Showing 39001 words to 42000 words out of 55893 words

Chapter 14 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt

masu matukar haske da suka kara fayau saboda gajiyan data kwaso...yarda Kasan da dutse take magana bece komai ba sai kallon Ammi yakeyi dake fitowa daga bedroom dinta da alama itama wankan tayi dan rage gajiya,kai tsaye dining din ta karasa ta zauna kafin tace"sai kace wani kurma? Ina kanajin kanwarka na gaisheka".bece komai ba ya karasa Dining din zuciyarsa na bugawa ya duka har kasa yace"ina wuni Ammi,dazu na shigo bakya nan,na kira wayanki kuma ba'a dauka ba".ansa gaisuwan tayi kafin tace"wayan na mota,na kai Layan lalle ne da gyaran kai,kasan in ba zuwa nayi ba nayi tsaye a kanta ba tsayawa zatayi ba shiyasa daga office na wuce can kawai".wani malolan bakin ciki ya tsaya masa a zuciya yanzu wannan y'ar iskan yarinyar ce katuwa da ita ace sai an kaita lalle da wannan bakin Hannun nata dan shi bega amfanin lallen bama kanma da askesa akayi kowa ya huta amma shine sai an wani rakata kwafa kawai yayi yace"to sai anjima"...Allah ya kaimu kawai Ammi ta fada ta soma cin abincinta ko kuma kallonsa batayi ba,sai bayan ya fita ta kalli Layan tace"kada kizo kici Abincin ki tsaya kina kallonsa kina b'atawa kanki lokaci yanzu inyi maganinki a gidan nan".A sanyayen ta karaso dining din gaba daya ma Abincin ya fice mata a kai kasa ci tayi daga karshe ganin Ammi tabar dining din itama ta fice kawai ko zatayi sanyi a zuciyarta....


*RUHIN JIKI*


_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*___________________________________*




