Showing 90001 words to 93000 words out of 93806 words
idanuwa a tsakanin Ameenatou din da Jamaal da Kuma siddeeq din.
Siddeeq Bai iya cewa komai bayan cewan suyi ciki da Ameenatou din shikuma ya kama Jamaal Wanda har lokacin kaman jiri yake Gani suka fito daga harabar gidan Kai tsaye motar da Jamaal din yazo da ita suka nufa shi siddeeq din yabar wadda yazo da ita a gurin.
Saida ya zaunar da Jamaal din a mota kafin ya zagaya da sauri ya shiga motar zai tayar Jamaal ya dago jajayen idanuwansa ya kallesa daqyar ya iya Bude Baki yace
"Bani key ni zanje na dubo Kai ka Jira anan din Sbd A,dole Ina buqatan barin wani anan din incase.
Siddeeq kallansa yayi da nasa jajayen idanuwan Shima Yana girgiza Kai sbd bazai iya barinsa yayi tuqi ba a lokacin da kansa.
Bude motar Jamaal yayi tareda fitowa ya zagayo ko gabansa Baya Gani dakyau wani irin wuta da radadin azabar nauyi yake ji a kirjinsa Babu abinda yakeso kaman ganinsa gurin da ake maganar.
Karban key din yayi Bai tsaya komaiba ya fada motar Yana rufewa ya tayar Kai tsaye yayi mata wani irin mugun ja yabar gurin siddeeq na bin bayan motar da kallo hankalinsa na mummunan sake tashi sbd kaman zata tashi sama tsaban mugun gudun da Jamaal din keyi.
Jamaal na barin gurin yayi cikin harabar gidan Yana fiddo wayarsa aljihu Yana rasa a cikin wainda suka tafin waye zai kira tinda Babu me lafiyan dauka Kila.
Jamaal kuwa tuqin yakeyi idanuwansa na Neman rufewa Amma karfin hali Dana zuciyarsa Basu bar hakanba Saida ya hau titin da zai Kaisa Aneyam nzki road Wanda yake kaman bypass Babu mutune sosai.
Yana Jin Nisa sosai a kan titin
Tin daga nesa yafara hango mutane da Jamaan tsaro sun rufe titin hakama hadda masu daukan hotuna da wata katuwar mota a gurin datake kokarin kamawa da wuta anata ihu da hayaniya.
Tin anan Kunnuwansa sukai masa wani irin dim suna kokarin dauke jinsu,
Idanuwansa kuwa wani dishi dishi suke son fara masa Amma ya rintse su da karfi tareda budewa Yana budewa motarsa da sauri ya fito batareda ya kasheta ba hakama wani parking din tsakiyar Titi yayi Yana qarasowa gurin da gudun gaske ganin motar Dad Omar data Abdul sun hade guri Daya kaman kayan wankin da aka hada aka matse cikin mafi muni da tashin hankalin kallo a kusan karkashin babbar motar wadda da alama itace tayi musu hawan tela.
Daukewa ganinsa yafara yi da gaske hakama kunnuwansa Dan haka take yafara Neman kasa karasawa sbd jiri da rashin Gani,
Daidai lokacin Mam ya iso gurin da drivernsa tareda Lameenu cikin matsanancin tashin hankalin da Bai taba Shiga ba Shima nasa ganin da Jin kusan daukewa yayi can sama sama yakejin maganganun mutane da iska suna kadawa hakama gabansa Baya Gani sosai Yana Sako Kai inda police din gurin janye masa shida Jamaal daidai lokacinda aka shimfide gawar Haroon da aka samu cirowa a gabansu cikin fararen kayansa da suka sauya take Babu ko dogon haskensu koina jininsa ne ya sauya kalar kayan gabaki dayanta.
Daga Jamaal har Dad lokaci Daya kafafuwansu suka sare a gaban gaban gawar suna zubewa Jamaal take ya qarasa zubewa qasa Yana rarrafowa gaban Haroon din Dan cetan ransa sbd Bai yadda da wani abin ya Riga ya faru ba da Haroon dinsa, Dad kuwa zubawa gawar idanuwansa yayi hannuwansa na wata irin rawar tashin hankali bakinsa na rawa yace
"Kuyi sauri ku kawo mota muje asibiti Dan uwansa likita ne kwararre gashinan zai taimaka masa kuyi sauri,
A kawo mota,
Me kuke Jira?
