Showing 30001 words to 33000 words out of 55893 words

Chapter 11 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt

a fuskarta tace"mom amma fa ya hadu,I loved him so badly, kawai ya daina kulani a Paris shiyasanya na hakura na koma akan Lamin amma Jabeer is my first love mom"...kyab'e baki Mom tayi tace"yau naga shirme wannan kyau ba hali ina amfaninsa,ai kara maki Lamin din,amma wannan Dan iskan yaron da ko gaisuwa bayajin zai iyawa mutun sai uwarsa da fatyn to ina amfaninsa,ni bama zan iya hada zuri'a da maryam ba sam bata mun ba"...Dafa Mom Ihsan tayi tace"kedai mom kawai dai na kama girmana na hakura da Jabeer ne,amma har gobe ina jin san sa a raina ,beside ma wannan y'ar kauyen yarinyar bata dace da Jabeer ba sam,ba girmansa bane sun gama zubar dashi ace duk class irin na Jabeer ya kare a wannan bak'ar yarinyar no beyi ba"Ihsan ta kare fada tana hade fuska kamar wacce akawa wani abun kuma...kallon tsab Mom ta mata sai kuma tace"to babu dai ruwanki,na kuma rabasa da ke kinsan kuma akai maganar Dan uwansa a kanki karna kara jin kin ambace sa,babu abunda Jabeer yafi Lamin sai bakin hali,kinji ma na fada"..tana kaiwa nan ta fice tabar mata d'akin ma gaba daya....Murmushi kawai Ihsan tayi tare da kwanciya ta rungume pillow tana tunano kyakyawar fuskar Jabeer kamar ta sace shi ta gudu. .....Daudauke duk wani clothes da Layan ta zubar a k'asa Ammi keyi fuskarta a daure tana jiran fitowar Layan daga bathroom gaba daya ta mayar da room din out of order kamar wata baby.tana ta tsaye Layan ta fito daure da Babban pink towel dinta daya sauka har gwaiwanta kanta sanye da hulan wanka,kallon d'akin tayi sai kuma ta ware manya-manyan idanuwanta tayi murmushi tace"Ammi I'm sorry dama yanzu zan tattara"....wani kallo Ammi ta mata taci gaba da abunda takeyi sai bayan ta gyara komai tace"kici gaba da acting like a baby gal kinji,zanyi maganinki ne"bata jira cewarta ba ta bar mata d'akin...Murmushi Layan tayi kafin ta wuce ta shirya ,tana duba kaya a so be careful gudun kada ta kuma batan d'akin Ammi tayi maganinta...


*RUHIN JIKI*


_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*___________________________________*