*JORDERH MAJIDADI*








31








"Look Ihsan duk wani abu da kike tunanin zaki iya bazai dameni ba,haka tsarina yake bana komai bana party ina na baki duk wani abu da kike bukata? Damuwarki ne kiyi ko kada kiyi is none of my business abu d'aya na sani Billah babu Inda zanje" be jira cewarta ba ya kashe wayansa yana sakin siririn tsaki,Tab'e baki Jabeer dake kwance a bed yayi cikin cool voice yace"ina dalili harka da mata? Kana zaman zamanka yarinya ta nemi juyaka,wannan ne abu na karshe da bazan iya jurar dauka ba".Tsaki Lamin ya kuma saki tare da cewa"mata sha'aninsu ai sai su,at all ni bana son hayaniyar nan amma ta matsa sai naje wani program, ta barni ma inji da tarbar bak'i na goben nan,lokaci ya kure kuma"....wani wawan Kuka Ihsan ta saki kamar wacce aka aikowa cewa uwarta ta mutu hada daura hannu bisa kai tana gunjin kuka da duk wani effort nata har wani shidewa takeyi,cikin sauri Husna da Yayarta Jamila suka turo dakin suka shigo dukkansu a rude suna tambayarta ko lafiya,hannu ta saka ta zare daurin head din da aka mata tana kokarin zare gown din kalar ash colour da aka gama mata shirin tafiya party din.saurin rike rigar Aunty Jamila tayi ta zazzaro ido tace"ke bansan isakanci meye haka kikeyi? Kinsan nawa aka kashe a wannan shirin da aka maki?.komai ace ba zaki bishi a hankali ba Ihsan Kuma rushewa tayi da kuka tana cewa"Aunty wai bazaije ba,wannan wanne irin abun magana yake son janyo mun ga kawayena I can't take it any longer wallahi Aunty"wani siririn tsaki Jamila ta saki wani haushi na kuma kumeta tace"to kimin shiru wallahi,danni ke kike bani ma haushin ba kowa ba,dama tun a waje zaki rinka lalata mana aiki to ba haka akeyi ba,kici gaba da shiri I assure you Lamin zaizo party din nan bana son sakarci"bata jira cewarta ba ta juya ta fice daga dakin abunta.sulalewa a gefan makeken sofa bed daya kawata dakin nata tayi hawaye na kuma wanke fuskarta da tasha make-up.....k'asa yayi da kansa ya kasa cewa komai,a tsawace Momy ta kuma kallon Jabeer tace"to in ma kai ke hure masa kunne da rashin tarbiyarka to ka fita a hanyata,danni wannan shiru shirun naka da rashin kunya wai baka son aure to ba yarda zanyi ba wallahi"ta kuma juya kallonta kan Lamin tace"idan na isa baso kakeyi ka walakantani ba to maza ka tashi ka shirya kaje auren nan ,tunda ba auren dole bane,gacan su Muhibba sun shirya"bata jira ansarta ba ta fice tare da buga masu kofan..Murmushi mai kyau Jabeer ya saki lokacin da suka hada ido da Lamin da gaba daya mood dinsa ya canza na maganan da Momy tawa Jabeer din,at all baya jin dadin yarda suke mu'amala a gidan.mikewa Jabeer din yayi yazo yana Dan bubuga shoulder din Lamin yace"guy wallahi ka tashi mu shirya kafin Mommy tayi band'ashenmu a gidan nan,especially ma ni"ya kare maganar yana dariya tare da zare T-shirt din dake jikinsa Wanda be dade da sakawa ba,take fara tas singlet dinsa ta bayya ya soma kokarin shiga wanka..mikewa Lamin yayi shima dariya na kubce masa dan yasan dalilinsa ne Jabeer yace zaije wurin,kuma kullun bai taba nuna abunda mommy take masa ta dameshi ba.kai tsaye dakinsa ya wuce dan ya shirya.....tura baki kawai Layan keyi dake tsaye fuskarta tayi wani irin fayau sai sheki takeyi jikinta kuma na fitar da wani irin sihirtaccen kamshi mai tsayawa a zuciya.kamar zata saki kuka take bin Basma da Muhibba da kallo ko wacce taci ado a cikin Sabon dinkin da Ammi tayi masu sosai dinkin atamfar ya zauna a jikinsu."kinga wallahi mu dai zamuyi tafiyarmu karshenta sai dai ki biyo motar su Yaya Lamin da Yaya Jabeer,dan su Yaya Jafar dukkansu basa gidan nan"Basma ta fada da alamun kosawa.Muhibba ta cabke da fadin "kara dai dan su Aminata da Jalila su Asma'u tun tuni sun tafi" wasu ne daga cikin cousins sister's dinsu da suka zo bikin....tab'e baki Layan tayi kamar zata saki kuka cikin deep and her sweet cool voice tace"dan Allah