Showing 21001 words to 24000 words out of 59965 words
Chapter 8 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt
hashmila sun gaji ainun, kuma raunukan dake jikin su sunyi tsami, Nan take su ka ɓingire su ka shiga sharar barci, koda ganin hakan sai Dattijon da kyakkyawar budurwar suka sanya mayafi su ka lulluɓe su, su ka miƙa tsaye su ka fiye ɗakin su ka janyo kofar ɗakin su ka rufe rufe!.
Sai da Dattijon da 'yar shi uzaima su ka shafe tsawon kwanaki talatin suna kula da su kuhairu, har yazamana raunukan sun warke sumul!, Wata rana da hantsi sarki Kuhairu, Hashmila tare da Dattijon da 'yar na zaune a cikin turakar sai ƙuhairu ya dubi Dattijon yayi gyaran murya sannan ya kawo gwaron numfashi ya ajiye yace,
"Yakai wannan Dattijo ma'abocin tausayi da jin ƙari, idan bazaka damuba ina buƙatar nayi maka waɗansu tambayoyi, Tambaya ta farko shin wane ne kai? Kuma mene ne dalilin da ya sanya ka ceci rayuwarmu?.
Ko da jin waɗannan tambayoyi sai Dattijon yayi shiru yana mai sunkuyar da kanshi ƙasa,daga bisani ya ɗago ya dubi kuhairu yayi gyaran murya a karo na farko yace" Da farko dai sunana kamzal ibn Abbas, wannan budurwa kuwa 'yata ce humaira. Yakai kuhairu ka yi sani cewa bakomai ne yasanya na ceci rayuwarku ba sai domin Amincin da ke tsakanina da mahaifinku sarki saruful-uzwar, A duk sa'adda da yaje farauta yakan zauna anan wajena yayi 'yan kwanaki kafin ya huce, haƙiƙa mahaifin ku mutumin kirki ne, na samu dukkan labarin abinda ya faru tsakanin da ɗan uwanka kuhairu, ina neman alfarma a wajen ki da ku zauna tare da mu da yardar Ubangiji za mu baku dukkan wani jin daɗin rayuwar duniya.
Sa'adda kuhairu yaji wannan jawabi daga bakin Dattijo kamzal sai ya cika da matuƙar mamaki ya dube shi yace" ya amintacce ga mahaifaina haƙiƙa zan riƙe tamkar abbbana kuma zamu zauna a tare da ku har Izuwa ƙarshen rayuwarmu.
Daga wannan furuci ne kowa yayi shiru, kawai sai kamzal ya miƙe tsaye ya shimfiɗa wani buzu da aka yi shi da fatar damisa ya tayar da Sallah yana mai fuskar gabas humaira ya tsaye a bayan shi tana mai yin koyi da shi.
Nan fa kuhairu da Hashmila su ka cika da matuƙar mamaki bisa ganin yadda kamzal da 'yarshi ke gudanar da ibadat su cikin Nutsuwa da annashiwa, saɓanin tasu ta bautar gumaka mai cike da kaɗe-kaɗe da raye-raye.
Tun daga wannan rana ne kuhairu suka kasance cikin farin ciki da su kamzal, idan kamzal zai je farauta tare suke tafiya, idan sun dawo sai Hashmila da humaira suka shiga gyara naman dabbar su gasa kowa yayi kalaci.
A cikin waɗannan kwanaki ne ciki ya bayyana a jikin hashmila, murna a wajen Kuhairu kuwa ba'a cewa komai, domin kwana yayi bai yi barci ba, duk bayan daƙiƙa goma sai ya duba yaga a wane hali Hashmila ke ciki.
Gaskiyar masu iya magana da suka ce Sannu-Sannu bata hana zuwa sai dai adaɗe ba'a je ba, sai gashi cikin Hashmila ya cika wata tara, a wata rana ne da maraice naƙuda ta kamata ta haifi kyakkyawar jaririyarta, sai da kuhairu ya zubar da hawayen farin ciki.
Yayin da mako guda ya kewayo aka raɗa yarinya suna sharilat, sharilat ta taso cikin ƙwazo da hikima, domin tun da tana Shekara tara a duniya ta ƙware ainun a horon yaƙin da kuhairu ke koya ma ta, don haka ko dakarun sumame suka kawo hari ita kaɗai ke fatattakarsu, wannan fa shine masu iya magana ke cewa "Barewa baza tayi gudu ba ɗanta yayi rarrafe".