*JORDERH MAJIDADI*




24




Rigace mai irin mai fadin nan ta material ash colour sai ta daura black veil a sakalken gashinta silent performs kamshinsu d suka gama bin jikinta ke tashi ,parlon ta fito tana tura dan karamin bakinta ta tsaya a bayan Ammi dake zaune a sofa da littatafai a gabanta tana dubawa,eyeglasses dinta ta cire ta dago tace"to tsayuwar me kike mun a kai kuma?"kuma tura baki tayi bata ce komai ba...shigowar Jabeer da Lamin yasa ta saki fuskarta ta kuma kura masu kyawawan fararen idanuwanta tana murmushi ,Lamin ne ya kalleta sai kuma shima ya saki murmushin yace"y'ar Ammi lafiya dai ko?"..Ammi ce tace"barni da yarinyar nan Lamin,nema takeyi yau nayi maganinta,tamun tsaye a kai kamar wata sabuwar kamu".Dariya sosai Lamin yayi yace"haba Ammi kema kin fada ne,wake shiga tsakaninku da Auta? Mudai namu kallo ne"ya fada yana tabo Jabeer daya zauna kasa kusa da Ammi yana latsa waya ko sanin abunda sukeyi ma beyi ba.kallon Lamin yayi sai kuma ya mayar da kallon ga Ammi yace"Good morning".."ka tashi lafiya ya hutun"Ammi ta bashi amsa, da Alhmdllh ya ansa ya kuma dukar da kansa yaci gaba da latsa wayan shi..."kije ki kawo masu breakfast"Ammi ta fada...Da sauri Jabeer ya dago yana kallon Ammi amma bece komai ba ya kuma dukar da kansa yana daure fuska ga wani abu daya masa tsaye a zuciya.kunshe Dariya Lamin yayi yana dukar da kai dan yasan irin yunwar da Jabeer ya shigo da ita,bedaice komai ba ya juya yana kallon Layan dake shirya table bayan ta karasa cikin sanyin murya tace"Ammi me za'ayi saving".kallonsu tayi ta mike tana tattare books dinta wuri daya ba tare data kallesu ba tace"to the dinning area"bata jira cewarsu ba ta mike ta wuce dining din,Lamin ya fara mikewa ganin Jabeer beda jiya yasa ya soma jansa da karfi,wani harara ya jefa masa yace"Malan meye haka kuma".."c'mon bansan fulako ka tashi muje ka kwashi girkin Lil sis ,ko ka kwantar da wannan mahaukaciyar yunwar da kake yawo da ita,ance mutun yayi aure amma ya gagara to a kare acin na kanne"...kyab'e baki Jabeer yayi amma bece komai ba ya dago kai ganin Ammi na kallonsu yasa ya mike suka karasa dining din ,yaja kujera ya zauna..Layan kam ta fara saving Ammi kafin ta karasa kan Lamin ,saurin mikewa Jabeer yayi ya dauki Cup da sosage din shi da tea spoon ya karasa a sink ya fara wanke su ya dawo ya zauna zaiyi making coffee, sake komawa yayi ya kuma wanke cup din sannan ya zuba coffee powder kallonsa Ammi tayi tace"har raina Jabeer ina tausayin matar da zata aureka,su cups din me sukayi? Wannan hali dai ba zaka barsa ba".shidai bece komai ba ya soma juya coffee shi Wanda bema tunanin zai iya saka shi a ciki saboda tsayuwarta a wurin...cikin sanyin murya a hankali tana tsoran kada yace ta masa ihu tace"Yaya me za'a zuba maka?".ko kallonta beyi ba bare tasa ran zai amsa tana ta tsaye a kusa dashi rike da plate.....kurba ruwan tea Ammi tayi tace"ina ga da kurma ake magana a wurin nan ko Jabeer"...marairaice fuska yayi ya bude baki zaiyi magana sai kuma yayi shiru,can dai yace"Ammi I'm not hungry "...Bata kulasa ba taci gaba da cin Abincin tace"Layan ajiye plate din ki zauna kiyi karinki shiya sani". Daure fuska tayi sosai ta dube shi in a serious note tace"kada na kara ganinka kazo nan cin abinci in ba haka ba zaka ga me zanyi".. Da kallo yabi Ammin data tashi tabar dining din.phone's dinsa ya dauka yabar dining din shima ....Hannu Lamin yasa ya dago fuskar Layan data dukar da kanta bata san dalilin da yasa hawaye ya soma bin fuskarta ba yana tsere a fuskarta,B'ata fuska yayi yace" lil kuka? Yau kika san Jabeer din ko meye?",Girgiza kanta kawai tayi tasa hannu ta share fuskarta ta ajiye spoon din hannunta tace"a'a Yaya kawai na koshi ne".Shima ajiye spoon din yayi yace"OK fine you can go"...kamar zata mike sai kuma ta kallesa tace"to ba zaka ci Abincin ba Yaya"...."na koshi"ya bata