Showing 54001 words to 57000 words out of 59965 words
Chapter 19 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt
sanya wannan makullin a wata siririyar rami na kwafi dake jikin murfin da ya rufe kushewar ya murɗa har sau uku, take kwaɗon ya buɗe kanshi, Baddadul-arus ya sanya hannunshi ya dage murfin, haƙiƙa komai hassadar mutum idan ya ga yadda Baddadul-arus a lokacin da ya ke ɗage murfin da aka yi da zallar jauhari dole ne ya jinjina masa ya tabbatar da cewa ya cika GWARZON DUNIYA.
Murfin na kammala buɗe wa sai wani farin haske da hayaƙi na musamman ya tuttuɗowa daga kushewar ya gauraye kogon baki ɗaya ta yadda ko allura ce ta faɗi da zarar mutum ya duba zai ganta.
Cikin matuƙar farin ciki Baddadul-arus ya ɗauko sarƙar tsafi a cikin aljihun rigarshi ya sanya ta a bisa wuyan gawar boka sharubu wacce ke rufe a cikin wani mayafi na sihiri da ba a iya ganin fuskar shi.
Faruwar hakan ke da wuya sai gaba ɗaya kogon na Garul-Shimshan ya shiga girgiza aka kwantsama wata tsawa mai ban tsoro tamkar hadari zai gangamo a ɓarke da ruwan sama, al'amarin da ya sanya sarki Baddadul-arus, Uzaima, Shaibat, sarki Huraisu da aljani zamzaru suka ɗimauce suka durƙusa ƙasa bisa gwiwoyin su suna masu sunkuyar da kawunansu,
Tsawon lokacin ana cikin wannan hali sai daga bisani ne kogon dutsen ya samu dai-dai to kuma a ka ɓarke da wata dariya mai kama da kukan jaki.
Tamkar ɗaukewar ruwan sama dariyar ta ɗauke sannan wata kakkausar murya ta ce "Lale marhaban da zuwan sarki Baddadul-arus na birnin madinatul-husuf mai burin zamowa sarkin sarakuna na nahiyar mufrad tare da sarki Huraisu ma'abocin baiwa da hikima izuwa kogin Garul-Shimshan, sai ku yi hanzari ku ɗago da kawunanku domin ku yi arba da sarkin bokaye Sharubu ibn shalyasu.
Ko da jin wannan batu daga bakin boka Sharubu sai su Baddadul-arus suka ɗago da kawunansu ya yin da suka yi arba da boka Sharubu sai suka firgice jikkunansu suka kama tsuma suna ƙyarma ba su san sa'adda suka faɗi ƙasa ba suka yi sujjada a gare shi.
Shi dai boka sharubu yakasance garjejen kato mai ƙirar samudawan farko, fuskarshi mummuna ce mai cike da kwarjini, Idanuwanshi jajaye ne tamkar garwashin wuta, hancinshi faffaɗa ne tamkar mazirari, bakinshi kuwa tafkeke tamkar ƙofar gari, gashin kanshi fari ne sol, ƙasumba da gemunshi baƙaƙe siɗik, kuma yana sanye cikin wata irin gagarumar shigar yaƙi ta baƙin sulke tun daga ƙasa har sama.
Haƙiƙa duk inda ake neman gwarzon mayaƙi boka sharubu ya cika, domin babu wata halitta mai numfashi da za ta yi arba da shi face ta ɗimauce.
Boka Sharubu ya bushe da dariya a karo na biyu Sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko ma shi da saƙon mutuwa ya dubi su sarki Baddadul-arus a lokacin da suka ɗago daga sujjadar ya ce da su "Ya ku waɗannan sarakuna ku yi sani cewa a rayuwa babu wata halitta da ta taɓa taimako na kamar ku, haƙiƙa ina mai tabbatar maku da cewa zan cika maku burikan ku na ɗauko littafin SIIHIRTACCEN KUNDI domin mallakar takobin sihirin sarkin bokayen duniya.
Na rantse da rayuwa da mutuwata idan har aka yi ganganci na dawo duniya domin sake Sabuwar rayuwa sai na zamo wa duk wata halitta gobarar daji.