A kawo mota da sauri 'dana Yana buqatan taimakon gaggawa,
Yaro na Yana buqatan Isa asibiti,
Lameenuuuu a yi gaggawan kawo mota Dan Allah karku bari yarona ya mutu a Haka yanada raunin zuciyaa, HAROON,HAROON,
HAROON my boy,
Yarona 'dan Albarka Karka tafi ka barni Kai kadai nake dashi a cikin abinda nake tsananin so a duniyar Nan,
Haroon,Haroon...... innalillahi wainna ilaihirrajiun....
Dukkanin maganganun da Dad din keyi Baya hayyacinsa sbd Bai yadda da Babu Rai a jikin Haroon ba sbd jamaal ma kwata kwata ya kasa yadda da Babu Rai a jikin Dan uwansa Dan haka yaketa kokarin dawo da numfashi a jikinsa ya hanyar dubarunsu na likitoci hannuwansa na wani irin tsananin rawa hakama nasa fararen kayan tini sukai kaca kaca da jinin Yana rungumo Haroon din idanuwansa na qanqancewa Yana ihun su kawo ambulance Shima.
Lameenu rudewa yayi Shima yafara cewa a kawo ambulance Maza Maza daga SEELAHs hospital Yana Jin tsananin tashin hankali da tausayin halin da yaga Mam a ciki yau harma da tsoro da fargaba duk ya shiga sbd dukkaninsu Basu taba kawo tinanin Haroon zai shiga motar Omar ba,to mema ya shigar dashi,
Babban tsoro da tashin hankali da mugun firgicin dayake ciki shine bayan wucewansu Omar din tareda Haroon Saida ya Jira Jamaal ya gama wayoyinsa tukuna ya fice kafin ya fidda wayarsa ya kira Lameenu din Kuma daidai wannan lokacin ne siddeeq ya shigo mansion din Bai dauka su Jamaal din sun wuce ba sbd yanata Kiran wayarsa busy yake.
BB ya sanar da Lameenu cewan Haroon fa yabi motar Sir Omar a dakatar da aikin kokuwa a qaddamar dashi yanda aka tsara sbd Haroon na ciki,
Kai tsaye Lameenu Bada umarnin yayi ayi aikin kaman yanda aka tsara sbd Ameenatou bazata taba zama sirikar Mam ba ta yanda zai fisa Iko ko mallakar dukiyar gaba dayanta bayan wuyar da suka shawo akanta Dan haka gwara Bata zama sirikar tasaba tin farko suna gamawa da Omar itama su gama da ita shikenan sune magada tinda sune ake kallan uwa Daya Uba Daya dashi Kuma kada a kuskura duk tsanani bayan aiki a cewa Mam an sani su tsaya akan Basu San Haroon yabi motar ba.
Hakan da siddeeq yaji ne ya sakashi Kiran Jamaal Wanda ya gama wayarsa harya fara Nisa a hanya ya fada masa take shikuma ya sauya hanya yabi zuwa gidansu Ameenatou Dan cimma su Dad din da bawa Ameenatou kariya kafin ya samu a dauro auren a dawo yasan Dan uwansa ya samu mallakar macen zuciyarsa.
Wuto babbar motar ta fara ci dashi Dan haka Akai saurin Bude ambulance din data iso aka fara dauke gawar Haroon aka Saka kafin ta Abdul wadda itama kallo Daya zakai masa ka fashewa gawar da kuka sbd daidai lokacinda su Abdul din suka iso gap da motar su Dad sun musu magana kenan babbar motar data taho da mugun gudun ta haye kansu gaba Daya cikin rashin tausayi kuma Yana hayewa kansu da motar sedai kafin ayi wata wata drivern ya Bude motarsa yana kokarin guduwa a raunane Dan Shima ya raunana sosai
Sedai Yana fitowa motan zai gudu yaran BB Dake gurin a rarrabe suka taso suna rufesa da dukan mutuwa suna cewa ya kashe mutane zai gudu
Take mutane da Jamaar gurin suka tayasu aka rufesa da dukan da take aka kashesa a gurin Shima duk yanda Yan Sanda suka so samunsa da Rai tini Rai yayi halinsa cikeda baqin ciki suka dauki gawarsa Shima aka jefa wata motar daban.
Dad Omar da Babbah sune Basu rasu ba Amma sunfi wainda suka rasu kakkaryewa sosai tareda wahalalliyar azaba hakama gabaki Daya sun sauya daga mutanen da aka Sansu Dan Babu Wanda ake gane ko fuskansa sunyi mummunan raunana Tako ina Dan haka a cikinsu Babu ma Wanda alamun sauran Rai yake a jikinsa amma dai an duba suna raye din Dan haka Akai gaggawan daukansu zuwa asibiti,
Sai Ahmed da Hafiz da Suma sukai Mummunan kariya ta hannuwa da kafa hakama sun raunana sosai sedai su suna hayyacinsu sedai rikitacciyar azaba Da jininsu Dake zuba kaman ba daga jikinsu yake fitowa ba.
