Showing 21001 words to 24000 words out of 55893 words
Chapter 8 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt
kikaji kina sonsa kina son kasancewa dashi?".wannan karon kallon Ammi tayi daga zuciyarta take jin tsananin gamsuwa dan haka tace"wannan ai ba wani hali bane marar kyau Ammina,sanin kanki ne babu wacce ba zata so ta mallaki Yaya Jabeer ba saboda duk wani qualities da ake buk'ata he has it,wannan ai halittar Allah ne kuma Wanda ya hada duk wasu nagartattun halaye mezai hana a same shi mishkili irin haka duba da irin rayuwar daya taso,kawai Yayana he's a man of principle kawai"..Rike hannuwanta Ammi tayi duk biyun tana kallonta kafin tace"ni na haifi Jabeer my Dear,amma bana jin soyayyar Jabeer a zuciyata kamar yarda nake jin soyayyarki a raina Layan,aure rayuwane na har abada ba jeka ka dawo ba,sanin kanki ne akwai wata kaddara da Allah ya kaddara a tsakaninku da Jabeer Wanda babu Wanda yasan mafarinta bare kuma ranar karewarta kullun namu shine kawai addu'a,amma nayi maki fatan kiyi auren kina so ana sanki ,in da zakiyi mutunci ki kuma shinfida zuri'arki cikin aminci Layan,sai dai zuciyarki bata bi dake ta wannan bigirin ba,sai tabi dake tsani mai tsananin wahalar wucewa ,in da zakbi shawara da kin hakura da Jabeer ,rabuwa da Jabeer is not the end of your life my Dear kawai zaki sake sabuwan rayuwane kiyi addu'a Allah zai kawo maki da wani Wanda yafi Jabeer din,amma auren Jabeer bana jin hanyace mai billewa a gare ki Daughter "...hawayene Ammi ta gani suna riga rigan safkowa daga idanuwan Layan cikin dishewar murya da rudewa da rashin sanin abunyi tace" Ammi bazan iya ba,banzan iya ba,nasha gwada hakan a rayuwata amma bana tashi da komai sai damuwa da tsananin tashin hankali,even kasancewa dashi will be the last thing da zanyi a rayuwata Ammi zanso hakan ,muddin na rabu dashi wallahi Ammi mutuwa zanyi".ta karashe zancen tana fadawa jikin Ammi ta saki kuka daga zuciyarta...Bubbuga Bayanta Ammi taci gaba dayi tana tunanin tabbas tana da ikon saka Jabeer Auren Layan sai dai bata san wanne irin zama Layan zata yi ba,dan ba zata bisu gidan auren ta zauna dasu ba,tasan waye Jabeer ta kuma san wacece Layan tasan tunda yace baya yi ko ya ansa hakan bazai taba sa yaso Layan din ba,Jabeer wani irin murdaden mutun ne Wanda keda wata bakar zuciya, izza da mulki duk a cikin jininsa suke duk da bai kasance dan sarauta ba amma rayuwarsa da tsari,ga taurin kai kamar mutanan farko,bata fatan Layan tayi rayuwar kunci a gidan Aurenta sai dai kuma tayi nisa bata jin kira kuma bata iya jin zata iya tursasata tayi mata dole akan rabuwa da Jabeer din...