Ko da gama faɗin hakan sai boka Sharubu ya sanya hannunshi na hagu ya shafi damtsenshi na hagu wani dogon mashi na sihiri ya bayyana ya nuna su Baddadul-arus da tsinin mashin, take su ka ji wani irin gagarumin ƙarfi ya shige su, duk wata lalura da ke jikin su ta fice,
Sannan ya sake nuna su karo na biyu take dukkanin su suka ɓace ɓat tamkar ba su taɓa wanzu ba.
Wannan shi ne abin da ya faru da su sarki Baddadul-arus a cikin kogon Garul-Shimshan mafakar dukkan wata musiba a duniya.
*****
Al'amarin su jarumi Humairu kuwa, Sai da Humairu ya shafe kwanaki bakwai ya na koyar da gimbiya Mashlira da jama'ar ta yadda ake gudanar da bautar Ubangiji, Tun daga alwala, sallah da karatun Alkur'ani mai tsarki.
Lokacin da gimbiya Mashlira da jama'ar ta suka tsinci kan su cikin sabuwar rayuwa mai cike da tsafta da farin ciki, Sai suka cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa, Yazamana cewa duk wani abu da za su gudanar sai da umarnin shi.
Boka Hushaib, Yarima Muzaifar, Sharilat sai da suka cika da matuƙar mamakin yadda a lokaci guda Humairu ya canza halayen arnar dajin, har da sanya tufafinsu da zamantakewar su.
A safiyar kwana na goma ne bayan jarumi Humairu ya yi wa gimbiya Mashlira da jama'ar ta limancin sallar asuba sai ya sanar da su sarki Himras da su gimbiya Hulaifa cewa yau ne za su yi bankwana da jama'ar birnin arnar dajin domin cigaba da tafiyar su.
Bayan kammala shiri ne sai jarumi Humairu ya naɗa wani dattijo mai suna Abu-damzur da ya ɗara kowa fahimtar addinin Islama a matsayin sabon sarkin birnin arnar dajin har zuwa lokacin da za su dawo daga tafiyar su.
Ko da zartar da hakan sai aljani Narguz ya ya ɗauke su duka ya tashi zuwa sararin samaniya ya na mai tsala matuƙar gudu,
A halin yanzu dai tafiya ta koma ta mutum tara saɓanin huɗu, wato sarki Himras, yarima Muzaifar, tsoho kuhairu, jaruma Sharilat, gimbiya Hulaifa, boka Hushaib, sarkin yaƙi Nuhairu gimbiya Mashlira da jarumi Humairu.
A na fara wannan tafiya ne jarumi Humairu ya dubi sarki Himras dake zaune daf da yarima Muzaifar ya ce da shi "Ya kai Himras shin yanzu ina za mu nufa kai tsaye?,
Ko da jin wannan tambaya sai Himras ya murtuke fuska tamkar aiko ma shi da WASIKAR MUTUWA ya ce "Ya kai Humairu shin na manta alkawarin da ke tsakanin mu da kai na cewa kana ƙarƙashin kulawar Mashlira ka ga kenan yanzu ita ce ya dace ta yi mani wannan tambaya,
Al'amarin su sarki Himras kuwa sai da suka shafe tsawon Sa'a huɗu suna tafiya a sararin samaniya bisa kan aljani Narguz sannan suka iso fadar Sarkin bokayen duniya,
Bayan kowa ya sauko daga kan aljani Narguz sai jaruma Sharilat ta dubi mahaifinta ta ce "Ya abbana a halin yanzu ne ya kamata mu karɓi addinin Humairu domin buɗewar idanuwanka kafin mu shiga fadar Sarkin bokaye".
Da jin wannan batu sai kuhairu ya ce "Zancen ki dutse ya ke 'yata haƙiƙa kin kawo magana mai kyau, Yanzu sai ki je ki sanar ma shi da hakan.
Ko da jin wannan batu sai Sharilat ta juya ta nufi inda Humairu ya ke tsaye ta dube shi ta ce "Ya Sarkin Sadaukai kuma jarumin jarumai ka yi sani cewa a halin yanzu ni da mahaifina mun amince mu karɓi addininka, yanzu ma haka shi ne ya ce na zo na same ka.
