Showing 48001 words to 51000 words out of 59965 words
Chapter 17 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt
sai kawai ya shiga neman taimakon Ubangijin musulunci a cikin ran shi, kawai sai ya falfala da azababban gudu yana mai make dakarun da ke gaban shi yana samarwa kan shi hanya domin ya isa inda sarki shabbar ya ke.
Lokacin da sarki shabbar ya hango shi sai ya rugo gareshi yana mai ƙwala kabbara da ƙarfi kawai sai shi ma ya rugo gare shi domin tarar juna,
Lokacin da ya rage saura taku goma tsakanin su sai ya daka wawan tsalle ya sauka a daf da inda Humairu ya ke ya kai mashi sara da dukkan ƙarfin shi.
Cikin baƙin zafin nama Humairu ya sunkuya takobin shabbar ta sari iska, sannan suka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban sha'awa,
Suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta ta gaban kwatance.
Wohoho haƙiƙa duk wanda Allah ya ba shi jarumtaka ya huta domin komai hassadar Mutum idan ya ga yadda Humairu ke kare hare-haren shabbar dole ya jinjina mashi ya tabbatar da cewa ya cika SARKIN SADAUKAI.
Sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana wannan artabu babu sassauci amma shabbar bai samu nasarar lakutar jikin Humairu.
Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa shabbar kai kenan kuma ya fusata shi,
Abin da ya bashi mamaki shine ya a ka yi a matsayin shi na Gwarzon mayaƙi da ya saɓa gwagwarmaya da ZARATAN MAYAƘA amma wannan jarumi ya gagare shi,
Shin dama a wannan nahiya akwai wani jarumi da ya kai shi ƙarfin damtse,
Abin da ya fusata shi shin ne ya za a ce gwarzon mayaƙi Kamar shi wani jarumi ya wanzu a gaban shi ya gagare shi hallaka.
Lokacin da sarkin arnan dajin yazo nan a tunanin shi sai ya zurfafa cikin Kogin tunani domin samun mafita, koda samun mafitar sai ya shiga yin amfani da karfin sihirin tsafin shi a inda ya dunga turawa Humairu miyagun abubuwa, idan ya tura mashi cuta sai Humairu ya karanta addu'a ya tofa take wutar zata nace ɓat ta zama hayaƙi, idan kuwa ya tura mashi kibbau kafin su isa inda ya ke sai su narke su ɗige a ƙasa.
Haƙiƙa duk wanda Allah ya yarda da shi sai ya zamo garkuwa a gare shi, domin wasu lokutan ma wutar har kama tufafin Humairu take amma bata tasiri.
Sai da sarki Shabbar ya gama amfani da dukkanin sirrikan tsafin shi domin ganin ya cutar da Humaira amma babu nasara, al'amarin da sanya ya fusata ainun kenan ya ja da baya yana haki tamkar mayunwacin zakin da ke shirin tunkarar DANDAZON MAYAƘA ya yi wurgi da takobin shi gefe gudu kawai sai ya sanya hannayenshi biyu ya tsarga rigar shi gida biyu ya yi wurgi da ita,
Take ƙirjin shi ta bayyana a fili ɗauke da gauraye da layu na sihiri yana da manyan damatsa masu curin tsoka tamkar duwatsu aka cusa mashi a ciki.
Duk da dakewar zuciya irin ta Humairu koda ya yi arba da sarki Shabbar a cikin wannan hali sai da zuciyarshi ta buga da ƙarfi ya tabbatar da cewa yau ya gamu da gamon shi.
Shabbar ya bushe da dariyar mugunta sannan ya dubi Humairu ya ce "Yanzu tun na kasa samun nasara akan ka da makami sai mu gwada 'yar ƙashi ina mai farin cikin sanar da kai cewa yanzun nan zaka zamo gawa.
Koda gama faɗin hakan sai shabbar ya cire layu da gaurayen da ke jikin shi ya yi jifa da su suka ƙone suka zama hayaƙi, sannan ya falfala da azababban izuwa kan Humairu yana mai kurma wawan ihu gami da dunƙule hannayen shi biyu,
Koda ganin hakan sai Humairu ya yi koyi da shi ya ruga izuwa gare shi yana mai ƙwala kabbara da ƙarfi tare da dunƙule hannayen shi,
Ana haɗuwa aka ruguntsume da sabon azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini.
