Showing 45001 words to 48000 words out of 59965 words

Chapter 16 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt

09 Dec 2024

9369

Har Mashlira ta huɗi baki da nufin ta ce wani abu sai sarki Himras ya tari numfashin ta fuskar shi a murtuke babu annuri ya ce "Ya ke Mashlira kiyi sani cewa ni da 'yan uwana za mu iya yaƙar mahaifin ki da jama'ar shi har mu ceto rayuwar sauran abokan tafiyar mu batare da mun nemi taimakon wannan jarumi ba don haka sai ki zo mu tafi ko.
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Himras sai gimbiya Mashlira ta dube shi a nutse ta ce "Tun da kunga dukkan abin da ya faru tsakani na da baƙon jarumi to ai babu bukatar na sake wani bayani domin tattaunawar da mu ka yi da Humairu ni kaɗai ta shafa ba ɗaya daga cikin ku ba don haka Humairu na ƙarƙashin kulawa.
"Tabbas masu iya magana sun ce wai ba'a ƙin ta Mutum".
Yarima Muzaifar ya faɗi yana gyara tsayuwar shi.
"Amma ai duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, kuma masu iya magana na cewa tsautsayin akuya gaishe da kura".
Inji sarki Himras".
Ko da gama faɗin hakan sai sarki Himras ya juya ya shige gaba da nufin ya fara tafiya, amma sai jarumi Humairu ya yi zumbur ya shige gaba Mashlira ta bi bayan shi da sauri, Himras, kuhairu na mara mata baya yarima Muzaifar ne a ƙarshe a ka cigaba da tafiya.
Lokacin da aka fara wannan tafiya sai su sarki Himras suka cika da matuƙar mamaki, abin da ya basu mamakin shine yadda Humairu ke ratsa saƙo da lungu na dajin yana bin hanyar da Mashlira ta biyo da su a lokacin da ceto rayuwar daga hannun jama'ar ta, tamkar wanda ya ke bin hanyar a koda yaushe,
Wani abu da ya fi basu mamaki shine yadda tafiyar ke yin sauri.
"Haƙiƙa wannan shi ne zai ceto 'ya ta Sharilat domin na ga yakasance ɗaya cikin Mutanen su tsoho kamzal wato ma'abota addinin Musulunci shin ko Humairu yana da alaƙa ne da Humaira 'yar tsoho kamzal".
Tsoho kuhairu ne ya yi wannan furici a cikin ran shi batare da ya bayyana ba.
Haka dai aka cigaba da wannan tafiya ana ratsawa duwatsu, ƙoramu da kwazazzabai, ana cikin wannan tafiya ne yarima Muzaifar ya lura cewa Mashlira na satar kallon Humairu har ta na yi mashi murmushi mai taushi.
Al'amarin da ya sanya ya ji azababban kishi ya turnuƙe shi, amma sai ya shiga tuhumar kan shi yana mai cewa shin mene ne ya sanya zan yi kishi akan Mashlira bayan cewa ina da tawa abar ƙaunar wato sharilat,
Amsar tambayoyin da ya kasa bawa kanshi kenan ya ce a cikin ran shi wannan shine masu iya magana ke ce "So tsuntsu ne ".



*****
A can birnin arnar daji kuwa, sai da jama'a suka shafe sa'a ɗaya cur a tsaye a kofar fada suna jiran fitowar sarki, sannan suka ga an buɗe gidan sarauta sai ga sarki ya fito tare da tawagar shi shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, zaratan dakaru ɗauke da miyagun makamai na mara mashi baya.
Tun daga nesa jama'a suka fahimci cewa sarki yana cikin matuƙar fushi da alama akwai wani mummunar al'amari da ya faru,
Sai da sarki da tawagar shi suka yi kamar taku goma sannan suka ja suka tsaya, sarki ya yi gyaran murya cikin matuƙar fushi maral-musaltuwa ya yi buɗi baki ya fuskanci jama'a ya ce " ya ku jama'a ta ku yi sani cewa bakomai ne ya haddasa jinkirin fitowa ta daga cikin gidan sarauta ba sai domin wani abun baƙin ciki da ya same mu,
'ya ta mashira ta da na fi so fiye da komai a rayuwa ta ta ci amanata ta tseratar da rayuwar fursunonin da aka farauto mana domin shayar da jinin su ga abin bauta.
Haƙiƙa dole ne ya yanke wa Mashlira hukunci laifin da ta aikata Mani, binciken da na gudanar bisa halarar tsafi ya tabbatar mini dacewa 'ya ta mashira da fursunonin da suna zaune a dajin wannan birni namu,
Saboda haka na fito ne yanzu domin mu farauto su domin bayar da jinin su ga abin bauta, daga nan kuma za'a shiga shagalin ɗaurin auren mu.
Sa' adda sarki shabbar ya zo nan a jawabin shi sai jama'a suka cika da matuƙar baƙin ciki maral-musaltuwa kowa ya shiga faɗin albarkacin bakinshi.
Har sarki shabbar ya buɗe baki a karo na biyu da nufin ya sake furta wani abu sai kawai aka jiyo ihu da kururuwar dakaru masu tsaron ƙofa,
Kafin ayi wani yunƙuri sai aka ga waɗansu irin azababbun kibiyoyi na sauka a wajen jama'a suna hallaka,
Cikin matuƙar fushi sarki shabbar da ya ruga izuwa tsakiyar gari dakaru suka mara mashi baya.
Nan fa wajen ya kaure da guje-guje gami da ifice-ifice ana banke jama'a masu rauni suna faɗuwa ƙasa magashiyan.

