Showing 57001 words to 60000 words out of 93806 words

Chapter 20 - Ameenatou Book Original Complete Book .txt

25 Nov 2024

4032

su Babbah na tambayar yanda ya baro mutanen gida.


Irin son dayake mata itama take masa basa buqatan ma wai saisun kebe sbd a jininsu suke jinsa shiyasa duk firar da sukeyi anan dai tareda kowa tsakar gida ake yinta Kuma ahakan suke soyewansu a gaban su Babbah Dan shi Kam idanuwansa ne basa iya kaucewa daga kallanta matiqar tana gurinda yake ita kanta kallansa shine ke sake sakawa duk tana sake shagwabe masa ko agaban su Babbah ne kuwa sai idan Hafiz ya gaji da sakarcin ya dinga fada kenan Yana hararta idan Haroon din ya tafi.


Washe gari ne zaa tafi da Ameenatou Abuja gurin rubuta jamb nata Daman hadda shi ne ya Saka Haroon din dawowa da wuri Kuma kaman yanda yaso university na Lagos aka cika Mata Dan haka tin 6 da mintina ya iso gidan da motarsa Daman Abdul tini ya shirya itama duk rigimarta Saida aka lallabata tayi wanka tin asuba ta shirya dadah ta shirya mata abincin karyawa da wuri Babbah ma sai addua yake binta da ita Yana cewa saita cinye har marking din Daya wuce Wanda akeso.


Abuja zatai jamb din Dan haka Babu Bata time suka fito itada Yaya Abdul da Haroon din suka kama hanyar Abuja idanuwan Haroon na cikin mirror Yana kallanta itama shi take kalla suna jifan juna da murmushi tana masa magana kadan kadan kaja Yaya Abdul din yaji Mai take fada masa batasan Yana ganinta ba yayi mata banza sbd yasan ma maganar idan yayi Bata bakinsa zaiyi Dan haka yayi kaman ma baisan me sukeyi ba fatansu dai kar Haroon din ya jefar dasu gurin wannan mayen kallan nasa da kullum sai Babbah yace tsoron yakeyi Haroon din ya cinye masa ita da ido ta rame kafin a tashi auren.


Sai 3 suka dawo gida a gajiye budurwan gidan ta dawo harma da zazzabi sbd kaf rayuwarta Bata taba Shan wahalan tafiya ko wata yar gwagwarmayar ba sai yau duk da komai na gata Akai mata Dan kuwa ko Rana Haroon dinta Bai bari ta shiga ba Saida zata shiga exams din ta fito mota hakama bayan fitowanta lafiyayyar tsadaddiyar restaurant yakaisu sukaci abinci Amma Sam Bata iya cin wani abincin ba sbd gajiya gida kawai takeso karshe ma haka suka koma daga shi har Abdul din suna lallabata har aka iso gidan.


Haroon ajiyesu kawai yayi ya wuce Shima Dan haka wanka dadah ta taimaka mata Tayo ta zo ta kwanta take bacci ya dauketa sedai Koda yamma tayi zazzabi sosaine ya rufeta Dan haka hankalin dadah ya Dan tashi zuwa dare Saida aka Kaita chemist kafin su dawo zazzabin ya Dan saketa Se zuwa dare ya sake dawowa.


Koda gari ya waye Haroon Bai Isa gurin aikinsa ba Jin rashin lafiyanta Kai tsaye gidan ya taho karshe dai asibiti aka kwasa aka Kaita duk da narkewanta ne yake Saka ciwon zama wani babba.


Suna zuwa haka aka kwantar da ita sbd ganin yanda hankalin duka ahalin ya tashi hakama Haroon seelah din.


Kwananta Daya a asibitin aka sallameta bayan Haroon yagama lalacewa akanta tareda mantawa da aikin dayake gabansa Wanda duk iya kokari da sadaukarwan siddeeq gurin ganin project din ya tafi daidai ko kadan ne Hakan Bai faru ba Dan haka yake cikin tashin hankali da rashin nutsuwa.


Aikuwa Haroon na dawowa hayyacinsa ya nutsu ya fahimci gagarumar tashin hankalin Dake gabansa take ya shiga firgici Shima Dan tini ma sbd sakacinsu aka sace plans da komai da komai na project din.


Wannan mummunan tashin hankalin ya kusan Sakasa zaucewa Dan kuwa Yanke jiki yayi ya Fadi Saida siddeeq da sauran ma'aikatan suka taresa sedai gaba Daya Jin yayi Yana fita hayyacinsa kansa na Neman Juyewa hannuwansa na rawa.