A ɓangaren su sarki Himras kuwa sun wanzu a tsakiyar arnar dajin suna shayar da su azabar KAIFIN TAKOBIN su duk inda suka sanya a gaba sai dai kaga dakaru na zubewa ƙasa matattu tamkar suna sassabe a gonar auduga.
Duk da irin ɓarnar da suke yiwa arnar dajin amma suma sun yi masu manyan raunuka fiye da shida kowanne na zubar da jini, wani abu da ya ɗaure masu kai shi ne Gashi dai kashe arnar dajin suke amma ƙara kwararowa suke daga kowa ne saƙo na birnin mazan su da matan su.
A sannanne su sarki Himras suka fahimci cewa tabbas sun gamu da gamon su, ana cikin wannan artabu ne wani garjejen ƙari ya kaiwa tsoho kuhairu wawan sara a kafaɗar shi.
Cikin wani irin baƙin zafin nama kuhairu ya sanya mashin shi ya kare harin wani tartsatsin wuta ya tashi, kafin katon ya mayar da martani kuhairu ya soka mashi mashin a ƙirji ya billo ta gadon bayanshi, jini ya yi feshi gami da tsartuwa ko shurawa bai yi ba ya sheka barzahu.
Cikin zafin nama irin na gawutattun JARUMAN DUNIYA kuhairu ya cizge mashin na shi ya make fuskokin waɗansu dakaru biyar, take suka baje a ƙasa suna kurma ihu hanci da bakunansu na zubar da jini.
A can cikin gidan sarauta kuwa, al'amarin jaruma Sharilat bayan dakarun arnar dajin sun shigar da ita zuwa gidan sarauta,
Sannan hodar sihirin da aka shaƙama ta bata sake ta ba sai da rana ta hudo ta yi haske, koda buɗe idanunta sai ta tsinci kanta a cikin wata irin ƙasaitacciyar turaka da aka ƙawata ta nau'ikan kayan alatu na jin daɗin rayuwar duniya.
Yayin da ta buɗe idanunta taga an canza mata tufafin dake jikinta an canza ma ta Waɗansu ƙayatattu na sarauta, kuma taga kada ina ciki turakar ɗauke ya ke da barori da kuyangi na ta hidima suna ta kai komo, sai kawai ta yunƙura domin ta buɗe bakinta tayi magana kuma ta tashi zaune amma sai ta ji hakan ya gagara.
Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin ta kenan ta shiga damuwa ainun, abin da Sharilat tun a daren jiya sarki Shabbar ya shayar da ita wani tsumin tsafi ta yadda bazata iya aiwatar da wani abu ba face da umarnin shi.
Sa'adda ta tsinci kanta a cikin wannan hali sai Kawai ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya.
A can filin yaƙi kuwa sarki Shabbar da jarumi Humairu sun wanzu suna kaiwa juna bugu da naushi hannu da ƙafa cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta,
Idan ɗayan su ya kaiwa abokin gwamin shi naushi sai kaga shi ma ya mayar da martani cikin matuƙar zafin nama,
Wohoho haƙiƙa artabun Manyan Mazaje daban ya ke da na ƙananan kwari inda ace mutum zai ga yadda jaruman ke naushi da bugun juna sai ya rantse cewa jikkunnan su ba su kasance na jini da tsoka ba.
Ana cikin wannan artabu ne sarki Shabbar ya shammaci Humairu ya ciri wata wuta siririya mai ɗauke da guba ya caka ma shi a gefen cikinshi ta shige ciki,
Humairu ya ƙwala kabbara da ƙarfi sakamakon raɗaɗi da zugin da ya ji.
Kafin ta sake yin wani yunƙuri Shabbar ya taƙarƙare ya haure shi da ƙafa a ciki, Saboda ƙarfin dukan sai da Humairu ya yi katantanwa sau biyu a tsaye sannan ya faɗi ƙasa magashiyan yana mai dafe cikin shi yana turmutsutsu.
Ko da samun wannan gagarumar nasara sai sarki shabbar ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta sai da ya yi ta ishe shi sannan ya murtuke fuska tamkar an aiko ma shi da saƙon mutuwa, ya taka da ƙafafuwanshi har zuwa inda Humairu ke kwance ya raba ƙafafu a kan shi ya dube shi cikin murmushin mugunta ya ce "Shi yaƙi da ka ke gani ɗan zamba ne ai dama na faɗa maka bazaka samu nasara akai na ba yanzu zan maishe ka gawa.
