Showing 1 words to 3000 words out of 59965 words
Chapter 1 - JARUMAN DUNIYA Book Complete Littafin yaki Writing by Sarkin Marubutan Yaki .txt
JARUMAN DUNIYA
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071
A wani zamani can baya mai tsawo daya shude,lokacin da jahilci yayi katutu a zukatan bil'adama, karfi da jarumtaka suka zamo jari,rashin tausayi da adalci yayi kaura da zukatan mutane.
A lokacin an yi wata nahiya a yankin ƙasashen larabawa mai suna mufrad.
Nahiyar mufard tayi kaurin suna a fagen yake-yake,zalunci da sihiri, Duk sarkin daya fi dan uwansa karfin runduna ko na sihiri sai ya yake sa ya mamaye kasar sa ta dawo izuwa karkashin mulkin sa.
Akwai manyan kasashe guda biyu da su kayi fice anahiyar.
Ƙasa ta farko ana kiran ta da suna madinatul-husuf,sarki Baddadul-arus shi ne ke rike da kambun mulkin ta.
Sarki Baddadul-arus yakasance garjejepn kato mai kirar samudawan farko yana da matukar jarumtaka dadin dadawa kuma yakasance mashahurin matsafi.
Yana da wata kyakkyawar ya guda ɗaya mai su na uzaima, uzaima ta taso cikin gata da kwanciyar hankali kuma ta kasance basadaukiya mace maikamar maza.
Duk lokacin da sarki Baddadhl-arus zai kai farmaki wata kasa shi da yarsa uzaima kadai suke yakar garin su yiwa sarkin JUYIN MULKI.
A rayuwar sarki Baddadul-arus babu abinda yake so sama da wannan ya tashi, bisa wannan dalili ne yasanya duk inda zashi baya rabuwa da ita face kwanciyar barci.
Ƙasa ta biyu kuwa ana kiranta da suna Darul-kushur,sarki Himras ne ke mulkin ta,sarki Himras ya kasance gwarzon mayaƙi mai tarwatsa maza afilin daga, ya shahara ainun a sanin ɗalasiman tsafi da tarin dukiya.
Yana da ɗa guda ɗaya mai suna muzaifar, Yarima muzaifar ya kasance kyakkyawan gaske kuma gwarzon duniya, Domin shi kaɗai ya na iya baje gari guda ya ci su da yaƙi batare da wani ya taimaka mashi ba.
Saboda matuƙar jarumtakar shi yasa wasu suke ganin cewa yafi mahaifinshi sarki Himras ƙarfin damtse
Gaba ɗaya jama'ar birnin Darul-kushur suna matukar tsoran yarima muzaifar kasancewar shi azzalumi maras tausayi.
A ƙasar Darul-kushur akwai ƙananan sarakuna guda bakwai dukkanin su suna karkashin mulkin sarki Himras, Duk shekara sarakun kan biya Himras harajin da yakai dinare miliyan takwas da dubu ɗari biyar gaba ɗaya sarakunan sarki himras ne yayi musu juyin mulki ta karfin tsiya.
***
Gaba ɗaya wadannan sarakuna biyu, sarki Himras da sarki Baddadhl-arus sun kasance abokan gabar juna, A kan hakan sun gwabza yaƙi sau arba'in da biyu amma ɗayan su baya samun nasara sai dai ayi ragas!
Burin dayansu shi ne ya yiwa abokin gabarsa juyin mulki ya zamana shine sarkin sarakunan nahiyar baki daya.
Saboda tsananin gabar dake tsakanin sarakunan biyu, babu wanda ɗan kasar shi ya isa ya shiga ƙasar ɗayan face hukuncin kisa ya tabbata akanshi.
Gimbiya uzaima da yarima muzaifar suna matuƙar gaba da juna wacce ta huce ta haifansu.
Lokacin da sarakunan biyu su ka fahimci cewa bazasu iya kawar da juna da karfin runduna ba sai dukkanin su su ka nutsa cikin halarar tsafin su domin su gano hanyar da ɗayansu zai iya mallakar nahiya.
A rana guda sarakunan su ka gano mafitar, sai dai mafitar nada matukar wahalar gaske.
Abin da sarakunan su ka gano shine ɗayan su bazai samu nasarar kawar da abokin gabar sa ba face ya mallaki wadansu abubuwa masu wahalar gaske waɗanda nemo su dai dai yake da buɗe taskar ANNOBA DARI.
Da farko dai sarakunan zasu mallaki wata salƙar tsafi dake ajiye a wani tsohon ƙabari abirnin rum, shi dai ƙabarin an gina shi ne a cikin wani ɗaki yau shekaru ɗari tara babu wanda ya taɓa shiga inda ƙabarin yake.