Share
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
17
Cikin isa izza da tsantsar kamewa yake barin parking lot din in da yanzu Driver ya dauko shi daga Airport, sam ya kasa samun wayar Buddyn nashi bare kuma yaje ya d'aukosa kai tsaye d'akin Ammi yayiwa tsinke sai dai turus ya tsaya daga k'ofa ya kasa karasowa yana wani sauke ajiyar zuciya...plate din hannunta ya subuce indomie din dake ciki ta zube a wajen jikinta har rawa yake ta kuma rasa what next da zata iya yi,wani irin takaici ya kumesa yana kuma kara ganin rawar kai da rashin hankalinta dan shi a rayuwa bai taba daukar Monster a matsayin mai hankali ba,k'asa kawai ta tafi akan k'afafunta tana niyar saka hannu a Abincin daya zube muryar Ammi ta karade parlon da fadin"ke kam lafiyarki? Da zafin zaki saka hannu? Bana son sakarci kin bar wajen nan ko kuwa"Ammi ta kare maganar tana bin shigar jikinta da kallo,3quater siket ne mai robar Wanda ya fitar da dan sirirn kugunta kamar an zana ash colour sai armless fara k'al kanta babu ko hula,sai a lokacin kuma Ammi ta mayar da kallonta kan Jabeer dake tsaye jikin k'ofa ,sai yanzu ta gano bakin zaren tabbas shi Layan ta gani har tayi mata b'ari a nan sharewa tayi tare da cewa"oya work out idan ba zaka shigo ba".ji yakeyi kamar ya juya sai dai yasan Ammi won't take it easily yasan sarai zata masa tas ne ta masa koran gaske, karasowa kawai yayi ciki yana mata sannu da gida,zama tayi a chair din dake facing dinsa ta ansa kafin tace"Layan ,Layan".lumshe idanuwansa yayi yana jin yarda zuciyarsa ke halbawa da karfi kamar zata fasa kirjinsa ta fito a iya jin ambatar sunanta ma kadai,bai gama recovering ba muryar Ammi ta karasa hargitsayi ya soma regretting zuwa garinma gaba daya"zaman me kikeyi a d'aki ? Ki kawowa Yayanki abun sha ".samun Kansa yayi da marairaice fuska ya tsurawa Ammi ido as if his life come to an end yana son yin magana amma he's speechless at all....Layan kam jiki na rawa ta karasa kitchen ta hado masa ruwa da drink din da tasan don shi Ammi ke ajiyewa ta daura duka a tray with glass cups ta taho making sure babu wani abu daya b'aci ko ya nuna rikicewarta.A cup ta zuba komai with cool voice tace"Yaya gashi". Ji yayi kamar an zuba masa wuta a kunnuwansa musamman data kasance a kusa dashi,sai dai ya kasa yin komai ganin yarda Ammi ta tsare shi da ido yasa ya sauke ajiyar zuciya yana kuma yin k'asa da kansa kamar bazaiyi magana ba yace"zan dauka"... murmushi Layan tayi ko ba komai yau kam zata bugi kirji tace yayi mata maganar arziki ko domin darajar Ammin data ci dama ta sani ko a lahira wani yana cin albarkacin wani...Mikewa tayi a sanyaye tabar wajen......da idanuwa kawai ya tsarr Ihsan dake fitowa cikin tankamemen parlon nasu Wanda ya gama tsaruwa da haduwa dan kyau ya kuma ji kayan more rayuwa.sanye take da atamfa dinkin gown tayi matukar d'ameta kamar a jikinta aka zana rigan,ga fuska taci uban make-up sosai tayi kyau amma sam hakan ya kasa burge Lamin dake kallonta kamar wata halitta ta daban,dauke kansa yayi ya mayar akan waya yana pressing kamar besan tana tahowa ba.da Dan sarsarfa ta karaso wurinsa fuskarta cike da farin ciki Ihsan bata da tsawo sosai sai dai tana da cika tana da kyau daidai misali bata da haske can sai dai man da take Shafawa ya hadu da Hutu ya karasa mayar da ita fara tas ,kusa dashi tazo ta zauna fuskarta kamar gonar auduga cikin dauki tace"baby sannu da zuwa,ya hanya? Ai na dauka ba zaka zo ba harna gaji da jira".Kokarin danne zuciyarsa yayi kafin ya kalleta yace"mezai hanani zuwa ,yasu Momy?".d'age kafad'a tayi Wanda yanayin dinkin ya bayyanar dasu a waje tace"sun