Showing 24001 words to 27000 words out of 55893 words
Chapter 9 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt
the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
Telegram at
https://t.me/jorderhmajidadi
19
Daidai kofan shiga room dinsa yaga Ammi tana niyar juyowa kallonsa kawai tayi ta kawar da kai sai kuma tace"ina kaje".cikin k'asa da murya kamar ko yaushe yace"no where".jinjina kai tayi tana karantar yanayinsa tsab sai kuma ta share tace"meet me at my room immediately "bata jira cewarsa ba ta fito kawai da kallo yabi bayanta sannan ya tura d'akinsa ya shiga dan canzawa...wani irin murmushi ne ya subucewa Momy Badiyya ta fito rike da hand bag da alamar fita zata yi tace" a'a maryam kwana biyu bamu hadu ba,ince dai kinji niyya da kuma abun alkhairin dake tunkaro d'ana ko ince ya dangwalo arziki ya samo yar gidan tarbiyya,aure insha Allah nan da wata d'aya za'a daura"..Murmushin itama Ammi tayi cikin ko in kula dan tsab ta gama fahimtar in da Momyn ta dosa tace"Allah yasa alkhairi ai munyi magana da Lamin din,Allah ya kaimu lokacin lafiya"bata kuma jira cewarta ba ta wuce abunta dan a yanzu abubuwan dake kanta sun fi mata sa'insa ko ta zauna Momyn ta bata mata rai duk lokuta da dama tana shakkar hakan dan tasan maryam din ba kanwar lasa bace,kallon Basma tayi dake gaisheta da mata sannu ta ansa tana kallonta ,sunkuyar da kai Basma tayi tace"Ammi Abba yace wai kizo".jinjina kai kawai tayi ta kuma jan mayafin abayarta kafin ta wuce wuce part din Abban,kamar ko yaushe da barkwanci suka gaisa da Aunty Amarya kafin ta mata jagora zuwa parlon Abban ta fita ,ganin suka Yayun nata yasa ta tabbatar maganar mai mahimmanci ce ta zauna a daya daga cikin sofas na parlon sannan ta soma gaishe su...gyara eyeglasses Abba yayi kafin yace"Maman Layan mun kira ki ne akan maganar Jabeer,a cikin satin nan nake so a tsayar da ranar auren Lamin to sanin kanki ne bazanwa Lamin aure ba nabar Jabeer, munyi magana da shi duk da ba wani mahimmanci yaba maganar ba amma sam banga alamun ma yana da wacce zai iya gabatarwa ba,wannan dalilin ne yasa na kiraki ki zauna dashi kiji ko yana da wani ra'ayi ko wacce zai gabatar idan kuma babu mu Sai mu zab'a masa nasan insha Allah kuma bazaiyi dana sani ba"....Murmushi Daddy Sadeeq yayi kafin yace"gaskiya lallab'a mun my son za'ayi dan bashi ma da wacce yake so a yanzu kam,bana tunanin a zaba masa kuma mafita ce in an zaba din ma ina rokar mana alfarma a bamu lokaci muji mun aminta da ita"..."kace kuwa Yaya Sadeeq babu ranar da Jabeer zaiyi aure kenan,kafi kowa sanin halinsa da kafiyarsa hasalima mata basa gabansa ,ni a gani na batun ma a tsaya tambayar ra'ayinsa bata taso ba ,Ku ke da iko da Jabeer nasan ba zaku samu matsala da dangin mahaifansa ba tunda abun alkhairi kuke da niyar kullawa,duk abunda kuka yanzu hakan za'ayi bamu da wani ja a cikinsa fatanmu kawai Allah ya tabbatar mana da alkhairi ".jinjina kai Abba yayi ya kuma cewa" duk da haka Mamana jin ra'ayin nasa nada mahimmanci,kiyi magana da shi sai ki sanar da ni yarda kukayi insha Allah koma menene zan nemi General kuma akan maganar".Da haka suka rabu Momy ta taho tunaninta na kuma rabuwa gida biyu,a yanzu ne take da damar aikata abunda ke ranta sai dai can kasan ranta tana jin rashin kwarin gwaiwa da kuma fargaba amma tana ganin kamar hakan shine mafita da kuma kwanciyar hankali da zasu samu baki d'aya.a parlonta ta same shi a zahiri ya kurawa TV manya manyan idanuwansa masu matukar haske da kyau sai dai sam hankalinsa gaba daya baya kan TVn dan bama zai iya fad'ar me ake cewa ko akeyi a ciki ba,shidai kawai kallah yakeyi yayin da zuciyarsa tayi nisan kiwan lulawa duniyar tunanin takaicin da kuma yarda