Showing 15001 words to 18000 words out of 55893 words
Chapter 6 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt
magani uban kowa yayi ta kansa dan ba zan ragawa kowa ba bama-bamai kawai zasuita tashi a cikin gidan nan haske ya bayyanar mana wallahi".....
Share.
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
12
Da sallama ya shiga bedroom din ya tsaya bakin k'ofa fuskarsa a sake yana kallon Momy dake mayar da kaya a press kallo d'aya ta masa ta dauke kanta bata dai ce komai ba.cike da murmushi Lamin yace"Momyna maganin kukana ,yau kuma ba zaki kula Dan gaban goshin naki ba? Momy nayi kewarki ,ina tashi yau kuma ake cemun kinje unguwa bamu samu damar haduwa ba sai yanzu".still batace komai ba,karasawa yayi cikin d'akin a hankali ya daura hannuwansa akan kafadarta tare da langabar da kai ya koma abun tausayi yace"Kiyi hakuri dan Allah Momyna! Fushinki a gare ni masifa ne ,yana kuma d'agamun hankali fiye da komai a duniyar nan,in ma wani abu nayi insha Allah bazan kuma aikatawa ba,ki sani sai dai idan na yishi bada sani na ba ,tuba nake farin cikin rayuwata".Ya kare maganar da kashe ido d'aya.kayan dake hannunta ta jefa masa gaba d'aya sannan ta koma gefan bed ta xauna tana kallon shi kafin tace"Lallai Lamin tambayama kake yi idan kayi wani laifi?,kuma tambaya kakeyi na fita bamu haduba? To ansa d'aya ce da wacce ka dauka ka bawa matsayina ce ai da kasan da fitarta ko ince har ka kaita ma,amma ni da ba a bakin komai nake ba ,baka ta tawa ai saidai daga baya kazo kana damuna da surutu marar amfani,aini tuni Lamin ina niyar sallamaka ga Maryam wallahi,tuni na kusa cire hannuna daga lamuranka"...dukawa yayi akan gwaiwowinsa ya kama hannuwanta yace"Momy dan Allah ki daina fadan haka,har abada bani da madadinki ba kuma zan tab'a samu ba,matsayinki gaba yake dana kowa a zuciyar Lamin,kawai dai naga Ammi batayin wani abu Wanda be dace ba kuma duk d'aya ta dauke mu da Dan data Haifa babu wani banbanci ko wani abun kyara data tab'a nuna mana Hasalima nakanfi Jabeer matsayi a...."."ya isa dakata mun daga nan,in dai aka ce yaro to har abada yaro ne,duk wata soyayya da Maryam zata nuna maku ni nasan karya ce Maryam bata taba sona to haka zalika ba zata taba son abunda na Haifa ba,Wanda ya kika tun farko gaba ko yace yana sonka karya ne,but is a matter of time lokaci zai maka bayanin komai Lamin ,ka barni zan karasa aikina"...Murmushi kawai yayi ganin ta hassala kuma yasan ko zai kwana yana mata bayani ba zata taba fahimta ko yarda ba yasa kawai yayi shiru yace"ki bari zan karasa maki "be jira cewarta ba ya soma karasa kwashe kayan nata yana jera ko wanne in da ya dace....."ko kad'an na kasa gane wannan halin da kike neman daurawa kanki Layan,shin a ko yaushe kin fi son Ammin naki ta kasance cikin tunani,ni dai kinsan bazan dauki wannan sakarcin da kika Riga kika saba dashi ba,bafa zai yiwu kizo ki saka ni a gaba ba cas ba as kita mun kunburi ace yau kwana biyu kina ciwo kuma abinci ya gagareki ci ba,k'arama kin tattara kayanki ki koma wurin Annien ko Ammin taki nikan Fatima bada ni ba"... Rau rau da ido Layan tayi sai kuma tace" Umma yaushe Yaya zai dawo?".kallonta kawai Umman tayi ta kawar da kai sai kuma tace"I think you have his number? Meye amfaninta a wayanki ?"kallonta Layan tayi sai kuma ta kawar da kai kokari kawai takeyi ta hana hawayen da suka taran mata a ido zubowa,da sauri ta tashi tayi d'akinta na part din tana jin zuciyarta ta mata wani irin nauyi gani takeyi kamar duk wani kuncin duniya ita aka tattarawa a kai ganin bata da abunyi kawai yasa ta daura kanta akan pillow tana sauke numfashi hawayen nabin gefan fuskarta. Tuni ta Lula tunanin sai yaushe ne sai wace shekara ne Jabeer zai yi mata koda kallon mutunci ne,a duk duniya burinta d'aya a rayuwa ko da zai zama aiki na karshe a rayuwarta ya zama Jabeer ya kulata ko da bazai