Showing 18001 words to 21000 words out of 55893 words
Chapter 7 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt
dariya kafin Jalila tace"Ma'u na wanka nasan yanzu kin ganta da wannan suna nata na yan gayu da kika saka mata".sai kuma ta matso tare da kama Hannun Layan tace"your welcome sis".harara Layan ta watsa mata tace"sai yanzu kika ganni? Dadin abunm a Annie ai ba'a mata gwaninta beside ga Yaya Lamin fa".zaro ido Jalila tayi fuskarta na nuna tsantsar farin ciki tace"wallahi Allah Yaya ban lura da kai ba sam",sannu da zuwa ,Good morning".Murmushi kawai yayi tare da cewa"ya kk ya school".Alhmdllh ta bashi ansa dukkansu suka mayar da kallonsu kan Asma'u dake fito sai wani sinsinne kai take tana murmushi daga dan nesa da Annie ta zauna kafin tace"barka da zuwa Annie ,ina kwana"ta fada tana kallon kasa sai kuma ta fara wasa da zoben dake hannunta."meye kuma haka Ma'u? Sai wani sinsinne kai kikeyi kamar wacce akace taje gaishe da sirikai? "Dariya kawai Jalila da Layan sukayi sai kuma Jalila tace" hmm kya kara gani Annie kuma aike Kaka ce".kallonsu kawai Ummi keyi da alamar tambaya ganin kuma Asma'un taki cewa komai sai saukar da kai takeyi kasa,tab'e baki tayi bata dai ce komai ba,cikin sanyi ta kuma gaishe da Lamin shi kanshi yayi mamaki ganin sanyin da Asma'un tayi kuma har lokacin bata karaso in da yake ba,Asma'un daya sani da shegen surutu da rawar kai abun ba'a cewa komai.."wait wait what's going on here ? Ina lil Husnata dana sani ko dai an canza mun ita ne?"Ganin abun nasu bana k'arewa bane Ummi tace"Annie muje Ku gaisa da Janar din naji shigiwarshi yanzu daga ki shiga ki huta dan yaran nan ba barinki ki huta zssuyi ba"kyab'e baki Annie tayi tana masu wani kallo kafin ta tashi ta kwashi k'atuwar jakarta tabi bayan Ummi zuwa d'ayan part din...Sai lokacin Layan ta samu damar kara gyara zama tace"wallahi Yaya ka kara gani ,duk tsabar kinbibi ne wai ita an fad'a komar soyayya ina kaga zama kana matsayin Babban Yayan ango "sai kuma ta kwashe da dariya.Mikewa kawai Asma'un tayi da gudu tabar parlon.Jalila ta dauki zancen da cewa" she's your feature in law Yaya Faruk ke crushing ".shi kanshi Dariya ta basa yarda ta k'are maganar sai bai kuma cewa komai ba ,kallon tsadaden agogon hannunsa yayi tare da cewa" I think I will take my leave now,anjima after magrib zan dawo da daukeku"da to ta ansa kafin suka raka shi ya tafi,ta parlon suka biyi Jalila tace"baki ma ci komai ba duk zamanki a nan,bari na iba maki sai mu wuce d'aki".catfish din ta iba mata kad'an sai ruwan shayin dan tasan bacin sauran zatayi ba,kai tsaye bedroom dinsu suka wuce.small stool ta janyo ta daura komai da suka had'o spoon ta sanya taci kifin so d'a sai kuma ta koma tana juya spoon idan ba zata manta ba wannan cimar yana d'aya daga cikin best Abincin da Yaya Jabeer yafi so a duniya ,Ammi takanyi shi sosai saboda shi musamman idan zai dawo gari tun bata so harta koya ci ."kun gama mun tereren a cikin mutane ko?"Asma'u ta tambaya."Allah babu kowa Yaya kadai muka fadawa,amma kinsan Ummi zata sakamu a gaba ne kam".Ganin Layan bata ma san me sukeyi ba ta lula duniyar tunani yasa Jalila girgizata "as always and for ever thinker lady,ke ba zaki bar zuciyarki da Ruhinki su huta ba,anya Layan kinwa rayuwarki adalci kuwa? Cikin few minutes har kin tafi duniyar tunani ? To zaki kashe kanki ne saboda soyayya? Bayan kinsan Wanda kikeyi dan shi bema san kina yi ba". Jalila ta fad'a