Showing 30001 words to 33000 words out of 93806 words
yanda Mam ke bugun gaba da alfahari da Jamaal haka yake wannan alfaharin dashi Dan kuwa manyanci ya Saka da yawa fiyeda Rabin nauyin dayake kansu Jamaal din ya dauke musu hakama Bai taba banbanta matsayi ko kaunar Dad dinsa akanshi ba sbd sanin shi din qanin mahaifinsa dayake kallo uwa Daya Uba dayane Dan haryanxu kaf familyn Babu Wanda haryanxu yasan ba uwa Daya Uba Daya SEELAHs suke ba.
Allah ya hore musu Jamaal din fiyeda yanda sukai tinanin samun ya dawo gurinsu dan haka Dr JAMAAL JEEY MAM SEELAH ya zama tamkar wani kofa ko bangon kariya da dukkanin ahalin seelahs Tako ina shi zaka fara tinkara idan zaka tinkari familynsa musamman iyayensa.
Haroon seelah tini ya zama kaman wani shadow a gidan baka cika jinsa ba idan ba mugun abinsu da Jamaal Bai saniba bane zasu yi to shine zaa nemosa.
Kauna da shakuwa dayake tsakanin twins din wani irin karfi gareta da Babu ranar da Dad Baya bawa Haroon tabbacin kada Koda wasa Jamaal yasan meye sirrin dayake gudana a cikin seelahs Dan hakan daidai yake da rabasu da zaiyi har abada,
Shi kansa Haroon tsoro da shakkar bari Jamaal Koda tsautsayi yasan wani abu ko fahimtar wani abu bare sanarda shi Dan gudu da shakkar fitintinu da tashin hankalin dazai iya biyowa Baya,
Shi kansa Yana shakkar Jamaal yasan cewa shi yasan komai Amma Bai sanar masa ba Dan haka Shima a cikin shakka da taka tsantsan din Jamaal yake.
******Yau a gida ya kwana sbd tafiyan dayayi wani aiki da suke Gina sabuwar kamfanin qera karfe na Seelahs a Nasarawa ba a cikin gari ba can wajen gari sosai kusada wani kauyen da Baya nesa da cikin Nasarawa din hakama kusan filin Gina kamfanin ya shiga garin sosai Dan haka kaman a garin ma zaa ce kamfanin take dan girmansa yaci kusan garin sosai.
Baccin ragewa jikinsa gajiya yayi na kusan awa uku bayan dawowan nasa kafin ya tashi sanyeda farar doguwar wandon TT me santsi ta kayan bacci.
Jikinsa Babu Riga daga doguwar wandon data zauna a qugunsa kaman zata sauka sai farar fatar jikinsa Dake glowing tana daukan ido hutun dayake cikin Yana bayyana.
Ba slippers a fafaren qafafunsa sbd saukowansa daga gado kenan Kai tsaye toilet ya nufa Kai tsaye ya Bude ya tareda zira takarmin toilet din marasa nauyi da dadin takawa ya zare doguwar wandonsa Yana nufar shower Kai tsaye Dan wankan yake buqata kafin komai.
Ya jima a cikin toilet din ba sosai ba kafin ya fito daure da towel ash daure a qugunsa kaman towel din zata Fadi sbd lazy daurin da yayi masa
qamshin shower gel na LE LABO SANTAL ne ke tashi jikinsa ahankali me sanyin dadin shaqa.
Ficewa yayi daga bedroom din nasa a yanda yake ya nufi hanyar dining room.
Fridge ya nufa Kai tsaye ya Bude ya dauko energy drink din E-Bull ya Bude yakai bakinsa yasha Yana juyowa yaji an Bude kofar palonsa Kai tsaye an shigo batareda ya waiwayoba yasan Haroon ne sbd shi kadai ne me shigowa bangarensa Kai tsaye batareda buqatan kira a waya Dan Jin Yana Nan ko Neman izinin shigowa.
Haroon Daya qaraso tsakiyar palon tareda nufo inda Jamaal din yake Kai tsaye
Yana kallan yanayinsa Haroon yayi ya Dan dauke Kai Yana Bude fridge din shima ya dauko drink din me sanyi kadan ya Bude yafara Sha Yana son sanar da Jamaal din son karban harkar sabuwar kamfanin nasu na Nasarawa.
#MAMUH#
#DR JEEY SEELAH
#BARR HAROON SEELAH
#AMEENATOU BABBAH
#THE SEELAHS
#ROMANCE
#ZAFIN KAI
ASHNA BEAUTY SKINCARE
Free class free class
Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta
Carwash
Airfreshner
Liquid soap
Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058
Karku Bari wannan damar ta wuceku
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
#Arewabooks@Mamuhgee
19
Haroon duk yanda yaso sanar da Jamaal kasawa yayi sbd shigarsa a aikin site din bazaiyiba tinda kwata kwata bayason aiki guri Daya da Jamaal inde na kulawa da harkokin Dad dinsu ne Dan tsoron bawa Jamaal daman fahimtar wani abin Koda tsautsayi ne Dan haka yauma hadiye zancensa yayi Yana dawowa Palo ya zauna a daya daga cikin lafiyayyun kujerun palon Yana cewa
"Amma yau din a gida zaka kwana tinda tafiya ka dawo ba buqatan zuwa asibitin ko?"
JEEY din baice komaiba Saida ya karasa shenye abinda yake hannunsa ya ajiye gwangwanin E-Bull din ya juyo Yana nufar hanyar bedroom dinsa Yana gyara towel dinsa kadan Daya kusa zubewa a qasa ya Bude Baki Yana cewa
"Inada patients Dake jiran dawowana na dubasu,
And inada ma da surgery da zanyi so meyasa zanyi kwanciyana a gida?
I can't even sleep or have a rest if ba hospital din naje ba you know that"
Yana kaiwa Nan ya shige bedroom dinsa Dan shiryowa.
Bai wani jima sosai ba ya fito shirye cikin farar freesize Casablanca hoodie rigar data bayyanarda freshness dinsa sosai
sai half trousers fari Shima da slippers din Bally a kafarsa da haskenta da tsaftanta kaman ba akai yake tafiya ba.
Qamshin turaren Allure ne na Chanel ya gauraye palon gabaki Daya daga fitowarsa Wanda ya tabbatarwa da Haroon ya fito ya Dan dago nasa fararen idanuwan Shima ya kallesa Yana ajiye remote dayake hannunsa Yana sauya channel Yana duba time na agogon dayake daure a hannunsa yace
"Please kayi dinner damu mana to kafin ka tafi asibitin,Dad yayi tinanin zuwanka da Rana Kaci abinci tareda mu amma baka fito ba."
Zama yayi kusa da Haroon din Yana kunna wayarsa da tinda ya shigo gida ya kasheta Dan samun hutun dayake buqata.
Zamansu guri Daya ne kadai wasu lokutan yake taimakawa kowa ganesu da tareda banbance waye Jamaal waye Haroon sbd fatarsu Daya Dan banbanta sai Kuma halayya da yanayi Amma suna rabewa basa guri Daya shikenan gane waye wannan waye wancan zaiyi matiqar yin wuya har Dad dinsu kuwa musamman idan zaiyi maganar Sirri da Haroon ya ringa kokarin tantancewa kenan kada yaje yayi da Jamaal ya lalata aikin shekara da shekaru.
Cikin sauti me nutsuwa da Kwanciyar hankali ya Bude Baki yace
"Idan na tsaya Kaine zaka kaini asibiti bazan driving ba ka yadda da Hakan?"
Murmushi me kyau da nutsuwa Haroon ya sake Yana gyada Kai da cewa
"Har bakin office ma kuwa zan kaika DR JAMAAL SEELAH."
Murmushi Shima ya saki Yana kallan Haroon din Dake Dora masa da bayanin yanda Dad zaiji dadin Hakan Dan farin cikinsa a rayuwa ya zauna table cin abinci da gabaki Daya iyalinsa.
Kiran sallan magrib ya Saka Haroon miqewa ya nufi hanyar Daya bedroom din dayake palon na Jamaal Yana cewa
"Kayi magana da mum kuwa?takira dazu tana buqatan sanin yanda ka dawo wayanka is off."
Shigewa yayi bedroom din batareda yaji amsan JAMAAL din ba,
Toilet ya nufa Kai tsaye yayo alwala ya fito suka fito tare zuwa masallacin gidan da suke sallah a ciki tareda su Dad da masu gadinsu da securities.
Tareda iyayensu sukai sallah suna gamawa sukayo ciki gaba Daya Banda Dad Lameenu daya fita tareda drivernsa zuwa wani gurin.