Gaggawan mayar dashi hotel siddeeq yayi Shima nasa hankalin baa kwance ba Dan kuwa yasan ko Dad yaji wannan zancen sake samun hawan jini zeyi gashi Babu ya yanda zata yiyu cikin qanqanin lokaci su hada sabuwar plan din dazata sakasu Kai labarin wannan project da aka fara.


Haroon Neman zaucewa yafara yi zuciyarta na tsananta bugun Daya wuce misali hakama baisan ta inda zai fara ba.


******Dad Lameenu Dake zaune tareda Mam a palonsu na office suna magana wayarsa ce tayi ringing Ya juya ahankali ya Kalli sunan me Kiran yaga BB ne Dan haka Kai tsaye ya dauka tareda Kai wayar kunnensa Yana cewa


"Yes BB"


Bayanin komai daki daki BB ya fara korowa tin daga kan sunayen ahalin gidan Babbah da Kuma yanda Haroon gaba Daya rayuwarsa ta mace akan yarinyar gidan da Baya gane komai ba a yanzu idan ba abinda ya shafeta ba harma da bautawan dayake musu da gagarumar tsautsayi da aka samu akan project din....


Dad Lameenu Bai gama Jin karshen zancen ba wata mummunan zufa ta tsinke masa Yana cewa


"What???
Yaushe wannan babban balain ya samu??
Ina Haroon din yake yanzu??


Mam na Jin Hakan ya ajiye wayar hannunsa Daya karanta wani article da aka rubuta gameda rushewan da SEELAHs keyi a boye batareda sun bari duniya ta saniba.


Ajiye wayar yayi Yana Dan rintse idanuwansa da suka fara sauyawa Dan kuwa Yana fatan ba abinda zuciyarsa ke Saka masa bane zaiji daga Lameenun.


Cikin tashin hankali lameenu ya buqaci ganin BB yanzu yanzu Dan zuciyarsa bugawa zatai idan Yana sauraron wannan mummunan tashin hankalin ta waya.


Kashe wayar yayi Yana kasa kallan Mam da shima ya kasa tambayar Lameenun komai BB din yake Jira yaji komai Dalla dalla daga bakinsa.


Kafin BB ya iso daga Mam har lameenu da jininsa ya Dade da Hawa Dan tini aka kirawo likita Yana cikin auna BP dinsa BB ya iso take ya sallami likitan akan saisun gama magana.


iPad din hannun BB ya fara kamo hotunansu Hafiz da Yan gidan kaf ya ajiye ipad din gabansu bayan ya kamo hoton Ameenatou datake sanye cikin hijab dinta na islamiya tana murmushi asalin kyanta da kuruciyarta a bayyane tana kallan gefe Dan kuwa batasan ana daukanta hoton bama.


Bayani Daya bayan Daya a tsanake BB yafara jerowa Wanda yayi mugun girgiza su musamman Mam Dan kuwa Bai taba tinanin Shima Haroon zai fada irin kaddarar Dan uwansa ba ta yiwa mace son da Bai kamata ba adaidai lokacinda suke buqatan nutsuwansa da hankalinsa tareda sadaukarwansa fiyeda komai a duniya yanzu.


Ameenatou dukkaninsu suka zubawa idanuwansu da sukai jajir,


Tayaya Haroon zai bari zuciyarsa ta mutu akan mace bayan yasan Menene a gabansu,
Tayaya Haroon zai bari mace ta shiga zuciyarsa,
Tayaya zasu iya samun yanda suke so daga zuciyar Daya mutu akan mace.


Kenan shi tasa mummunan kaddarar akan matan da yayansa suke so ne ko me?
Shima Haroon macen ce zata shiga tsakaninsa da ita?
Ta Ina zai fara karban wannan kaddarar ta Haroon bayan haryanxu Bai fito daga baqin ciki da radadin ta Jamaal ba.


Wani nauyi kirjinsa yayi Yana tafasa da wani irin zafi da radadin da baisan mezaiyiba akan Haroon din Daya kashesu da ransu a Rana tsaka.


Lameenu da tini jininsa ya sake hayewa akan babban tashin hankalin da Basu Saka masa Rana ba da sauri aka sake dawo da likita.


Da sauri likita ya dawo Yana cewa a kwantar masa dashi flat.


Mam tsaban tafasa da qunan da zuciyarsa keyi Jin yayi Haroon baida sauran amfani a garesa ko kadan Dan haka take ya Bada umarnin a Siya masa ticket a ranar zashi Nasarawan.


