Showing 3001 words to 6000 words out of 55893 words

Chapter 2 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt

gidan Hajja wato Mahaifiyar Abbansa mai rasuwa..tunda ya shiga gidan ya beko kallon ma'aikatan daketa masa sannu da zuwa kai tsaye ya shiga parlon Hajja bakinsa d'auke da siririyar sallama Wanda ba lallai kowa yajisa ba.farar Dattijuwa ce wacce manyanta ya kamata idonta sanye da farin glass tana duba hisnul Muslim sai da takai k'arshen addu'ar da take yi kafin ta d'ago fuskarta fad'ad'e da fara'a tana kallon Fuskar Jabeer da tayi wasai sai dai alamun k'unci da b'acin rai ne ke kai kawo akan kyakyawar fuskar tasa.Ajiye littafin tayi cikin so da k'auna ta mik'a masa hannu tare da fad'in"meke damun Autana? Waya b'atamun ranka? In ce dai ba Maryama bace dan itama wannan karon hukuncina bazai shallake kanta ba".Lumshe idanuwansa yayi yana kuma jin tsananin soyayyar Hajja na ratsa shi kai tsaye wurin k'afafunta ya zauna tare da d'aura Kansa a k'afarta ya kuma runtse idonsa gam-gam yana jin b'acin ransa na sauka a hankali a hankali. Murmushi Hajja tayi ta soma saka hannunta tana d'an bubbuga bayansa alamar lallashi.Sake da baki Ummi ta bisu da kallo duk da ba yau ta soma ganin lallashin Hajja ga jikan nata ba,k'arasowa tayi cikin parlon ta zauna tare da saka hannu ta dungure keyar Veer tace"oya d'agamun uwa,tunda kai kace ba zaka bar zucitarka ta zauna lafiya ba,kullun ayi mutun fuskarsa a d'aure dinkim ba fara'a? Kullun sai fushi".ringing din wayar Ummi shiya katse mata magana kallon wayan tayi ta kuma kallon Veer da suka had'a ido cikin alamar tambaya tace"me kayiwa Annie?".shiru yayi tare da d'aga kafad'a ya kawar da kansa..Daga wayar Ummi tayi tare da sakawa a speaker tare da cewa "Assalamu alaikum Annie an tashi lafiya ,ina kwana"...." Wa'alaikis salam shima dan ya zama dole na ansa,batun na tashi lafiya ko ban tashi bama duk bata taso ba dan kin jiyewa kunnanki ahto,jiya gigice na kwana Allah ,Allah nake garin Allah ya waye kada na kiraki jiya kuma ace Janar na nan,to gaskiya matsalar babba ce Wanda kab dangi sai kun hallara dan samun maslaha ,jiya jiya nan nake gaya maki akan Laya muka kwana irin wasan kuran da wancan mai bakin halin Jabiru yayi laga-laga da ita baki gani ba,dan ni da farko nasa ma rai zaiyi halinsa,kinga k'ara tun wuri a shiga tsakani to Allah na tuba meya hadasa da laya banda ni dana haifi uwarsa ita kuma na haifi ubanta? Ahto ba ruwana kara asan nayi dan Sam bani so Jabiru ya mutu a haka dan nasan Allah wuta zai saka shi kodan hakki,kuma ai Wanda kake so ya wuce nan." "Adaiyi hakuri Annie insha Allah zan tsawatar hakan bazai kuma faruwa ba,amma gaskiya Veer be kyauta ba,ayi hakuri "Ummi ta fad'a dan bata so ta kuma tono Annie tsab yanzu zata masu tas...kashe wayan tayi tana bin Veer da kallo Wanda ya sunkuyar da kansa k'asa " Abunda kakeyi kana ganin daidai ne ko Jabeer,is this the best gift da zaka sakawa Umma da Abba da soyayyan da suke maka? Kai bakaji kunyar kanka ba? Let me tell u this,Umma ita macen da tun yayenka ta d'aukeka ta rikeka ita da Abban Layan basu tab'a bari kayi kukan rashin mahaifi ba,ko wani abu na bukatan rayuwa har gobe komai naka a hannunsu yake amma ka rasa Wanda zaka tsana sai gudan jininsu d'aya da suka Haifa a duniya Jabeer.one day one time zakayi nadaman da ba ita ake so ba,in ka gyara kanka idan ka kiya shima ruwanka." "Ya isa haka Ummin yara,insha Allah kuma zai daina Layan dai jininsa ce ta har abada kuma k'anwarsa ce ni kinga kuga kuwa babu yarda za'ayi ace baya sonta sai dai wani dalili na daban kuma komai zaiyi daidai kuci gaba da yi masu addu'a" Hajja ta fad'a tana mayar da kallonta ga Jabeer cikin sanyin murya da rarrashi tace"Babana meke had'aka da Maryama k'arama? Kasan yara hakuri ake dasu ka daina yin duk wani abu da kasan zai janyo maka magana ,Babana shifa alkhairi danko ne bibiya yake yi ,duk da