fita"sai kuma ta mayar da kallonta a gabansa cike da zafin nan nata da yauk'i ta soma kwala kiran"suwaiba,suwaiba,uban meye kikeyi a ciki? In ajiye Mijina a nan amma baki kawo masa komai ba".Cikin sauri Suwaiba ta fito jikinta har rawa-rawa yakeyi tace"Aunty dan Allah kiyi hakuri ina had'a kayan ne ba'a shigo da drinks da wuri ba".tsuka kawai taja ta karbi tray din ta kori suwaiba tana kuma kara ruwan masifarta,Lamin kam bece komai ba sai binta kawai yake yi da ido.duk irin yarda suke gaisawa yasanta tun yarinta amma yau sai yaga ta canza masa ta zama wata ta daban duk ta koma masa wata bakuwa .....Murmushi kawai yayi ya karbi cup din drink da Aunty Amarya ta bashi yana kuma kallon Daddy kafin yace"kai maa sha Allah,Allah ya tabbatar mana da alkhairi".."badai bakuyi magana da shi Dan biyun naka ba?"Abba ya tambaya.drink din Kamun ya shafa kansa fuskarsa a sake yace"a'a na sani Abba,ban dauka azarbabi yasa harya fada maka bane".jinjina kai Abba yayi kafin yace"to kai fa Captain? Kasan dai bazan aurar da Lamin kai na zuba maka ido ba,kamar yarda kukeyin komai a tare to haka ma aurenku bana fatan na raba ba Jabeer".k'asa da kai Jabeer yayi baidai ce komai ba ,to mema zai ce bayan yasan ansan shine shi bashi da matar aure babu kuma wacce ya tsayar."aishi aure lokaci ne Alhaji,kowa daka gani Allah ya tsara masa nasa lokacin,ta yiwu ta nan Allah ya banbanta,kamar yarda ya banbanta nisan sama da k'asa sai a fara yin Wanda ya samu kawai ,tun da ba'a zauna zaman jira ba"Momy Badiyya ke fada tana zama kusa da Abba.abincinsa yaci gaba da ci kafin yace"insha Allah babu abunda zai raba,tare duk zan rika aurar da yarana da yardar Allah".sosai Aunty Amarya ta fad'a da fara'arta race"Allah ya amince ai ba dadi rabawan kam".Lamin da yayi sallama ya katse masu firan gaishe dasu yayi kafin ya zauna suna musabaha da Jabeer kafin cikin sanyi yace"Abba ka kira,jiya banji dadi bane shiyasa ban shigo ba"..sannu da jiki suka masa kafin Abba yace"naji sakonka wurin Mommynku to shine nake so na kuma jin tabbacin zance daga wurinka..."haba Alhaji to zan kirkira abunda bashi bane na fad'a? Yaron nan shi da kansa yaga Ihsan kuma kowa ya sansu tare tun ba yau ba,abune na tun kuruciya"Momy ta fad'a...tsura mata idanuwa Abba in a serious note yace"kinga Badiyya idan ba zaki mun shiru ba ga hanya ki fita,idan kin fada magana bazanyi aikina matsayina na uba ba?".kasa da kai Momy tayi sai kuma tace"ayi hakuri banyi tunanin haka zaka dauki zancen ba"...kuma kallon Lamin Abba yayi.Lamin kam Sau daya ya kalli Momy ya dauke kansa da Sauri sai kuma yayi kasa da kai ,all his attention is with him trying to figure what's going on da Lamin din dan tunda aka fara maganar ya gama fahimtar komai kawai out come na Lamin din yake son ji kafin ya gama tattara komai....sanyayyar ajiyar zuciya Lamin ya sauke sannan yace"eh Abba,ni nace mommy ta fara fada maka ,ni na zabi Ihsan din".A boye mommy ta sauke ajiyar zuciya duk da tasan Lamin din bazai taba bada ita ba,amma taba tsoron Abban ya gano wani abun..."to Alhmdllh insha Allah za'ayi komai kamar yarda ya dace dan bana so a ja lokaci,kaima Jabeer kaje ka huta zuwa gobe zamuyi magana da kai insha Allah".godiya sukawa Abban sannan suka fita.at all Lamin is looking so disturb kallo daya zaka masa ka fahimci haka,jan kunnansa Jabeer yayi da karfi har ya dan saki kara kafin yace"you okey? Waya fada maka ana wasa da aure ? Shifa har abada ne,tunda ka ansa kasan kuma magana bata canzuwa so guy chill".kyab'e fuska Lamin yayi kafin yace"Mommy love's the girl so I think I will do this for her,ba wata damuwa"....