yanzu fa nake shigowa a gidan nan,ga gajiya da bacci na kwaso sai kace wata wacce za'awa aure ba Hutu"..."to Yaya Lamin kam zaice maki ya gode da safe kam insha Allah,dan haka mu kinga tafiyarmu"kafin ta ankare sun bar parlon Umman,Wanda gudowa tayi dan ta samu ta dan rage gajiyan data kwaso ta rasa duk gyaran menene haka Ammi keta faman yi mata ina dalili ko hutawa da zuwa IT dinta kwana biyu an hanata"...daga sama har kasa Umma ta kalleta kafin tace"inaga ke kin cire kanki daga jerin yaran gidan nan ko ?bana son tashin hankali da neman magana Layan,ki wuce ki shirya kibar gidan nan yanzu"...ji tayi inama kasa ta bude ta shige ciki ta boye saboda gajiyan data kwaso kuma tasan tunda Umma ta saka baki tayi kad'an ta gujewa zuwan nan"kasa karasa shigowa tayi ganin Ammi na shigo parlon da sallama ga kaya a hannunta a Leda sai wata y'ar budurwa tana biye da ita,gaisawa sukayi da Umma kafin tace"Layan maza kije ki kuma watsa ruwa ga mai kwalliya nan zata dan gyara maki fuska kiyi sauri Yayanku na jiranki zaku wuce,kowa ya tafi bana so kuma a fassara rashin zuwanki ta wani fuska"kamar wata doluwa haka duk ta bisu da kallo to amma bata da wani zabin daya wuce bin umarnin Ammin Wanda haka Umma ta kuma jaddada mata shi murmushi ta mayarwa mai kwalliyan daketa mata tun dazu kafin su wuce ciki,cikin kasa da minti arba'in Layan ta fito d'as cikin hadaddiyar lite blue wedding gown dinta wacce ta fitar da shape ko ina kamar an zanata a ciki Dan kugun nan yayi carab.kasan rigan kuma a bude,white head aka daura mata daga hannuwanta har wuyanta duka gwalagwalai ne da Ammin ta kawo aka saka mata,plate shoe white shima ta saka ga fuskarta da yasha lite make-up ba hayaniya ko kadan ya kuma fiddo da tsananin kyawunta,masha Allah shine abunda Ammi da Aunty Amarya ke fada lokacin da suka fito parlo gaba daya ko ina ya dauka wani kamshi da Layan din ke fitarwa ta haska parlon gaba daya ta fito a amaryarta sak.hannuwanta Ammi ta kama sosai cikin nata ta fito da ita compound din gidan tana gwada number Jabeer,A sanyaye ya d'aga wayan Wanda tun dazu yake zaune a parking lot yana jiran kiran Ammi,tun dazu ta tsayar da shi hakan yasa Lamin shima ya zauna a motan suna jiran Ammin.A kasalance yace"ina parking lot Ammi".bata kuma cewa komai ba taja Hannun Layan ta karasa wurin.kamar wani statue haka ya kafe Ammi da ido kamar yaga sabbin halitta ganin ta riko mace zuwa wurinsu,bai wani kalleta ba bare kuma ya gane wacece.sakin baki ya kuma yi lokacin da take mika masa Hannun Layan tana fadin"ga y'ata nan amana Veer aje lafiya a dawo lafiya a kulamun da ita kamar ina wurin,idan kaci amana kuma Amanar Allah zata cika Jabeer,hannunka hannuna zaka dawo mun da y'ata idan an tashi.tunda suka taho Lamin ya kafeta da ido yana jin zuciyarsa na tsananin bugawa ya soma karanta innalillahi wa'inna ilaihir raju'un ya soma karanto sunayen Allah ,a hankali yaji zuciyarsa na sauka yana kuma dawowa natsuwarsa dake neman kaura dashi ganin wani irin kyau na musamman da Layan din ta masa....Layan kam manya manyan idanuwanta Wanda suka sha ado da kwalli ta d'aga tana k'arewa Jabeer kallo Wanda tuni kamshinsa ya cakude da nata ya bada wani kamshi na daban.sanye yake da wata bugaghiyar shadda sky blue sosai ta haska farar fatar jikinsa,Riga ne da wando,rigan iya gwaiwa da gajeran hannu sai wani azababben aikin hannu data sha daga Rasheed Makera fashion Design Wanda suka san aikinsu.hula ta zauna d'as a kansa kamar danshi aka yota a Hannun hagunsa agogon Rolex ne daure wacce ta lashe kudade da yawa sai kyalli takeyi,kafarsa na sanye a half cover na maza masu azabar kyau.kamar Ammi ta daura masa mutuwarsa haka yaji lokacin data saka masa Hannun Layan a nasa kafin ta wuce tana masu Allah ya tsare,yana ganin ta wuce yayi saurin sakin hannunta a gaggauce yace"ki wuce muje ko kuwa na tafi na barki a nan sokuwa kawai".