tana rike kugu da fuskar tausayi irin abun ya dameta.Sanyayyar ajiyar zuciya Layan ta sauke kafin tace" ko kusa Jalila batun bema san inayi ba bata taso ba,ko ba komai duk yarda yake kuntata mun hakan namun dadi dan yasan ina tare dashi ko yaushe,kinyi kuskuren fahimta,ita soyayya ana so ne ko mutun na sane ko baya sane,ana so ne ko mutun na Raye ko yana a mace ,zuciya ake so ake da muradin mallaka ba sura ba ko wani kyalekyalen duniya,k'ask'antar da kai kuma duk a cikin bautawa soyayya ne,nasan one day one time Yaya Veer zaiji kiran da zuciyata take masa ko da hakan shi zai zama aikina na karshe a duniya to zanyi farin ciki da burin cikar burina,kuma Allah maji rokon bawansa ne,so ki daina ganin wai ina wahala wani lokacin zaki fahimci manufata".sake baki kawai Jalila tayi tana binta da fuskar tausayi sai kuma ta tab'e baki tace"wallahi nikan zan maki addu'a Allah ya yaye maki ne kawai,ina dalili ni har Yaya Jabeer din nan ma ya soma fita a kaina acwe mutun sai shegen taurin kai kamar mutanan farko,ina ma ina ma ina zuciyarki ta maki adalcin kai ki in da aka san daraja da kimarki aka san mutuncinki ake kuma sonki,ji kalli idanuwan Yaya Lamin babu komai a ciki sai zallar soyayyarki da begenki sai dai kash ke da yakeyi danke ma baki san yana yi ba".saurin ture plate din gabanta tayi da sauri tana dafe zuciya sai kuma ta saki dariya tace"kinyi kuskuren fahimta Jalila,kin kuma karanto ba daidai ba,babu wani abu makamancin wannan a zuciyar Yaya Lamin son da yake mun yarda yake son Muhibba da Basma haka nima yake sona Yayana abun alfaharina hakan bazai taba faruwa da mu ba".kallon tausayi kawai Jalila tayi kafin tace"time will tell,ni kinga mubar wannan maganar mu koma wani gobe kinsan muna da CA".manya manyan text books suka ware tare da fara karatu.
Share
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
15
After Magrib Lamin ya dawo daukar su Annie sai dai fir taki komawa cikin had'e fuska tace"dama ni da kayana kala biyu na taho,ina so insha iska shi Ahmadun bai fad'a maka ba? A'a ni kam bana son takura gidan nan ai da can duk d'aya ne".k'asa da kai Lamin yayi yana murmushi dan yasan za'a rina,Annie bata taba zuwa gidan Ummi ta tafi a ranar ba bare kuma ta samu General yana nan.Murmushi General yayi tare da cewa"hakane Annie sai in da kike so zaki zauna dan haka kiyi kwanakin ki ni da kaina ma zan kira Alhaji Ahmad din"..."to tashi ban wuri kaji Wanda suka san zumuncin Allah,kwana biyu zanyi na dawo,itama Layan din kuma ba in da zataje".Tura baki Layan tayi sai kuma tace"Yaya zanje nikan".kallonta kawai Annie tayi sai kuma ta kyab'e baki bata dai ce komai ba ta gyara kafarta d'aya akan d'aya tana girgizawa .Sallama sukayi Ummi ta bawa Layan perform guda ukku a jaka tace ta gaishe da yan gidan....tunda motarsu ta tsaya a compound take k'are mata kallo as if her life depend on it,since fitar Lamin da bayan magrib ta kasa zaune ta kasa tsaye daga benen still take kuma kallonsu yarda hasken wurin ajiye motocin ke haskosu abu ta hadiye da kyar sannan ta koma saman ta zauna shima dan bata so Abba ya fito ya sameta a wurin..kama hannuwan Layan yayi duk biyun yana kallonta,sunkuyar da kanta tayi sai kuma ta d'ago da sauri tace"Yaya wani abun yana damunka ne?"sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke sai kuma yace"nothing kawai ina ga gajiyane"."to Yaya kaje ka huta ka daina bawa kanka wahala haka da yawa,bana jin dadi naga kana