bansan dalilinka ko hujjarka ba amma dan Allah a kiyaye danni bazan tirsasaka sai ka fad'a ba abunda kawai nake so shine naga canji".sosai Ummi ta shak'a tace"Hajja lallashinshi fa kike yi? Kuma keda kanki kinji meya aikata,baya da wata hujja data wuce yace maki baya sonta ne kawai,kuma ai bazai kasheta ba tunda bashi ya halicceta ba wallahi wallahi ina mai tabbatar maka ka kusa dawowa gidan nan kabar yarinya ta huta ko ka tattara kayanka ka koma wurin aiki hutun ya isa haka,Allah ya bada lada tunda kai baka San kara da kawaici ba"....sosai Ummi ta masa tas,dan Ummi irin matan nan ne da nasa wasa ko daukar al-amari da sauki kuma tasan sarai irin abunda Jabeer yake yiwa Layan ,maca ce ita mai zafi bata son raini kwata-kwata...kallon Ummi kawai Jabeer yake yi maimakon yaji zuciyarsa tayi sanyi a'a saima zafi da kuma tsanar Layan ke kwarara da ratsa duk wata gab'a,k'ashi da b'arko na jikinsa har wani d'aci d'aci yakeji a makoshinsa saboda tsabar takaici yanzu akan wannan mai kama da y'an ruwan yarinyar ake masa fad'a kamar wani yaro? Ya tambayi kansa sai dai bece komai ba illah"Ayi hakuri Ummi" "sorry for your self Jabeer ,Hajja ni zan wuce sai na shigo jibin insha Allah" Ummi ta fad'a tare da tattara belonging's nata tabar parlon ranta a b'ace.......kwance take akan makeken bed dinta taja white duvet ta lullube duka jikinta banda fuska,yalwatacciyar sumar kanta bak'a sid'ik itace baje ta rufe gaba d'aya fuskarta ta bazu akan lallausan pillon da take kwance tana bacci hankalinta kwance...turo door din Ammi tayi kasancewar yau weekend bata zuwa hospital ta shigo tana kuma kallon agogo 11:20am ta gani k'arasowa tayi a bed din tare da tapping laps din Layan dake sharara bacci,sake juyawa tayi cikin bacci a hankali take fad'in yaya Veer,Yaya Veer sai kuma magana wacce Ammi sam bata tsaya ta saurara ba ta tapping dinta da k'arfi.a firgice Layan ta tashi tare da turo d'an karamin bakinta gaba kamar zatayi kuka tace"Ammmmi"kallon da Ammi ta jefa mata yasa tayi shiru tare dayin k'asa da kanta "bazance ki daina ba kije ki kashe kanki saboda shi,karki focusing akan rayuwanki kullun ki tsaya kina dreaming da b'atawa kanki lokaci ,ki kalli time ina ga zaman jiranki za'a tsaya yi...A hankali ta zuro siririn doguwar k'afarsa tare d Santa bedroom silifas dinta kafin ta mike tana goggoge fuskarta da kallon Ammi ta bita sanye take da White sleeping dress trouser ne Rabin labs dinta sai shirt mai vest hand iya west dinta.bajajjen sumar kanta ta tattare ta saka hula tayi toilet..in minute Ammi ta gyara d'akin tas Wanda Layan ta mayar dashi out of order sannan ta fita tare da janyo mata k'ofan....A k'a'idar gidan duk weekend a parlon Annie kowa ke haduwa anan ake breakfast, lunch even Dinner tare da iyayensu da kowa.....Gyara zama Abba Ahmad ya kumayi yana cin d'umamen tuwan da Annie ta kawo masa yace" nifa har yanzu taron nan ya kasa cikamun banga Mamana ba da Son".tab'e baki Hajiya Badiyya tayi tare da cewa"inafa zakaga y'ay'an milkin ai ba kamar gwanar nasan ana can ana bacci marar amfani."Murmushi Aunty Amarya tayi mace mai kawaici da Hakuri tace"Haba yanzu zakaga yar tawa Mamar masu gida,Veer kam jiya anje gidan Hajja bana da tabbas ko ya dawo,shima Dan neman guda"ta k'are zancan da dariya dan kawar da zancen da Hajiya Badiyya tayi....kafin wani ya sake magana Layan ta shigo cikin shirinta tsab da ita sai tashin kamshi take. Murmushi sosai ya bayyana kan fuskarta da sauri ta iso gaban Abba ta zauna dab da shi,sai kuma tasa hannu ta rike hannunsa sosai cikin nata race"Abbana I missed you so much".."nikan nayi fushi Mamana yau almost to 4days we haven't meet bansan meke hanaki zuwa dubani days din nan ba."....wani takaici ne ya kume Hajiya Badiyya har bata gani da kyau ta tashi ta fice rai a matukar b'ace bata so tayi magana kuma Annie ta daura daga in da ta tsaya dama basa shan inuwa d'aya.