*RUHIN JIKI*


_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*___________________________________*




*JORDERH MAJIDADI*




32




Cikin mutuwar jiki tana kuma kallon fuskar veer din ta shiga motar ko lura da irin kallon da Lamin ke mata ma batayi ba,tafiya ya zama so silent kowa da abunda ke damunsa musamman Veer da yake Jin duk motar ta matse masa gaba daya duniyar tana jujuya masa as if Layan akansa take zaune haka yake Jin takaicin kasacewa da ita inuwa d'aya a haka har suka karasa wurin program din.lallai Ihsan yar gata komai a wurin yaji kai kanka idan kasan matsayinka be kai ba bama zaka fara dosar wurin ba,wani irin decorating wurin sukayi kamar ba za'a bar wurin ba,Amarya na mota har lokacin bata fita ba tana jiran karasowar Lamin.kamar an sauke mata wani lodin kayan data dauko haka taji tare da sauke sanyayyar ajiyar zuciya lokacin da Lamin yake fitowa daga gaban motar Veer yayi mata matukar kyau sai dai fuskarsa a daure Babu fara'a ba kuma zaka iya gano wai wani abu na damunka ba.tuni wurin ya dauka da hayaniya aka saki kida na tarbar Amarya da angonta...cikin kufuluwa Jabeer ya juyo bayan motarsa in da Layan take zaune yace"hala Jira kike nazo na dauke ki?let me tell you idan ma kin fita in kin so kibar wurin get out"ya fada a tsawace Wanda yasa Layan zabura da sauri har tana niyar kifowa daga motan ta sauke kasa da sauri tana rarraba manya manyan fararen idanuwanta Wanda kwalliya ta Kara fito dasu ras.wurin ba kowa hakan ke Kara tabbatar mata da kowa ya shiga dakin Taron kenan.wurin da suke babu wadatuwar haske sosai saboda parking lot ne,hakan yasa ta danji tsoro cikin sauri ta koma side din da Jabeer yake tana matse rigarta da kyau kamar zata saki kuka tuni ta saki wannan shagwab'ab'iyar fuskar tata wacce bata rabo da koke koke da shagwaba sak ta koma Layan din Ammi .kafin kace me hawaye ya taru a fuskarta,duk da a cikin duhu suke hakan bai hanata ganin irin azabben kallon tsanar da Jabeer yake jefa mata ba,cikin rawar murya tace"Yaya tsoro nake ji"kuma kallonta yayi ko kad'an beji mamaki ba Dan yasan wannan kad'an daga iskancinta ne da kuma rainin wayanta to shikam bazai dauki wannan ba,sa'arta d'aya da Ammi tace amana amma billah da sai ya kulleta a wurin yaga ko mutuwa zatayi.beko kulata ba ya rufe motarshi ya soma takawa cikin sassarfa irin takun irgarman namijin da yake jinsa ya isa ya kuma kai tsaiko ga wani irin fitinan kanshi dake baibaye wurin gaba daga.hannu tasa ta d'an tattare gown din jikinta ta bisa a baya harda d'an gudunta saboda tazarar da ake samu a tsakaninsu kuma sam ba zata iya wannan saurin da yakeyi ba...gaba d'aya holl din ya natsu har an fara gabatar da program mc nata bayani.kamar fitowar farin wata daga sararin samani haka suka dauki idanuwan dubban mutanan dake wurin .tuni kallo ya koma garesu wani sanyayyen kyau kamar dansu aka tanadi Taron haka sukayi Yana gaba tana biye dashi a baya daga gefansa kad'an hakan sai ya bada wani abun dabban.ganin idanuwa da yawa ya kuma linka tsoron Layan Sam bata Saba zuwa party ba bare kuma har ta fita babu hijabi a jikinta,ji tayi kamar gaba daya mutanan duniyar sun taru a kanta ne ,tuni siririn hawaye sun soma silalowa akan kyakyawar bak'ar fuskarta wacce tasha sanyayyen ado ,tuni ta manta da Wanda take tare a hankali ta kuma matsawa jikinsa ta zuwa dogon hannunta daya k'awatu da Jan lalle da bak'i ta zurashi cikin na Jabeer ta kuma matse hannuwan nasa sosai cikin nata,har jikinta na neman fara rawa rawa.rintse idanuwa yayi da matukar karfi lokacin da hannuntaa ya sauka a cikin tattausan nashin hannu.lokaci daya ya ware idanuwa shi tas suka daukar masa hoton fuskarta tana mashi wani irin kallo,kallon Idi cikin Ido,yasan Layan farin sani tun tana zanin goyonta bashi da shamaki a halayyarta tar tar suke a kansa a kuma hardace kamar yarda ya hardace ayyukansa na yau da kullun .tunda suke a duniya bata taba masa irin wannan kallon ba Mai wuyar fassaruwa kallo ne da take masa na rashin madafa,rashin