damuwa ".murmushi kawai yai mata ya bude motar ya fito itama ta fito.part din Umma suka soma shiga ya gaishe tana zaune da littafin hisnul muslin a hannunta fuska a sake ta ansa kafin yace" Daddy fa"."tunda ya fita sallahn isha bai shigo ba ina ga ko ya tsaya wani abunne"Umma ta bashi ansa kafin ta mayar da kallonta kan Layan tace"kije kiyi sallah ki fito ga abinci a can,dan yanzu zan zubawa Lamin bamai biye maki".Murmushi yayi tare da cewa"ko Umma kamar kinsan na shigo da yunwa kilama duka zan cinye".dariya duka suka saka kafin Umma tace"kasan kuma favorite dinka ne"Dan waro ido yayi be jira komai ba ya karasa dining din.Layan kuma ta wuce bedroom dinta bayan kaman 10mint ta fita tayi joining dinsu a table,ba laifi ta dan sake taci Abincin musamman da Daddy da Lamin suke firar Jabeer a nan ne kuma take jin cikin weekend zai shigo gidan duka kwannan shi 8 kenan da tafiya,wani irin farin ciki taji ya lullubeta sai dai ganin Umma a wurin yasa bata ce komai ba hardai ta samu ta wuce b'angaren Ammi.tana shiga main parlo din ta samu wayarta tana ta faman ringing karasawa tayi tare da daukar wayar sunan data gani akan wayar yasa ta kura mata ido,kasa rike hannunta tayi akan daga wayar sai da ta dauka takai a kunne tana sauraro daga can b'angaren cikin cool voice sanyayya yace"Ammina".wani irin ajiyar zuciya ta kub'uce mata bata san tayi kewarsa ba sai da daddar muryarsa ta daki dodon kunnanta cikin sarkewar murya tace"Yaya".Jabeer dake zaune yayi saurin mikewa sai dai ya kasa furta komai daga karshe kawai ya kashe wayar yana jin zuciyarsa ta hawa na daga masa kira da wancan Monster din tayi sosai yaji d'acin hakan komawa yayi ya zauna tare da lumshe ido yana ambaton sunan Allah...sororo Layan tayi wayar da kallo bawai tayi mamaki bane dan tasan zaiyi fiye da haka ba,tasan ko a mafarki yaji muryarta zaiyi kokarin tashi a barcin ne babu shiri,sai dai har gobe ta kasa gane musabbabin wannan kiyayyar da yayan nata yake mata hannu tayi saurin sawa ta tare hawayen dake kokarin zubowa akan kumatunta ,dukawa tayi zata ajiye wayar taga Ammi na kallonta cikin son kawar da yanayinta tace"Ammi Yaya ya kira baki kusa".Ammi kam bata ce komai ba ta karbi wayar sai kuma tace"ya kuka baro Ummin naku?""Alhmdllh tace ma duk a gaishe Ku,Annie kuma dai ana can wai zata kwana biyu tunda Abban Husna yana nan",Murmushi kawai Ammi tayi dan tasan dama za'ayi hakan sai kuma tace"kije kici abinci kiyi shirin bacci"."naci abinci wurin Umma zan daiyi wanka ne"Layan ta bata ansa tana yin kasa da kanta.k'afadarta Ammi ta dafa tana kallonta kafin tace"mun fara boye damuwarmu ga juna ne Daughter? Those days ina lura akwai abunda yake damunki amma kina boyewa".Murmushi kawai layan tayi tare da rungumar Ammi tace"kawai dai Ammi ina jin zuciyata tayi mun nauyi,amma bayan nan babu komai ,dan Allah kimun Addu'a".rabata da jikinta Ammi tayi tace"kije ki kwanta,sai da safe".bata jira cewarta ta wuce zuwa bedroom dinta tana dialing number din Jabeer...kwance yake akan makeken bed dinsa idanuwansa a lumshe as always tunani yake yi ji yakeyi kamar ya fasa zuwa gidan sanadin muryarta da yaji dan harga Allah ya manta da ita a duniyar shi amma yanzu kwatsam dan raini ta d'aga masa waya dan raini kuma take kiransa Yaya gaba daya ta bata masa mood.a hankali ya bude lumsasun idanuwansa kamar mai jin bacci ganin Ammi ke kiran yasa ya d'aga wayar yakai kunne bedai ce komai ba.Zama Ammi tayi a gefan