Ko da jin wannan batu daga bakin Sharilat sai fuskar Humairu ta faɗaɗa da murmushi ya juya ya shige gaba Sharilat na biye da shi suka durfafi inda kuhairu ya ke tsaye.
Suna isa inda kuhairu ya ke sai jarumi Humairu ya ɗaga hannunshi sama yana mai cewa "Ya Ubangijin halitta don tsarkin mulkinka ka buɗe idanun wannan bawa naka kuhairu ka ba shi lafiya.
Haƙiƙa Ubangiji shi ne mai yiwa bayinshi komai ba wani abun halitta ba, Humairu na kammala yin wannan addu'a sai idanun tsoho kuhairu suka buɗe tarwai tamkar bai taɓa yin makanta ba,
Saboda matuƙar farin ciki Sharilat bata san sa'adda faɗa bisa ƙirjin mahaifinta ba suka rungume juna cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.
Duk wannan abu da ke faruwa tsakanin Humairu da su kuhairu su sarki Himras suna tsaye a gefe guda suna kallo cike da matuƙar mamaki,
Amma a ɓangaren Himras kuwa zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar za ta ƙone,Abu na farko da ya faɗo ma shi a rai da ya fusata shi shi ne haƙiƙa buɗewar idanuwan kuhairu abu ne mai haɗari a gare shi, domin ya kowa sanin wane ne kuhairu,
Abin tambaya a nan shi ne yaushe kuhairu da Sharilat suka yanke wannan shawarar Ba tare da sun ne mi izinin shi ba?.
Amsar tambayoyin da Himras ya kasa bawa kanshi kenan zuciyarshi na cigaba da yi ma shi ƙuna,
Wani tunani da ya faɗo ma sa a yanzu ma shi ne tabbas buɗewar idanuwan kuhairu zai iya janyo zuciyar yarima Muzaifar zuwa addinin Musulunci.
Sai da Sharilat da mahaifinta suka ɗauki tsawon lokaci a rungume da juna, sannan daga bisani kuhairu ya janye jikinshi daga na ta ya dubi Humairu da Idanuwanshi fuskarshi cike da annuri ya ce "Ya kai jarumin jarumai ka yi sani cewa a shirye mu ke mu karɓi addininka domin cika ma ka alƙawari".
Ko da jin wannan batu sai Humairu ya karanta kalmar shahada, kuhairu da Sharilat suka maimaita take ya yi kabbara domin nuna godiyar shi ga Allah SWT.
Ko da sarki Himras ya ga cewa kuhairu da 'yarshi sun karɓi Musulunci sai ya fusata ainun ya nufe su ya na isa gare su ya dube su ya ce "Ya kai kuhairu haƙiƙa kun tafka babban kuskure da kuka karɓi addini Humairu yanzu ta ya ya zamu iya shiga fadar Sarkin bokaye har mu ɗauko TAKOBIN SIHIRI.
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Himras sai kuhairu ya murtuke fuska tamkar an aiko ma shi da wasikar mutuwa ya dube shi ya ce "Ya kai wannan sarki ka yi sani cewa wannan abu da ka tuhume mu baya daga cikin sharaɗin tafiyar mu tare da ku, saboda haka wannan abu bai shafe ka ba".
Ko da jin wannan batu sai zuciyar Himras ta kama tafarfasa tamkar za ta tsaga ƙirjinshi ta fito waje, ya ji tamkar ya zare takobinshi ya afkawa kuhairu da yaƙi,
Amma sai ya fasa bisa wani tunani da ya faɗo ma shi, tunanin shi ne, ko da su kuhairu sun karɓi addinin Musulunci sun yi aikin banza domin ka na gab da mallakar takobin sihiri da zarar hakan ta faru za su zamo bayin ka sai yadda ka yi da su.
Da wannan tunani ne ya matsa kusa da ɗan shi Muzaifar aka fara kallon-kallon yadda ƙofar shiga fadar Sarkin bokaye ta kasance.