Comment and share.
Oum Aryaan.
*RUHIN JIKI*


_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*___________________________________*




*JORDERH MAJIDADI*




Page 4




Kanta ta kwantar a kafad'an Abba cikin cool voice tace"I'm sorry Abbana,I missed you so much,bazan sake ba".Hannunsa ya daura a kanta tare da cewa"Allah yayi maki albarka Mamana ,Allah ya zama gatanki ya jib'anci lamurranki"Duk Wanda ke a parlon da Ameen kawai yake ansawa banda Veer da zuciyarsa tayi bak'ik'in tsabar takaici da wani irin k'unci dake tokare masa zuciya.lumshe kyawawan idanuwansa yayi Wanda tsabar b'acin rai suka soma canza kala hannu yasa yana shafa tulin sumar kansa dake ta shek'i alamar gyara ya kamata.Daddy ne ya lura da shi fuska cike da fara'a yace"a'a My son k'araso mana,yaushe ka shigo?"b'ude idonsa yayi cikin Dan sakin fuska kadaran kadahan yace"yanzu na shigo Daddyna"sai ka saurara sosai zakaji abunda ya fad'a kafin ya shigo ya gaishe da Abba dasu Aunty Amarya..Umma kam tunda Veer ya shigo ina taka saka taka ajiye ta soma had'a masa abun kari sai tattalinsa takeyi tanaji kamar shi kadaine yaron a wurin..tab'e baki Ammi tayi jin abunda Umma ke fad'a tace "Haba Yaya Fatima ai son kanku yawane da shi yanzu duk girman parlon nan amma ace kin mayar da gandamemen saurayi kamar wani jariri,ai shiyasa yake tab'ara yarda yaga dama ,duk laifinki ne ai"...." Annie ta mele baki kamar taga abun k'i tace"a'a a'a Maryama bansan kuma yaushe kika maida Hassada abincinki ba ,yo in banda haka,gaskiya mutun sai Allah yanzu ki rasa dawa zaku cakud'e sai Dan da kika Haifa a cikin ki? To ke ba abun murna bane,ni bana son haka,karki takura yaro a barshi ya b'ararraje in ba haka ba dai Allah yana kallonki,karkizo ki biyewa son zuciya"...sake da baki Ammi tabi Annie da kallo sai dai bata ce komai ba dan tasan halinta ba kuma dainawa zatayi ba,yanzu yanzu zata gama cashewa da mutun amma anjima babu tamkar shi.A haka akayi Karin cikin jin dadi da ammshuwa kafin su Basma sukayi shirin Islamiyya suka shiga babban masallacin gidan dan bada harda da sauransu dan duk girman yaro a gidan dole kaje islamiyya in har akwai lokacin.....ciki ciki yayi sallama ya shiga cikin parlon ya samu daga daga cikin Sofa's na parlon ya zauna yana sauke ajiyar zuciya ruwa masu saukin sanyi ya daukar akan table Wanda aka ajiyewa Ummi ya b'alle marfin robar ya soma sha a hankali yana sauke ajiyar zuciya.Ummi dake waya ta juyo tana k'are masa kallo sai dai bata ce komai ba har sai da ta k'arasa wayar Wanda da Ammi ne sannan ta sauke tana kallonsa tare da ansa gaisuwar da yake mata.Ummi ta had'a fuska tace"ni Jafar nace a turomun ba kai ba,bazan bika ba so I can drive my self ".Murmushi Jabeer yayi yace" kiyi hakuri"...harararsa Ummi tayi tare da cewa"hala wani abun kayi kuma?".sunkuyar da kansa kawai yayi bece komai ba yana kallon zara-zaran fingers dinsa kamar mai son tuno abu.Dama tasan bazaice komai din ba sanin ko Ladi ta kawo abinci baci zaiyi yasa ta tashi da kanta zuwa kitchen din ta had'o masa abincin da drinks da ruwa duk a tire tazo ta ajiye gabansa tace"kaci bari in shirya kafin yaron nan su shigo daga school sai mu wuce..gyad'a kai kawai yayi sannan ya soma tsakaurar abinci a hankali kamar Wanda akawa dole yaci..beci wani sosai ba ya ture tire din ya jingina da sofa yana latsa waya...runtse idanuwa yayi da k'arfi jin muryarta ta karad'e parlon tun daga k'afarsa har cikin tsakiyar k'walwar kansa yake ansawa dandanan fushinsa ya tashi amma be d'ago ba bare ya kallesu ita da Asma'u da Jalila ne yaran Ummi Wanda suke kai d'aya suketa zuba surutu suna dariya da yake school dinsu d'aya..turus tayi showing her thirty-two