A lokacin da sharilat ta cika shekaru ashirin ne Dattijo kamzal da mahaifiyarta Hashmila suka rasa rayukansu sakamakon waɗansu miyagun 'yan fashi da su ka kawo musu farmaki,
Su Kuhairu sun yi kukan baƙin ciki tamkar ransu zai fita, bayan mako guda ne humaira tayi bankwana da su domin cika burin mahaifinta na yaɗa addinin Musulunci suna kukan rabu da juna.
Tun daga wannan rana Tsoho kuhairu da 'yarshi sharilat ke zaune a cikin wannan daji cikin ƙuncin rayuwa.
Wannan shi ne dalilin da ya haddasa gaba tsakanin tsoho kuhairu da sarki Himras mahaifin yarima muzaifar.
****
Al'amarin Yarima Muzaifar kuwa Tun Sa'adda ya rabu Da Mahaifinshi Sarki Himras A lambun shaƙawa Bayan Ya Sanar Da sarki Abin da ya Wakana Tsakanin shi Da Jaruma Sharilat.
Sai Kawai Ya Huce Kai Tsaye Izuwa Turakarshi Ya Fara Sharar Barci, Bai Farka ba Har Sai Da Rana Ta hudo, Sa'adda Ya Buɗe Idanuwanshi Ya lura Cewa Ya Makara Wajen Fita Fada, Sai kawai Ya ƙwallawa Wata Kuyanga Kira Mai Suna Shahira.
Shahira Ta Bayyana A Gareshi Ta Zube Ƙasa Ta Kwashi Gaisuwa Cikin Ladabi Kanta A Sunkuye.
Yarima Ya Dube ta Yace" Ya ke Shahira Shin ina Dalilin Rashin Tashi Na Daga Barci?.
Shahira Ka Gafarceni Ya Shugabana Ai Tuni An kai Ruwan Wanka Izuwa Kewaye Kuyangi Suna Can Su na jiranka, Kuma Mai Martaba Ya ce A faɗa Maka Idan Ka Kammala Yana Jiran Ka A Turakarshi Domin za kuyi Kalaci.
Da Jin Amsar Wannan Tambaya Sai Yarima Ya Miƙe Tsaye Daga Kan Gadonshi, Shahira Ta Shige Gaba Domin Yi Ma Shi Jagora, Shi kuwa Na Biye Da ita Su ka Fice Daga Cikin Turakar.
A Can Turakar Sarki Himras Kuwa Yana Zaune Bisa Wata Ƙasaitacciyar Kujera Ta Alfarma A jiye A Gaban Shi Akwai wani Dogon Teburi Mai Ɗauke Da Nau'ikan kayan Ciye-Ciye Da Tanɗe-Tanɗe, wani Irin Ni'imtaccen Ƙamshi Ya Gauraye Turakar Haɗi Da wata Ɗaddaɗar Iska Na Kaɗawa.
Haƙiƙa wannan Turaka Ta Cika Aljannar Duniya Komai Ƙasaitar Basarake Ko Attajiri idan Ya Tsinci Kanshi a Wannan Waje Dole Ya Tabbatar Da Cewa Gaba Da Gabanta, Ko iya Kilishin Da aka shimfiɗe Turkar Abin Kallo ne Ballantana Batun Kayan Kyale-Kyale Waɗansu Ma idanu Basu Taɓa Gani ko Jin Labarin su ba.
Yana Cikin Wannan Hali ne Yarima Muzaifar Ya Turo Kofar Shigowa Turakar, Cikin Matuƙar Farin ciki Sarki Himras Ya Miƙa Tsaye Ya Tare Shi Suka Rungume Juna Fuskokinsu Cike Da Annuri, Sai Daga Bisani ne Sarki Ya ja Hannun Yarima Har zuwa Kan Kujerar Su ka Zauna A Tare.
" Ina Fatan Sharilat Da Mahaifinta Sun Amince Za su yi Tafiya Da mu Izuwa Ɗauko TAKOBIN SIHIRI.
Yarima Muzaifar Ya Tambaya A ƙagauce".