bed tace"dama nasan ai ba magana zakayi ba,Jabeer na fada maka ka fita hanyar yarinyata,ka daina sakamun yarinya kuka wallahi zanyi maganinka akan Layan cikin gidan nan ,menene na duk wannan fisabilillah me innocent yarinyar nan ta tab'a yi maka,to bana so kar na kuma ji karna kuma gani dan hakurina ya fara k'arewa".sanyayyar ajiyar zuciya Jabeer ya sauke tare da cewa"keda waye haka Ammi? Wani abun ya faru ne?".wani takaici ya kama Ammi tace"a'a da kaina nake tunda ni da wani nake waya bada kai ba".Dan sake fuskarsa yayi alamun murmushi sai kuma yace"kiyi hakuri"daga haka yayi shiru tasan ko kwana xasuyi a haka ba wani abun zai kuma cewa ba,sai da safe tace masa ta kashe wayarta tana tunanin yarda zata bullowa wannan al-amarin....Daga toilet Abba ya fito da alamu alwala ya gama yana mayar da links din hannunsa yace "a'a Momyn yara me yake faruwa naga kuma kin daddaure fuska ?". murmushin yake Mommy ta kirkiro tare da cewa" ina fa babu komai kawai na fada tunanin duniya ne da kuma sakon da Lamin ya bani na fada maka sai yanzu ma nake tunawa".Murmushi Abba yayi ya zauna tare da jan plate din da Mommy ta zuba masa Abincin yayi bismillah ya soma ci sannan yace"ina jinki ,Allah yasa alkhairi ne".murmushi sosai ya bayyana fuskar Mommy ta kuma washe baki"tace alkhairi ne mana tunda mun kusa daukar sirika,yace mun a sanar maka ya tsayar da Ihsan y'ar wajen Hajiya Sha'awa a wacce xai aura tunda ta karasa karatunta".sosai fuskar Abba ta kawata da yalwataccen murmushi yace"kai alhmdllh ashe ina da Rabon fara aurar da yarana,Ihsan dai yar wajen Alhaji Sada dana sani,to Allah ya amince bari Dan uwansa yazo shima sai ya gabatar da tasa sai ayi gaba daya dana Jabeer din,in zai yiwuma Faruk da Jafar duk zaman me zasuyi a gidan".dandanan fara'ar fuskar Mommy ta bace jin ya ambaci Jabeer da kyar ta iya saita kanta tace"to Allah ya kaimu"."ki turo man da Lamin din".Abba ya fada.
Share
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
16
A can edge na bedroom ya hango Mommy zaune da alama zaman jiransa kawai takweyi,karasawa yayi ya zauna kusa da ita kafin yace"Mommy kin kira".kallonsa tayi na tsawon mintuna kafin ta sauke sanyayyar ajiyar zuciya tana kuma jin tayi na'am da shirinta dan tasan yarda Ihsan kesan Lamin tun kafin subar k'asar tasan ba za'a kuma samu matsala ba,fuska a daura tace"so nake ka fada mani matsayina a wurinka Lamin".Dago idanuwansa yayi yana kallon Momy yace"ban gane wannan tambayar ba Mommyna".."eh ai kaji abunda na fada abunda kuma kaji shi nake nufi kuma nake son ji".shiru yayi sai kuma yace"kece Mamana wacce ta haifeni ta kuma so ni tun ina ciki ta Raine ni har izuwa girmana ,bani da wani tamkarki duk duniyar nan".Jinjina kai Mommy tayi kafin tace"in dai har ka yarda da wannan matsayin da nake da shi a wurinka kuma ni na tsugunna na haifeka ina so ka ansawa Abbanka a matsayin kai ka fitar da Ihsan a matsayin matar Aure,kuma kaje Ku ganta dan mun gama magana da Hajiya Sha'awa na zaba maka matar aure".Tunda Mommy ta anbaci Aure sam Kansa ya daure yayi masa wani mumunan sarawa wani tsoro da fargaba a take zuka lullubesa gaba daya ya dabaurce ya kasa fahimtar manufarta,irin kallon da yake binta dashi yasa ta gane ya daina fahimtar komai ne hakan yasa ta kuma jaddada masa maganarta da zallar bada umarni.Gyad'a Kansa kawai ya soma yi kafin cikin cool voice mai nuna alamar karaya yace"Mommy Ihsan dai dana sani?"