Asalin ƙabarin na wani hatsabibin boka ne da ya yi mulki a birnin na Rum.
Idan mutum ya mallaki wannan sarƙa da ita zai yi amfani wajen tashin wani boka a birnin kisra.
wannan boka shi ne kadai yasan dokoki da ƙa'idojin tafiyar da sarakunan zasu yi, wannan boka ana kiran shi da suna sharubu, a yanzu haka ya shekara ɗari bakwai da mutuwa.
Abu na biyu da sarakunan zasu mallaka shi ne, SIHIRTACCEN KUNDI dake ajiye a cikin wata tsohuwar rijiya a can fadar boka zammar da zamanin shu ya shuɗe a can baya.
Abu na ƙarshe da sarakunan zasu mallaka ita ce wata sihirtacciyar takobi da akewa laƙabi da TAKOBI SIHIRI, Takobin tana ajiya ne a fadar sarkin bokayen duniya na uku.
Baza a samu damar shiga fadar ba face an karanta waɗansu ɗalasiman tsafi dake cikin wancan SIHIRTACCEN KUNDI.
Takobin tana ɗauke da wadan su sirrika guda hudu.
sirri na farko shine idan mutum yana tare da ita babu wani tsafi dazai yi tasiri akan shi.
Sirri na biyu shine dukkan abin da ka sara da takobin walau mutum ko aljan nan take zai zagwanye ya narke.
Sirri na uku idan mutun ya mallake ta zai zamo abin tsoro a cikin yan uwanshi mutane kuma zai iya sarrafa ta yadda ya ga dama.
Bokayen duniya sunyi ittifaƙin cewa a kaf sarakunan aljanu na duniya ba a taɓa yin hatsabibi kamar boka Ayyamul-layal ba, domin shi kaɗai ne ya taɓa yaƙar rabin sarakunan duniya su ka dawo ƙarƙashin mulkinshi.
Bai kai ga yaƙar sauran ba rai ya yi halin shi sakamakon gwanbza yaƙi da yayi da wani jarumi ma'abocin addinin musulunci.
Kafin mutum ya isa fadar boka Ayyamul- layal sai ya ketare waɗansu miyagun dazuzzuka guda tara.
Har yau har gobe bokaye sun gaza gano adadin musibun dake tattare da dazuzzukan.
lokacin da sarakunan biyu su kaga gagarumin aikin dake gaban su na ɗaukoTAKOBIN SIHIRI sai hankalansu ya dugunzuma ainun domin suna ganin ajali zai iya riskar su kafin su cika burin su amma da suka tuna irin gabar da ke tsakanin su sai kowanne ya yi aniyar shiga duniya mallako takobin.
***
Wata rana daga cikin ranakun da yarima muzaifar kan zagayawa cikin gari domin yin nisaɗi da walwala.
Yana tafe akan ingarman doki shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matukar kwarjini daban tsoro, waɗansu irin samudawan dakaru masu jajayen tufafi na take mashi baya.
kallo ɗaya za ka yi musu kasance cewa sun cika ZARATAN MAYAKA masu dakakkiyar zuciya, gaba ɗaya dakarun su na ɗauke da miyagun makamai masu barazana ga duk wata halitta mai numfashi.
Lokacin da yarima muzaifar da waɗannan dakaru su ka cigaba da tafiya a cikin babbar birnin Darul-kushur, sai ya zamana cewa duk inda jama'a suka hangosu sai kaga sun tarwatse tamkar sun ga mutuwarsu, Masu kasuwanci ba a barsu a baya ba domin tattare hajar su su ke yi suna cika wandunansu da iska saboda tashin hankali.
Idan kuwa har su yarima da dakarun sa suka riska mutum bai gudu ba, Nan take dakarun zasu gabzawa mutum duka da kulaken dake hannunsu take zai faɗi ƙasa matacce ko shurawa bazai yi ba.
Sai da yarima da dakarun suka shafe sa'a uku suna tafiya babu sassauci, Ana cikin wannan tafiya ne yarima muzaifar ya fahimci cewa dokinshi yana bukatar ya sha ruwa, koda gama ayyana hakan sai yarima ya hangi wata hijiya nesa kaɗan da inda suke ga jama'a nan A wajen wasu na shayar da dabbobin su wasu suna ɗauraye tufafinsu.
Nan take yarima yasakarwa dokinshi linzami ya durfafi rijiyar.
Ai kuwa koda mutanen dake wajen suka hango su yarima sai suka cika wandon su da iska su ka bar wajen tamkar sun hango mutuwarsu, kafin kiftawar ido babu kowa a wajen sai wata budurwa da wani tsoho tukuf ne basu gudu ba.
Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa yarima kai kenan kuma ya bashi mamaki, Domin tun da yake fitowa rangadi hakan bai taɓa faruwa ba.
Shin wannan budurwa mai take taƙama da shi da har zata gan shi bata razana ba.
Abin da yafi Ɗaure yarima muzaifar kai shi ne tufafin dake jikin budurwar sun kasance tsofaffi tukuf!, saboda tsufan su har waɗanda ke jikin tsohon sun fi nata Tsafta kuma budurwar bata tare da wani makami ajikinta da za tayi taƙama da shi.
Dakarun dake bayan yarima kuwa sai zuciyar su ta kama tafarfasa tamkar zata ƙone jikkunansu su ka kama tsuma, kawai umarni suke jira su afkawa budurwar.
Da isowar su yarima bakin rijiyar sai kawai yaga budurwar taci gaba da ɗebe ruwa Guga tana zubawa a salkarta batare da ta waigo ta dube shi ba, sai zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata kone, har dakarun dake bayanshi sun yunƙura zasu afkawa budurwar sai kawai yarima ya rike linzamin dokinshi ya sauko ƙasa, ya taka da kafafunshi har izuwa inda budurwar take ya dube ta yana mai dakamata tsawa yace.
"wace ce ke da bazaki girmamani kamar yadda jama'a ke girma ma ni ba?
Ba tare da budurwar ta ba shi amsar tambayar ba, kawai taci gaba da ɗebe ruwan tana zuba acikin salkarta.
Al,amarin daya ƙara fusata yarima muzaifar kenan bisa ganin cewa ya mace wacce ba kowa ba, tana wulaƙantashi a matsayinshi na hamshaƙin BASARAKE kuma GWARZON DUNIYA.
cikin fushi yarima ya kai mata wawan naushi a gefan kuncinta na hagu da nufin bazar da ita a kasa.
Cikin gwanin ta kyakkyawar budurwar ta sunkuya hannun yarima ya naushi iska.
Nan take su kacame da azababban yaƙi suka wanzu suna kaiwa juna naushi da bugu hannu da ƙafa cikin matukar zafin nama JURIYA DA BAJINTA, A wasu lokutan sai kaga budurwar ta daka tsalle ta raba kafafunta biyu akan rijiyar tana cigaba da kaiwa yarima muzaifar naushi da bugu cikin zafin nama naban al'ajabi.
Duk wannan artabu da ake fafatawa tsakanin yarima muzaifar da kyakkyawar budurwar daga can nesa mutane sun buɗe tagoginsu suna kallon abinda ke faruwa. Koda su ka ga irin masifaffan yakin da a ke yi sai suka cika da marukar mamaki.
Abin da ya basu mamakin shi ne wai ace yau yarima ne ke fafata yaƙi da ya mace.
Nan take su ka raya a zuckatansu cewa an ya kuwa wannan jaruma ba gimbiya uzaima ba ce yar sarki Baddadul arus tayo badda kama domin ta yaki yarima muzaifar?.
Amsar tambayoyin da su ka kasa bawa kansu kenan kawai su ka zuba idanu domin su ga abinda zai faru.
Koda yarima yaga an shafe sa'a ɗaya ba tare da ya samu nasara akan budurwar ba,
sai kawai ya canza salon fadanshi, inda ya dunga daka tsalle yana kaiwa budurwar naushi da bugu hannu da ƙafa.
Wohoho! tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da su ka ce "idan kaga ki gudu to fa sa gudu ne bai zoba."
kuma haƙiƙa idan gwani ya haɗu da gwani dola ne ƙananan jarumai su zamo yan kallo.
To hakanne ya faru da dakarun birnin domin ana cikin wannan yaƙi ne su ka rugo izuwa wajen ɗauke da miyagun makamai.
ko da suka ga irin baƙin artabun da ake yi sai suka koma gefe guda suka zuba idanu.
Ana cikin wannan yaƙi ne wani tunani ya fadowa yarima muzaifar, Tunanin kuwa shine
"wai wannan wata irin hatsabibiyar jaruma ce yau ya haɗu da ita wacce take nema ta kunya tashi a gaban jama'a, lallai fa wannan shi ne masu iya magana ke cewa "Gaba da gabanta aljani ya taka wuta".
ko da gama tunanin hakan sai yarima ya yiwa dakarunshi inkiya ta wutsiyar ido dake nuni da basu umarni.
Kamar dakarun jira suke sai kawai su ka ɗaga makamansu sama suna ihu da kururuwa mai firgitarwa su ka yunkura izuwa kan wannan tsoho makaho mahaifin budurwar domin su hallakashi.
ko da ya rage bai fi saura taku shida su afka masa ba, kwatsam! bazato babu tsammani sai makahon ya dako wawan tsalle daga inda yake sannan ya sanya kirjinshi ya daki kirjin ɗaya daga cikin dakarun da dukkan karfinshi saboda karfin dukan sai da badakaren yayi sama tamkar an janyeshi da kugiya sannan daga bisani ya faɗo ƙasa tim! tamkar an jefar da bijimin sa.