sota ba,ta yarda ita zata so shi ko da bata numfashi .saurin mikewa tayi zaune ta d'aga hannuwanta duk biyun ta kalli gabas cikin tsiyayar da hawaye tace"Allah kai ne ya Allah,kai ne buwayu gagara misali,Kaine mai bayarwa kuma mai hanawa idan ka bada ya badu,Kaine kuma Wanda kace mu rokeka da darajar annabinka, annabi muh'd SAW kayi alkawarin zaka ansa mana,ya Allah dan girma da iko da buwayarka gareka nake nema bani da wayau ko dubaran da zan taimaki kaina sai in kai ka taimake ni,ya Allah na miko kukana zuwa gareka albarkacin sunayenka tsarkaka kyawawa ya Allah na rokeka kafin nabar duniya kasa ina da rabon zama a karkashin inuwar auren Yaya Jabeer ko da bazai so ni kamar yarda nake sonsa ba ya Allah na rokeka kasa akwai ranar da ko gaisuwata zai ansa cikin saukin rai,ya Allah ka rage masa zafin tsanata da yake ji a ransa".ta k'are addu'ar tana silalewa akan bedsofa ta runtse idanuwanta tana ambaton sunayen Allah tare da dafe saitin zuciyarta dake barazanar tarwatsewa...in same time Jabeer ne zaune yana shan iska a madaidaicin parlonsa ,sanye yake da white 3quater sai short sleepless armless yana fitar da wani irin sihirtaccen kamshi gashin kan nan sai sheki yakeyi a always coppee cup ne a hannunsa sai tirir yakeyi ya mike long legs dinta a glass table da yake gabanta,idanuwansa a lumshe yayin da zara-zaran lashes dinsa suka sauka a fuskarsa gwanin kyau ,wayace kare kunnansa yana sauraran me ake fad'a masa,cikin husky voice yace"yanzu dan zubar da mutunci yarinyar sa'ar wannan yarance zakace ta kusa zautaka?".sanyayyar ajiyar zuciya Lamin ya sauke daga d'ayan bangaren yace"to gyambo uban son girma idan ban so y'ar 22 ba sa'an Annie kake so na nema?".sosai fuskar Jabeer ta sake kamar zaiyi murmushi sai kuma ya daure yace"ai itace daidai da kai mayen mata! Ni har abada bazan taba so ba,bani da lokacin b'atawa,kai da kaga zaka iya to bismillah".Dariya Lamin ya saki tare da cewa"na roki Allah yasa a maka auren dole dai in ga ta cika baki,kai kamar ba mutun ba,ace mutun bashi da feelings sai shegen taurin kai kamar na mutanan farko"."dafe kai Jabeer yayi alamun Lamin ya soma isarsa da surutu cikin law voice yace"to ko dai zaka gwada yimun ne ubana"."ai da nazo a iyayenka wallahi Jabeer da ka gane waye kai duk wannan fankan fankan din da bakayi ba,a kullun ma dukan da zaka rika kwasa kawai ya isheka,ina kuma fada maka I'm in love,yarinyar nan rayuwata ce kuma numfashina ce bana jin zai iya yin rayuwa mai tsayi idan har ban mallaketa ba to tabbas nima bazan wani amfana a duniyar ba zan mutu,ina so na zame mata garkuwa bango abun jigina na kuma jib'anci lamuranta sai dai bansan wani bigiren rayuwa zata kai ni ba,amma ina rokon Allah daya tabbatar da kasancewarmu a tare ko dan Ku rika gane kaina k'anena"..tsaki Jabeer yaja bece komai ba ya kashe wayarsa yana jin ansa kuwar maganganun Lamin a kunnuwansa kamar yanzu yake fad'a masa,tabbas a duk duniya bayan Ammi babu wata halitta da yake so take kuma fahimtarsa irin Lamin baya jin zai iya juran wani abu ya samu Lamin a duniyar nan,yana masa wani irin so marar algush so na tsakani da Allah Wanda yake jin har ransa xai iya badawa fansa a rayuwarsa idan yiwuwar hakan ta taso.Luckily ya saki murmushinsa mai tsananin kyau Wanda ba kasafai aka fiya ganin yayi shi ba sai dace tuna abunda Lamin yace na a masa auren dole.shi a rayuwa he's a man of principle yana da tsari da dokoki yana son ko aure xaiyi mace ta so shi dan Allah tayi masa tsananin so kamar yarda yake tanadawa duk wacce ta samu damar shiga gidansa a matsayin mata, shiyasa be taba soyayya ba bai kuma taba nuna zaiyi baa dan duk macen daya kallah sai yaga bazai taba samun abunda yake so ba shiyasa ma bai fara ba,a rayuwa ya tsani kalmar dole balle kuma hakan ta kasance a aure baya jin zai iya lamunta ko goyon baya ayiwa wani ma bare kuma shi......
Share fisabilillah.
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
13
"Yau kuma a zama d'aki zaki k'are iyeee Laya? Ni gaba d'aya ma na kasa gane maki duk kwanakin nan,halan cuta na damunki bayan wacce kowa ya san kin goga daga dangin mahaifiyarki,dan mu kaf danginmu babu wani mai cutar azo a gani sai dai wacce Subhana yake daurawa bayi lokaci zuwa lokaci" Annie ta k'are magana tana kallon Layan dake kwance a bed.Tura baki gaba tayi sai kuma tace"wallahi ke Annien nan sam ba zaki barni in huta ba,na gudo wa fad'an Umma amma kema kin saka ni gaba,ni babu abunda yake damuna"."kedai kika sani,ki tashi ki shirya ki rakani gidan wancan narkekiyar matar kafin a kwana biyu kuma mujewa Hajja itama,danni ina so in fita hakkin zumunci bana so Allah ya kama ni,Allah yasan ina kokartawa iya iyawata komai dai ina yi daidai gwargwado dan baka biye ta halin mutun ba".Shiru Layan tayi sai kuma ta tuna idan ta fita duk tarin damuwarta ta rage mata ko da na kafin su dawo ne,dan yanzu yarda take jin gidan kamar kurkuku haka take daukarsa ya zamar mata kango indai har Jabeer baya cikinsa...Mikewa tayi sai tace"to ki jira ni na shirya zanje b'angaren Ammi"."wacece wace Ammi? Me hadinki da ita? Me kuma kika manta a can,ina in tsumakarai ne kina dasu a nan,to ni bana son terere yanzu sai kija ta bijiro da maganganun da ni ba iya dauka zanyi ba,sai in sa kai dama Laminu ne zai ajiye ni sai in wuce abina,komai ai yana son sirri".Layan bata kuma cewa komai ba ta shiga toilet din Annie dake bedroom din danyin wanka cikin minti 30 ta gama shiryawa cikin atamfarta brown mai ratsin fari da blue sosai tayi sanyayen kyau atamfar ta dace da chocolate skin dinta sai fitar da sanyayen kamshi take,as always agogo ta daura a left hand nata sannan ta dauki gogegen lite blue long hijab dinta data sha turare ta saka sosai ta kuma hadewa dan ita duk rawan kan Layan bata rabo da long hijab nasa school ne kawai shima dan akwai lab coat yasa take saka mini hijab amma sam ko gyale d'aya bata dashi duk kuwa irin yarda su Basma ke daukar wankansu ita bata damuwa ba Wanda ya tabayin complain akan shigarsa phone dinta ta dauka with white hand bag da with flat shoe saboda yana yin tsayinta ,tarkacenta ta saka sannan ta fito parlo ta samu Annie data gama gadewa cikin sabuwar Atamfarta ga babban mayafi an yafa sai Jikka irin tasu ta manya,sosai Annie ta washe baki tace"to ko kefa da kin tsaya nuku-nuku? Zamanin nan wa yake cutar kansa?komai ai a bude ne tunda ba zaman kowa kake ba,dama tun asuba na fadawa Ahmadu zan fita ".....lockily tunda suka fito idanuwansa na akan kofar part din Annie ,idanuwansa ne suka sauka akan kyakyawar fuskar Layan da tayi wani sanyayen kyau mai daukar hankali duk da a fuskar nata white lip gloss ne kawai sai kajol data saka a dara-daran idanuwanta Wanda suka kara girma da matukar haske ,sosai ya shagalta da kallonta yana sauke wani sanyayen ajiyar zuciya a Jere a Jere ,a ko wanne lokaci ji yakeyi Layan tayi daban ta kuma yiwa sauran mata xarrah,shine kadai daya mayar da hankali a kanta ya fahimci tarin qualities dake tattare da ita,sabanin yan gidan da suke mata kallon mai rawar kai da son hayaniya da guje-guje ga neman tsokana.tunaninsa ne ya katse lokacin da small cool voice dinta ta dokin dodon kunnansa tana kuma tafa zara-zaran dogayen siraren hannuwanta Wanda yatsun suka sha ado da Jan lalle a daidai fuskarsa,wani irin sanyi ya cakude da sanyayen kamshinta ya doke shi lokaci d'aya,lumshe idanuwansa yayi yanajin natsuwa sosai na ratsa duk wata gaba ta jikinsa,Murmushi kawai ya mata kafin yace" you look so Good".Murmushin itama tayi tare da cewa"thank you Yaya"Front seat ya bude mata ta shiga kafin ya budewa daketa kyab'e baki ita ala dole ya fara budewa Layan mota,shiga tayi sannan ya rufe ya zagaya driver seat ya tada motar da bismillah yabar gidan....kallon motar kawai Momy keyi har suka fice daga gate din gaba daya,ji tayi zuciyarta ta mata nauyi kamar an daura wani abu a kai,sakin curtain na kofar benan tayi dama Abba ne tazo ta kawowa Abinci yace ba dadewa zai shigo kuma a sama zai zauna dan yana so ya huta baya dan jin dadi.warmer din karshe ta ajiye ta fita zuwa parlonta tabajin zuciyarta kamar zata fasa kirjinta ta fito,A zaune ta samu Hajiya Sha'awa taci ubansun gayu da wani Danyan less wuya da hannuwa duk gold fuskarta dauke da murmushi take kallon Momy kafin tace "Barka dai Hajiya Badiyya,gani bakuwar da zuwa ba sanarwa na daizo goge laifina". Sake baki Momy tayi kafin tace" yaushe a gari Aminiya? Kin barni nan abubuwa duk sun dau zafi,yaushe ma kuka dawo k'asar?"ta kare zancen tana zama kusa da ita suna tafawa ta irin yaushe gamo.Hajiya Sha'awa aminiyar Momy ce tun ta yarinta ,ita tana auren Ministern ilimi ne to sun jima a England sai satin nan suka dawo Nigeria gaba daya saboda y'arsu kuma Autarsu ta karasa University a can yaransu biyu duk mata Jamila ita ce babba tayi aure sai Ihsan waccew ta d'an girmewa su Layan Auta...."wallahi 2days back muka dawo kinsan Y'ar taki ta karasa University din nata".Hajiya Sha'awa ta bata ansa,"kai alhmdllh kice sai munzo hada fati,Allah yawa abunda aka karanta albarka".Hajiya Sha'awa ta ansa da Ameen.kafin tace"naga kin shigo a birkice? Badai har yanzu kin kasa shawo matsalar gidan nan ne ba Badiyya!".Nauyayen ajiyar zuciya Momy ta sauke tare da cewa"bari kedai k'awa,wallahi nayi kewar tafiyarki,ni bama matsalar gidan nan bace gabana,wannan duk mai sauki ne akan mugun abunda ke shirin tinkaro ni ,nikan akan shi na yarda nayi yawo tsirara in dai zan hana faruwar wannan al-amarin"."to menene zai tinkaroki da har zata fiye maki matsalar gidan nan,gidan da aka cika da mata birjik".."bari Hajiya Yaron nan Lamin,Lamin na gama gano take takensa wancan yarinyar Mayyar mai zubin mutanan farko yake nema ya bayyana yana so kinsan idan hakan kuma ta faru kowa zai Goya baya,nikan kara na mutu dana hada jini da Fatima wallahi".wani kallo Hajiya Sha'awa tabi Momy dashi kafin tace"dankari,wannan shine an gudu ba'a tsira ba,lallai kuwa tashin hankali Wanda ba'a saka masa rana ,wannan kam abunda bazai taba yiwuwa bane,kara ki tashi tsaye in zaki tashi,amma