Suma kwasansu Akai zuwa asibiti gaba Daya,
Jamaal har acikin ambulance din rungume yake da gawar Dan uwansa ya kasa sakonsa duka jikinsa rawa yakeyi sosai kaman zai jijjige Haroon din Dan haka koda aka Isa asibitinma da qyar aka bambare gawar daga jikinsa Akai ciki da ita.
Dad Koda ya iso Lameenu na biye dashi sbd kada ya Fadi hakama su Mum Atee tini suka qaraso asibitin
Hakama su Aunt Didi matar Ahmed da Fatmah duk sun iso
Mum Nur kuwa Kuka kawai takeyi sbd tsoron dataji duk ya dabaibaiyeta.
Siddeeq Daya kasa hakuri wayoyin kowa kira yakeyi gashi itama Ameenatou din taqi farfadowan sai ruwa ake zuba mata Dan haka ya daukosu tareda dadah cikin sabon tashin hankali sukayo asibitin da ita.
Suna isowa itama aka karbeta sedai samun ahalin seelahs kaf a asibitin ya Saka su dadah cikin masifaffen tashin hankali kafin dukkaninsu su motsa daga inda dukansu suke tsaye Dr zayyan ya fito daga dakin emergency din da suke ciki da duka su Omar da Haroon din bayan fama da taqaddamar da sukasha da Jamaal kafin ya yadda Allah ya karbi ran 'dan uwansa ya koma garesa Dan haka kallansu Dr zayyan din yayi idanuwansa jajir hakama Shima hannuwansa yar rawa sukeyi idanuwansa na cikowa da kwallan Daya kasa riqewa ya kasa kallan Dad dake tsaye shi yake jiran abinda zai fada,mum Atee da Dad Lameenu na gefensa kowa Dr zayyan din yake kalla,
Su mum Sarat da Dadah ma duk a tsinke suke,
Sai su mum Nur da kukanta ya tsaya cak suna kallo bakin Dr zayyan din ya Bude cikin sauti me tsananin sanyin gaske yace
"Sai hakuri,sai hakuri, Haroon seelah da AbdulRasheed Allah ya Riga ya dauki ransu lokaci yariga yayi Babu abinda zamu iya sai hakuri da rungumar hukuncin ubangiji"
#MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_AMEENATOUH_*
_Mamuhgee_
#Arewabooks@Mamuhgee
#ZafafaBiyar
57
Ahankali Dad ya daga hannunsa da yayi masa wani irin mugun nauyi ya Dora a kirjinsa inda yaji wani abu ya tsaya masa Yana hanasa Jan numfashi kwata kwata kafin ma ya sake kokarin Jan numfashin ya yanke jiki a gurin Yana kokawa da numfashin Daya Yanke daga kirjinsa gabaki Daya idanuwansa na tsiyayo wasu zafafan hawayen masu radadi ahankali.
Mum Atee da Dad Lameenu ne suka durkushe gabansa suna ambatar sunansa cikin tsananin tashin hankali da rikicewa.
Dr zayyan ma cikin tashin hankalin me tsanani ya kira nurses da masu daukansa tini aka daukesa Akai ciki dashi Dr zayyan na cewa cikin sauri a kawo oxygen da gaggawa kafin numfashin nasa ya yanke.
Dadah kuwa da Karan farko Bata gane Abdul dinta ake nufi ba saida umman fadila ta rungumeta tana fashewa da kuka sbd dawo mata sabuwa da ranar rasuwar Taya 'yar tayi a wannan asibitin itama ranar aurenta.
Dadah sai alokacin ta fahimci me ake nufi Dan haka ta silale qasa tana Neman numfashin itama sbd kukan ma mantawa tayi da ana yinsa a duniya iskan numfashi kawai take nema a kirjinta kafin ayi yunqurin Kiran likita ya some a gurin gaba Daya jikin umma.
Mum Nur dasu Aunt Didi kukan baqin cikin rasuwar Haroon din dana farin cikin mazajensu dake raye suka sake lokaci Daya tareda tausayinsu.
Fatmah ma kukan takeyi sbd ta dauka zaace Dad dinta da Dad Omar sun rasu suma sun barsu.