zaiyi da rayuwar yarinyar can da duk yarda yake sai ta bata masa rai ko san ganinta baya yi,har Ammi ta zauna kusa da shi sannan ya juyo yake kuma gane wani ya iso in da yake be furta komai ba ya kuma jingina da kujerar yana lumshe ido.tasan idan za'a kwana a haka bazai taba cewa komai ba zallar b'acin rai da damuwa karara kawai take iya fahimta a kyakyawar fuskar shi.bata damu ba sam Dan tasan bakin halin nasa ne ya motsa tace"Abbanku ne ya aiko ni wurinka, yana so yaji shin ka tsayar da wacce kake so ,ko kuma kana da ita wacce kakejin hankalinku ya hadu da ita?".sai a lokacin ya ware manyan idanuwansa yana kallon Ammi sai kuma yace"ban gane ba Ammi".."ya za'ai ka gane dama ? ,kasan na zama k'awar wasanka ai".wani kyakyawan k'yataccen murmushi ya sub'uce masa Wanda ba kowa ke samun damar ganinsa yana murmusawan ba sai Ammi kawai da Hajja na ukkunsu kuwa LAMIN,ita kanta sai da tayi kasa da kanta tana tasbihi ga Allah daya cika halitta ya kuma wanzar da kyau a jikin Danta Jabeer ."babu ,ni meye hadina da Mata kuma Ammi?"Yayi maganar cike da shagwab'a .kallonsa take yana kuma tuna mata da abubuwa da dama sai fuskarsa duk yarda ake cewa tana tsananin kama da shi a yau sai ya juye mata sak mahaifinshi dama ba'a maganar murya da yawancin halayayyansa...Daure fuska ta kuma yi tace"to count your self among wa'anda zasu fara kulla alaka da matan "...Shidai kawai kallon Ammin yake yi as if his life defend on ita ko yana shirin gano wani abun a jikinta sai kuma yayi murmushi yace" ni dai ki fada masa bana son auren kuma".ko kallonsa bata yi ba ta tashi ta wuce d'aki abunta tana kuma tinano irin durgar da za'asha da wancan murd'ad'en halin nasa to amma kuma duk da hakan bashi zai sa a kyale shi ba .aure kam ya zama dole ko yana so ko baya so...Sosai Ummi tayi dariya ta kara gyara wayan dake hannunta tace"kai lamarin Jabeer sai shi Allah,yanzu dan Allah in banda shirme meye na wani a fadawa Abban baka son auren?"...other side Ammi tace"to ai Dan naki ne sai kin tashi tsaye kam sam baya jin ya girma sai shiririta cike da kai"..."kuma ai ba kyaleshi za'ayi ba,ni sai yanzu ma nake jin son auren daga baya ya gode mana duk zaiyi ya gama,ni yanzu babban tashin hankalina akan Asma'u ne,bansan ya akai hakan ta faru ba,ko kusa bana jin zan iya sarakuta da Badiyya bare harna wanke y'ata na kaita gidan nan a matsayin sirikarta ,I just can't think zan iya gaskiya"...ajiyar zuciya ammi ta sauke sai kuma tace"addu'a dai shine mafita, tunda yara suna son junansu bamu da sauran abunyi,kuma duk abundata in Allah yace za'ayi ai dolenta tayi hakuri,beside bana jin ma in maganar taje wurin Yaya zaki iya yin wani abu a kai"..."ko wajen General taje kuwa,ni gaba daya bana cikin natsuwa Allah Aunty Maryam ,Asma'u nason ta janyo mani abunda bazan iya jurewa ba"..."just pray Fatima,Allah ya zab'a abunda yafi alkhairi "...da Ameen ta ansa kafin ta ajiye wayar tana zancen zucin idan hakan ta kasance a ina zata saka kanta,dan ko kusa ba zata iya daukar lamurran Momy Badiyya ba dole ta taka mata burki....." Shi Jabeer din ya fada haka?"Abba ya tambaya.Dariya sosai Aunty Amarya tayi kafin tace"kasan dai wanene Jabeer to na jadadda zance kam be ta so ba,yanzu ina ga sai abi wata hanyar"...jinjina kai Abba yayi yace"to Allah ya zab'a abunda yafi alkhairi zan ganshi da kaina,in banda sakarci waye yake kin aure a wannan shekarun nasa.beside zan ma ga General kawai amma zamansa hakan bazai yiwu ba,bana so kuma wani ya sake tada masa maganar a cikin gidan nan Ku barsa kawai nasan abunda zanyi insha Allah"gaba dayansu da addu'a sukabi lamarin musassan Daddy dan shi in a nashi ne beki an gyale Jabeer ba har zuwa ranar da zai shirya da kanshi....
Share
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
*SHIN KINA D PALMPAY ACCOUNT? KO KINA NAN ZAUNE GIDA ANAYI BABU KE? GASKIYA A GAISHE KI,SANNU D ZAMA ANA SHANAWA BABU KE ,PALMPAY ALKHAIRI NE,HAJIYATA KINA ZAUNE A GIDA ZAKI IYA SAMUN 3K ,5K,10K,22K ME KIKA MANTA BABU AIKI KOMAI? KAI SHIFA DUK IN DA KIKA TABA KUDI NE,ACCOUNT KAWAI ZAKI BUDE DASU. BABU SISINKI BARE KISHA WAHALA,ME KIKA MANTA KULLUN KIN SAMU KIDINKI A ACCOUNT. TO MAZA GARZAYO DAN SAMUN NAKI RABON.GA MAI SO ZAI IYA TUNTUBAR*
07033636337
Page
20
Kallon Hajjan kawai yake yi sai kuma yace"kika ce zakije can?".cike da dattoko da tsantsar mutunka irin wacce ta kama ta tun yarinta ta murmusa kafin tace"to Jabiru wani abunne dan nace zanje gidanku? Wannan ai daddan abunwe tsakanina da Annie Wanda ka riga ka dade da sani,tsufane kawai da ciwan k'afa ke hanani dan zagayawa,amma insha Allah kam wannan karon babu fashi"....jinjina kai yayi sai kuma ya kama Hannun masoyiyar kakar tasa Wanda yakeji tana d'aya daga cikin matan daya keb'ance a zuciyarsa yake masu madaukakiyar soyayya yace"to ki zauna sai na kawo maki Annie,itama naji tana cewa zata zo,kinga baki da lafiya Hajja".ya karashe zancen cikin cool voice dinsa wacce ta riga ta gama kama masa jiki..Girgiza kai tayi tace"wannan ladan zumuncin sai na sameta,zanje na zagaya kowa,wama ya sani ko shine na k......"kafin ta karasa yayi saurin tsureta da idanuwansa da suka soma sauya launi lokaci d'aya fuskarsa tana nuna madaukakin tashin hankalinsa ya soma Girgiza kai muryarsa a dishe yace"Hajja dan Allah kada ki soma,ni bana son irin maganganun nan,nasan mutuwa dole ce,amma bana kwatanta tafiyarki a yanzu ban shirya dauka ba,dan Allah ki daina".wani murmushin ne ya kwace mata a kan kyakyawar farar fuskarta Wanda daka kalla zakasan a zamaninsu anyi gwagwarmaya a kyau,ta shafa kansa tace"Ayya Jabiru mutuwa ta Allah ce ko yanzu ya kira mu dole mu ansa kira,fatan kawai Allah ya mana arzikin kyakyawan karshe ya mana maganin abunda yake damunmu"ta kare zancen tana tattare littafanta na addini da take karantawa tare da carbahan hannunta ta saka a jakarta irin tasu ta tsaffi tace"to tashi muje ka kaini,dan yau a can zan wuni".karbar mata jikkar yayi kafin suka fito a hankali yake bin bayanta har wurin mota ya bude mata back seat ta shiga ya gyara mata Hijab dinta ya rufe kofar sannan ya zagaya Driver seat ya shiga ya rufe ya tada motar suka wuce gida......A parking lot ya ajiye motar kafin ya fito Layan dake tsaye a wurin tana bawa gateman kulan Abincin da Umma ta bata yana mata godiya ta juyo da sauri ganin Hajja a motar Jabeer din ,kwata kwata ta manta da duk wani abu da zai iya yi mata ta rugo da gudunta zuwa wurin motar,Daga glass na motar yake hangota ,English wear ne jikinta siket red irin mai budadden nan sai ya baje sosai ko kafarta baka iya gani,sai white T-shirt itama mai fadi red veil mai dan girma ta yafa a sakalkeken dogon gashinta data tunkushe wuri daya wani tsabar takaici da kunci ya tokare masa zuciya ganinta da yayi.saurin dauke idonsa yayi yana hadiyar yawu da kyar na takaici.kafin yayi wani yunkuri tuni ta iso taja murfin motar ta budewa Hajja wani irin farin ciki yana cikata kallo daya zaka mata ka gane irin farin cikin ganin Hajjan da tayi,cikin sanyin muryan nan nata take fadin"oyoyo Hajjana sannu da zuwa ,barka da zuwa ,lallai tsohuwar nan da kokari kike harkin rigamu zuwa gobe muke cewa muzo tare da Annie"jin muryarta yake har cikin kokon kwanyar kansa saurin lumshe idanuwansa yayi ya daura kansa a sitiyari sai kuma kamar Wanda aka mintsina ya mike ya balle murfin motar da sauri ya fito,sai dai yayi tsaye yana kallonta harta fito da