ni a ganina ki turosa su daidaita da Ihsan kawai ita dama kinsan tana sansa ,dauketa a k'asar nan ne ya nisanta alakar dan ko yanzu sai da ta bani sakon gaisuwa zuwa ga barristern"Ajiyar zuciya Momy ta sauke tare da cewa"shikenan kuwa,kafin yayi wani yunkurin ni zan bijiro masa da bukatata wallahi badai ya kwaso man jinin matsiyata ba,kisa a ranki anyi har an gama Ihsan ta gama zama matar Lamin aini kara mun hakan,kai wallahi naji dadin dowarki dan kaina ya kulle duk wannan tunanin bai zomun rai ba,tashi mu shiga daga ciki ki samu kici ko wani abun,rudu yasa ko lemo bansan an kawo maki ba"."kinga ni wucewa xanyi dama nazo ne na goge laifina ki kuma san na dawo,to ashe zan iske wani abunne kuma,duk yarda ake ciki dai kya kira ni danni banma so kafin yasan da maganar ya fara ganina a gidan nan"..rakata Momy tayi har gate in da driver dinta ke xaune yana jiranta,sallama sukayi Kafin Momy ta dawo ciki zuciyarta cike fal da farin ciki,tana kuma tunanin ta ina zata fara.
Share
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
14
Da Murna Ummi ta tari Annie cike da karramawa a babban parlon dake gidan ta sauketa, tana rungume Layan tare da cewa"your welcome Daughter ".Murmushi Layan tayi tace" I miss you Ummi"."ke tafi can idan kinyi kewata meya hanaki zuwa? In dai kince nan ne nasan Fatima ba zata hanaki zuwa ba uwa uba kam Ammin taki".kyab'e baki Annie tayi tare da cewa "to ko yanzu ma sai da na dinga hadata da Allah kamar ina neman wani abu wurinta sannan yarinyar nan ta fito sai kace wata sarauniya". Dariya taso kama Lamin sai kuma ya daure fuska yana gaishe da Ummi.cike da kulawa take ansa masa tana tambayarsa su Mummy da Aunty Amarya yace duk lafiya...rike haba Annie tayi tace" hmm barni barni Halin Badiyya ai sai ita ,yanzu ke kin manta komai har lafiyarta kike tambaya to amma badai Badiyya ta tako k'afarta tazo Ku sada zumuncin Allah ba".saurin kawar da zancen Ummi tayi wurin fad'in bari a samo maku breakfast, kafin a daurawa Annie lunch yau dole ayi gargajiya ai".washe baki Annie tayi tace"wallahi shiyasa sam ban kullace ki ba,nasanki akwai karrama bako da son zumuncin Allah,munci mun koshi Inaga Laya ce kawai ta tashi daga baccin sakalcin da suka saba".Ummi bata bi takan Annie ba taje ita da maid dinta suka kwaso kulolin da suka k'arsa break kamar ta sani akayi yau da yawa.tana jera kulolin ta soma kwalawa Jalila kira ,Gurasa ne da farfesun kan rago sai ruwan shayi da yaji kayan kamshi sai farfesun catfish. Jalila ne ta fito with much of surprise ta tsaya tare da zaro ido sai kuma ta saki dariya ta karaso parlon da sauri ta zauna kusa da Annie tana fadin"lale lale da Hajiya Annie ,kai yau rana ce mai kyau sannu da zuwa sannu da zuwa yau dole na daura tukunyar dambu ".kyab'e baki Annie tayi tare da cewa" ke wuce can kinsan zakiji dadin ganina amma kika gagara takawa in da nake? To ni dan uwarku nazo badan Ku ba,Dan in an biye ta taku a hanya ma sai in juya kai dama mena had'a daku wacece wata Lila ana zaune k'alau to ina kuma Ma'un take ne?".sosai Jalila da Layan suka kwashe da