ansa ya soma tattara wayoyinsa cikin sanyin murya tace"to kayi hakuri ka zauna sai muci".Girgiza kai yayi yace"no na koshi ina sauri akwai wani case da nakeyi ne".raurau tayi da ido ta turo baki.Murmushi yayi ya zauna yace"let eat"suna cin abincin yana kwantar mata da hankali duk da ba wani ci takeyi ba dan gaba daya kuma yanzu damuwa ta gama kanainaye zuciyarta batajin dadin ganin Yaya Jabeer a haka,gaba daya sai ta rasa sukuni taji kamar taita yin kuka ga zuciyarta ta dinga mata zafi kenan,a kullun kuma kamar kara mata tsananin son shi akeyi ta rasa ta ina zata fara ma...kamar saukar aradu haka taji tambayar Lamin a kwalwar kanta duk da ba yau ta soma jin irin tambayoyin ba amma bata taba tsammanin ya gama fuskantarta ba cikin rawar murya tace"a'a Yaya"...Da manya manyan idanuwansa ya kalleta da kyau yace"karya kikeyi Maryama,idanuwanki basa iya boye gaskiyar abunda ke zuciyarki,kowa ya kalleki zai iya fuskanta kina son Jabeer just accept the fact"...wani hawayen ne ya kuma zubo mata amma bata ce komai ba...kafin yaci gaba da cewa"kiyi addu'a in alkhairi ne Allah ya shige maki gaba ya mallaka maki shi,,,nima fa na taba yin irin haka,ko ince ina ciki ma".saurin Dago kanta tayi tace"you mean"..."ina son wata sosai kamar raina,har gobe ina jin idan na rasa ta ko wani abu na cutarwa ya sameta zan iya rasa raina a kanta ,bana jin kuma zan iya daina sonta har karshen rayuwata lil"...waro ido tayi da alamun tashin hankali tace"to yaya ka aureta mana,tana ina kuma".murmushi yayi mai ciwo yace"is too late lil,ita ai bata sona akwai Wanda take so,kuma nima kinga aure zanyi"...tura Dan karamin bakinta tayi tace"ai ana auren mata fiye da biyu,kuma banga Wanda zaice baya Sonka ba".Dariya yayi yaja kumatunta yace"to ni dai kinji kiyi addu'a kawai ni zan fita" harya fara tafiya tace"to Yaya baka fada mun wacece ba"...waro ido yayi yace"ba amfanin sanin haka gaskiyar dai itace ina sonta kuma zanci gaba da sonta har karshen rayuwa Lil".be jira cewarta ba ya fita daga dining din....da kallo tabi bayansa harya fita a parlon.ji kawai tayi tausayinsa ya kamata gaba daya abincin ya kuma fice mata a kai ta tashi ta tattare wurin ta wuce dakinta dan bata son ma fita yau din nan bata son yin magana ...Dafe kirji Annie tayi tare da furta"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"tayi tsaye a kofar bedroom room din tana mayar da numfashi sai kuma ta karasa kwashe labulen ta shiga taba kabbara tace"wallahi wallahi maryam ta haifo mana jaraba a gidan nan,anya Jabiru kana tsoron Allah kuwa,har yanzu ba zaka daina sata ba?"sai kuma ta fashe da kuka tana bin kwanon furarta da tasha fresh nono ta dame abunta da daddare ga kular farfesun yan cikinta Jabeer yaci yayi nak kadan ya rage furan yana ta shan farfesun abunsa..."ka sani ba yafe maka zanyi ba,hakkina kadai sai ya hanaka kwanciyar kabari,yau sai ka bar gidan nan ,ka koma can wurin dangin ubanka,yanzu in yi magana ace nayi maka sharri,amma kuma mugun halinka yafi karfinka Jabiru"tana kuka tana goge fuskarta da habar zani....Jabeer kam bece komai ba ya ajiye sauran farfesun ya goge bakinsa da tissue ya mike ya kwashi phones dinsa yace"tunda a kanki nake zaune ai sai ki Kore ni ko",...Duka Annie ta kai masa a baya tace"da uwarka Maryam kake badai ni ba,mutumin banza labcecen kawai ai kara ma a maka auren kabar gidan,ko sadaka sai an bayar da kai".Dafe bayansa yayi in da ta masa dukan yayi murmushi yace"to kin daki kazarki Allah"...gwalo ido tayi tace "a'a ai bansan zaka siyomun kazar ba,to yi hakuri, karasa cinyewa maza ,zauna bari ma na kawo maka Fankasu dana toya dazu da miyar kai"... Bata jira cewarsa ba tayi waje...murmushi mai kyau ya subucewa Jabeer Wanda ba kasafai ake ganin Yana yi ba,tuni yaji duk wani damuwarsa ta yaye yana matukar jin yarda yake son Annie a ransa ga kwadayi ga rigima
*RUHIN JIKI*