Dad cikin kulawa ya Kalli Jamaal Dake cika masa ido tamkar bashine ya haifesa ba ya tambayesa yanayin aikin Nasarawan Dan kuwa ba qananun dukiya zuka zubawa wannan aikin ba Wanda idan bakiyiba zasu tafka asarar da jijjigasu matiqa Dan haka Koda wasa bari kowa ya Saka hannu a aikinba sai Jamaal ne kadai project din da komai da komai yake hannunsa.
Cikin nutsuwa suke tattaunawa har suka Isa cikin main palon mansion din inda yake tsare da luxuries na Jin dadin rayuwa da asalin Hutu.
Hanyar dining room suka nufa dukkaninsu daidai fitowan mum Atey da itama Hutu da Jin dadin rayuwa yake bayyane a tattareda ita.
Tana ganin Jamaal ta washe Baki cikin kulawa tana cewa
"Dr jeey tin dazu nake cewa kana hutawa baka fitoba bare muyi Maka barka da dawowa"
Dan kallanta tayi a gazarce Yana Dan sake fuska kadan batareda murmushinsa ya bayyana ba ya amsa da
"Eh na gaji ne Koda na iso Ina buqatan ishashiyan Hutu,.thank you"
Fitowan Ayesha 'yarta ne ya sakashi Dan daga girarsa Daya sama Yana Dan dauke kallansa daga gefen kwata kwata suna cigaba da magana da Dad akan abinda suke tattaunawa.
Gurin Haroon ta nufa tana sake fuskanta gaba Daya da farin cikin ganin Jamaal din tace
"Dr sannu da dawowa."
Batareda ya waiwayoba yanda ya kamata ya Dan juyo kadan yace
"Yawwa thank you"
Zama tayi a kujeran kusa da Haroon tana gaida Dad Shima kafin ta dawo da kallanta kan Haroon tana magana kasa kasa kada kowa yaji me take fada masa Yana dariya fuskansa a sake sosai sbd akwai shaquwa da kulawa sosai a tsakaninsu.
Mum kuwa gefen Dad ta zauna sai ya zamana gefen Jamaal din shi kadai ne Daman Hakan shine raayinsa Dan haka take masu aiki suka qarasa kawo abubuwan da Babu a dining din su ruwa da drinks da cutlerys Dan Basu gama hada table ba masu gidan suka hau.
Mum Atee sosai takeson samun shiga kamar me gurin Jamaal sbd tini ta gama da kame Haroon ta koma itace uwarsa komai da ita yakeyi a matsayin uwa shi kuwa Dr ko a mafarki ba'a Haifa macen da zata maye gurbi ko samun matsayin mahaifiyarsa ba bayan mum dinsa itace kadai tak dinta Dan haka duk tsananin dagiya da son nuna masa tsananin kauna da kulawa da mum Atee keyi Bata taba samun shiga yanda takeso ba Amma dayake ta iya naci da kisisina Bata Dena nuna masa kulawa da tattalin ba saima sake dagewa datakeyi Dan tagama fahimtar Dr din shine SEELAHs ma gaba dayanta yanzu da zuwa Nan gaba hakama Dr ne kadai zata kama ta kama dahir a zaman seelahs harma ta taka matsayin shugaba a cikin matan zuriar duk da akwai wainda suka rigata dadewa a family harda manyan Yaya Amma dai nata burin daban ne akan nasu Dan ita ba zaman auren kadai tazo yiba hadda nemawa Kai suka da matsayi.
Cikin nutsuwa da wayewa sukecin abincin da sakewa dukkanin kulawan mum Atee akan Jamaal take tana tura masa abubuwan datasan Yana ci tana basa tabbacin sbd shi Akai girkin.
Sun jima sosai gurin cin abincin kafin suka gama suka baro dining din Kai tsaye Palo suka dawo suka zauna harsu mum din suka zauna suna magana tsakaninsu ita Dan Haroon da Ayesha shikuma Yana magana da Dad.
Anayin ishai suka fito Sallah suna gamawa Kai tsaye bangarensa ya nufa ya sauyo kansa daga guntaye zuwa dogon Riga da wando na Dior black ya fito Yana qamshi ahankali wayarsa kawai ce a hannunsa sai laptop.
Haroon already Yana harabar gidan Yana waya Dan haka Yana ganin fitowan Jamaal din ya Bude motar ya shiga Shima Yana isowa ya Bude ya shige suka fice harabar gidan securities da suka San Dr Jamaal din ba dawowa zeyiba a Daren suna masa a dawo da safe lafiya.