Mummy Sarat ma dasu Aliyah kuka sukeyi sosai musamman Ayeesha datafi kowa shakuwa dashi Kuma ita kadaice yakeda kauna mara sirki daga zuciya a tsakaninsa da ita duk cikin family Dan haka ta zube a gurin kasa tana fasa kukan Daya Saka gaba Daya gurin daukan shiru tana Kiran sunan Haroon din.
Emergency Akai gaggawan shigewa da Dad sbd oxygen din Neman gagararsa ja ma yakeyi Dan haka hankalin likitocin ya fara tashi Dan hak suka Taru akansa ana yaqin cetan numfashin nasa hankali tashe.
Su Lameenu Dake waje ma hankalinsu tashi yayi Dan haka kusan asibitin tayi tsit ba dogon motsi bare hayaniya sbd masu asibitin ne da kansu cikinta a mafi wahalan yanayi da tashin hankalin dasuke ganin Basu taba shigarsaba.
JAMAAL Babu Wanda yagansa har lokacin sbd Yana ciki inda gawar Haroon din take tareda ta Abdul a gefensa,
Gawar Haroon itace gawar datafi masa rayuwar duka Wanda yake duniyarma yake Gani,
Gawar Haroon itace abinda ya kasa dauke idanuwansa daka kansa,
Rabin jikinsa ya tafi yabarsa,
Haroon yasha wahala da baqin cikin rayuwa fiyeda komai,
Bai samu farin ciki ba tinda ya taso harya komawa ubangijinsa,
Yaso samun sauyin rayuwa a tareda Dan uwansa da mahaifiyarsa Dan matarsa bayan auren sedai Allah baiyi zaiga hakanba,
Meyasa suka kasance acikin zuria da jinin marasa imanin duk duniya da rashin tausayi?
Kasa riqe kansa yayi daidai lokacinda ya Tina maganar Dan uwan nasa ta karshe akan farin cikin dayake ciki a yau din sbd zai auri farin cikin rayuwarsa.....
Wani irin kuka Mai tsananin radadin zuciya ne ya fashe dashi Yana Dora goshinsa gefen kan gawar Haroon din duka jikinsa na rawa da jijjigan kukan da yakeyi Mai ciwo da baqin cikin ya rabu kenan da Dan uwansa shikenan.
"Innalillahi wainna ilaihirrajiun"
Kukansa ne sosai ya Saka siddeeq kasa riqe nasa kukan tausayin Haroon da irin rayuwar rashin kaunar da ake nuna masa Daya gudanar tareda wahalan ciwo Daya ringa fama dashi batareda kowa ya sani ba daga karshe ya tafiyarsa yabar duniyar da Babu komai a cikinta sai son zuciya da azaba a gurinsa.
Dadah da Akai gaggawan taimakawa tana farfadowa wani kuka Mai ratsa zuciyan duk uwar Datake da 'yaya ne da uban dayake da yayane ta fasa tana Jin kirjinta Yana kasa daukan radadin Datake Jin kanta acikinsa,
Rashin 'dan ta Babba tareda mummunan halinda mijinta yake ciki na tsakanin Rai ko mutuwa baa San wanne zai faru ba da Kuma Hafiz da Shima aketa kokarin ganin an ceta rayuwarsa sbd jininsa da kusan ya tsiyaye da kariyar datafi nawa a jikinsa.
Mum Nur ma da Aunt Didi lokacinda suka samu bayanin halinda su Dad Omar suke ciki mum Nur kasa dauka tayi dole Akai gaggawan mayar da ita gida tinda itama lafiyar tata sai ahankali,
Dadah tin tana iya kuka Dan idanuwanta har lamarin yaci karfina ta sake rikicewa jikinta ya rikice gaba Daya dole dai itama akai gaggawan Bata kulawa aka mayar da ita baccin dole da wahala sbd zuciyarta Dake Neman samun matsala sbd BP dinta yayi mummunan hawan daya fara Sakata kaman zatai jijjiga.
Daidai wannan lokacin ne Ameenatou ta farfado sedai umma kasa barinta tayi tasan meyake faruwa ta dawo gida da ita a taxi sedai Koda suka Isa gida gaba Daya gidan anyi cirko cirko kowa idanuwansa jajir masu kuka sunyi masu shiga tsananin damuwa da tashin hankali duk suna ciki Dan kuwa labarin wannan mummunan ranar ta ahalin SEELAHs ya isarwa kowa.
Duk yanda akaso taimakon Dad abin yaci tura sai da kyar suka samu damar daidaita numfashinsa sedai Kuma Bai San inda kansa yake ba Dan a cikin qanqanin lokaci Allah ya mayar dashi abin tausayi kaman Wanda yayi watanni a kwance take ya jeme.