Sarki Himras ya buɗe Sihirtaccen kundi ya shiga karantawa tsawon daƙiƙa ɗari biyu amma babu alamun ƙofar za ta buɗe har sai Himras ya tsagaita da karatun aka yi shiru babu wanda ya ce uffan,
Daga can sai Humairu ya yi gyaran murya ya ce "Ya abokanan tafiyata shin yanzu haka za mu tsaya muna jiran gawon shanu, idan kun amince mani sai na buɗe kofar bisa taimakon Ubangijina,
Da jin wannan batu daga bakin Humairu sai kowa ya yi shiru, ya yin da Humairu ya fahimci cewa babu wani mai jayayya da maganarshi sai ya matsa daf da ƙofar ya karanta sunayen Allah tsarkaka,
Nan fa wani abun al'ajabi ya wakana ai kuwa sai aka ga Humairu ya na tura makekiyar ƙofar fadar da aka yi ta da zallar ƙarfen jauhari mai nauyin gaske wacce inda za a sanya ƙarti majiya ƙarfi mutum hamsin ba za su iya ture ta ba,
Jim kaɗan bayan buɗewar ƙofar sai a ka ga wani irin farin haske baban mamaki ya ratso daga cikin fadar.
Ba tare da fargabar komai ba sarki Himras ya kunna kai izuwa ciki hannunshi na hagu ɗauke da Sihirtaccen kundi na daman kuwa rike da wata sharbebiyar takobi,take Yarima Muzaifar,boka Hushaib, gimbiya Hulaifa, gimbiya Mashlira, Sarkin yaƙi Nuhairu,aljani Narguz suka mara mashi baya, jaruma Sharilat tsoho kuhairu da jarumi Humairu ne a ƙarshe,
Aka fara tafiya babu sassauci nan fa aka dunga ganin abubuwan al'ajabi nau'i daban-daban.
Tabbas na zaune bai ga gari ba, haƙiƙa fadar sarkin bokaye ita ce ƙarshen aljanna duniya,
Gimbiya Mashlira ce ta yi wannan furuci a ranta batare da ta furta wani ya ji ba,
Nan fa kowa ya sha jinin jikinshi bisa ganin yadda shiru ya wanzu a fadar tamkar babu wani abu mai numfashi a cikin ta,
Duk sa'adda ɗaya daga cikin tawagar ya ajiye ƙafarshi ɗaya sai ka ji ƙarar takun sawun ya mamaye fadar.
Da ga cikin waɗansu ɓangarori a fadar na ɗauke da waɗansu gumaka da aka sassaƙa su da surorin dodanni da miyagun aljanu, Duk da kasancewar su a sandare suke sai su sarki Himras suka ji hankulansu sun dugunzuma ainun,
Tsawon lokaci ana cikin wannan tafiya kwatsam sai ganin fadar ya fara tsagewa wani irin ƙara da rugugi tamkar aradu ya fara bayyana, Ba shiri kowa ya ja ya tsaya aka shiga lalle kalle da dube-dube domin ganin mene ne zai faru,
Jim kaɗan kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu miyagun samudawan dakaru na ratsowa daga cikin garun fadar tamkar yadda ruwa ke tsattdafo wa daga cikin ƙarƙashin ƙasa,
Su dai dakarun sun kasance daga ƙugunsu zuwa yatsun ƙafafuwansu suna da jiki ne irin na gwaggwan biri, a tsakiyar kawunansu suna ɗauke da wani ƙaho irin na ɓauna, a gwiɓin hammatarsu hagu da dama suna ɗauke da fuka-fukai irin na tsuntsun batoyi, idanuwansu jajaye ne tamkar garwashi a hannayensu suna ɗauke da waɗansu sharɓa-sharɓan takubba na haske.
Haƙiƙa Waɗannan dabaru sun cika abin tsoro, babu wata halitta mai numfashi da zata arba da su face ta yi nadamar wanzuwar ta a doron duniya,
Nan fa jikkunan su sarki Himras ya kama tsuma saboda matuƙar tsoro, Tsoho kuhairu, Sharilat da jarumi Humairu ne kaɗai ba su razana ainun ba su ma ɗin sirrin kalmar shahada ne ya sanya ba su firge ba,
Domin duk wanda ya ji tsoron Allah sai Allah ya dauke ma shi tsoron halittarshi.