waje mad'aukakin farin ciki na ratsa duk wata gab'a ta jikinta wani sanyin dad'i ke ratsata Murmushi kawai take saki da Sauri ta iso gabansa tace"Yaya"bakinta ya kasa rufuwa d'ukawa tayi har k'asa kusa da k'afafunsa ta rike hannunsa cikin nata tace"Yaya yaushe kazo? Amma Ammi cewa tayi Yaya Jafar zaizo daukar Ummi ba kai ba"....kamar Wanda aka jonawa wuta haka Jabeer yaji a jikinsa duka wani zafi ya rufeshi da iya k'arfinsa yasa du biyun hannuwansa ya ingije Layan ,in seconds ta isa da table din da yake wurin ta fad'a a kansa hannunta data bige ta rike hannu tana jin wani tsananin zafi da zugi yana ratsata sai dai idanuwanta akan Jabeer k'yar ta kasa d'aukesu tare da murmushin dake kan fuskarta..zazzaro dara daran idanuwansa yayi cikin tsananin b'acin rai yace"this should be the last Monster, don't you there in your life repeat this mistake,if not wallahi wallahi azeem sai dai a haifo wata ko kuma ki k'are rayuwarki babu hannu,ni sa'anki ne?".ganin kallonsa kawai take yasa ya kwashi pillows ya wurga mata a fuska yace"mayya ba zaki daina kallona da wannan aljannun idanuwan naki ba?" Cikin Sauri Layan ta janye idanuwanta tana fad'in I'm sorry,I'm sorry Yayana,na daina bazan kuma ba ,kada ka b'ata ranka dan Allah I'm sorry"...zazzaro ido Jalila da Asma'u sukayi da Sauri suka zo suka d'aga Layan zuwa d'akinsu....cikin tsawa Asma'u tace"jar ubancan waike Layan kin haukace ko kina da hankali kuwa? Dole sai kina zuwa wurin Yayan ne? Kina so a kashe ki ne? Ni bansan wannan wacce irin tsana bace ,sannan kice wai kada a fad'awa Ummi."Harara Layan ta bakawa Asma'u tace"to meye damuwanki a ciki? Ina ga dai jikina ya daka? To nace kuma na yafe kar a fad'a dan Allah kiyi hakuri abar maganan,ni nasan komai mai wucewa ne ,and even in second bazan tab'a jin zafin abunda Ya Jabeer kemun ba sai ma addu'ar Allah ya cikamun burina a kansa,so u not worry ba yau aka fara ba ,ba kuma za'a k'are yau ba so chill."kallon mamaki kawai suke binta da shi murmushin takaici Jalila ta saki tare da cewa"to Allah ya baki lafiya Layan ina ga jinnul Ashk'i sun kawo maki hari sai an rik'a had'awa da rokin Allah"..shigowan Ummi d'akin yasa duk sukayi shiru"shine kunsan Ku nake jira kuka shigo ban baku da lokacina?,to maza Layan tashi kici abinci ki wuce muje Amminki tace k'afata k'afarki"...Gaishe da Ummi kawai tayi ta tashi cikin sanyin jiki kamar wacce k'wai ya fashewa a ciki ta wuce kitchen jin cikinta takeyi a toshe gudun kada ta musawa Ummi ne ta gano wani abun yasa tayi shiru .kad'an ta saka abincin bayan ta gaishe dasu Ladi anan ta zauna tana ci ba jimawa ta gama duk da ba ci ta wani yi ba ta fito ta koma ta dauki school bag dinta ta fito parlo wurin Ummi da suke jiranta..kallon sama da k'asa Ummi tayi mata kafin tace"yanzu nan har kinci abinci?to ke kika sani wuce muje."Murmushi kawai tayi batace komai ba kafin suka fito gate da Ummi.kallonsu kawai Jabeer keyi amma bece komai ba ya taso ya bud'e mota ya shiga,Ummi ma ta shiga,Layan tazo zata bi bayan Ummi.Ummi tace "halan shi Jabeer din Driver ne ko? My friend kin wuce gaba ko kuwa". Turo baki kawai Layan tayi ta bud'e motar ta shiga,Jabeer kam bece komai ba ya soma driving suka bar cikin gidan ya doshi unguwarsu..A motan bece komai ba sai dai tsab Ummi ta gama karantar tsananin b'acin ran da yake ciki sai ko kusa yaki nunawa kuma ko da wasa be kalli in da Layan take ba...sosai Ummi ta zurfafa tunani tana jinjina wannan tsananin kiyayyar da Jabeer kema Layan sai dai duk yarda taso lalubo wani abun amma abun ya faskara dan ta kasa samo wata hujja ko madafar da zata rike akan lamarin Addu'ar shiriya kawai tayi masa taci gaba dayin wani tunanin daban.