A hanyar ta zuwa tinda suka fito Jamaal ya kira mum dinsa ya Saka handsfree ya ajiye a tsakiyansu suna magana da ita su duka biyun cikin tsananin kaunar datake musu da wadda sukewa junansu Suma.
Suna Isa Haroon a harabar asibitin ya ajiyesa ya juya ya fice sbd ana jiransa wani guri.
Shi Kuma Kai tsaye ya wuce office dinsa duk inda ya wuce ana masa barka da zuwa cikin girmamawa da kulawa harya Isa office ya Bude ya shige.
Laptop din ya fara ajiyewa da wayarsa kafin ya rage AC kadan sbd tin kafin ya iso ake sake tsaftace office dinsa a kunna AC dasu humidifier.
Ajiye remote din yayi bayan ya rage AC Yana nufar files din dayake kan desk dinsa Bai taba ba ya nufi toilet ya wanko hannuwansa ya fito bayan ya goge hannun da towel fari qarami.
Sensitizers ya fara shafawa hannuwansa kafin ya nufi files din ya fara dubawa.
FADILA ALIYU MUHD shine sunan dayake kan file din.
Budewa yayi cikin nutsuwa Yana dubawa tareda karanta dukkanin bayanan dake ciki.
Dr zayyan ne ya shigo office din bayan yayi knocking Yana sanyeda kayan theatr da fitowansa kenan ganin Jamaal ya sakashi sakin ajiyan zuciya da numfashi me sanyi sbd suna tsananin buqatansa akan patient din da aka juye masa file nata.
#MAMUH#
#DR JEEY SEELAH
#BARR HAROON SEELAH
#HASSAN AND HUSSAIN
#AMEENTOU
#FADILA
#LOVE
#ROMANCE
#CRAZYINLOVE
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
20
Dagowa yayi bayan ya gama sauraron bayanan Dr zayyan akan patient din Daya gama karanta severe long term asthma take fama dashi Wanda gabaki Daya rayuwarta da oxygen take rayuwa.
Idanuwansa ya dago yakai kan inda ake rubuta shekarun patient yaga shekarunta duka duka ashirin da Daya.
Dagowa yayi ya kalle Dr zayyan kafin yace komai nurse ta kwankwasa office din cikin sauri ya shigo ta sanar dasu ana buqatansu emergency ne yanzu yanzu fadilan taqi yadda a Saka mata oxygen dinta tayi nisa komai zai iya faruwa a daidai lokacin.
Dr jamaal dinne ya wuce gaba riqesa file din suka biyo bayansa cikin sauri.
Tin kafin ya iso nurse Farry na hangosa ta dauko masa hands gloves ta tarbesa da ita ya miqa mata file din hannunsa yana sakawa Yana karo sauri Dan isowa ga patient din da kusan ranta ma zaa iya cewa ya kusa fita Dan kuwa ta fizge oxygen nata gaba Daya gashi matsalanta pneumonia ne yafara mata mummunan kamu kafin asthma ya rikido.
Yana qarasawa da sauri yakai hannuwansa duka biyu ya Dora akan nata tareda dafeta Yana cewa ayi sauri a Saka mata oxygen din da gaggawa.
Dayake tayi nisa sosai Babu Bata lokaci aka mayar mata da oxygen din har lokacin Bai saketaba sbd Nisan datai ba lallai oxygen din ta shigeta da sauri ba Dan haka ya Bada umarnin ayi gaggawan kawo alluran da zai mata.
Gaba Daya sauri sukeyi Dan cetan rayuwarta musamman iyayenta dake kofar dakin suna kuka sosai Dan tini suka cire Rai daga gareta ganin yanda rayuwarta yake sama Yana qasa numfashinta na barin jikinta.
Addua suka hau cikin tashin hankali da fatan samun sauki da lafiyan Fadilan.