Lameenu na Jin Hakan yaso wartsakewa su tafi Amma Ina hawan jinin ya sharbesa da kyau Dan haka Yana ji Yana Gani Mam din ya tafi.
##MAMUH#
#DR JEEY
#AMEENATOU
#MAM SEELAH
#BABBAH




*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_


Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
37
Motoci ne na alfamar guda biyu harda securities suka dauko Alh Mam seelah daga airport.


Wayarsa Dake gefensa ya dauka tareda kasheta gabaki dayanta Dan kuwa Baya buqatan Kiran kowa sbd har lokacin zuciyarsa a cikin wani matsanancin zafi da radadin take Mai tsanani.


Daga Haroon har sauran ma'aikatansu manya da abokan huldan Babu Wanda yasan da zuwansa a ranar Kuma aaukan dare sukai Dan haka Kai tsaye masaukinsa Dake cikin Abuja aka nufa dashi Saida safe zai fuskanci Haroon, Haroon dinma ya fuskacesa.


Bayan samun nutsuwa da komai cikin Daren kasa tintsawa yayi ya shiga tinani masu zurfi da sakawa da warwaran ta Ina zai bullowa wannan masifu haka wani bayan wani,


Idan har Haroon na son wannan yarinyar sosai Yana buqatan sauya ha yar handling na abubuwan ta wata hanyar ba irin hanyar dayayi ta farko ba ta rabasa da Jamaal a daidai lokacin dayafi buqatansa da sonsa a kusa fiyeda komai dayake buqata a duniya Dan ko dukiyar Omar da sukeso idan basuda tasu dukiyar tayaya zasu karbeta?


Dole Yana buqatan sauya takun kammala komai cikin hanya mafi sanyi da karfin gaske Amma kwata kwata Babu maganar yabar Haroon yin auren wannan auren a yanzu Dan baima gama zama me amfanin dasuke buqatan ya zama ba ya moru bare idan yayi auren gaba Daya qarasa zama mara amfanin zeyi Kuma sai yanda mace tayi dashi Wanda baqin cikin haka zai iya sakashi yafesa ko illatasa Dan haka bazai taba barin ayi Hakan ba a yanzu saiyaga sauyin Haroon din.




****Har washe gari Haroon Baya cikin cikakkiyar lafiyan hankalinsa Dan shock da tsoron da zuciyarsa take ciki tareda mummunan firgici da tashin hankali ya Hanasa dawowa daidai duk da maganin Daya kwana Yana Sha a cikinsa Wanda harya wuce kaidarsa.


Ya boye kansa bayan siddeeq Babu Wanda yake iya ganinsa duk da ma'aikatansu da yawa dakeson ganinsa da masu zuwa da masu bugo waya duk ya kasa ganin kowa sbd state din dayake ciki bamai dubuwa bane hakama siddeeq din kansa duk ya dage sosai da kokarin hada mafitar gagurumar matsalar shiyasa Shima kansa Baya guri Daya.


Duk daqiqa Daya Dake wucewa sai Haroon ya Tina mahaifinsa da abinda zai iya biyo bayan wannan mummunan aikin kaddarar Daya samesa Dan haka hankalinsa ke sake tashi.


Tinda safe ya samu labarin Dad dinsa na Abuja daga bakin siddeeq Dan haka cikin sabon rikicewa duk da halin dayake ciki ya shirya ya fita aiki Dan Neman mafita koman kankantarta akan aikin kafin Dad ya iso Nasarawan.


Hafiz da siddeeq ganin Halinda yake ciki yana aiki gaba Daya cikin ficewa hayyacinsa riqesa sukai tareda zaunar dashi sai a lokacin idanuwansa suka ciko da wasu irin hawaye masu radadin gaske.


Kallan Hafiz siddeeq yayi tareda cewa ya tafi aikinsa kawai inshallah zaa samu mafita.


Dayake duk ma'aikatansu manya da wainda sukeda kusanci sosai irin Hafiz sunsan ansamu gagarumar matsala Amma bayansu Babu Wanda ya sani shiyasa Hafiz yake cikin damuwa sosai na ganin Halinda Haroon ya shiga akan Hakan.


Kasa aikin yayi ya taho gida Shima bayan siddeeq ya sauke Haroon din sunbar site gaba Daya Dan ciwonsa Daya tashi gadan gadan a gurin tin kafin kowa ya fahimci wani abu ko a gane musamman Hafiz da bazasu so yagani ko ya san ciwon Haroon din ba.