Ko da sarki Himras ya fahimci cewa dakarun ba su da niyyar afka ma su, sai kawai ya kurma ihu ya ɗaga takobinshi sama ya afkawa dakarun ko da ganin hakan sai su yarima Muzaifar suka yi koyi da shi, kuhairu, jaruma Sharilat, Humairu suna ƙwala kabbara da ƙarfi,
Sa'adda dakarun suka ga cewa su sarki Himras sun tunkaro su cikin mugun tanadi sai suka tare su aka yi KARON BATTA aka yamutse da masifaffan yaƙi mai matuƙar muni daban tsoro.
Haƙiƙa KARON MAZA sai 'yan maza, kuma idan jarumta ta haɗu da juriya dole ne KARFIN DAMTSE su yi aiki,
Da a ce mutum na tsaye a wannan waje zai yi arba da irin yawan dakarun sai ya ce su sarki Himras sun taru a radu da ka amma dai masu iya magana na cewa duk wanda ya ƙona rumbunshi ya san inda toka take daraja.
Nan fa ɓangarorin biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta ta gaban kwatance,
Sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana wannan artabu batare nasara ga kowa ne ɓangare ba.
Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankulan su sarki Himras kenan, suka fahimci cewa tabbas idan za a kwana biyu ana wannan artabu waɗannan dakarun ba Za su gaji ba,
Wani abu da ya fi dugunzuma hankulan su shi ne duk sa'adda takubbansu suka sauka a bisa dakarun sai su ji tamkar dutse suka sara ko gezau basa yi sai dai tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara mara daɗin saurare.
A ɓangaren dakarun kuwa sa'adda suka ga an shafe tsawon Sa'a batare da sun samu nasara akan su Himras sai suka cika da matuƙar mamaki kuma suka fusata ainun,
A tsawon wanzuwar su a fadar ba su taɓa yin artabu da halitta mai zafin nama tamkar su sarki Himras ba har yazamana an shuɗe wannan lokaci ba tare da samun nasara ba,
Abin da ya fusata su shi ne taya ya za a ce MAZAN JIYA irin su da suka saba yin bakin artabu a Dajin mutuwa a ce bil'adama ya gagare su hallaka wa,
Ko da suka zo nan a tunanin su sai suka canza salon faɗansu yazamana sun zage damtse wajen kaiwa su sarki Himras miyagun hare-haren fiye da ɗazu.
Faruwar hakan ke da wuya sai labari ya sha bamban domin a halin yanzu dakarun sun fara samun nasarar yiwa su Humairu manyan raunika fiye da shida kowanne na ZUBAR DA JINI,
Sa'adda jarumi Humairu ya fahimci halin da suke ciki sai kawai ya shiga neman taimakon Ubangijin talikai ta hanyar yin kamun ƙafa da tsarkakan sunayen Allah (SWT).
Kafin wani lokaci jiri ya fara ɗibar su sarki Himras sun shiga cikin mawuyacin hali, kafin wani lokaci kowa ya zube a ƙasa magashiyan,
Sai Humairu, Sharilat, kuhairu da Mashlira ne kaɗai ba suke tsaye,
Ko da ganin hakan sai Humairu ya ƙwala kabbara da ƙarfi, ya afkawa dakarun, Al'amarin da ya sanya kuhairu, Sharilat da Mashlira suka ji wani sabon ƙarfi na musamman ya shige su suka rufa ma shi baya aka yamutse da sabon masifaffan yaƙi,
Tabbas duk wanda ya yi imani da Ubangijin halitta sai ya zamo ma shi jin shi da ganin shi,
Ana fara wannan sabon artabu ne sai wani abun mamaki ya fara gudana domin a wannan lokacin duk inda ɗaya daga cikin su Humairu ya sanya a gaba sai dai kaga dakarun na zubewa ƙasa matattu tamkar ana sassabe a gonar auduga.