_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*___________________________________*




*JORDERH MAJIDADI*






25


Gaba daya b'angarorin biyu shirin biki sukeyi,kyab'e baki Layan keyi kamar wacce zata fasa kuka tace"Dan Allah Aunty Amarya nikan na koshi da abunnan,babu dadi banma san menene ba"Harara Aunty Amarya ta watsa mata tace"ina guba nake baki,kin dauka kin shanye ko sai nayi maganinki a nan".Murmushi Layan ta saki tare da saka dogayen zara-zaran yatsun hannunta da suka sha ado da jan lalle duk yatsa ta rufe bakinta tace"Allah ya baki hakuri Auntyn mu,nikan wasa nake"..."ke kinma samu tana baki,nikan nama kasa gane kan gidan nan kwana biyu gaba daya,ina dalili mu ba'a tamu ko ina ke ko ina ke"Basma ta fada tana kyab'e baki Muhibba kam jinjina kai tayi tace"to ina dalili ki kwallafawa ranki shan abu ba dadi Basma?"..pillow Aunty Amarya ta dauka ta jefa masu tare da cewa"find your way guys"sun san Aunty Amarya ba wasa har Riga rigan fitan sukeyi suna kunshe dariyar da sukewa Layan daketa mammate ido.....kayane baje kama daga less,atamfa jadda all women's wear daya kama a saka a boxes na lefe jibge a tsakiyar parlon Mommy tana hakimce a babbar tausashiyar sofa dinta waya a hannunta tana lissafa kayan ita da kanwarta Hajiya Sadiya da tazo daga Kaduna dan hada lefen,yanzu duka duka auren be wuce 2weeks ba shissa komai take yinsa akan lokaci,so takeyi ayi auren da ba'a taba yinsa ba,wani Less Hajiya sadiya ta daga tace"nikan in an biye ta nawa boxes din sunyi yawa kayanma gasu a jibge sai kace za'a kaiwa yar Governor, a'a gaskiya sai kace a bola Lamin din yake ebo kudin Yaya? Ke ba zaki tsawata masa ba". Lamin dake zaune gefe murmushi kawai yayi dan duk abun nan da akeyi shidai Mummy sai dai tace ya tura kudi kawai,amma be taba kin turawan ba,shine ta hada da nata ta jibga uban kayan nan,shi kallon abun kawai ma yakeyi duk kamar a mafarki...tsuke fuska Mummy tayi tace"ni dai gaskiya Halima mitarki ta ishe ni haka,kedai kiyi abunda ke gabanki ko in nemi kawayena su shirya mun,sai kace kin mance wacece Hajiya Sha'awa? Ko ita Ihsan din ke baki sani ba,su dai ba kananun mutane bane bare a masu karanta meye marabar Ihsan da yar Governor? Wallahi biki zamuyi na kece raini,duk hadawan da za'ayi so nake a banbance a karara babu yaron da zaiyi auren gata sama da Lamin"...ita dai Aunty Sadiya bata kuma cewa komai ba dan ita tun farko Hajiya Sha'awa ba mutuniyarta bace bare kuma wata Ihsan dan dai tasan Yayar tata ba mai fada mata taji ne tun bayan rasuwan iyayensu,ita wani abunma har mamaki yake bata,meye wani Ihsan Allah na tuba...wayarsa ce keta ringing ba kakkautawa tun dazu yake silenting wayan dan shi a tunanin shi wani abun Annie ta cewa Ummi yayi,ganin ba sarki sai Allah yasa ya daga wayar ya kara a kunne bakinsa dauke da sallama yace"Ummi"...."Halan Jabeer ka makance baka ganin missed call's ne?,bana son sakarcin nan naka,tun dazu nake kiranka amma baka dauka ba kuma baka biyo ba"...kasa yayi da murya sai kuma yace"kiyi hakuri ina office ne,wani abun ya faru ?"...."yaushe zaka shigo bikin Lamin din"Ummi ta tambaya ,shiru yayi sai kuma yace nan da one week insha Allah Ummi"...shiru Ummi tayi sai kuma tace idan ka tashi tahowa ka dauki hutun saki ko ukku ne a gaba akwai tafiyan da nike so muyi".Waro manya manyan idanuwansa yayi dake cike da gajiya yace"Ummi ina da aiki after bikin da da 2days fa"..."to kawai kace mun ba zakaje ba yafi mun sauki,aikin har yafi zumuncin Allah Jabeer wannan ya zama dole ne"...shiru yayi sai kuma yace"to sai na shigo insha Allah,ina aiki sai anjima "be jira cewarta ba ya kashe wayar yana tunanin ina kuma zasu ko mai zasuje yi,haka nan dai ya ajiye tunanin gefe yaci gaba da aikinsa kawai .....Agogon parlon nashi ya kallah yana zaune a reading table sai kuma as if his life defend on the phone haka ya kura mata ido yana kallon sunan Ammi a jiki,haka nan kawai yake jin wannan kiran da suke masa is like he's smelling something amma bamai fada masa komai,tattausan gashin kansa da yasha aski ya shafa wayar na dab da katsewa ya daga,daga can b'angaren Ammi tace" where have you been Son?"