Ko da ganin hakan sai sauran dakarun su ka firgice bisa ganin yadda tsohon makaho yayi wannan bajinta haka lallai akwai alamar tambaya ?.
kawai sai suka afkawa ma shi da azababban yaki suka shiga kai ma shi sara da suka da makamansu gami da bugu da kulakensu.
Shi kuwa ya wanzu yana kare hare-haren su da sandar da yake dogarawa tare da mayar da martani cikin Matuƙar JURIYA DA BAJINTA taban al'ajabi.
Da ace mutum yana wajen lokacin da ake fafata wannan yaƙi sai ya rantse yace tsohon yakasance mai idanu ba makawo ba.
kallo ɗaya mutum zai yi ma shi ya fahimci cewa a lokacin da yake samartaka ya cika GWARZON DUNIYA, mai karfi na Allah ya isa koda cewar ya tsufa akwai alamun sadaukantaka a tare dashi.
kaico! nanfa makahon ya zamewa dakarun alaƙaƙai kuma kadangaren bakin tulu suka rasa yadda zasu yi dashi ya wanzu yana mako su daga kan dawakansu su na yin MUGUWAR HALLAKA.
Koda yarima muzaifar ya kyallara idanu, yaga halin da dakarunshk ke ciki sai zuciyarshi ta harzuƙa fiye da ko yaushe.
kawai sai ya shammaci budurwar ya gabza ma ta wawan naushi afuska a lokacin data raba kafafunta biyu akan bakin rijiyar.
Ai kuwa sai kafarta ta zame ta fada cikin rijiyar amma sai ta tokare da wani dutse sannan ta maidawa yarima martanin naushin a lokacin da ya daka tsalle ya dira abakin rijiyar.
Nan take ƙafafun yarima su ka zame ya afka cikin rijiyar,
Amma saboda gwaninta irin ta JARUMAN DUNIYA sai ya ƙi yarda ya kai ƙarshen rijiyar ya rarraba kafafunshi a tsakanin rijiyar su ka cigaba da kaiwa juna naushi da bugu a hakan cikin juriya da nacin tsiya.
Tabbas yau yarima muzaifar yayi gamo da mace mai kamar maza kuma BASADAUKIYA UWAR SADAUKAI.
Sai da rabin sa'a ta shuɗe su na kaiwa juna naushi da bugu, Duk sa'adda ɗayan su ya naushi ɗan uwanshi sai kaga ya gwara kan shi da jikin rijiyar kuma yayi kasa lu! zai afka rijiyar amma sai kaga ya turje ya mayar da martani.
Babu abin da zai bawa mutum mamaki ga jaruman biyu face yadda su ka shafe lokaci mai tsawo su na artabu ta hanyar yiwa juna lugudan naushi amma ko kaɗan babu alamun gajiya a tare dasu.
Ana cikin wannan yaƙi ne Budurwar ta shammaci yarima muzaifar ta gabza masa naushi a fuska kanshi ya gwaru da jikin rijiyar, ya tsage jini yayi tsartuwa saboda tsananin zafin da yarima ya ji bai san sa'adda ya tsandara ihu ba kafafunshi suka zame ya afka ciki.
koda samun wannan gagarumar nasara sai kyakkyawar budurwar ta sunkuyar da kanta ƙasa tana mai kallon yarima dake kwance tsamo-tsamo acikin ruwan, tana mai yi ma shi murmushi mai taushi.
Sannan ta shiga kama bangon rijiyar tana yo sama kamar yadda kadangare yake tafiya a jikin garu.
koda fitowar kyakkyawar budurwar daga cikin rijiyar.
Dakarun dake yaƙi da mahaifinta su kayi arba da ita sai dukkaninsu su ka dakatar da yaƙin su ka ja da baya a tsora ce.
kyakkyawar budurwar ta tsugunna ƙasa ta ɗauki salkar ruwanta ta rayata a gadon bayanta sannan ta je ta kama hannun mahaifinta suka juya su ka tafi gaba ɗaya dakarun dake wajen su ka bisu da kallo cike da matukar mamaki da al,ajabi.
Ana cikin wannan hali ne yarima muzaifar ya fito daga cikin rijiyar jikinshi ya jiƙe sharkaf da ruwa ga kanshi ya tsage jini yana zuba.
koda dakarun su kayi arba da halin da yarima yake ciki sai hankulansu yayi mummunan tashi kuma a ka ra sa wanda zai tare sa.