****
Sa'adda gimbiya Hulaifa, boka Hushaib da sarkin yaƙi Nuhairu suka fice daga birnin Rum suka nausa izuwa cikin daji suka wanzu suna gudu bisa dawakan su suna ratsa kwazazzabai, sarƙaƙiya da duhuwar bishiyu.
Sai da suka shafe tsawon Sa'a biyar da daƙiƙa hamsin suna wannan tafiya ana cikin halin Gimbiya Hulaifa ta fahimci cewa dawakan su sun fara gajiya, don haka sai ta ɗaga hannunta sama aka tsaya cak domin a yada zango,
Bayan an tsaya ne aka shiga kafa tantuna inda aka tsaya yakasance mai tattare da ni'ima.
Bayan an kammala ne kowa ya shiga na shi tantin ya shiga yin kalaci,
Jim kaɗan bayan kammala hakan sai boka Hushaib ya zira hannunshi a aljihun shi ya ɗauko madubin tsafin shi ya shafe shi da hannunshi na hagu ya shiga gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi sarkin yaƙi na zaune a gefen shi.
Tsawon daƙiƙa hamsin yana gudanar da binciken sai daga bisani ne ya mayar da madubin ya juya ya dubi sarkin yaƙi ya ce "Sai ka taso muje zuwa tantin gimbiya domin akwai wata muhimmiyar magana da zamu yi yanzu".
Boka Hushaib na gama faɗin hakan sai ya miƙe tsaye ya fice daga tantin su sarkin yaƙi ya mara mashi baya cikin hanzari, Lokacin da suka isa bakin tantin sai boka Hushaib ya yi gyaran murya gimbiya ta yi masu izinin shigowa, kai tsaye suka kunna kai ciki suka samu waje suka zauna bisa shimfiɗa, a wannan lokaci gimbiya Hulaifa na zaune a bisa gado ta tanƙwashe kafafuwanta, bayan shiru ya wanzu a tsakanin su na wani lokaci sai boka Hushaib ya yi gyaran murya ya ce " ya shugaba ta ki yi sani cewa binciken da na gudanar bisa halarar tsafin ya tabbatar mani da cewa baza mu taɓa mallakar takobin sihiri ba domin samun sassaken bishiyar Shajarul-kair ba sai mun nemi taimakon wani jarumi ma'abaocin addinin musulunci wanda zai mallako mana duka abubuwan biyu a cikin kwanaki ɗari kacal kafin jama'ar birnin mu su hallaka daga Annobar fari da cutuka,
Sai dai binciken bai bayyana mani inda jarumi ya ke ba kin ga kenan akwai buƙatar mu kwana a wannan waje domin mu gano inda zamu sadu da jarumin ".
Lokacin da boka Hushaib ya zo nan azancen shi sai gimbiya da sarkin yaƙi suka cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.
Wannan shi ne abin da ya wakana da su gimbiya Hulaifa akan hanyar su ta nemo maganin da zai warkar da al'ummar birnin su.