Comment and share
Ouhmm Aryaan


*RUHIN JIKI*


_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*___________________________________*




*JORDERH MAJIDADI*




Page 5






Kallonta kawai Ammi keyi lokacin data zauna kusa da ita tana ajiye school bag dinta kafin tace"shine daga labari kika kwasa kika yi can wurin Ummin,da kinsan Wanda xaije d'aukota aida ba kije ba,danna tabba bazai barki haka nan ba."Murmushi kawai Layan tayi tare da cewa"Allah Ammina bemun komai ba"ta k'arashe zancan tana mak'alota sosai a jikinta kamar wasu aminan juna.dungure mata kai Ammi tayi tace"dadai ba Jabeer bane ,to ki adana kalamanki ki fadawa wata danni kinsan nayi hardar karyar da kika saba zubawa a kansa".Tab'e baki Ummi tayi tace"wannan kuma lamarinsu ai sai su.Mikewa kawai Layan tayi ta fice daga part din ta wuce na Umminta da sallama ta shiga Parlon a d'aya daga cikin kujerun d'akin ta hango Umma zaune ta cab'a ado kamar ko yaushe dan Umma badai kwalliya ba,k'aramin azkar me hannunta tana karantawa bata kula Layan ba sai da takai aya sannan tace"wane sabon salone kuma zaki zo kimun tsaye aka kamar wata bishiya".zunb'uro baki Layan tayi kafin tace"nifa kawai zuwa nayi "." To an gode Allah yayi albarka sai ki koma wurin Ammin taki dan kinsan ni bazan dauki wannan sakalcin naki ba yanzu ma sab'a"."to ai Ummi ce tazo sai na basu wuri ko."Layan ta bada ansa Umma bata kuma cewa komai ba taci gaba da karatunta dan tsab ita bata daukar rawan kan Layan yanzu ta kai mata duka...Tura baki Layan tayi kafin ta wuce d'akinta danyin wanka ta canza....kallon Hydar kawai Momy Badiyya keyi zuciyarta cike da tsabar takaici da k'unci cikin fad'a tace"shin wai Hydar Fatima ta Haifa mun kai ko ko uwarme kake nufi?,wallahi wallahi ka fita idona sakarai Wanda besan kishin uwarsa ba kawai,kai yanzu Fatima da wata y'arta har abun sone a wurinku in banda rashin zuciya irin taku,matar da aka fifita ta zama mowa ita da yarta akan karan kanku da mahaifitarku duk da baku had'a komai ba baccin Sadeeq daya jajibo mana,in kyautar ka tashi yi baga Muhibba nan ba,kai kara ka bawa Basma ma daka ba wancan bak'ar yarinyar mai kama da tsinken tsintsiyar kwakwa,sallamamme bani agogon nan".ta daure fuska tare da mik'a masa hannu.Bece komai ba ya d'auka ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login