."to ina da wata bayan ita ne?".Nan ma girgiza kai kawai yayi sai yace"Mommy ki rufa mun asiri dan Allah,wallahi ni da Ihsan sam bamu dace ba,Ihsan bata da natsuwar da zamu iya zama a mazaunin maaurata,ki ceci rayuwata Mommy wallahi ina da wadda nake so"."bana kuma son jin komai daga bakinka,wacce irin dauka to kakeyiwa Ihsan din? To Ihsan ita na zaba kuma haka na bada umarni,batun kana da wacce kake so wannan ka ajiyesa gefe dan nasan wacce kakewa hari sauran cuta to Lamin ko ina cikin kabarina ban lamunce maka ka auri Layan ba bana bukatar hada jini da Fatima in dai ni na haifeka"..Runtse idanuwansa yayi yana jin yarda zuciyarsa ke bugawa ga wani zazzabin dake rufesa lokaci daya,cikin deep voice yace"kiyi hakuri wannan be kai ki bata ranki ba,insha Allah zanyi duk yarda kika ce,zanje na gantan harda Abban ma"Hydar da yake tsaye a bakin k'ofa zuciyarsa na tafasa ya turo dakin ya shigo dawowarsa kenan daga Gombe fuskarsa a matukar daure yace"yanzu Mommy dan Allah ba zaki tausayawa Yaya Lamin ba,ki kallesa lokaci daya yarda ya juye,meye da Lay uncut arts zaki ce ba za'a aureta ba? mommy dan Allah ki tausaya masa rayuwar aure fa ba kwana daya ba biyu bace rayuwace ta har abada so please let him be".sakin baki Mommy tayi tana kallon Hydar ta sani duk cikin yaranta babu mai zafin ranshi duk da yana mata biyayya amma baya iya hadiye magana idan tazo bakinsa tsab a gaban kowa zai fada mata wani irin murdadden hali ne dashi baya shakka baya tsoro,dakuwa ta watsa masa tace "kaniyarka ubana bari na zauna kamun bayani sai ayi abunda kake so,wallahi wallahi Hydar idan baka fita a hanyata ba a gidan nan ni da Kaine ne,wato labe ka soma mun ko? Daga gidan ubanwa ma kake ka dawo ba sanarwa?". Kallon Momy kawai yake bece komai ba ya juya yabar dakin,kwafa kawai Mommy tayi tana jin zuciyarta na zafi." Kiyi hakuri Mommy insha Allah za'ayi yarda kika ce"ta tsinkayi muryar Lamin".Murmushi ta saki dan tasan tsananin biyayyarsa gareta tace"Allah ya maka albarka tashi kaje Abban naka na jira"...koda ya fita ji yakeyi har baya gani sosai kasa wucewa yayi dakin Abban da kyar ya gaishe da Aunty Amarya dake parlon ya wuce part dinsu ya shige d'aki ya kwanta yana sauke numfashi a jere-jere....hannu Ammi ta sanya ta karbi karamin picture din dake hannun Layan ta tsurawa ido tana zancen zuci Wanda hakan yasa har bataji shigowar Ammi dakin ba,saurin yin kasa tayi da kanta tana wasa da zara-zaran dogayen yatsun hannunta,zama kusa da ita Ammin tayi tana k'arewa hoton Jabeer kallo Wanda ta karba a hannun Layan,Murmushi tayi sai kuma tace"gashi kuma Yayan naki yayi kyau a hoton".fuskar Layan sosai ta fad'ad'a da murmushi ta rike hannun Ammi sosai cikin nata tace"to Ammi aishi dama Yaya Veer mai kyau ne,duk gidan nan babu mai kyan sa"...Murmushin Ammi ta sakar mata tare da cewa"kuma Layan saboda kyau kenan kike son sa".kallon Ammi tayi duk da tasan aduk duniya yarda Ammi tasan komai nata ko Basma da Muhibba basu sani ba,yes Ammi ta raineta amma ta zame mata uwa,kawa kuma abokiyar shawara tana taka muhimman bangarori da yawa a rayuwarta sam mantawa ma takeyi da Ammi ce mahaifiyar Yaya Jabeer .girgiza kanta tayi duk da kunyar data rufeta cikin sanyin nan nata Wanda ba kowa ya Santa dashi ba tace"ko kusa Ammi,ai kyau yana gushewa ko ba mutuwa ai akwai tsufa,kawai so ne na tsakani da Allah marar algush".Jinjina kai Ammi tayi kafin tace"kuma duk da zuciya,izza da d'agawa da nuna mulki irin na Jabeer amma