Showing 30001 words to 33000 words out of 59965 words

Chapter 11 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt

09 Dec 2024

9384

Rundunar Abokan Gaba.
A Lokaci Guda Tawagar Biyu Suka Afkawa Rundunar Birnin Rum Aka Rincaɓe Da Azababban Yaƙi Mai Matuƙar Muni, Bantsoro, gami Da Tashin Hankali.
Komai Dakewar Zuciyar Mutum Da Rashin Tsoron shi Idan Yaga Yadda Filin Yaƙin Ya Rincaɓe Dole Ne Ya Firgice, Haƙiƙa Tashin Hankali Ba'a Sa Mashi Rana, Kuma idan Kaji Ana Ga Ƙi Gudu To Sa Gudu ne Bai Zo ba.
Nan Fa Ihun Mazaje Ya Gami Da Ƙarar karafniyar Ƙarafa Ta Cika Dodon Kunne, Kofatun Dawakai Na Kartar Ƙasa Suna Tayar Da ƙura, Jini kuwa Ya Dunga Kwaranya, Tsayuwa, Yana Malala A ƙasa.
Sassan Jikkunan Bil'adama Suka Dunga Washagi A Sararin Samaniya Suna Zubowa A Ƙasa Tamkar Ana Ruwan su ne Daga Saman.
Duk In da Sarki Himras Da Baddadul-arus Suka Sanya A Gaba Sai Dai Kaga Dakaru Na Zubewa Ƙasa Matattu Suna Samar Da Fili Fetal, Tamakar Suna Sassabe A Gonar Auduga.