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
18
Without any concerns dan yasan dama hakan zata faru,murmushin daya dade beyi bane ya sub'uce masa yana kallon Annie data takarkare tana mashi bayanin yarda akai tabar gida tazo gidan Ummi"to ni yar banza ce Jabeeru ? Ai kana barin gidan nan naji ya koma mani imty wallahi sam zaman ba wani armashi kawai na hada kayana na taho nan,ahto naga ai duk an zama d'aya zumunci dai Wanda yayi dan kansa, nasan ina komawa zaka samu maryam din can tana wani bubud'a hanci to ni bata daman ba,babu kuma Wanda ya iya ya sanya ni in yanke zumunci,jiya nan har Ali ta turo mun nayi masa fata-fata nayi masa korar kare,amma yau kafarka kafata"...."to ni ba gidan zanje ba".ya fad'a slowly ".." To meye wani ba gida zaka ba?,Allah na tuba kai kana da wurin zuwa ne?".Ummi ce ta katse masu firan tana fadin"yaushe a gari"...gaisheta ya farayi kafin ya fada mata lokacin daya dawo ,jinjina kai tayi tare da cewa"yau kuma Annie sai gida zaki bar mana kewa kuma".washe baki Annie tayi kafin tace"ai ba jimawa na dawo insha Allah,balle kinji auren yaron can aketa kokarin shiryawa kara naje kafin waccan narkekiyar matar tayi Kane Kane akan komai ta nemi maida kowa bare,ni kuma a lokacin zan nuna mata ba a banza muke ba wallahi,dan in zuciya ta ibeni tsab zansa Ahmadu gaba yayi mani maganinta".murmushi kawai Ummi tayi tana jinjina lamurran Annie jiya ba yarda Aliyu beyi da ita ba harda albishir din auren amma tayi fatali kuji yanzu kuma hankalinta gaba daya ya karkata can gidan Hajjan ma ta fasa zuwa...ba wani dadewa Jabeer ya ibi Annie suka wuce gida,kafin ta dawo Ammi taje ta gyara mata part dinta duk da ba wani barinshi akeyi ba gyara ba amma tasan Annie tana zuwa zatace dan anga bata nan aka wulakanta mata gida an barshi duk datti....d'aya kan d'aya Annie ta zauna tana k'arewa ko ina kallo ta tsuke fuska dan sam bata bukatar wata doguwar magana bare a kawo mata ba'asi .har k'asa Ammi ta dauka ta gaisheta tare da mata sannu da dawowa.ba wani sakin fuska Annie ta ansa tana wani kawar da kai kafin tace"to Allah yayi albarka tashi kije,ina so zan gana da jikokina".Murmushi Ammi tayi dan tsab ta gama gano in da Annie ta dosa maganar zaman gidan Ummi fatyma ke bata so a mata dan haka batace komai ba ta mike ta fice.sai lokacin Annie ta saki fuska ta kuma yi k'asa k'asa da murya tace"kaga yanzu ai nayi maganinta da yanzu tana nan yana kare mun tanadi kamar wata uwata,to haka duk zan fatattaki Ahmadu da Sadeequ in nuna masu ni na haifesu basu suka haife ni ba,nima su gane matsayina".kallonta kawai Jabeer keyi bece komai ba yadai lumshe ido kawai..da sallama Layan ta shigo d'akin ganin Jabeer a zaune yasa ta kuma kame kanta cikin sanyi tace"ina wuni Yaya" jin zuciyarsa ta halba da karfi ya kuma ji abunda ya tsana ya tabbatar masa ta shigo wurin bai gama tunani ba muryarta wacce take masa ansa kuwwa yake jin kamar ana masa idin tashin hankali a kai ,kuma runtse idonsa yayi bece komai ba yasa tayi saurin karasawa ciki.a hankali kuma asanyaye ya bude idanuwansa yana niyar mikewa idanuwansa suka sarke cikin nata da azama ya kawar da kansa sai kuma ya zazzare lion eyes dinsa a matukar fusace yace"you you,ko ke mayya ce to naman Jabeer yafi karfinki,har abada na haramta a gareki.Witch tsakiya...