Gama faɗin hakan ke da wuya sai sarki Shabbar ya ɗaga hannunshi ɗaya izuwa sama wani zabgegen gatari na sihiri ya bayyana a gare shi, kawai sai ya ɗaga gatarin domin ya datse wuyan Humairu,
Al'amarin da ya jefa tausayi a zuciyar gimbiya Mashlir kenan ta shiga zubar da hawayen baƙin ciki.
*****
Lokacin da ya rage saura taku biyu aljanin ya isa inda su Sarki Baddadul-arus suke na da nufin ya talitse su, kwatsam bazato babu tsammani sai Baddadul-arus ya miƙe tsaye zumbur ya zare wata sharbebiyar takobi a damtsenshi ya sokawa aljanin a cinyarshi ta hagu jini ya yi tsartuwa ya kurma wawan ihu.
Kafin ya yi wani yunƙuri Baddadul-arus ya dako tsalle tamkar an harbo shi daga cikin baka yana saman ya zare ƙananun wuƙaƙe masu kaifin gaske ya soka a idanuwan shi, take jini ya dinga kwaranya tamkar an ɓalle kan fanfo, take aljanin ya faɗi ƙasa rikica! tamkar an jefar da toron giwa ko shurawa bai yi ba.
Cikin gwaninta sarki Baddadul-arus ya sauka bisa turba, sannan ya matsa izuwa inda gimbiya Uzaima ta ke kwance magashiyan ya shiga ƙoƙarin ture dutsen da ya danne su, da ƙyar da siɗin goshi ya ture dutsen sannan ya sa ke faɗuwa ƙasa a galabaice.
Cikin hanzari aka ɗauko jakar guzuri Kowa ya sanyawa raunukan shi magani, kuma aka yi kalace bayan kowa ya samu nutsuwa ne sai sarki Baddadul-arus ya dubi kowa ɗaya-bayan-ɗaya sannan ya yi gyaran murya ya ce "Ya ku abokai na tafiya ta ku yi sani cewa duk da a halin yanzu a matuƙar galabaice mu ke sakamakon artabun da mu ka yi da wannan aljani, amma yazama wajibi mu cigaba da tafiya domin isa inda kushewar boka Hushaib ta ke".
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki sai hadimi Shaibat ya dube shi cikin alamun matuƙar damuwa ya ce "Ya shugabana shin kana ganin cewa idan aka cigaba da tafiyar ɗaya daga cikin mu bazai rasa rayuwar shi kuwa ?.
Sa'adda Baddadul-arus ya ji wannan tambaya daga bakin Shaibat sai ya dube shi ya ce "Ya kai Shaibat shin ka manta cewa a halin yanzu abokan gabar mu suna biye da mu a kowa ne hali su na iya cinma na baka tunanin cewa za a iya yin abun nan da masu iya magana ke cewa "kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi" na fi ka sanin wane ne sarki Himras da makircin shi".
Da zafi-zafi a kan doki ƙarfe ina ji masu iya magana".
Sarki Huraisu ya yi wannan furici yana duban Shaibat.
Kafin wani ya sake furta wani abu Baddadul-arus ya miƙe tsaye zumbur ya zare wata sharbebiyar adda a gadon bayanshi ya sake kunna kai izuwa cikin kogon, ko da ganin hakan sai sarki Huraisu, Uzaima, hadimi shaibat su ka yi koyi da shi suna masu mara ma shi baya da sauri aljani zamzaru a ƙarshe aka cigaba da tafiya.
Sai da aka shuɗe sa'a ɗaya ana tafiya a cikin kogon Garul-Shimshan, sannan aka iso kushewar boka sharubu, Ita dai kushewar an gina ta ne da zallar farin gilashi mai ƙyalli an ƙwata ta da da zinare, jauhari da lu'ulu'u, wani irin farin haske na musamman ya gauraye wajen baki ɗaya ta yadda ko da allura ce ta faɗi da mutum ya duba zai ganta,
Saman ƙabarin an sanya wani narkeken murfi da aka yi shi da zunzurutun ƙarfen jauhari mai nauyin tsiya, inda za a sanya ƙarti majiya ƙarfin mutum hamsin baza su iya buɗe murfin ba, kuma murfin yana ɗauke da wani kwaɗo na musamman.