Yana Isa gida jikinsa duk a mace zuciyarsa ba dadi,
Bai boyewa su Babbah ba ya sanar dashi damuwa me tsananin da Haroon yake ciki take Babbah ya daga wayarsa ya Saka Kiran Haroon din Dan basa kwarin gwiwa da adduar samun mafita da nasara a duk inda take Amma wayar Haroon din a kashe Bata shiga kwata kwata.


Ameenatou ma Kiran nasa ta Saka kaman zatai kuka Jin halinda yake ciki Amma kayinsa Baya shiga kwata kwata.
Yaya Abdul ma ya gwada Kiran da tasa wayar duk dai Bata shiga.


Dadah da tashiga damuwar itama kallan Abdul tayi bayan sunkai har kusan rana Ana kiransa baa samu tace


"Bara na sauke abinci saina hada masa nasa kwando ka Kai masa saika dubo mana lafiyar tasa tinda Kiran ya kasa samuwa"


Ameenatou na Jin Hakan ta marairaice fuska akan zata bisa
Dadah ta girgiza mata Kai tana cewa


"Kul na haneki da wanna tinanin Dan Babu inda Zaki....


Karbe zancen Abdul yayi da cewa


"Har sai kin fada? Ni hauka nakeyi zanje da ita gurinsa"


Tana Jin Hakan ta Bata fuska tana komawa jikin dadah din ta kwanta tana kokarin fara Hawaye Hafiz Dake gefen Babbah Yana rubuta text yace


"Kina tsiyayo Hawaye a gurin Nan saina fasa ruwan idonki Daya muga karshen hawayen rainin wayo."


Katsesa babba yayi da cewa


"Ba zataiba ta fasa"
Maida kallansa yayi kan Ameenatoun Yana cewa


"Mayar da abinki yar budurwan gidan Babbah tare zamu dubosa idan naje ai kaman kinje ne ko??"


Gyada Kai tayi tana mayar da hawayenta tana hararan inda Hafiz yake zaune Yana jifanta da tasa hararar me zafi Shima.


Saida sukai sallah sukaci abinci dayake Babbah baida gurin zuwa ranar sai suka fita tareda Abdul din Dan dubo Haroon din.




******Isarsu yayi daidai da isowan Alh Mam seelah Wanda tin a masaukin Haroon din ya tabbatarda Haroon Baya cikin cikakkiyar hankalinsa me amfani Dan kuwa duk kyau da tsananin tsadan hotel din ganin yayi 'dan cikinsa jinin Seelahs yafi karfin zama yayi rayuwa a gurin Amma sbd ba shine ya kawosa ba abinda ya kawosa yafi wannan mahimmanci a yanzu.


Babban abinda yasa yake fatan ganawar gaske suyi budaddiyar wasika da Haroon din shine yasan Lameenu akan lamari na faduwa bayada hakuri,
Bayason abinda zai Saka Lameenu ya kasa hakurin dazai iya aikata wani abin batareda saninsu ba Dan idan har zaisa abibiya lamuran Haroon din batareda saninsa ba zai iya rashin hakurin yin wani abun batareda saninsa ba haka zalika alkawarinsu ne dayake yawo a jininsu Dan zuciyarsu kowa ya shiga hanyar shiga tsakaninsu da arzikinsu ciresa sukeyi daga hanyar kwata kwata Dan haka yake buqatan Saka hankali acikin tosashiyar kwakwalwan Haroon din idan ba Hakan ba zai barwa lameenu kulawa da komai Wanda yasan me Hakan ke nufi.


Su babbah ne suka Riga Mam din isowa Dan haka ko ganinsa Basu samu yi ba Yana bedroom dinsa Dayake suite ne yake rayuwa a ciki saiga shigowan siddeeq a gaba Alh Mam seelah din da securities dinsa duk a tsaye bakin Kofar dakin ya shigo siddeeq ya rufe kofar Yana biyo bayansa cikin tsananin girmamawa.


Yaya Abdul na ganin Hakan ya miqe a natse daga inda yake zaune Shima cikin nuna girmamawa Yana masa barka da zuwa cikeda nutsuwa.


Babbah ma miqewan yayi Yanawa mahaifin Haroon din barka da zuwa a mutunce suna kallan juna sbd kowannensu sai fuskan tayi masa kama da Wanda ya sani Amma sbd kada su kure juna da kallo sai kowannensu ya Dan dauke kallansa Dad din Yana amsa gaisuwan a mutunce Shima Dan Daman shi mutum ne Daya iya taku da mu'amalantar mutane shiyasa SEELAHs sukeda mutunci sosai a idanuwan mutane sbd iya tafiyan da lamuransa.