Lameenu ma cikin tashin hankalin da jemewan yake sbd bazai taba son ya rasa Mam ba tinda a yanzu shi kadai ne yake dashi a rayuwarsa,
Idan ya rasa Mam bazai taba iya komai na rayuwarsa shi Daya ba Babu Dan uwan nasa,
Sun rasa sauran Yan uwansu Badan basa sonsu ba sai Dan son zuciya da shedan tareda muguwar zuciya datake rinjayarsu,
A yanzu tashin Mam da ganin lafiyansa shine abinda yake cikeda zuciyarsa ya Sanyaya jikinsa Dan haka gaba Daya ya koma Kalan jemewan Shima yana cikin tsaka me wuya.
*******Hudu bayan la'asar aka iso da gawar Haroon da Abdul mansion din Dad Omar sbd jamaal Daya Bada umarnin anan zaayi janazah dinsu wadda tini mutane masu yawan gaske suka fara halarta sbd daurin auren da sukai Niya tafiya shine ya koma janazah din Dan haka manyan mutane da Jamaa Tako ina.
Saida aka gama suturtasu siddeeq yaje gida ya dauko Ameenatou wadda take gida ta rikice musu gaba Daya Babbah da Yaya Abdul da Yaya Hafiz kawai take ambata sbd wayarta ce numbern da aka fara kira a wayar Babbah cewan sun samu mummunan accident wanda Dayan police din Kuma numbern Jamaal ya kira da wayar Dad Omar.
Zuwan siddeeq gidan ya tararda sauyawan lokaci Daya da Ameenatou din tayi sbd duk abinda yake jikinta na adon auren da Akai mata ta ciresa ko Dan kunne Bata bari ba daga ita sai doguwar Riga mara nauyi da mayafi ya fito ko gabanta Bata Gani Saida umma ta riqeta suka shiga motar datake jin kirjinta na sake toshewa tana Jan numfashi kaman me asthma.
Suna isowa har cikin harabar Mansion din gidan tana fitowa mota kafafunsa suka sare ta kasa daukan kanta sbd ganin tarin mutane Tako ina.
Umma da Aliyah data fito ne suka kamata har cikin palon farko na mansion din Wanda gawar biyu suke a shimfide fuskan Abdul an Riga anrufe ta Haroon ce ake kokarin rufewa ta iso gurin idanuwanta akan fuskan ta fara sauka kafin ta kyafta idanuwata suka sauka akan dadah Dake gaban dayar gawar zaune kaman mutum mutumi take numfashinta yayi sama Yana Neman fita daga kirjinta jikin tsananin tashin hankalin da Bata taba shiga ba da mummunan shock kafin suyi yunqurin tarota tafara kokawa da numfashinta Wanda yake kokarin ficewa.....
Umma datai saurin Kiran sunanta Bata ma gama rufe Baki ba kwakwalwan Ameenatou din ta juye gaba Daya sbd rashin Babbah da Haroon shine abu na karshe da kanta zai iya dauka Yanke jiki tayi a jikin umma ta zube qasa umma na binta kasan tana Kiran sunanta da tsananin tsoro da tashin hankali sbd wannan yanayin nata ya banbanta matiqar gaske Dana farko data Suma.
Daukanta Akai akayi ciki da ita sedai ko qarasa shigewa da ita baayi ba aka dauke gawar Dan yi musu sallah aka fice dasu.
Ficewan da Akai dasu yayi daidai da sake Saka dadah mummunan halin Daya Saka ita Kam dole asibiti Akai da ita.
Daga gurin janazah din suna dawowa wayar Jamaal ta samu mummunan sakon Daya Saka kansa sake ciki fitinanniyar tashin hankali sbd mum dinsu data yanke jiki kasamakon Jin rasuwar 'danta Kuma likitan ya tabbatar masa data samu paralyze suke tinanin Amma dai Bata farfadoba Dan haka suna tsananin buqatansa da gaggawa kafin ta farfado din.
Wannan mummunan labarin sabon tashin hankalin ya kusan Saka zuciyar JAMAAL bugawa take yafara kokarin tafiya sedai Kuma hankalinsa na rabuwa biyu da barin Ameenatou baa hannun kowaba,.
Babu Haroon,Babu Babbah,Babu Dad Omar,Babu Abdul Babu Hafiz bare Ahmed Dan haka barinta a daidai wannan lokacin kaman barin nama ne a tsakiyar damisoshi.
Babbar tashin hankalin sabo shine Ameenatou