Sunyi tsananin laushi da zama abin tausayi akan ciwonta da lalurarta tsawon shekaru,
Duk abinda suka mallaka ya qare tas basuda komai bayan rayuwarsu sbd ciwon fadila,
Da oxygen take rayuwa koyaushe Yana tareda ita,
Mahaifiyarta da mahaifinta ita kadai garesu hakama tayi karatu sun inganta rayuwarta sedai ciwonta a yanzu da itama take ganin ta gaji sbd ta zamarwa iyayenta lalura,
Komai dasuka mallaka tana kallo ya qare duk sbd ciwonta dayake cin kudin da yanzu sun Dade da fin karfinsu dan haka take ganin kaman idan ta mutu zasu rage Shan azabar da sukesha sbd ita,
Mahaifinta yakai a yanzu ayyukan wahala yakeyi ya samo musu abinci Dana ciko cylinder oxygen dinta,
Takai ta kawo ma yanzu ba cinsu da shansu yake nemowa ba oxygen dinta yake yiwa nema a wahala da kunci tareda tsananin rashi suke rayuwa.
Kusan lokaci me tsayi likitoci suka sauka akanta kafin suka samo numfashinta ya dawo daidai duk da ba sosai oxygen din take kawai lungs dinta ba sbd mugun Nisan datai
Allah ne kadai yayi tanada kwana a gaba ma da tini wani zancen akeyi Amma dai ta samu oxygen din Kuma Daman nata Dan kadan ne ya rage dole Dr Jamaal ya Bada umarnin aka Saka mata sabo na asibitin tasu.
Rubuce rubuce yayi sosai a file nata tareda zuba mata fararen idanuwansa masu kyau Yana kallanta kafin ya dauke idanuwan nasa ya maidasu kan rubutun dayakeyi ya gama ya miqawa nurse din Dake gefensa suka fito Yana zare gloves din hannunsa Yana tattaunawa da sauran likitocin suka nufi wata patient dinsa Dayake ji da ita dattijuwa ce sosai tana fama da diabetes duk ya rikitata kaman me matsalan kwakwalwa ga tsufa Dan haka aketa fama da ita shikuma Yana lallabata sosai shiyasa idan ba shi ya Bata magani ba Bata sha sai anyi daqyar.
Round yayi a asibitin ya duba patients sosai har kusan 11 kafin ya juyo ya dawo dakin dasu fadila suke ya sake dubata yayiwa iyayenta tambayoyi sosai akan ciwonta Yana sake rubutu acikin file din kafin ya Basu tabbacin Inshallah zata tashi Amma ba yanzu ba zata iya kawai gobe da Rana ko Yamma ba Dan haka su kwantar da hankalinsu.
Sai 12 ya koma office dinsa yana shiga Kai tsaye toilet dinsa ya wuce ya wanke hannuwansa sosai tareda fuskansa ya sake shafo sensitizers ya fito ya rage hasken office din yazauna tareda janyo laptop dinsa ya Bude bayan ya dauko ruwa me sanyi kadan daga fridge dinsa ya Bude yasha kadan ya ajiye gefe yafara aikin dayake gabansa.
Washe gari bayan sallan asuba kaman yanda ya Saba Saida ya sake duba patients dinsa da yawa harda fadila kafin ya wuce gida.
Haroon Bai zo ba driver ne yazo ya daukesa sbd safe ne sosai.
Suna Isa gida Kai tsaye part dinsa ya nufa Yana shiga ya tube kayan jikinsa ya jefasu laundry room dinsa ya fito da underwear kawai ya jikinsa ya nufi bedroom dinsa.
Wayarsa kawai ya kashe ya jefar kan sofa ya nufi toilet ya shige
Wanke bakinsa kawai yayi da mouthwash na spray mint flavor batareda yin wani brush din ba Dan yayi a office
Yana gamawa wanka yayo ba jimawa sosai ya fito daure da towel cikin nutsuwa ya shirya a gaban mirror tsaye kafin ya saka underwears da kayan bacci marasa nauyi ko kadan ya haye gadonsa ya rufe jikinsa tareda kashe hasken dakin take bacci ya daukesa me dadi da nutsuwa.
Baccin awa biyu da rabi yayi kafin ya tashi ya sake brush ya shirya ya fito cikin ash Armani's ya nufi cikin gida Kai tsaye palon Dad dinsa ya nufa acan suka gaisa ya fito daidai fitowan Haroon suka nufi dining room tare suna magana.
Breakfast sukai suna gamawa suka fito Kai tsaye motarsa Bentley continental gt ya nufa ya Bude ya shige tareda tayarwa Kai tsaye ya nufi gate securities suka Bude masa gate ya fice
Shima Haroon ko gate din baa rufeba ya Saka kan tasa tsadaddiyar