Nan fa Manyan Sarakunan Biyu Suka Zamo Tamakar GOBARAR ANNOBA A Filin Yaƙin, Yazamana Suna Ƙoƙarin Kutsa kai Izuwa Cikin Birnin.
Wani Abu Da Yake Ɗaure Masu Kai Shine, Gashi Dai Hallaka Dakarun Suke Tamakar kiyasai, Amma Tuttuɗowa Suke Daga Cikin Birnin Tamkar Bazasu Ƙare ba.
A Ɓangaren Birnin Rum Kuwa Sa'adda Sarki Usulul-Haibar, Gimbiya Hulaifa Da Boka Hushaib Suka ga Irin Mummunar Ɓarnar Da Sarakunan Biyu Ke Yi Masu, Sai Zukatansu Suka Fusata Ainun Suka Kama Tafarfasa Tamkar Zata Ƙone.
Cikin Matuƙar Fushi Boka Hushaib Ya Rintse Idanuwanshi Ya Karanto Waɗansu Ɗalasiman Tsafi Gami Da Ɗaga Sandarshi Sama, Faruwar Hakan Keda Wuya Sai Akayi Wata Tsawa Da Walƙiya Sai Ga Waɗansu Irin Tsuntsayen Tsafi Sun Ratso Daga Sararin Samaniya Suna Sauka A Turba.
Cikin Baƙin Zafin Nama Boka Hushaib Yakama Tsuntsun guda Ɗaya Ya Haye, Gimbiya Hulaifa Da Sarki Usulul-Haibar Suka yi Koyi Dashi, Kowannen Su Ya Zare Wasu Makaman A Jikinsu Yazamana Suna Riƙe Da Makamai Biyu.
A Lokaci Guda Tsuntsayen Suka Yunƙura Izuwa kan Su Sarki Baddadul-arus, Suna Kai Masu Miyagun Hare-hare Ta Ko ina Cikin Baƙin Zafin Nama JURIYA DA BAJINTA Suna Ƙoƙarin Hanasu isa Izuwa Birnin.
Nan fa Filin Yaƙin Ya Sake Rincaɓewa Da Masifaffan Artabu Mai Tayar Da Hankali.
Wohoho! Haƙiƙa Duk Mahaluƙin Daya Taɓa Ziyartar Filin Fama Yaga Yadda Mazaje Ke Yin MUTUWAR JARUMTA Rayukan Mutane Na Salwanta Suna Rabuwa Da Gangar Jiki, Haƙiƙa Shine Yaga ma Ganin Tashin Hankalin Da Babu Kamar Shi.
Sai Da Aka Shafe Tsawon Sa'a Uku Cur Ana Wannan Artabu Har Yazamana cewaiSu Sarki Himras Sun Samu Nasarar Kutsawa Cikin Gari Duk bar Su Sarki Baddadul-Arus A Baya Sun Basu Tazara Mai Yawa, Ana Cikin Wannan Artabu ne Sarki Usulul-Haibar Dake Shawagi Akan Tsuntsun Tsafi A Sama Ya Kaiwa Sarki Himras Wawan Hari Da Takobinshi Cikin Nasara Ya Yanke shi A Kafaɗa, Inda Ya Sareshin Ya Haddasa Wani Lafcecen Rauni, Kuma Ya Suɓuto Daga Kan Aljani Narguz.
Ko da Himras Ya Shafa Kafaɗarshi Da Hannunshi Yaji Jini Sai Kawai Ya Taƙarƙare Ya Kurma Wawan Ihu Ya Miƙe Tsaye Zumbur Yayi Jifa Da Takobinshi Ya Cire Wani Makami A Jikinshi Mai Kama Da Lauje Ya Kurma Wawan ihu Ya Falfala Da Azababban Gudu Izuwa kan Usulul-Haibar Yayin da Ya Rage Saura kamar Taku Goma Sai Ya Dako Wawan Tsalle Sama Tamkar An Janye Shi Da Ƙungiya Ya Kaftawa Tsuntsun Da Usulul-Haibar Dake Kai Sara Take Tsuntsun Ya Ɓace Ɓat Tamkar Bai Taɓa Wanzuwa Ba, Usulul-Haibar Ya Faɗo Ƙasa Tim.
Cikin Matuƙar Zafin Nama Da Fushi Ya Miƙe Tsaye Zumbur Ya Riga Izuwa Kan Himras A Lokacin Da Himras Ɗin Ya Rugo Gareshi Makaminshi Na Kartar Ƙasa Yana Fitar Da Wata Koriyar Wuta.
Yayin da Ya Rage Saura kamar Taku Biyu Tsakanin su Sai Kowannen su ya Dako Tsalle Sama Ya Kaiwa Ɗan Uwanshi Sara A Fuska, Cikin Matuƙar Zafin Nama Suka Sanya Makamansu Suka Kare Harin, Sannan Suka Diro Ƙasa Bisa Gwiwoyinsu Suka Cigaba Da Kaiwa Juna Sara Da Suka Cikin Matuƙar Zafin Nama JURIYA DA BAJINTA Ta Gaban Kwatance.
Ana Fara Wannan Artabu ne Sarki Usulul-Haibar Ya Fara Gane Kurenshi Domin Ya Gane Cewa Shayi Ruwa ne Ba Abinci Mai Nauyi ba, Yazamana Daƙyar Yake Iya Mayar Da Martani, Sarki Himras ɗin Kuwa Ya Samu Nasarar Yi Mashi Sara Fiye Da Goma, Duk Sa'adda Makamansu Suka Haɗu Da Juna Sai kaji Wani karai Mara Daɗin Saurare Tamkar An Sanyawa Dutse Nakiya Yayi Bindiga.
A Ɓangaren Tsoho kuhairu kuwa Wani Abin Mamaki ne Ya Faru Domin Duk da Kasancewar Idanuwanshi Basa Gani A Zahiri Amma Sai Yazamana Yana Iya Kare Hare-haren Dakaru Gami Da Mayar Da Martani, Duk Sa'adda Yaki Hari Da Mashin shi Sai Kaga Dakaru Na Zubewa Ƙasa Matattu, Kuma Yana Wurƙilawa Da Zamewa Hare-hare Batare Ya Suɓuto Daga Kan Aljani Narguz ba.


































