Hajjan tana rike da hannuwanta cikin nata tana kuma gyara mata takalmanta dan suyi mata saukin sakawa tana a duken tace"Yaya Jabeer ka dauka mata Jakkan a mota sai in karasa da ita wurin Annien ".bata damu ba sam ko tuna yanayin da zai iya kasancewa ba ta soma jan hannun Hajjan suna yin gaba,lallausan gashin kansa ya shafa Wanda ya ragewa yawa kasancewar ya koma aiki yayi ,jakkan ya dauko ya rufe motar ya biyosu baya,very carefully take tafiya da Hajjan da tsantsan gudun kada tayi wani abu ba daidai ba,musamman ma yarda take tsananin son Hajjan da kuma jin tausayinta jinta takeyi kamar Anninta suna zuwa daidai k'ofa cikin kausashiyar murya yace" ya isa haka,barta zan shiga da ita".kallonsa tayi da manya manyan idanuwanta tace"Yaya zan iya,ai ina shigowa da ita idan baka nan"..."kaji mun ja'irin yaro Maryam din meta kasa mun? Tsakanina da yarinyar nan ai sai dai saka albarka Fatima da Sadiqu sunyi farar haihuwa,Allah ya jibanci lamurata ya bata miji na gari".saurin yin kasa da kai Layan tayi dan maganganun Hajja sai suka mata nauyi a kai taji kadaukakiyar kunya ta rufeta tace"Hajja muje"har kan sofa na Annie ta ajiyeta d'akin Fes da sai tashin kamshi yakeyi kamar ba'a shiganshi sai gyara kullun .daidai k'afar Hajjan ta zauna tana dan mamatsa mata kafan da mata sannu tace"bari a kirawo Annien nasan tana kitchen ".kafin ta kik'e ta nufi kitchen din tana kwalawa Annie kira .Hajja ta dubi Jabeer tace" Allah da Sadeeq xai iya daya bani yarinyar nan mun zauna,Allah ya sani ina matukar sonta da jin dadin zama da ita fiye da ko wacce yarinya".kallon Hajja kawai yayi ya kawar da kai bece komai ba,danshi nan zuciya ta gama kaishi karshe gaba daya duk tayi kane-kane da Hajja ta hana ya mata komai,bayan aikinsa ne in dai yana tare da ita baya bari wani ya mata wani abu ko da su Ummi ne ke zaune kuwa..."lafiyarki kuwa? Kamar wata tsohuwar makauniya zaki isheni da kira ko me zan maki ma oho"Annie ta fada tana karasa juye miyan zogalen da tayi a kula...Dariya Layan ta saki tace"ni bazan biye maki bama,Hajja ce tazo".saurin ajiye ludayin hannunta tayi tace"kai dan Ma'aiki? Hajjan dai dana sani? Hajja tawa? Dan duk garin nan bani da kamarta wani ma sai ya fiye maka dan uwanka na jini wallahi"..."ita dai da kanta tana parlo tana jiranki"Layan ta fada tana dauko tray ta nufi fridge zata dauko ruwa da lemun tattatun itatuwa da Annie keyi ta ajiye dan bata shan na kwali ko roba sam"....Baki a washe Annie ta karaso tana lale lale da ganin Hajjan tana nuna jin dadin ganinta da tayi ta zauna tana fadin"godiya ta tabbata ga Allah kafa tayi kyau alhmdllh,kinga Wanda bega damar kaini ba,tun jiya nake rokonsa kamar wani abun arziki zai bani amma yamun kunnan uwar shegu,dama Laminu ko Faruqu nake jira gobe su kawo ni kuma sai gaki".Jabeer be kula Annie ba ya fita yabar mata dakin gaba daya dan yasan yau tsab sai tayi masa terere na duk wani abu da Wanda ya sani da Wanda bai sani ba......"nima sai yanzu da yaje na taso shi gaba in ba haka ba ya fita ba kuma ganinsa zanyi ba,sai yace wai bazan fita ba"...rike baki Annie tayi tace"to Hajja wake biyewa Jabiru ? Waya gaya maki yana zumunci shi? Ai lamurran Jabiru sai dai addu'a kawai kam ya sab'a da Sadiqu mariganyi Allah ya jikansa ,muda muke so ya zama makwafinsa amma kin ganshi nan kullun fuska a hade ba annashuwa zuciya cike da bakin hali,ya zamarwa yarinyar nan kamar Dodo duk kokarin da uwayenta sukeyi a kanshi amma sam baya duba wannan,na kusa fara sawa a fara masa rokon Allah ko Allah zaisa a dace da wannan hali nasa mu samu sauki".Annie ta kare maganar tana kallon Kayan dake bawa Hajja Lemu a glass cup,ta karba ta saka mata albarka....
Share
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
*SHIN KINA D PALMPAY ACCOUNT? KO KINA NAN ZAUNE GIDA ANAYI BABU KE? GASKIYA A GAISHE KI,SANNU D ZAMA ANA SHANAWA BABU KE ,PALMPAY ALKHAIRI NE,HAJIYATA KINA ZAUNE A GIDA ZAKI IYA SAMUN 3K ,5K,10K,22K ME KIKA MANTA BABU AIKI KOMAI? KAI SHIFA DUK IN DA KIKA TABA KUDI NE,ACCOUNT KAWAI ZAKI BUDE DASU. BABU SISINKI BARE KISHA WAHALA,ME KIKA MANTA KULLUN KIN SAMU KIDINKI A ACCOUNT. TO MAZA GARZAYO DAN SAMUN NAKI RABON.GA MAI SO ZAI IYA TUNTUBAR*
07033636337
21
Jinjina kai Annie keyi cike da alhini sai kuma ta tab'a hannuwa tare da cewa"gaskiya kinzo da babban al-akari duk da abun duka na gida ne kowa naka ne,kuma kowa zaiso jin hakan wannan gyaruwar al-amarin amma ,kuma ai an zama daya komai kika yanke bazance a'a ba in dai ni yar halasce wacce bata manta alkhairi to amma kamar yarda kika ce bari yanzu in da Laminu yamun kiran Ahmadun dan shi Sadiqu ba'a ma ta tashi shima cewa zaiyi a tuntubi amadun".waya Annie ta lalubo tace "bari a sanar da muta gidan zuwanki in kuma kira shin dan ba'a barki da girmanki kina jiran shi ba". Murmushi Hajja tayi cike da jin dadin duk da tayi tsammanin kin amincewar Annie duba da yarda al-amuran ke kasancewa amma kuma sai taga sam ba hakan bane ita a nata b'angaren bata wani ba....Bakinta dauke da sallama ta shiga parlon duk suna zaune Hydar ne yace" a'a Hajiyar masu gida da kanta,tuba muke yau ke da kanki kika fito"Aunty Amarya na dariya ta karaso gaban Annie tana gaisheta with Respect tana sunkuyar da kai tace"Annie akwai wani abunda kike buk'ata ne?"ansa gaisuwar tayi sai kuma tace"dukanku Baku san Hajiya Aisha tazo bane da babu Wanda yaje ya gaisheta?".sunkuyar da kai Aunty Amarya ta kuma yi tace"a hafarcemu Annie dama ina so na karasa girki ne sannan kun gama gaisawa sai mu shigo,amma tun dazu Jabeer ya sanar mana da shigowarta,to ina so a taho mata da abincin ne"....kyab'e baki Annie tayi tace"itafa Badiyar?".kallon sashen Momy Badiyyan Aunty Amarya tayi sai kuma tace"tana ciki".wuceta Annie tayi ta mikawa Faruq wayarta tace"latso man ubanka".Dariya Faruk din ya kunshe cikin son tunzura Annie yace "uwayen nawa ai da yawa to wanne daga ciki?". Sake baki Annie tayi sai kuma tace" to da wancan narkekiyar matar kake,nace ka kira man Amadu kana mun marshin kunya".kafin yayi magana ya tsinkayo hararar da Momy Badiyya ke xabga masa ba arziki yaja