Ya yin da aka yi arba da kushewar sai kowa ya sha jinin jikin shi,
Sarki Baddadul-arus ya matsa kusa da inda kushewar ta ke ya sanya addar shi ya sari kwaɗon dake jikin murfin da dukkan ƙarfin shi, amma bisa mamaki sai ya ga ko motsi bai yi ba,
Abu Kamar wasa sai da sarki ya shafe daƙiƙa hamsin yana saran mukullin amma shiru babu labari har ya tara zufa yana haki.
Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin kowa kenan ya shiga damuwa ainun,
Sarki Huraisu ya matsa kusa da Baddadul-arus ya dube shi ya ce "Tun da yanzu ka gaza samun sa'a sai ka ba ni na gwada tawa sa'ar.
Ko da jin wannan batu sai Baddadul-arus ya ja da baya yana haki da huci, Huraisu ya ƙurawa murfin idanu yana nazari tsawon lokaci.
Daga bisa ya juya ya dubi Baddadul-arus ya ce "Bisa nazari da na yi baza mu iya buɗe wannan kwaɗo ba face mun ɗauko wani mukulli a cikin wannan kogo".
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Huraisu sai Baddadul-arus ya ce "Zancen ka dutse tabbas dole mu nadama neman wannan mukulli tun da babu damar na gudanar da bincike bisa halarar tsafi na domin na gano inda mabudin ya ke.
Sa'adda sarki Baddadul-arus ya zo nan azancen shi sai ya kunna kai izuwa cikin kogon Garul-Shimshan aka cigaba da tafiya.
Ana cikin wannan tafiya ne kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga ƙasa ta na motsawa wani irin tiririn ɓakin hayaƙi yana sirnamowa daga cikin ta, sannu a hankali hayaƙin yana canza launi har ya rikiɗa izuwa wata irin shirgegiyar maciji mai kawuna casa'in da tara,
kowa ne kai ɗaya ya kai girman namijin zaki kowa ne baki na furzar da dafi,
A bisa saman kawunan akwai wani kai guda ɗaya da ya kasance na bil'adama mai ɗauke da jajayen idanu, hanci, gami da baki masu matuƙar muni gami da ban tsoro.
Sa'adda sarki Baddadul-arus, Uzaima, Shaibat, sarki Huraisu da aljani zamzaru suka yi arba da macijiyar sai cikin su ya duru ruwa, har Shaibat na sakin fitsari a wando saboda da firgici.
Ko da macijiyar ta ga halin da su sarki Baddadul-arus suka shiga sai kawai ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta sannan daga bisani ta murtuke fuska tamkar an aiko ma ta da WASIKAR MUTUWA, ta buɗe baki cikin kakkausar murya mai ban tsoro ta ce " Ya ku waɗannan bil'adama ku yi sani cewa yau fiye da shekaru dubu biyu babu wata halitta walau mutum ko aljan da taɓa shigowa wannan kogo na Garul-Shimshan sai ku,
Na rantse da mai gidana boka sharubu ɗayan ku bazai fita a raye ba, domin kun shigo da kan ku cikin taskar ANNOBA DARI mai wahalar fitarwa,
Ina mai tabbatar maku da cewa daga kan ku babu wata halitta da zata sake kwaɗayin zuwa nan.
Kafin ɗaya daga cikin su ya furta wani abu macijiyar ta kanannaɗe su da jelar kuma waɗannan bakuna nata guda casa'in da tara suka shiga kafta masu sara a sassan jikkunan su.
*****
Kamar yadda boka Hushaib ya faɗawa gimbiya Hulaifa da Sarkin yaƙi Nuhairu haka al'amarin yakasance, wato a daren ranar ya sake gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi inda ya gano cewa ba za su taɓa samun nasarar riskar jarumi Humairu face sun yi tafiyar sa'o'i goma.
Bayan boka Hushaib ya sanar da gimbiya hakan sai kowa ya yi kalace ya kimtsa cikin shi, sannan aka cigaba da tafiya babu sassauci aka wanzu ana ratsa duwatsu tsaunuka da ƙoramu.
Wannan shi ne abin da ya wakana da su boka Hushaib akan hanyar su ta nemo sassaƙen bishiyar Shajarul-kair domin magance cutukan da suka addabi al'ummar su.
*****
Kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga Humairu ya na daga kwancen ya sanya ƙafafuwanshi ya daki sarki a cikin shi da dukkan ƙarfin shi,
Saboda ƙarfin dukan sai da Shabbar ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya sannan ya faɗo ƙasa a matuƙar galabaice jini na zuba a baki da hancinshi addar da ke hannunshi ta faɗi can gefe.