Haƙiƙa Babu Wani Bil'adama Ko Aljan Dazai Ga Yadda Tsoho kuhairu ke Yin Wannan Bajintar Face Ya Tabbatar Da Cewa Ya Cika SARKIN SADAUKAI.
Al'amarin Jaruma Sharilat kuwa Ta Wanzu Tana Hallaka Dakarun Sukesu Da Mashinta Suna Faɗuwa ƙasa Matattu.
Da Wannan Dama ne Aljanu Narguz Yayi Amfani ya mangare Dakarun Dake Gabanshi Ya kusa Cikin Birnin, Duk Inda Ya Sanya Gaba Baka Ganin Komai Face Gwarwakin Dakaru Kwance Fulu-Fulu Cikin Jini Babu kyawun Gani.
Haƙiƙa Waɗannan Dabarun Suna Ganin Tashin Hankalin Da Basu Taɓa Ganin Kamarshi ba, kai Hatta Duwatsu, Bishiyu,Dabbobi Haɗe Ƙananan Ƙwari Suna Cikin Wannan Tashin Hankali.
A Ɓangaren Sarki Baddadul-arus, Gimbiya Uzaima,Sarki Huraisu Tare Da Hadimi Shaibat, Sun Wanzu Suna Kare Hare-haren Su Boka Hushaib Dake Shawagi A Saman Su Bisa Tsuntsayen Tsafi, Gami Da Mayar Da Martani Cikin Zafin Nama JURIYA DA BAJINTA.
Sa'adda Su Sarki Baddadul-Arus Ya An Shafe Tsawon lokaci Basu Samu Nasarar Lakutar Jikin Abokan Gwanin su ba, Sai Suka Fusata Ainun Zukatansu Suka Kama Tafarfasa Tamkar Zasu Ƙone, Kawai Sai Baddadul-arus Ya Buɗe Bakinshi Ya Karanto Waɗansu Ɗalasiman Tsafi A lokacin Guda Ya Kaiwa Boka Hushaib Da Gimbiya Sara Da Nufin Tsinke masu Wuya.
Cikin Baƙin Zafin Nama Suka Wurlila Domin Kaucewa Harin, Amma Duk da Sai Da Takobin Ta Zaftare Wani Yanki Na Gashin Kansu, kuma Ta Sauka Akan Fuka-fukan Tsuntsayen Tsafin Da Suke Zaune Akai.

























Nan take Suka Rikito Ƙasa Suna Masu Tsandara Ihu, Makaman Yaƙinsu Suka Faɗi Can Gefe Guda.
A dai-dai Wannan Lokaci ne Sarki Baddadul-arus Ya Lura cewa Su Sarki Himras Sun Basu Tazara Mai Yawa.
Koda Ganin Hakan Sai Ya Fusata Ainun Idanuwanshi Suka Kaɗa Suka yi Jawur, Jikinshi Ya kama Tsuma Yana Kyarma Har Wani Farin Hayaƙi Na Fita Daga Jikinshi.
Kawai Sai Ya Kurma Wawan ihu Ya Daka Tsalle Yana Tafiya A Sama Tamkar yana Tsaye A Turba, Yana Mai Sanya Takobinshi Yana Sare Kawunan Dakarun Sarki Usulul-Haibar Suna Zubewa Ƙasa Matattu.
Koda Ganin Haka Sai Gimbiya Uzaima Da Sarki Huraisu Suka Dako Wawan Tsalle Daga Kan Aljani Zamzaru Tamkar An Harbosu Daga Cikin Baka, A Dai-dai Lokacin Da Boka Hushaib Da Gimbiya Hulaifa Dake Kwance Suka Miƙe Tsaye Zumbur, Suka Zare Sabbin Makamai A Jikinsu Suka Tari Su Gimbiya Uzaima Aka Kacame Da Azababban Yaƙi Mai Cike Da Al'ajabi.
Nan fa Ihu Da kururuwar Mazaje Haɗe Da Haniniyar Dawakai Suka Cika Dodon Kunne, Jini Ya Dunga Kwaranya,Tsartuwa Yana Kwaranya A ƙasa, Sassan Jikkunan Bil'adama Na Zubewa Ƙasa.
Lokacin Da Aka Shafe Tsawon Sa'a Ɗaya Ana Fafata ƙazamin Artabu Tsakanin Sarki Himras Da Sarki Usulul-Haibar Kawai Sai Himras Ya Shammaci Usulul-Haibar Ya Tafka Mashi Wani Wawan Sara Al Kafaɗarshi Ta Hagu, In da Ya Sare Shin Ya Haddasa Wani Lafcecen Rauni, Usulul-Haibar Ya Kurma ihu Sannan Ya Zube Ƙasa Yana Nishin Wahala NunfashinShi Na Fita Sama-Sama.
Ko da Samun Wannan Gagarumar Nasara Sai Himras Ya Bushe Da Dariyar Mugunta Ya Shafi Wani Gurun Tsafi A Damtsenshi Ya Ɓace Ɓat Daga Filin Yaƙin Tamakar Bai Taɓa Wanzuwa ba.
Bai Bayyana A ko ina ba Sai A Cikin Wani Ƙasaitaccen Ɗaki Ma'abocin Tsawo, Faɗi, Gaba Ɗaya Gininshi An yi Shine Da Waɗansu Duwatsu masu Daraja, Duk In Mutum Ya Kalla A Ciki Babu Abinda Zai Gani Face Kayan Ƙawa Gami Da Alatun Jin Daɗin Rayuwar Duniya Duk Yanar Gizo-Gizo Ta Lulluɓe Su Alamun Dake Nuna Cewa Wata Halitta Ta Daɗe Bata Ziyarci Wajen ba.
Idan Mai Kallon Yakai Duban Shi A Ɗakin Zai Yi Arba Da Wani Gayayyen Tudu Mai Tsawo Da Faɗi Da Akayi Shi Da Zallar Karfe Zinare Da Lu'ulu'u Aka yi Mashi Feshi Da koren Ruwan Yaƙut, Wani Irin Koren Haske Na Zagaye Wajen, Daga Saman Shi Akwai wani Ɗan Madaidaicin Kasko Na Azurfa Mai Ɗauke Da Ruwa Garai-Garai Ruwan Yana Zubowa Kan waɗansu Kyawawan Furanni Dake Gazaye Da Wajen Gwanin Ban Sha'awa.
Bakomai Ba ne Wannan Zagayayyen Tudu ba Face Ƙabarin Boka Aulad Ibn Zumbar Daya Fara Tun Mulki A Birnin Rum Bayan YAKIN DUNIYA na Ɗaya.
Ko da Bayyanar Sarki Himras A Ɗakin Sai Kawai Ya Matsa Daf Da Kabarin Cike Da Matuƙar Farin Ciki Maral-Musaltuwa.
Yana Isa Ya Karanto Waɗansu Ɗalasiman Tsafi Yana Mai Nuna Ƙabarin Da 'yatsanshi Na Hagu Take Ƙabarin Ya Tsage Gida Biyu Wata Ƙofa Ta Bayyana Da A Kayi ta Da Karfen Jauhari Wani irin Farin Hayaƙi Ya Tuttuɗo Daga Cikinta, Batare Da Wata Bargaba ba Sarki Himras Ya Zira Hannunshi A Cikin Ƙofar Sai Gashi Ya Ɗauko Wata Sarƙar Tsafi Da Aka Sana'anta Da Zinare Da Zubar Daju Tana Sheƙi, Walwali Da Ɗaukar Idanun Duk Mai Kallo.
Koda Samun Wannan Nasara Sai Sarki Himras Yayi Kamar Taku Uku Ya Sanya Hannunshi A karo Na Biyu Da Nufin Ya Shafi Gurin Tsafin shi Ya Ɓace Ɓat, Ƙwatsam! Bazato Babu Tsammani Sai Yaji An Gabza Mashi Naushi A Ƙeyarshi, Saboda Ƙarfin Naushin Sai Da Yayi Karantawa Sau Biyu Sannan Ya Faɗi Kasa Tim inda Aka Naushe shin Na yi Mashi Raɗaɗi.
Cikin Matuƙar Fushi Ya Miƙe Tsaye Zumbur Yana Mai waigawa Bayanshi Domin Yaga Wanda Ya Naushe Shin, Yana Waigawar Yayi Arba Dashi Ba Wani ba ne Face Sarki Baddadul-arus Shirye Cikin Gagarumar Shigar Yaƙi Zaune A Ƙasa Ya Tanƙwashe Ƙafafuwanshi Hannunshi Riƙe Da Wani Gabgegen Gatari Na Ƙarfen Jauhari, A Wuyanshi Yana Rataye Da Wata Sarƙa Mai Matuƙar Kama Da Wacce Sarki Himras Ya Ɗauko A Cikin Ƙabarin Boka Aulad, Fuskarshi Cike Da Annuri.
Sa'adda Sarki Himras Yayi Arba Da Baddadul-Arus Sai Ya Cika Da Matuƙar Mamaki Yace A Cikin Ranshi Ya Akayi Baddadul-arus Ya San Dacewa Ina Cikin Wannan Ɗaki, A Ina Ya Samo Waccan Sarƙa Dake Wuyanshi Da Tawa Da waccan Ɗin Wacce Ce Ta Gaskiya?.
Amsar Tambayoyin Da Sarki Himras Ya Kasa Bawa Kanshi Kenan, Nan Take Zuciyarshi Ta Kama Tafarfasa Tamkar Zata Ƙone, Kawai Sai Ya Zare Wata Gabgegiyar Takobi A Damtsenshi A Cikin Kubenta Ya Falfala Da Azababban Gudu Izuwa kan Baddadul-arus Yana Mai kurma Wawan ihu.













































































Yayin da Sarki Baddadul-Arus Ya Hango Sarki Himras Ya Rugo Izuwa Gareshi Yana Kurma ihu Hannun shi Riƙe da Takobi Tsirara, Sai Kawai Ya Taƙarƙare Ya Bushe Da Dariyar Mugunta Sai Da Yayi Dariyar Ta Ishe Shi Sannan Ya Murtuke fuska Tamkar An Aiko Mashi Da WASIƘAR MUTUWA Yayi Wuf! Ya Miƙe Tsaye Ya Ruga Gareshi Domin Tarar Juna, Lokacin da aka haɗu Sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro haɗe da tashin hankali.