" Me kake Ci Na Baka Na Zuba Daɗi Na Da Kai Gajen Haƙuri Ai Saboda Da wannan Magana Na Sanya Kazo, Yanzu Sai ka Bari Idan Mun yi kalaci Sai Mu Tattauna".
Sarki Himras Ya Ba shi Amsa".
Daga wannan Jawabi ne Suka Shiga Kimtsa Cikinsu Sai Da Suka ci Su ka Ƙoshi Sannan Sarki Yayi Gyaran Murya Ya Dubi Yarima yace " Ya Abin Alfaharina Kayi Sani Cewa A'a daren Jiya Na Samu Ganawa Da Sharilat Da Mahaifinta Kuma Sun Amince Zasu yi Tafiya Da mu Domin Ɗauko TAKOBIN SIHIRI, Sai Wani Hanzari Ba Gudu ba Matsawar Ka bari Wata Alaƙa Ta Shiga Tsakanin ka Da Sharilat To fa Baza mu Samu cika Burin Mu Na Mallakar TAKOBIN SIHIRI ba Yaushe Sauran Mako Guda Mu Gudanar Da Wannan Tafiya.
Ko da jin Wannan Bayani Sai Yarima Muzaifar ya Cika Da Matuƙar Farin ciki Maral-Musaltuwa, Amma Sai Ya Tambayi Kanshi A Cikin Ran shi Yana Mai Cewa, Shin Mene ne Ya haɗa Alaƙata Da Sharilat Da Mallakar TAKOBIN SIHIRI, Taya ya Zan iya Goge Alaƙar Dake Tsakanin mu Bayan Cewa Mun Daɗe Da Tsunduma Haɗe Da Ninƙya Cikin Kogin Soyayya.
Ko da Yarima Ya zo Nan A Tunanin shi Sai Yaji Zuciyarshi Ta Buga Da ƙarfi Kuma Jikinshi Yayi Sanyi.
Daga Wannan Batu ne Sarki Ya Miƙe Tsaye Tsam Ya kama Hannun Yarima Suka Kofar Fita Daga Turakar Domin isa Fada, Duk inda Su ka Gifta a Cikin Gidan Sarautar Sai Kaga Kuyangi,Barorin, Dakaru,Hadimai Haɗe Da Bayi Na Zubewa Ƙasa Suna Kwasar Gaisuwa Kawunansu A Sunkuye Tamkar Zasu yi Sunada.
Lokacin Da Suka iso Wata Ƙofa A Gidan Sarautar, Sai Waɗansu ZARATAN MAYAƘA Ma'abota Jajayen Tufafi Su ka Mara Ma su Baya.
Kamar Yadda Sarki Himras Ya Faɗawa yarima Muzaifar Haka Al'amarin Yakasance, Wato Ranar Da Mako Guda Ya Cika Sai Yarima Da Sarki Suka Shiga Shirye-Shiye, Bayan Sarki Himras Ya Bada Riƙon Sarautar shi A hannun Waziri Huzmal, Sai ya kira Wani Hadimin Aljaninshi Mai Suna Narguz Ya Ɗauke Su Ya kai Su Izuwa Jejin Da Su Sharilat Ke zaune.
Har Sarki Himras Ya Yunƙura Zai Sauko Daga Kan Narguz, Sai Kawai Ya Hango Sharilat Da Kuhairu Sun fito Daga Cikin Gidan su Gaɓa Ɗayansu Suna Sanye Cikin Tufafi Da akayi su Da Fatar Barewa, Kuhairu Na riƙe Da Sandarshi.
Ko da ganin Hakan Sai Kuhairu Da Yarima Su ka Yunƙura Su ka Sauko Daga kan Aljani Narguz Suka Taka Da Ƙafafunsu Suka Durfafi in da su Sharilat Ke Tsaye Tun kafin Su Haɗu Yarima Da Sharilat ke jifan Juna Da ƙayataccen Murmushi Mai Tattare Da So na Kauna.
Lokacin Da Yazamana Saura Taku Biyu A tsakanin su Sai Su ka ja Suka tsaya, Sarki Himras Yayi gyaran Murya Yace" Ya Abokan Tafiyar mu ina Fatan Kun kammala Dukkan Shirye shirye-shirye?.
" Mun kammala komai Yanzu Tafiya ce Kaɗai Ta Rage".
Kuhairu Ya Ba shi Amsa.
Ko da jin Wannan Batu Sai Sarki Himras Da Yarima Himras Su ka Shige Gaba, kuhairu Da Sharilat Na Biye da Su aka durfafi in da Aljani Narguz yake Tsaye, Narguz Ya shimfiɗe gadon bayanshi Sarki Himras, Mazaifar, Kuhairu Da Sharilat Suka haye suka zauna Sannan Ya buɗe manyan fuka-fukanshi Ya Yunkura Ya tashi zuwa Sararin Samaniya Yana Mai Tsala Azababban gudu Tamkar Giftawar Tauraruwa Mai Wutsiya.
Cikin Fushi Sarki Himras Ya Daka mashi Tsawa Ya Dube shi Ya ce "Aikin Banza Kai Da kake wannan Gudu Shin Kasan inda Za ka Kaimu?.
Ko da Jin wannan Batu Sai Aljani Narguz Ya Tsaya Cak A Cikin Iska Ya Buɗi Baki Cikin Ladabi Yace " Ka Gafarceni Ya Shugabana.
" Yakai Narguz ibn Shamlazul-jafsul Kayi Sani Cewa Ina So Yanzu Ka kaimu Izuwa Birnin Rum Domin Mu Ɗauko Sarƙar Tsafi a cikin Tsahon ƙabarin boka Auladu ibn Zumar.
Ko da Jin Wannan Batu Daga Bakin Sarki Sai Aljani Narguz Yace "An Gama Ya Shugabana Bin Umarninka Shine Ibada Yana Gama Faɗin Ya Kaɗa fuka-fukanshi Ya Shiga keta Gajimare Cikin Matuƙar Gudu.
Tun da Aka Fara Wannan Tafiya Babu Wanda Yace Ƙala, Amma Fuskokin Yarima da Sharilat Cike Da Annuri Har ma Suna Satar Kallon Junansu.
Wannan shi ne Shi ne Abinda ya Wakana Tsakanin Su sarki Himras Da su Tsoho Kuhairu A lokacin Tafiya Ɗauki TAKOBIN SIHIRI.
*****
Al'amarin Sarki Baddadul-Arus da 'yarshi Uzaima Kuwa, Tun Sa'adda Daga Ranar Da Suka Fafata Artabu da Sarki Huraisu Na Birnin Jarul-Iman, Sai Su ka kasance Cikin Shirye-shiryen Tafiya Izuwa Birnin Rum.
Wata Rana Sarki Baddadul-Arus Na Zaune A Turakarshi Da Aka Ƙawata ta Da Nau'ikan kayan Ƙawa Da Alatun Jin Daɗin Rayuwar Duniya, A wannan Ya na Shan Taceccen Ruwan Inibi A cikin wani ƙayateccen Kofin Zinare.
Yana Cikin wannan Hali ne Kawai Sai Ya Ajiye Kofin Ya Zira Hannunshi A Aljihunshi na Hagu Ya Ɗauko Madubin Tsafin shi Ya karanto waɗansu Ɗalasiman Tsafi Yana Gama Rufe Bakinshi Sai Ga Hoton Aljani Narguz Ɗauke Da Su Sarki Himras yana Tsala Azababban gudu A Sararin Samaniya.
Ko da ganin Wannan Al'amari Sai Ya Taƙarƙare Ya Bushe Da Dariyar Mugunta Tamkar Ba zai Daina ba, Sai da Yayi Dariyar Ta Ishe Shi Sannan Daga Bisani Yace Amma Sarki Himras Ya Cika Waqa Marasa Fahimta, Shi Yanzu Har Ya na Tunanin Cewa Zai Riga Ni Mallakar Sarƙar Tsafi. Bayan Cewa Nine Nake Da Hadimi Mafi Ƙarfin Gudu A Cikin Jinsin Aljanu JARUMAN DUNIYA.
Yana Gama Faɗin Hakan Sai Ya Miƙe Tsaye Tsam Ya Shiga Yin Shirin Yaƙi, Baƙaƙen Sulke Ya Saka Tun Daga Ƙasa Har Sama, A jikinshi Yana Sanye Da Makaman Yaƙi Fiye Da Guda Arba'in, A Gadon Bayanshi Yana Rataye Da Waɗansu ZARATAN Takubba.