garkuwa,kallo ne dake masa tuni da cewa itadin amanarsa ce wacce Ammanshi ce ta bashi amanar lokaci daya fuskarta ta juye masa zuwa ta Amminsa sak da sak,ga kallon dake nuna masa a yanzu ta mance da kowa a wurin bata kuma ganin kowa sai shi,shine garkuwanta kuma abun dogaronta a wurin.tuni Layan ta kuma takurewa ta matsar da jikinta zuwa nasa jikin Dan samun kariya daga masifaffan kallon da mazan wurin suke mata rakiya da shi.sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tuni bugun zuciyarsa ya sauya ya kuma Kara dadda sauti,bece komai ba sai hannunta da yaja da d'an sassarfa ya soma nufar wurin zama in da bayawaitar idanuwan jama'a.ido suka hada da Lamin ya sakar masa wani sanyayyar murmushi duk da Yana Jin wani nauyin abu da yazo ya tare masa makoshi ya kuma danne masa zuciya.sai dai abun ya masa dadi yarda Jabeer bai hantari Layan ba ya kuma zama bango abun jingina a rayuwarta,shi kansa yasan hudubar Ammi ya tuna amma daba haka ba,da yanzu an kwasheta a tsakiyar holl din yayi rugu-rugu da ita,haka yake fata da buri kuma kamar a ko yaushe da Jabeer kan iya tsayawa a rayuwar Muhibba da Basma dasu Asma'u yaran Ummi haka yake fata yaga Jabeer yayi tsaye akan duk wani lamurran rayuwa na Layan Yana fatan ko bayan ranshi Allah ya ansa addu'ar nan...suna isa bayan ya tillar da hannunta har tayi taga yaga zata Fadi sai kuma ta tare kujeran dake gefan tayi mata garkuwa .cikin silent voice din san nan da murya Mai kama da gargadi yace"to uban meye ya kawo ki wurin Nan ba? Kinsan ba zakiyi iya zama ba kika soma ? Na fada maki kuma karki kuma kuskuren yin garkuwa da ni ,ba zaki taba samun wannan karar daga gare ni".kalaman Jabeer da masifarsa babu bako a cikinsu a wurinta amma sai take Jin hakan bai mata ba,na yau Sam bata ji dadinsa ba,kafin ya sake wata magana kuma ta saki Siririn kuka.a harzuke yace"ko kimun shiru ko na ballaki na zubar da abanza a wurin nan idiot kawai".jikinta har rawa yake ta samu wurin ta zauna,sosai tayi nadamar zuwa wurin Nan Dan danan kafin a kasarasa taron wani irin zazzafan zazzabi ya rufeta har hakoranta haduwa sukeyi...lokaci lokaci yake kallonta kafin a tashi wurin kawai ya fizge hannunta suka fice ta baya.har kofar part din Annie ya rakata bece komai ba ya wuce part dinsu Dan Sam ji yakeyi kansa ya masa wani irin zafi ga zazzabi dake neman rufesa.......Tun safe gidan ya soma daukar harami ko ince unguwar gaba daya .Ammi ce data ci ado cikin wani danyan leshi sai rawa yake,ta dauko atamfar super Holland data gama haduwa ta dinku take tsaye akan Layan dake dukunkune cikin duvet,time ta kuma kallah d'aya saura ta Gani,hannu tasa ta janye duvet din tare da cewa"yi hakuri Layan tashi ki Saka kayan Nan sai ki kuma Shan magani feature Dr a kwance,ae naji zazzabin ma ya sauka".mikewa tayi sannan ta karbi kayan daga hannun Ammi ta mike ta zare towel din dake jikinta ta soma shirya tun daga tasasun undies din da Ammin ta bata,sosai tayi matukar kyau cikin atamfan duk Wanda ya kulleta so daya zai so ya kuma a wannan lokacin.duk da babu makeup a jikinta wani sanyayyen kyau tayi...ras angwayen suka fito cikin shigar shadda white colour with brown sosai sukayi kyau komai nasu irin daya kai kace twins ne.jiki a sanyaye Jabeer ya Kalli Lamin kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa,kawai tun jiya gaba daya yake Jin like is not him.hulan shi kawai ya dauka ya wuce mota,saboda sun kusa makara ko Yan gidan basu gaisar ba suka wuce babban masallacin gidan in da a nan za'a daura aure...


*RUHIN JIKI*


_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*___________________________________*




*JORDERH MAJIDADI*






33






Kamar ko yaushe kuma kamar kullun masallacin a cike yake sai dai wannan karon yasha banban dan duk wasu danginsu na nesa dana kusa suna wurin ga manya manyan k'asa y'an kasuwa da dai sauransu taro ne daya tara manyan mutanan da basu tab'a zato ba.kallon kowa Jabeer yake yi musamman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login