."Good evening Ammi"..."evening baka ce komai ba Jabeer is everything right ?"Ajiyar zuciya ya sauke yace "komai lafiya lau Ammi yana yin aiki ne ". Ai kunyi waya da Umminka ko?" Kamar tana kallonsa ya jinjina kai yace"eh Ammi"tace "to dan Allah karka bata lokaci ko wani abu da beyi daidaiba "... Cikin cool voice yace" to wai ina zamuje beside ina da aiki lokacin Ammi,ni bansan ya zanyi ta fahimta ba"..."kilan dai siyar da kai Fatimar zatayi ko Jabeer,kasan bana son halin nan naka na kafiya just obey shikenan ka dauko hutu as she say na fada maka bana son other reasons kuma ko wani maybe a lamarina Bawan Allah,tun da ai kasan ba'a taba maka haka ba,in kuma baka yarda ba do what suit you dama ko yaushe ai gaban kanka kakeyi "..." Kiyi hakuri Ammi,,sai na shigo insha Allah".sallama sukayi Ammi ta kashe waya ta dubi Ummi tace"idan ba haka aka masa wuta wuta ba kinsan ba zuwan zaiyi ba,wallahi Jabeer is the real copy of his late Father komai ba abunda ya baro"Dariya Ummi tayi tace"to saukin ma ai yana sauraranki ko wannan zuciyar ta gado ta taso,shissa kika ga ni ban masa da sauki duk da nasan wannan ba zai hanasa iyar shegensa ba,shiyasa tsab na shiryawa duk wata tabararshi bayan auren nan,dan naga almun sai munyi da gaske wallahi".Murmushi Ammi tayi tace"to kun daifi kusa,yanzu me da me kike ganin za'a kara a boxes din? Yanzu na maki transfer a karasa,kinsan idan na koma office ba time balle duk kusan weeks din nan ina da Wanda nakewa CS to bana samun isashen lokaci".kallon Ammi Ummi tayi tace"haba sai kace dai Jabeer din tsintarsa nayi Ammi? Kin mata ubansa ne kadai Allah ya bani ? Daga ni har Janar ubansa ne silarmu zuwa wannan matsayin,shine kuma a hidimarsa har sai kudinki sun shiga? Can dai kya masa wani abun amma boxes 16 duka an gama saka komai shoe ne kawai muke bukatar ki bamu size,even Gold's dinta duka an saka a boxes din kowa zaisan Jabeer yayi auren gata ranar daurin auren zamu kawo,kamar yarda kika bukata fatanmu dai Allah yawa abun albarka ya bida mana wannan Captain din".Dariya Ammi tayi ta tashi ta dauki handbag dinta da veil har gate Ummi ta rakata sannan sukayi sallama ta shiga mota zuwa gida......"ah kul na haneki da gulma,kidai kisa ido kawai ki kallo,koni nan da kika gani zuwa ido nakeyi dan wannan biki jinsa akeyi kamar yafi na kowa to a ranar daurin auren nima zan baza nawa tanadin sai na bawa ko wanne shege mamaki a gidan nan,kowa zaiga irin nawa ikon Wanda basu taba tunani ba,,wallahi zasu ga karshen iya shege,ranar Badiyya zata raina kanta".Dariya Layan ta tuntsure da ita tace"to gaskiya babu ruwa ,karma kice da ni kike maganar Momy a gidan nan,ni dai ba ruwana wallahi"kyab'e baki Annie tayi tace"menene kuma wata narkekiya Badiyya? Me akai akai Badiyarma gaba daya wacce muka yanta muka dauketa duk Doyi duk wari a gantaki? Sadeequ dai ubanki shine silar zaman Badiyya a gidan nan harta kankame mun 'Da danma Allah yasa nima ba a banza nake ba tsaye nake kamar hakori kullun cikin nema nake da yanzu wani bayani akeyi ba wannan ba,nidai dama da farko korarta nayi nace tsabta ma cikon addini ce ta rufa mana asiri ta tafi kafin ta goga mana wata cutar,amma Sadeequ ya tsaya kai da fata harna hakura ta auri Ahmadu sannannefa ta fara wanka da Dan gyarawa ga kan nan kamar hammatan Dan iska ke lamarin dai babu dadin tunawa,amma yanzu take ganin harta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login