Haƙiƙa Shigar Da yayi Ta yi Matuƙar Yi Ma Shi Kyawu Da Kwarji.
Kawai Sai Ya Durfafi Hanyar Da Zata Sadashi Da Turakar Gimbiya Uzaima, Yana Cikin Tafiyar Sai kawai Yayi Turus!, Ba wani Abu Ya Gani ba Face Gimbiya Uzaima Shirye Cikin Gagarumar Shigar Yaƙi Iri Ɗaya Sak Da Tashi.
Yayin da Da Su ka iso Daf Da Juna Sai Uzaima Ta Rungume Mahaifinta,
Sai Daga Bisani ne Sarki Ya Janye Jikinshi Daga Na Uzaima Ya Dube ta Yace" Ya Annurin zuciyata Shin Ya A kayi Kika San Cewa Na Kammala Shirin Tafiya?
Koda jin Wannan Tambaya Sai Uzaima Ta Saki Tattausan Murmushi Ga Abbbanta Sannan tace" Ya abbana Shin Ka Manta Cewa Ni ma Nasan Wani Abu Game Da Shirin Tsafi, Ka Sani Cewa Na gudanar Da Bincike ne Bisa Halarar Tsafina Na gano Dukkan Abinda Ke Wakana Da Kai, Da Abinda Ya faru Da Abokan Gabarmu Su Sarki Himras.
Ko da jin Amsar Wannan Tambaya Sai Daga Bakin Uzaima Sai Sarki Baddadul-Arus Ya Ƙwallawa Hadimin Aljaninshi Mai Suna Zamzaru Kira, Gama Rufe Bakinshi Ke da wuya Sai Wata Walƙiya Gami Da Tsawa Suka Bayyana A Sararin Samaniya, Al'amarin Da ya Firgita Jama'ar Dake Gidan Sarautar Kenan Su Ka Shiga Guje-guje Gami Da ifice-ifice Har Dakarun Gidan Sarautar Saboda Da Firgici Sai Suka Dunga Cika Wandonsu Da Iska, Kai Wasu Har da Sakin Fitsari A Wando, Saboda Tsawa Da Walƙiyar Sun Saɓa Da Irin Waɗanda Idanu Su ka Taɓa Gani.
Tsawon Daƙiƙa Hamsin Ana Cikin Wannan Hali, Sai Daga Can Sai A Hango Wata irin Shirgegiyar Halitta Ta Ketowa Daga Cikin Gajimare Ta Sauka A turba Tana Mai Shimfiɗe Fuka-fukanta, Ba Wata Ba ce Wannan Halitta ba Face Aljani Zamzaru.
A lokacinne Walƙiya Gami Da Tsawar Suka Ɗauke, Komai Ya Samu Saisaituwa,
Cikin Matuƙar Biyayya Aljani Zamzaru Ya Buɗe Wawakeken Bakinshi Mai Kama Da Ƙofar Gari Yayi Gyaran Murya Yace "Umh Ya Shugabana Gani Gareka Shin Wata Buƙata Ka ke Da ita A gare ni?.
Ko da Jin wannan Tambaya Sai Sarki Baddadul-Arus Ya yi Gyaran Murya Sannan Ya kawo Gwaron Numfashi Ya Ajiye Yace " Ya kai Zamzaru Bakomai Ya Sanya Na Kirawo ka Nan ba Sai Domin Ina So Ka Ɗauke ni Da 'yata Uzaima Ka Kaimu Zuwa Birnin Jarul-Iman Domin Mu Ɗauki Sarki Huraisu, Sannan Mu Huce Izuwa Birnin Rum Domin Ɗauko Sarƙar Tsafi Dake Cikin Ƙabarin Boka Aulad Domin Mu Tashi Boka Sharubu Daga KUSHEWAR Shi, Ina So ne Ka kaimu Waɗannan Wajajen A Cikin Abinda Bai Gaza Sa'a Uku ba, Domin Mu rigayi Abokan Gabarmu Su Sarki Himras isa Izuwa Can ɗin.
Ko da Jin Wannan Bayani Daga Bakin Baddadul-Arus Sai Aljani Zamzaru Ya Saki Wata Atishawa, Sannan Ya Samu Nutsuwa Ya Buɗi Baki