Yanda suka gaisa a mutunce Babu girman Kai ko nuna musu banbanci ya Saka su Babbah din sukai masa sallama suka tafiyarsu Dan Basu guri da 'dansa batareda Haroon din ya fito ba Dan abinda Basu saniba Haroon din Yana jinsu Amma bazai iya fitowa a halinda yake ciki ba su gansa.


Saida suka fice siddeeq yaje rakasu kafin Haroon din ya fito hannuwansa na tsananin rawa kansa a qasa idanuwansa jajir Babu kyan Gani hakama a jiqe yake da zufa Mai tsananin gaske,


Babu inda yakejin azaba me tsananin gaske kaman a tsakiyar kansa da kirjinsa,


Jin muryan Dad dinsa a dakin ya karasa karya dukkanin Wani karfin halinsa shiyasa ya kasa fitowa Saida su Babbah suka fice Dan ganinsa a wannan halin na mafi Munin rauni zai karya zuciyoyinsu akansa gameda Basu auren macen da bayajin zai iya rayuwar Nan Babu ita su kuwa Ayanda suke tsananin kaunar Ameenatunsu bayajin zasu taba bawa Wanda bazai iya tsayuwa a gaban mahaifinsa bama ya dago kansa aurenta sbd tinanin bazai iya Bata kariya ba ko kare martabarta.


Hannuwansa Dake rawa sosai kaman zasu qanqame yayi Baya dasu Yana kasa dagowa har lokacin kansa Juyewa yake Neman yi.


Zuba masa nasa jajayen idanuwan Mam yaji Yana kallansa sbd baisan ma me zai fara dashi ba sbd baqin ciki da damuwa me tsananin gaske Dan Shima Yana tsaka me wuyar da baisan ta inda zai fara bullowa zancen ba.


Tsadaddiyar wayarsa Daya ajiye gefensa bayan ya zauna ya miqa hannu ya dauka tareda kunnawa ya Nemo hoton Ameenatou ya ajiyewa Haroon din kan centr table Dake gabansa batareda yace komai ba tukuna.


Haroon Daya kasa motsawa bare magana dago jajayen idanuwansa yayi ya Kalli wayar da Dad din ya ajiye masa idanuwan suka sauka akan hoton Ameenatou Dake bayyane a ciki tana murmushi sanye da hijab din islamiya.


Mummunan bugawa kirjinsa yayi ya dago idanuwan da sauri sai alokacin ya Kalli Dad din da Shima shi yake kalla Yana kokarin karantar yanayinsa.


Hannuwansa Dake tsananin rawa ya sake kankamewa Yana sake kallan Dad din da kyau kafin ya Bude bakinsa Dake rawa da muryan Dake bayyanarda tashin hankalin dayafi wanda yake ciki yace


"Dad Kayi hakuri na.....




Katsesa Dad din yayi da cewa


"Ka manta mace ce ta Raba Dan uwanka da mahaifinsa rabuwa ta har abada?
Ka manta matsalolin rayuwar da muke cikinsu duka ayanzu duk sbd macen da Dan uwanka ya so ne fiyeda kansa da ni mahaifinsa?


Wasu Hawaye ne masu tsananin zafi da radadi suka gangarowa Haroon Dan Bai taba tinanin samun kansa a cikin irin yanayin da Jamaal ya samu kansa ba,
Gwara kaddarar Jamaal sbd shi yanada jarumta da karfin zuciyarsa fuskantar duk Wanda zai shiga tsakaninsa da farin cikinsa matars wadda ya tsayawa har ranar karshenta harma a bayan ranta ya tsayawa macen dayake so da dukkanin zuciyarsa.


Wasu zafafan hawayen ne suka sake gangaro masa Yana rintse idanuwansa sbd Yana fatan inama wannan jarumtar zata shigesa ya tsaya akan macen dayakewa mugun son dayakejin yafi Wanda Dan uwansa yayiwa tasa macen.


Hawayen Dake zubawa daga idanuwan Haroon dinne masu bayyanarda tsananin radadin da zuciyarsa take ciki ya Saka Dad zubawa masa idanuwansa hankalinsa na Neman tashi Dan kuwa duk tsananin quncin da rayuwar Haroon din take ciki Bai taba zubar da Hawaye ba sai yanxu.
#MAMUH#




*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_


Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
38
Ahankali Haroon din yayi qasa sbd kasa riqe jikinsa Dake kakkarwa sosai da yayi har lokacin idanuwansa na kan hoton Ameenatou Dake kan wayar Dad din Yana tsoron me Dad zeyi da hoton nata.


Zuciyar Dad Dake tsallen tafasa tana quna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login