Lokacin Da Aka Ruguntsume Da Azababban Yaƙi Tsakanin Sarki Baddadul-Arus da Himras A Ɗakin KUSHEWAR Margayi Boka Aulad, Sai Suka Wanzu Suna Kaiwa Juna Sara Da Suka Cikin Matukar Zafin Nama JURIYA DA BAJINTA Ta Gaban Kwatance.
Duk Sa'adda Makamansu Suka Haɗu Da Juna Sai Dai kaga Tartsatsin Wuta Ya Tashi Gami Da Ƙara Mara Daɗin Saurare, Sai da aka shafe tsawon Rabin Sa'a ana wannan Fafatawa, Har Yazamana Cewa Duk Makamansu Sun Lalace Sun Durƙushe A ƙasa Amma Har A Wannan lokaci Basu Samu Nasarar Lakutar Jikin Abokan Gwaminsu ba.
Al'amarin Daya Harzuƙa Zukatansu Kenan Suka Kama Tafarfasa Tamkar Zasu Ƙone, Suka Faɗa Izuwa Kogin Tunani Domin Samun Mafita.
Abu Na Farko Daya Faɗowa Sarki Himras A rai Shine Me Yasanya ya kasa samun Nasara Akan Baddadul-Arus Bayan Cewa Yana Riƙe Da Sarƙar Tsafi A Hannunshi, Shin ko Sarƙar Jabu ce, wacce ke Sanye A wuyan A Wuyan Baddadul-arus Ita ce Ta Gaskiya.
A ɓangaren Sarki Baddadul-arus Kuwa Abinda Ya Faɗo Mashi A rai Shine Tunda Yanzu Sarki Himras Ya kasa Tantance wacce ce Sarƙar Tsafin Ta Gaskiya Me Zai Hana ka Shamma Ce shi ka kwace Sarƙar.
Sa'adda Sarakunan Biyu Suka Zo Nan A Tunaninsu Sai Suka yi Wurgi Da Makamantansu kuma Duka ja Da Baya Sukayi Cirko-Cirko Ana kallon juna, Tamkar waɗansu zakaru.
Kawai Sai Kowannen su Ya Dunƙule Hannayenshi Ya Ruga Izuwa kan juna Suna ihu Da Kururuwa Mai Firgitarwa, Suna haɗuwa Suka kacame da Sabon Azababban Yaƙi Suna Kaiwa Juna Naushi Da bugu hannu da kafa.
Wohoho! Haƙiƙa Maza Sune Maganin Maza Ana Canza Wannan Salon Faɗane Sai Labari Yasha Bamban, Domin Cikin Abinda Bai Gaza Daƙiƙa Talatin ba Jaruman Sun fara haɗawa juna Jini Da Majina Suna Layi Jiri Na Ɗibarsu.
A wasu lokutan Idan Ɗayansu ya gabzawa Abokin Gwaninshi Naushi Sai kaga ya kife A Ƙasa Amma Sai ya Miƙe Tsaye Zumbur Yana Nishin Wahala, Shi ma ya mayar da martanin.
Lokacin Da Manyan GWARAZAN JIYAn Suka Ga Cewa Ana Yin Kare Jini Biri Jini Ma'ana Karfi Yazo Ɗaya Sai Suka Shiga yin Amfani Da ƙarfin Sihirin Tsafi Suna Turawa Juna Miyagun Abubuwa Domin Hallaka juna
Idan Sarki Baddadul-arus Ya Tura Himras kibiyoyin Shiri kafin Su Isa inda Hirmas ke Tsaye Ya Nuna su Da Ɗanyatsanshi Na Hagu Take Zasu Barke Su Zama Ruwa Su Narke A Ƙasa, Sai Himras Ɗin Ya Turawa Baddadul-arus Bakar Wuta shi kuma Baddadul-arus

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login