Showing 24001 words to 27000 words out of 93806 words

Chapter 9 - Ameenatou Book Original Complete Book .txt

25 Nov 2024

4052

ne Ashe na daukan ransa ne.


Kaman yanda Basu nuna komai na haka ya danne nasa baqin cikin yana fatan samun lafiyarsa data Nur tukuna yasan ta yanda zai fara bincike akansu Dan kuwa mutuwar kasim data aminatu itace mutuwa mafi zafi dasukaiwa Yan uwansa.


Ahmed ma Sam Bai nuna komai a fuska ba saima Shirin barin kasar a take Daya fara yiwa Omar Dan ko zasuyi bincike bazasuyisa Omar na kusa dasu ba Dan akwai hadari me girma tattare da Hakan,
Hakama idan a hukuma zasu miqa zancen meye hujja ko evidence nasu Kuma maganace akeyi ta cikin gida me duniya zata fada akan Omar idan Kai tsaye ya fito ya fada Yana zargin Yan uwansa na jini akan kisar matarsa da Yan uwansa a Baya batareda yanada hujja ba.


Ahmed Bai fadawa kowa kasar zasu bari ba shi kadai ya gama shirye shiryen komai hakama washe gari dukkanin abokan kasuwancin Omar take ya hada meeting na gaggawa dasu ya sanar dasu barin Omar kasar kwata kwata Dan haka dole a nada sabon president a kamfaninsa.


Ta bangaren kadarorinsa kuwa duk masu kulawa dasu ya qara musu tsaro da ma'aikata.


Su mam irin kulawan da suke bawa Dan uwansu tareda tattalawa yasa Shima duk da baida lafiya sosai yake nuna Jin dadinsa Yana jinjinawa kaunar da suke masa sukuma Hakan na sake musu dadi sosai ba qaramin tashin hankali suke ciki ba na Lameenu dayace kaman Omar yaso ganesa Dan haka suke ta bibiyar Omar din da kulawa me tsananin gaske Dan su Gano idan ya fahimci wani abin Amma basuga alamar Hakan ba dan sosai yake nuna musu Jin dadinsa akan kulawansu da kaunar junansu na asalin jinin Seelahs.


Basu San da tafiyar ba sai ranarda su Omar din zasu wuce ya sanar dasu zai koma Poland sbd jinyar kansa da Nur da har lokacin take kwance ba sauki.


Kallan juna sukai a sace zufa na Dan jiqa Alh Lameenu ta cikin tsadaddiyar shaddar Dake jikinsa kansa ya Dan Sara Dan kuwa idan har Omar ya tafi me Akai kenan?


Su da suke fatan daga asibitin Nan sai barzahu sbd sun gama kammala komai a asibitin mutuwar tsafta zeyi irin tsarin mamman seelah,


Banbanci Aikin mamman da lameenu shine shi mamman Baya aikin gilla sbd ya tsani Bata jikinsa ko hannuwansa da jinin Wanda ya kawar,
Koyaushe yafison neat aikin da bama zaa San wani ne yayisa ba,
Zai aikaka batareda ko kadan ansan wani ne yayi Hakan ba shiyasa duka ayyukansa dayayi da kansa suke neat ba zargi ba hukuma ba komai,


Ko a qasar turawa dasukeda bincike aikinsa neat ne,
Tin daga kan sirikinsa mahaifin Dr Aleena har sirikarsa da Mr Jaden babu Wanda zai taba kawo tinanin kisa ce ba mutuwar Allah ba Dan haka Babu wani bincike Daya hau kan mutuwarsu komai nasa a natse hankali kwance yake yinsa shiyasa ya masifar iya takunsa ko a gurin mutane anfi ganin girmansa da mutuncinsa ake masifar girmmamasa Dan ya iya Jan zarensa cikin aji da dubara.


Sabanin Alh Lameenu da shi Kai tsaye yakeyin Abu Babu kwana kwana Babu sauki ba sassauci idan zaiyi aiki da kansa na danyar jini yakeyi Dan kuwa shi jini ne zaa zubar ba Imani ba tausayi bare gudun abin zaije ya dawo shiyasa ma ya buqaci ko yanzu yayi aikin Omar da kansa sbd tabbatarda matsalarsu tazo karshe yasan shine ya kawar da ita matsalan da kansa abinda yake zuciyarsa na shekaru ya fada masa yaji sanyi.


Maganar tafiyar Omar ta girgizasu musamman mamman da yanzu ne yake buqatan daukaka kansa sbd yayansa dasuke gab da Isa riqon dukiyar mahaifinsu su zama matasan da Suma zaa ringa ambatar sunansu da mutuntawa a matsayin yayan Alh Mam seelah,
Hakama babban fargabar Mam itace Omar na komawa Poland 'dansa dayake jiran ya gama karatunsa ya dawo dashi hannunsa Hakan bazata yiyuba sbd matiqar Omar da Mum dinsa na guri Daya Jamaal bazai taba dawowa Nigeria gurinsa ba shikuwa yanzu Yama fi Jin tsananin so da kaunar Jamaal a tareda shi fiyeda Haroon Dake tareda shi sbd Jamaal Dake nesa yafi shiga ransa sabanin Haroon da kullum suna tare.


Lameenu kuwa shi a yanzu yafi buqatan rayuwar Omar din fiyeda dukiyar tasa,
Idan Omar yabar duniya shine zaiji ya samu nutsuwa sbd ya kasa yadda da Omar Bai ganesa ba yaqi nunawa ne kawai Dan haka shi yanzu asirinsa baa rufe yake ba matiqar Omar na duniya gashi Yanxu Yana maganar yabar inda suke ganin duk wani motsinsa zai tafi inda basa ganinsa Dan haka komai zai iya faruwa Dan haka hankalinsu su dukan baa kwance yake ba da tafiyar.


Ga babban mamakinsu da shock dinsu kafin suyi wani yunkurin rarrashinsa su hanasa tafiyar a ranar ma jirginsu zai daga Ahmed Babu Bata lokaci ya buqaci securities aka rakasu har airport suka daga.


Su Mam Basu sake shiga tashin hankali da firgici ba Saida suka samu tabbacin ba Poland Omar ya koma ba Nur ma tini aka bar Poland din da ita Ashe Kuma daga Dr Aleena har Jamaal Babu Wanda yasan kasar da suka koma Dan Ahmed baibar kowace irin clue ta inda ma suka tattara suka koma din ba sbd Yana buqatan lafiyar Omar da Nur ayanzu fiyeda komai da nutsuwa da samun Kwanciyar hankalisu su dawo daidai tukuna kafin su fuskanci komai.


Kaman bacewar hayaqin Daya tashi sama haka suka bacewa kowa bat Babu labarinsu,
Duk wainda suke communicating dasu Yan amanar asalinsu ne da ko zasu mutu bazaka ji sirrin Omar a bakinsu ba.


Shi kansa Jamaal hankalinsa tashi yayi sosai da Hakan sedai mum dinsa ta kwantar masa da hankali tareda basa tabbacin duk inda Omar yake ya kebance kansa ne Dan bawa kansa kariya da damar samun lafiya tukuna duba da abinda ya samu iyalinsa a lokaci Daya.


Wanna ya Saka hankalin Jamaal Kwanciya Badan ya Dena binciken inda Dad Omar din yake ba.


Su Mam kuwa tini hankali ya tashi musamman da suna zaune cikin damuwa da tsananta binciken akan Neman Omar da kwata kwata ya Yanke kansa daga kowa hatta su duk alaqa da kusancinsu suna matsayin Yan uwansa Bai nemesu ba ya datse hadda su kenan Hakan ya tabbatarda Kila yasan wani abun gameda su kenan ko me?
#MAMUH#
#MAM#LAM#OMAR#SEELAHS
#JAMAAL JEEY SEELAH
#DEEP
#LOVE
#ZAFIN KAI
#AMEENATOU OMAR JEEDEN SEELAH
#ROM


ASHNA BEAUTY SKINCARE
Free class free class
Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta
Carwash
Airfreshner
Liquid soap
Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058
Karku Bari wannan damar ta wuceku


*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_


Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
16
_*Turaren wuta da exculsive gyaran jiki course*_


*Assalamu alaikum yan'uwana mata, a yau na kawo muku sana'a mai matukar riba wanda kina zaune a gida zaki yi, kudade na shigo Miki*


Baya ga haka akwai abubuwan gyaran jiki masu yawa da
Wannan course din zai koya Miki, anyi shine musamman saboda samarwa mata sana'ar yi suna daga gida ba tare da sunje ko ina ba.


Da labarci muce *bakhoor*
Da Turanci muce *incense*
Da Hausa muce masa *turaren wuta*


Abubuwan da zaki koya a idan kika siya course din.


Zaki koya yanda ake hada turarenwuta kamar haka:


- Turaren wuta na ko wane irin icce mai hadin sugar.
- Turaren wuta marar hadin sugar
- Turaren wuta irin na Yan Senegal
- Turaren wuta irin na Yan Yemen
- Turaren wuta na wardrobe
- Turaren wuta na gari
- Humra fara
- Humra baqa
- Room freshener
- Mopping mist


*Abubuwan da zaki koya a gyaran jiki:*


- Halawa
- Body cleanser
- body scrub
- hadin kurkur
- hadin dilka
- turaren jiki
- dilka body wash
- dilka body oil


Duka wannan zaki koyesu ne a farashi mai sauki kan 20k kacal.


Sannan Bayan wannan akwai bonuses kamar haka:


- Yanda zakiyi branding kasuwarki


- Yanda Zakiyi packaging


- Yanda zakiyi ma kayanki kudi


- zaki samu littafin da zai koya maki yanda zakiyi kasuwanci online (WhatsApp)


- Zaki samu number mai siyar da kayan turarenwuta na 'yan maiduguri da kuma mai siyar da kayan turarenwuta na 'yan sudan.


Banda bonuses, duk lokacin da akayi upgrading course din, wato aka qara sababbin abubuwan qamshi zaki same su kyauta ba tare da kin qara biyan ko sisi ba. Saboda za'a qara koya wasu abubuwan nan gaba.


Idan kika siya wannan course din Zaki samu sana'a wadda zakiyi a gida, zaki koya kina daga gida, kina daga daki a kwance.


Idan kika siya wannan course din Zaki San sirrika na hada turarenwuta da kayan qamshi masu dadi. Zaki koya abubuwan da ba kowa ya sansu ba.


Idan kika siya wannan course din Zaki samu contact na masu siyar da kayan turaren masu inganci ba irin Wanda ake masu hadi da wani abun su rage qamshi ba. Zaki samu masu siyar da kayan turaren wanda ba algush sannan kuma ba tsada.


Idan kika siya wannan course Zaki samu access da support group inda a ko da yaushe kike neman wani taimako wajen hada turare, ko kina son kisan wani abun za'a fada maki.


Idan kika siya wannan course din, zan taimaka maki wajen gina kasuwancinki mai inganci ta hanyar baki shawarwari da kike buqata.


Idan kika siya wannan course din ko baki da jarin siyan kayan turare Zan nuna maki hanyar da zaki samu Jari mai tsoka wanda zai isheki kiyi kasuwarki hankali kwance.


Idan kin shirya siyan wanna course ɗin, ki min magana ta WhatsApp a 07082281566.




**********
A gombe kuwa Koda Babbah ya samu kansa ya farfado cikin Dan saukin Daya samu dadah tayi kukan Daya sauya kamannin fuskarta harta gaji,


Tayi kukan rashin Amina,
Tayi kukan tausayin babyn da Amina ta bari,
Tayi kukan tausayin Babba da yanda zai rayu cikin quncin da har abada bazai bar zuciyarsa ba na rasuwar Aminansa.


Kallo Daya Babbab yayiwa Dadan cikin ciwo yaji zuciyarsa ta sake samun rauni,
Yar datake rungume a jikinta ya kalla kafin ya miqa hannuwansa Dake wani irin rawa da rashin karfi yace ta doro masa ita.


Hadiye hawayen idanuwanta tayi kafin ta matso ta Dora masa babyn Daketa baccinta hankali kwance.


Rungumeta yayi jikinsa Yana tina ranarda mahaifiyarsa ta haifi Amina ta rasu ta bar masa ita a hannunsa a rungume,


Cikowa idanuwansa sukai da hawayen da suka kasa riquwa Saida suka gangaro kan fuskarsa data fada lokaci Daya kaman ya Dade a kwance Yana jinyar.


Gawar Aminansa ce ta dawo a idanuwannsa lokacinda take cikin jini Tako ina a jikinta.


Sake rungume babyn yayi Yana Jin duk wata so da kaunar dayake wa Aminansa ta ninkuwa so Babu adadi akan 'yar Dake hannunsa,
Idan Yana yiwa Amina kauna ninki dari to yana Jin yanawa 'yarta so dubu,
'yar hannunsa kyauta ce da Allah ya basa bayan ya amsar masa Amina,
Duk Wanda yakeda Saka hannu a kan mummunan kisan da akaiwa Aminarsa to matiqar zai sansan bazai taba barin yayi mutuwar mutunci ba Amma tinda Allah ya bar masa abinda Amina ta Haifa Yana yiwa Allah Godia hakama bazai taba barin ko wani Mai sunan Omar ya kusanci wannan yar ba bare wani abin ya sameta kaman yanda ya samu mahaifiyarta.


Sakon da Dadah ta sanar masa akan Omar ya buqaci da har abada idan bashine ya nemesu ba kada su taba fadawa duniya ko kowa cewan 'yarsa ce wannan ba,
Kada su taba barin asan waye mahaifinta koma tanada hadi da jininsa gaba Daya idan har suna son tseratar da ita su Bata kariya to su Yanke alaqa da komai Daya danganci ko sunansa ga wannan 'yar.


Wainnan kalaman sune sukai tsananin tarwatsa zuciyar Babbah fiyeda radadin dayake ji,
Shi dayake jiran bayanin dalilin mutuwar yar uwarsa a bakin Omar din shine zai Yanke alaqar komai dasu tareda Yanke alaqa hadda ta sunansa akan yarsa.


Wani nauyi kirjinsa ya dauka tareda zafi me tsananin gaske,


Dago babyn yayi daga kirjinsa ya Kai bakinsa kunnenta yayi mata huduba Shima a hankali cikin so da kulawa me tsananin gaske kafin Shima ya Bude Baki ya ambaceta da sunan AMEENATOU NUHU BABBAH batareda yasan sunan da mahaifinta Shima ya kirata dashi ba kenan na mahaifiyarta Dan haka yarinya taci sunan mahaifiyarta AMEENATOU
Banbanci kawai shi mahaifinta ya kirata da AMEENATOU OMAR JEEDEN SEELAH shikuwa Babbah ya ambaceta da AMEENATOU NUHU BABBAH.


duk wani taurin zuciyan Babbah da rashin hakurinsa dawowa yayi sabo fil a take Dan haka da karfin hali ya kwana gari na wayewa yasa aka sallamesa batareda ya warke yanda ya kamata ba Amma yanda yakejin zuciyarsa idan ba abinda zuciyarsa keso yayiba zai iya samun bugawar zuciya Dan haka Kai tsaye gida suka nufo.


Suna dawowa wanka kawai yayi ya fice daga gidan.
Bai dawo ba sai dare.


Yana dawowa ko abinci Bai iya ci ba ya shige dakinsa haka suka kwana jigum jigum kaman gidan zaman makoki.


Da sassafe sai ga baqi sunzo gurinsa.


Dadah na daki tanaji Akai cinikin gidan aka Kai karshe batareda tsayawa lissafin komaiba Babbah ya sallama gidan take aka Saka masa kudin a banki tareda rubuce rubuce da shedu ya miqa takardun gidan.


Suna wucewa ya sanar da Dadah duk abinda sukeyi a siyar da komai yau washe gari zasu bar garin.


Da farko hankalinta ya tashi Amma duba da yanda komai yake tafiya da abinda ya faru itama taji zatafi samun nutsuwa Subar inda aka Sansu su koma inda Babu Wanda ya Sansu su Gina sabuwar rayuwa tareda Ameenatou Dan Bata cikakkiyar rayuwar yancin data cancanta.




Tin a ranar suka fara shirye shiryen barin gari sedai Basu samu wucewa washe garin ba Saida Babbah yayi tafiyar kwana shida ya dawo yaje ya Siya musu gida a inda Babu Wanda ya Sansu Kuma baa birni sosai ba a local government sbd samun nutsuwa.


Sunyi bankwana da makota da abokan arziki da kasuwanci sun bar garin gombe batareda sanarwa kowa inda zasu komaba sbd ita kanta Dadah babban Bai sanar da ita ita zasu koma dinba sbd tsaro sedai sunje ta Gani.


Tafiyar wuni guda Mai Nisan gaske sukai sai gasu a wani garin da Dadah Batama tantance sunansa ba Amma dai akwai Fulani sosai a garin dayake a gajiya sosai Bata damu da tsayawa tambayar babban ba gashi dare yayi Dan haka Kai tsaye Dan karamin gidansu Daya Siya musu suka Isa Wanda yake sabo ne daidai misalin rufin asiri Kuma ya Siya komai ya zuba tin daga kan katifun Kwanciya da Yan abubuwan amfani.


Ruwan zafi ya fita ya siyo sukasha shayi da bread sai indomie,
Hakama ya sake fita ya samo ruwan zafi a gurin me shari Wanda bana shayin ba akaiwa Ameenatou wanka aka gasata sosai sauran su Hafiz suka sukai wankan,
Shima babban wankan yayi Dana sanyi itama dadah Dana sanyi tayi
Dayake sun Riga sunyi sallolinsu tini suka kwanta sai baccin wahala da rashin dadin Rai.


Washe gari duk wani sauran abinda basuda Saida ya fita ya siyo musu shi ya kawo,
Abinci ma haka ya Siya Wanda zai Dade musu Bai qare ba ya ajiye,


Bai taushe hannu ba ya bazama yaje ya nema makaranta ya Saka su hafiz a a biya kudin da komai daga bokon har Arabic sbd so yake Kai tsaye ya fuskanci rayuwarsa shida iyalinsa,


Kayan baby Ameenatou kuwa tin daga kayan sakawa har Madara da abubuwan buqatanta Babu abinda Bai siyo ba Dan haka dadah itama ta sake jikinta yanda ya kamata tana kulawa da ita tamkar ma itace ya haihu Dan duka makota da Wanda suka ringa shigowa suna gaisawa sun dauka itace ta haihu din itama Bata Musa din ba sai aketa mata barkan haihuwan ana tambayar sunan yar.


Dayake baai mata yankan suna ba sai da sukai kwana biyu sun gama hutawa da gyaran gidan kafin Babba ya yankawa Ameenatoun tasa rago Akaci Akai sadaka.


Tin dukkaninsu sunata fama da kadaici da bakunta har suka fara sabawa tini dadah tafara Yan sana'ointa data Saba Yara ma sun fara zuwa makaranta tini,


Babbah ma shago ya Bude a kusa ba nesa ba na siyarda hatsi Dan haka suka dauki hanyar zama Yan gari musamman Babbah Daya danne komai ya koma babbansa na Baya sbd kawai su zama cikin farin cikinda idan Ameenatou ta tashi itama zata tashi cikin farin ciki tsakanin iyayenta Dan baida niyar tasan basune asalin wainda suka haifetaba duk da sunyi mata tsufa a iyayen Amma dai sune suka haifetan kawai.


Dan haka ahankali suka nitsa rayuwa na tafiyar dasu cikin Kwanciyar hankali da amince Dan tini ya rufe Babin Omar a rayuwarsa data iyalinsa Dan kuwa bayajin har abada zai bari Omar ma yasan inda suke bare tinanin ma yanada 'ya a hannunsu.




*******
Lagos


Zaune suke duk inda jini yake yawo a jikin Mam seelah tafasa yakeyi Yana Jin kaman kansa zai rabe sbd baqin ciki da damuwa.


Shikuwa lameenu tini yafara ficewa hayyacinsa sbd kansa Bai sake cikakkiyar lafiya ba tinda lamarin Nan ya faru sbd ya kasa tantance gaskiyar abinda yake gudana a Kai da zuciyar Omar Wanda har lokacin baida alaqa da kowa Babu labarinsa.


Ga dukiyar dai ya tafi yabarta kusan a hannunsu Dan duka kadarorinsa yanzu kusan a hannunsu suke amman Sam basuda nutsuwan cinsu tinda basuda tabbacin Shirun nasa na Menene,
Amma dai ko na Menene Abu Daya suka tabbatarda shi shine fitowarsa Koda zasuyi gaba da gaba ne saisun kar karshen matsalarsu Dan yanzu rayuwarsa ma itace abin buqatan tinda yasan Menene sukai masa.




Shigowar BB babban Dan hannun damarsu Mam dinne ya Saka Lameenu dagowa da idanuwansa dasukai ja ya kallesa kafin yayi magana cikin girmamawa BB ya Kalli Lameenun kafin ya Maida kallansa kan Mam Yana Dan sauke Kai cikin nasa zafin zuciyar da fargaban abinda zai fada yace


"Ranka ya Dade binciken da muketa son tabbatarwa akan gawawwakin da jamian tsaro suka fitar bayan kashe gobarar gidan gaskia ne gawa uku kadai aka samu daga cikin gida sai gawar security dinnan Daya daga waje bayan Kuma idan aka cire Sir Omar da Ahmed gawa BIYAR ya kamata a Gani a cikin gidan.......


Wani mugun zufa me zafin gaske ne ya tsinkowa lameenu kansa na sarawa
Shikuwa Mam wata mummunan sarawa kansa yayi ya dauki ruwan Dake gabansa yakai bakinsa Yana Sha sbd Jin koina jikinsa kaman Yana ci da wuta.


Dan gyara tsayuwa BB yayi Yana kallan Lameenu Daya zuba masa ido Yana jiran sauran bayanin yaji Shima wani zufa ya tsitsifo masa sbd abinda zai fada yace


"Cikin gawawwakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login