****
Lokacin da aka ruguntsume da azababban yaƙi tsakanin su sarki Baddadul-arus da hadimin boka sharubu wato wannan narkeken Aljani a cikin kogon Garul-Shimshan.
Sai sarki Baddadul-arus, Uzaima, sarki Huraisu, Hadimi shaibat da aljani zamzaru suka wanzu suna kare miyagun hare-haren da aljanin ke kawo masu na naushi da bugu, duk sa'adda da ya kai masu naushin suka zille duk abin da hannun shi ya nausa sai kaga ya tarwatsa ya yi bindiga koda dutse ne idan kuwa a ƙasa ne sai kaga ƙasar wajen ta zaftare ta haddasa katon rami mai kamu goma,
Nan fa yazamana cewa halitta guda ɗaya jal ta zamo GOBARAR DAJI tsakanin ZARATAN MAYAƘA biyar, yawan su ya zamo a banza, kuma suka tashi hankalin kogon dutsen baki ɗaya tamkar zai tsage ya rugeje.
Sai aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana wannan artabu batare da su sarki Baddadul-arus sun samu nasarar fitarwa aljanin jini b, haka shi ma bai samu nasara akan su ba, a zahiri ga duk wanda ya ke kallon yadda artabun ke wakana dole ne ya tabbatar da cewa aljanin ya fi su Baddadul-arus ƙarfin damtse da juriya domin kafin su kai mashi hari sau uku ya kai ma su goma.
Wohoho! Haƙiƙa KARON MAZA sai GWARAZAN JIYA da suka saba gwagwarmaya a GUMURZUN SHEKARA DUBU da ZARATAN MAYAƘA ke FARAUTAR MAZAJE domin Cinye GASAR JARUMTA domin zamowa GOGA SHA FAMA,
Tabbas idan juriya da naci suka haɗu waje guda jarumta ta haɗu da Gwarzontaka dole ne artabu ya zamo tashin hankali da ban tsoro,
Babu abin da zai tayar da hankalin mutum fiye da yadda jaruman shida ke bawa hammata iska domin hallaka juna.
A wasu lokutan su sarki Baddadul-arus har daka tsalle sama suke yi su kaiwa aljanin hari Sannan su diro ƙasa bisa diga-digansu cikin gwaninta.
Ana cikin wannan gumurzu ne sarki Baddadul-arus ya daka tsalle tamkar an harba shi daga cikin baka, yana saman ya zare ya kaiwa aljanin sara bisa sa'a sai ya same shi a fuska ya yi mashi wani lafcecen rauni jini ya yi tsartuwa.
Ya yin da aljanin ya ji raɗaɗi a fuskarshi kuma ya ga jini na zuba sai kawai ya shammaci Baddadul-arus ya gabza mashi naushi a fuska a lokacin da yake kokarin dira ƙasa, take ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya ya bugu da saman kogon, sannan ya faɗo ƙasa fuskar shi ta daddauje jini na zuba cikin mawuyacin halin da ke tsakanin RAYUWA DA HALAKA.
Kafin su gimbiya Uzaima su yi wani yunƙuri aljanin ya daki wani bangare a kogon ya zaftare ya faɗo kansu ya danne su,
Ko da samun wannan gagarumar nasara sai aljanin ya matsa daf da inda suke ƙwance ya daga ƙafarshi domin ya murƙushe su su hallaka.