...tuni jikinta ya soma rawa tayi kasa da kanta dan dama tsautsayine ya saka su had'a ido ,itakam har abada ba tajin zata iya jurar had'a ido da Yayan nata sai dai kamar wata statue wacce aka dasa a wurin ta kasa motsawa bare tabar wurin...cikin saurin Lamin ya rike hannunsa da yake kokarin kai mata wani wawan Marin da take da yakinin jinta zai iya daukewa na wani lokacin,idanuwansa da suke a lumshe hawaye na tsiyaya ta soma budewa a hankali tarwai ta budesu a fuskar Lamin dake binta cike da matukar tausayi Wanda duk abunda ya soma faruwa yana bakin kofar a tsaye har a yau a wannan lokacin ya kasa gazagata irin doguwa kuma nisan kiyayyar da Jabeer yakewa Layan abun tun yana bashi mamaki harya daina cikin sanyin murya yace"still Jabeer? Har yau kuma abun bazai taba canzawa ba? Har yau kana nan a in da na barka ? Ya kake so muyi da rayuwa Jabeer"...fizge hannunsa da Lamin ya rike yayi cikin tsantsar fushinsa da yake kasa sarrafa kansa aduk lokacin da yayi tozali da Layan ya soma magana da kakkausar murya yace"wallahi billah idan har bata daina zuwa in da nake ba ina dab da ilatata ,illah mai yawa kuwa wacce kowa bazai so hakan ba,I just hate her with passion, har abada kuma har gaban abada zamu ci gaba da kasancewa a in da ka sanmu Lamin, she just stay away from me"...ko kad'an doguwar maganar da Jabeer yayi akan Layan bata bawa Lamin mamaki ba,sam yasan in dai har kaji doguwar maganarsa da hayaniyarsa to tabbas akan Layan ne,dafe kansa yayi ya kasa gane madosar wannan kiyayyar,wacce bata da asali bare kuma tushe,a yanayij yarda gidansu yake masu halayya da ra'ayika mabanbanta ya kamata a tsari kuma ace Layan da Jabeer sunfi kowa shiri amma sam lamarin ba haka yake ba,,,duk yarda Layan keson kasancewa da Jabeer amma shi kamar wuta yake yana kuma kallon Layan kamar karmami jiranta yake kawai ya ganta ya cinyeta without any though. Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin daya mayar da kallonsa in da Jabeer yake amma sai yaga wayau yayi halin NASA yabar wajen,wani irin tausayin Layan ya kamasa "ya Allah na rokeka ka kawo wani abun da zai sassauta wannan wutar kiyayyar ta Dan uwana ,Ya Allah na rokeka ka bude masa idanuwansa yaga haske idan zaiyi tsana yayita dominka idan zaiyi so yayi shi kuma dominka"... Cikin sanyin murya Layan tace" ameeen Yaya"hannu ta saka ta sahare hawayen fuskarta tana murmushi tace"Yaya ka manta kawai.ba yau aka fara ba bana tunanin kuma za'a kare yau,amma insha Allah komai zai wuce kamar ba'ayi ba,to karka damu kanka akan wannan as always,naji anata maganar aurenka ina dab da yin fuahi Yaya sai kuma nayi maka uziri ,nice ya kamata ace na fara sanin Auntyn nan tawa amma shine ko sanar da ni baka yi ba sai dai naji Daddy suna maganar kai kudi da Umma"...kallonta kawai yakeyi yama rasa me zaice ko mai zai fada can dai yace"I'm sorry lil komai ya faru ne da sauri,but surely I will take you to her".murmushinta mai karawa chocolate colourn fuskarta kyau ta saki ta soma zuba masa surutu da sam baya fahimtar komai bare kuma yasan in da ta dosa kallonta kawai yake yi,shi dai yasan koma menene kawai yana jin dadin kasancewa da ita a hakan..wani kayataccen murmushi ya subuce masa yana kallon dan karamin bakinta data tura a gaba alamun tayi fushi wai ita kadai ke labari sannan yahau aikin rarrashi.sai lokacin Annie ta shigo dakin daga kitchen hannunta rike da plate data saka Dan wake shigarta ajiye plate din tayi tana k'arewa Lamin kallo kafin tace"kai kuma fa daga ina? Sai kace Wanda aka jefo,daga jin dawowa harka lallabo ni wannan kwakwa haka har ina?".Dariya kawai Lamin ya saki tare da cewa"ki daice mun kawai rowarki ta motsa kuma ba abunda zai hanani cin Dan waken nan ni da kanwata"ya kare zancen tare da janyo hannun Layan suka saka Annie a tsakiya....
Share
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate