wanda da ala shi ne shugaban su yace da shi "ya kai Rauzub kayi sani cewa bakomai ne yasanya na kira ka nan ba sai domin ina so ka ɗebi dakaru har Izuwa turakar ɗan uwana Kuhairu, ka tabbatar da cewa ka hallaka shi tare da Amaryarshi Hashmila.
Rauzub ya risina yace"An gama ya shugabana, Kafin ya sake furta wani abu yarima Himras ya miƙa hannunshi na hagu Izuwa sama yana mai karanto waɗansu Ɗalasiman tsafi, yana gama rufe bakinshi sai waɗansu masuna guda biyu suka bayyana akansu.
Kawai sai ya miƙawa Rauzub ya dube shi karo na biyu yace "Idan ya tabbata ka yi amfani da waɗansu masuna wajen hallaka ɗan uwana Kuhairu da Amaryarshi, Nayi maka alƙawarin zan ɗaga darajar ka daga shugaban dakarun gidan waziri Izuwa shugaban dakarun wannan ƙasa baki ɗaya.
Koda jin wannan batu sai Rauzub ya miƙe tsaye ya huce gaba, dakarunshi na biye da shi su ka fice daga lambun, Nan take Yarima Himras da sharzila suka bushe da dariyar mugunta, A dai-dai wannan lokaci ne waziri Zuraisu ya shigo lambun yana mai taya su dariyar.




****
Lokacin da sarki Kuhairu ya fito daga kewayen wanka sai ya nufi gadonshi domin ya ɗauki alƙyabbarshi, Nan take yaga babu ita koda ya shafa damtsenshi Nan take yaji babu gurin tsafinshi, Nan take ya tabbatar dacewa garin nashi na cikin alƙyabbar.
Abin tambaya a nan shi ne wane ne ya ɗauke alƙyabbata alhalin babu kowa da yake da ikon shigowa wannan turaka face Ni da uwar gidana sharzila, Shin koda sharzila ta aka haɗa baki aka ci amanata.
Amsar tambayar da ya ka sa bawa kanshi kenan hawayen baƙin ciki suka zubo daga idanuwanshi Izuwa kan kuncinshi,. A dai-dai lokacinne ya jiyo ihu da kururuwar dakaru, ko da jin hakan ya zare wata sharɓeɓiyar takobi a gefen gadonshi ya falfala da azababban gudu yana mai ficewa daga turakarshi hawaye na cigaba da zuba daga idanuwanshi.
Yana cikin wannan hali ne ya hango dakarun sumame sun rugo Izuwa inda yake ɗauke da miyagun makamai suna ihu da kururuwa mai firgitarwa.
Ko da ganin hakan sai ya zare wani kwari da baka a gadon bayanshi ya shiga harbin dakarun cikin gwaninta, kafin cikae daƙiƙa ashirin ya hallaka dakaru fiye da arba'in.
Ko da dakarun su ka ga irin mugun kisan da kuhairu ke yi ma su, sai suka firgita ainun, Domin sun san cewa suna kusantarsu ne, amma da suka tuna wanda ya umarce su da hakan sai suka harzuƙa ainun.
Kafin cikar daƙiƙa Hamsin Kuhairu ya hallaka fiye da mutum ɗari, koda ganin hakan sai kuhairu ya mayar da bakanshi Izuwa gadon bayanshi ya zare Takobinshi ya daka wawan tsalle tamkar an janye shi da ƙugiya ya sauka a tsakiyar dakarun ya afka musu aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni,Ban tsoro da ban al'ajabi, ƙarar karafniyar ƙarafa, ihu gami da hargowar dakarun ta cika dodon kunne.
Duk in da kuhairu ya sanya a gaba sai dai kaga dakaru na zubewa ƙasa matattu tamkar ana sassabe a gonar auduga, jini ya dunga kwaranya,tsartuwa yana malala a ƙasa.
Tabbas sarki Kuhairu ya cika GWARZON MAYAKI mai ƙarfi na Allah ya isa, ina da ace mutum ya na tsaye a wannan waje lokacin da Kuhairu ke raba kai da gangar jiki da kafin takobinshi dole ya jinjina ma shi ya tabbatar da cewa ya cika sarkin sadaukai.
Ga shi dai ƙiri-ƙiri dakarun suna kai ma shi miyagun hare-hare, kuma suna ƙara tuttuɗowa daga gidan sarauta, Amma basu samu nasarar koda lakutar jikin shi ba.
Dukkan abin da ke wakana tsakanin kuhairu da dakarun sumame, yarima Himras, waziri Zuraisu da gimbiya sharzila sun gani a cikin madubin tsafin yarima a lokacin da suke zaune a lambun shaƙawar waziri.
Yayin da suka ga yadda Kuhairu ke samun nasara sai hankulansu suka ɗugunzuma ainun, Domin a cikin abin da bai gaza daƙiƙa Hamsin ba yana kashe dakaru fiye da guda ɗari, Tabbas nan da lokaci kaɗan zai hallaka su ba ki ɗaya.
Kawai sai yarima ya buɗe bakinshi ya karanto waɗansu Ɗalasiman tsafi, yana gama yana kammalawa sai waɗansu tsuntsaye na sihiri suka bayyana a sararin samaniya, Su dai tsuntsayen sun sha Bamban da waɗanda idanu su ka saba gani.
Su na girma tamkar mikiya, bakunan ya furzar da wani irin dafi, koda bayyanar su sai kawai su ka kaɗa fuka-fukansu suka durfafi gidan sarauta cikin matsanancin gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya.
Nan take Yarima, waziri haɗi da sharzila suka taƙarƙare su ka bushe da dariyar mugunta tamkar ba zasu daina ba.




****
Shirye yake cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini, kuka kuma ya rufe fuskarshi da rawani idanunshi kaɗai ake gani, a gadon bayanshi yana rataye da waɗansu dogayen ma su guda biyu.
Ba wani ba ne wannan mayaƙi ba face sadauki Rauzub wanda yarima Himras ya umarci ya hallaka sarki Kuhairu da Amaryarshi Hashmila.
Tafe a cikin wata hanya ta musamman yana ƙara kunna kai Izuwa ciki kai da gani kasan cewa hanya ta musamman da ba kowa ne ya san da ita ba, domin badakare koda guda ɗaya.
Lokacin da ya shafe tsawon rabin Sa'a yana tafiya a dai-dai wannan lokaci ne ya fara hango katangun turakar sarki Kuhairu, Don haka sai ya ƙara azama.
Koda yazamana cewa saura taku goma tsakanin shi da turkar, kwatsam! bazata Babu tsammani sai ya hango wani badakare ya bayyana tsulum a gabanshi, Badakaren yana shirye cikin gagarumar shigar yaƙi ta baƙin sulke ya rufe fuskarshi da baƙin yanki a kafaɗarshi yana rataye da wata sharɓeɓiyar takobi.
Nan fa Rauzub ya cika da matuƙar mamaki maral misaltuwa, abin da ya ba shi mamakin shine wane badakare yasan cewa ya biyo ta wannan hanyar har yayi GABA DA GABA da shi.
Koda Rauzub yazo nan a tunaninshi sai ya fusata ainun ya zare wata sharɓeɓiyar takobi a damtsenshi ya falfala da azababban gudu Izuwa kan Badakaren yana ihu da kururuwa mai firgitarwa.
Koda ganin hakan sai Badakaren yayi koyi da shi ya zare Takobinshi ya ruga gareshi, Yayin da su ka haɗu da juna sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni,ban tsoro da ban al'ajabi.
Duk sa'adda takubbansu su ka haɗu da juna sai dai kaji sun ba da sauti ƙal ƙal ƙal!, tartsatsin wuta ya tashi, Babu abin da zai burge mutum ya kuma ba shi sha'awa ga jaruman biyu face yadda suke kaiwa junansu hare-hare cikin mutuƙar zafin nama, Sai da suka lalata makaman dake hannun su, su ka yi jifa da su suka ciri wasu sabbin a jikin su suna cigaba da kaiwa junansu hare-hare.




****
A cikin gidan sarauta kuwa sarki Kuhairu ya cigaba da ragargazar dakarun babu sassauci, lokacin da Sa'a ɗaya ta cika a dai-dai lokacinne ya hallaka mayaƙan ba ki ɗayan su.
Kwatsam! Sai ya hango waɗansu tsuntsaye sun bayyana a sararin samaniya, idan ɗayansu ya sauka a turba sai kaji tamkar an jefar da ɗan maraƙi, bayan sun kammala sauka ne aka fara kallon kallo tsakanin su da Kuhairu.
A iya tsawon rayuwar Kuhairu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login