****
Sa'adda sarki shabbar shugaban arnar daji tare da tawagar dakarun shi suka riga zuwa bakin Kofar gari ɗauke da miyagun makamai a hannayensu sai suka hango gimbiya Mashlira da su sarki Himras a tsakiyar dakaru suna hallaka su.
Cikin matuƙar fushi sarki shabbar shabbar ya falala da azababban gudu izuwa gare su yana mai kwarara wawan ihu lokacin da ya rage bai huce saura taku goma tsakanin su ba sai ya daka tsalle sama tamkar an harba shi daga cikin baka ya sauka a daf da inda gimbiya Mashlira ta ke tsaye ya dube ta cikin matuƙar fushi a lokacin da Idanuwanshi suka kaɗa su ka yi jawur ya ce "Ya 'yata ban taɓa tsammanin cewa zaki haɗa kai da maƙiya na domin cutar da ni ba har ki ci amana ta,
Shin kin manta ne cewa ke kaɗai ce kika rage mani a cikin zuri'a.
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki sai Mashlira ta dube shi babu alamun nadama a fuskarta ta ce "Ya abbana kayi sani cewa bakomai ne ya sanya na juya maka baya ba sai saboda irin baƙin zaluncin da ka ke aiwatar wa a wannan birni namu na ɗauki tsawon lokaci ina roƙon abin bauta ya kawo ƙarshen wannan ɗabi'a taka".
Kafin Mashlira ta gama rufe bakinta sarki Shabbar ya kai mata wawan mari a fuska, cikin baƙin zafin nama ta sunkuya hannun domin kaucewa amma sai da hannun sarki ya shafi gefen kuncinta nan take ta yi adungure ta kife a ƙasa,
Amma sai ta miƙe tsaye zumbur ta kaiwa sarki sara da takobin ta, cikin baƙin zafin nama sarki ya sanya takobin shi ya kare harin tartsatsin wuta ya tashi da ƙara mara daɗin saurare.
Nan take suka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar muni daban tsoro suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta.
A dai-dai wannan lokaci ne dakarun sarki shabbar suka afkawa su sarki Himras aka yamutse da masifaffan yaƙi, mai matuƙar muni ihun mazaje, ƙarar karafniyar ƙarafa gami da haniniyar dawakai ta cika dodon kunne, jini ya dunga kwaranya yana tsartuwa yana kwaranya a ƙasa,
Sassan jikkunan bil'adama suka dunga shawagi a sararin samaniya suna zubowa kasa tamkar ana ruwan su ne daga saman, ƙura kuwa ta turnuƙe sararin samaniya saboda yadda dawakai ke yin dudufniya kofatunsu na kartar ƙasa.
Duk inda sarki Himras, Yarima Muzaifar da tsoho kuhairu suka sanya a gaba sai dai kaga dakarun arnar dajin na zubewa ƙasa matattu.
A ɓangaren Humairu ma'abocin addinin Musulunci kuwa lokacin da ya ƙwala kabbara sai ya tari abokan gaba ya wanzu yana ragargazar su da tsagwaron ƙarfin damtsenshi batare da ya zare makami ba duk inda ya sanya gaba sai dai kaga fili fetal dakarun sun zube ƙasa matattu wasu cikin mawuyacin halin da ke tsakanin RAYUWA DA AJALI.
Inda ace mutum zai ga yadda Humairu ke yin yaƙin dole ya jinjina mashi ya tabbatar dacewa ya cika SARKIN SADAUKAI,
Domin duk tsananin yawan dakarun arnar dajin da zafin naman su ya tashi a banza domin sun kasa samun nasarar koda lakutar jikin shi,
A wannan lokacin arnar dajin ƙara tuttuɗowa suke daga kowa ce kusurwa a birnin akan raƙumi, giwaye da dawakai ta gabas, yamma, kudu, arewa, ɗauke da makamai kuma mazan su da matayen su.
Tun daga nesa arnar dajin suka lura da cewa Humairu ya fi yi masu ɓarna, don haka sai kaso huɗu bisa bisa shidan su suka taru akan shi domin yi masa rufdugu.
Shi kuwa sai ya wanzu a tsakanin su tamkar wani shaiɗani duk wanda ya gabzawa naushi a fuskar shi sai kaji ya kurma ihu ya faɗi ƙasa, a wasu lokutan har dawakan su ya ke haɗawa.
A ɓangaren sarki shabbar da 'yar shi Mashlira kuwa sun wanzu suna bawa hammata iska, ana fara wannan artabu ne Mashlira ta fara gane cewa tabbas shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin ƙarfin damtse da gwanintar yaƙin mahaifin ta ya nunka na ta sau goma, idan ya kai mata hari ta sanya takobi za ta kare sai kaga har durƙushewa ƙasa take yi.
Kafin shuɗewar wasu daƙiƙu sarki ya rikita ta da hare-haren shi yazamana bata iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kai.
A wasu lokutan idan shabbar ya kai mata sara ta kare har faɗuwa ƙasa ta ke yi amma saboda juriya da naci irin na MAZAJEN DUNIYA sai ta miƙe tsaye a cigaba da fafatawa.
Ana cikin wannan hali ne shabbar ya shammace ta ya make takobin da ke hannunta sannan ya gabza mata wawan naushi a fuska ta yi sama tamkar an janye ta ƙugiya sannan ya faɗo ƙasa magashiyan jini na zuba daga bakinta da hanci.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai sarki shabbar ya bushe da dariyar mugunta sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da saƙon mutuwa ya taka ƙafafuwan shi har izuwa inda 'yar shi Mashlira ke kwance magashiyan ya dube ta cikin matuƙar takaici da baƙin ciki ya ce "Ya ke 'ya ta haƙiƙa kin tafka babban kuskure da kika fafata yaƙi da ni shin kin manta ne cewa ni ne na fi kowa ne jarumi ƙarfin damtse a cikin birnin mu, ke kan ki dukkan sirrikan tsafin da kike taƙama da su daga gareni kika same su,
Yanzu ba tare da ɓata lokaci ba zan yanke maki hukunci dai-dai da laifin da kika aikata.
Ko da gama faɗin hakan sai sarki shabbar ya karanta dalasiman tsafi ya nuna Mashlira da ɗan yatsanshi na hagu take waɗansu irin igiyoyin tsafi suka ɗaure hannaye da ƙafafuwanta, sannan wata bulalar sihiri ta bayyana ta shiga zane ta a dukkan sassan jikinta,
Duk inda bulalar ta sauka a jikinta sai ta kurma saboda matuƙar raɗaɗin da ta ke ji.
Sa'adda jarumi Humairu da ke tsaye a cikin abokan gaba ana gwabza yaƙi ya hango abinda ke wakana tsakanin Mashlira da mahaifinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login