Showing 45001 words to 48000 words out of 55893 words
Chapter 16 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt
a fan yayi zafi ta zuba kafin ya soyu ta hada egg tana karasawa shima ta soya egg din ta kuma hada ruwan shayi ta fitar da wormer 's din a dining.ta zauna ta cika plate ta hada ruwan Lipton ta soma ci a hankali tana tunanin ya rayuwa kuma zata sake juya mata ga kuma tunanin gida daya addabeta......fuska daure Jabeer ya dawo parlon ya zauna Yana pressing phone can dai yace"if you're done,Ina jiranki,mikewa kawai tayi ta iso gabansa sai tace"Yaya in ibar maka Irish din?"kallonta kawai yayi sai kuma yace zaki duk'a ko sai na shureki kin duka a dole?"b'ata fuska tayi ga kuma tsoronsa from no where dake kuma dirar mata,sai dai babu abunda ya ragu a soyayyar da takeji ta masa.ta duka akan kneels dinta tayi k'asa da kai.cikin dakakkiyar murya Jabeer yace"Allah yasa kina ji sosai,Dan wannan katton kunnuwan naki kada ace sun tashi a banza, firstly kisan ba hutu kika zo yi a gidan nan ba,idan kika karya dokata daya you will see the other side of me,which bana so mukau haka da ke,dama gidan nan kinsan kiyi harkarki ne,idan kin tashi jagolgolon girkin ki dama zakiyi iya ke kad'ai ne,bana son k'azanta da lalacin banza,ba wani Kato ko katuwar Yan aikin da zan bukata a gidan nan u will take all the duties since from gate to nan ciki in baki da nose max ki nemo tun wuri"saurin zare Ido Layan tayi tace"Yaya ai bana shara dust yayi yawa Asthma Dina zai tashi in ta wahala".wani banzan kallo ya mata a tsawace yace"kinsan kina da Asthma din kika aure ni,yar yarinya dake har kinsan aure?let me not repeat my self if not you will make your life a living hell a gidan nan Layan"ya kare zancen cikin cool voice.wani iri taji daya kira sunanta sai taji kamar duk duniya yafi kowa iya Kiran sunanta sosai hakan ya dauki a hankalinta tuno makarantarta kuma tace"Yaya school fa".bece komai ba sai kuma yace"idan kina cika duties dinki to zaki koma school,shima akan sharuddan da zan gindaya maki idan lokaci yayi,aikinki zai fara daga gobe.bana son tuna maki kuma"...jinjina kai takeyi sai a hankali tace"bani da nose max din Yaya"..ledan kusa da shi ya tura mata bece komai ba ya mike ya fita daga gidan dan dama ya shirya fita zaiyi.A hankali ta mike ta nufi dining ta dauki fork amma gaba daya taji abincin ya fice mata a kai rufewa tayi,ta mike da ledanta a hannu ta wuce bedroom dinta tana ji gaba daya duniyar ta mata ba dadi a stool na morrow ta zauna sai kuma ta turo bakinta sai hawaye sharrr sharr,tasa hannu ta goge tana kallon ledan data shigo da shi a hankali tace"ni da bama da lafiya ta yaya zanyi duk wannan aikin? "Tama kanta tambayar da bata da ansa a nan ta zauna tasha kukanta har ta gangaro k'asa a rug's na wurin bacci ya dauketa da tunanuka iri iri.....ba ita ta Farka ba sai gab la'asar da sauri ta Kalli agogo ta zaro manyan idanuwanta tana tura baki,ta wuce toilet wanka ta sake yi ta dauro alwala ta fito ta shirya sannan tayi sallah ta kuma fita dining kallon Irish din dake ajiye tayi ita bata San ya zatayi da shi ba kuma dole a haka ta zauna tana cinsa tana tura baki da k'yar ta cinye ta tattare kayan ta wuce kitchen ta wanke ta ajiye komai in da yake sannan ta fito parlon ta zauna a sofa tana karewa ko Ina kallo ga kadaici da kewa ya dameta ko waya babu a hannunta...
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
36
Kallonta kawai yake yi kamar Mai son gano abu ko kad'an beyi mamaki ba,girgiza kansa yayi ya karasa cikin bedroom din nata ya soma kiranta"ihsan,ihsan" Jin shiru yasa ya bubbuga pillown da take kwance da dan karfi sannan ta bude Ido tana kare masa kallo be bata change ba yace"Amma Ina ga tun asuba nace ki tashi kiyi sallah Kalli lokacin almost 8 na safe amma bakiyi sallah ba,haka kikeyi a gidanku?"wani irin turo baki ihsan tayi cike da masifa tace"Dan girman Allah Lamin let me be,ban taba ganin ango kamarka ba,Ina dalili ka tafi ka barni sai da na gaji na kai maka kaina sannan kuma bayan na kwaso gajiya kazo ka wani dameni ko karfe nawa ne ai dai dole nayi sallahn na gaji da irin walakantani da kake yi this is real you Lamin".wani murmushin takaici ya saki kafin yace"to komai zakiyi zan iya dauka Ihsan amma banda rashin sallah tunda gidan ba gidan kafirai bane,dama tun wuri ki ajiye wannan d'abi'ar ko kuma zakiga yarda zanyi maganinki a gidan nan."be Jira cewarta ba ya nufi kofa ya fita yana tunanin ta wacce hanya zai zauna da Ihsan.siririn tsaki ta saki kafin ta mike ta shiga bathroom ta hada ruwan zafi tayi wanka tare da alwala tana fitowa tahau shirinta ta tsuke cikin Riga da skirt na material Wanda suka kamata sosai ta murza dauri ga fuska tasha make-up tako Ina,sai a sannan ta kuma tunawa da sallah ta zura hijab tayi sallahn ta mike ta fita Dan yau kamar an kwashe mata Yan cikinta haka takeji don yunwa,kai tsaye stairs ta nufa tana kallon Lamin dake zaune ya lumshe idanuwa kamar Mai bacci Yana kallon sama tab'e baki tayi ta karaso ta zauna kusa dashi cikin cool voice tace"hey,Good morning ".bude lumsassun idanuwansa yayi Yana kare mata kallo bece komai ba ya Dan gyada kai kawai sannan tace"to nifa yunwa nake ji".wani kallo ya mata yace"to wa kike Jira ya shiga kitchen din"waro idanuwa tayi tace"ai Amarya bata girki beside bayan tafasa ruwan zafi ma billah ko indomie ban iya girkawa ba,bana son stressing kaina"da mugun mamaki Lamin ke binta da kallo sai dai bece komai ba ya mike ya nufi kitchen ruwa a flaks ya Iban mata a cup sannan ya soya mata egg ya dauko da break ya daura a tray ya kawo mata tana nan parlo tana danna waya.wani kallo ya mata kafin yace"dama kisan yarda zaki nema abunda zaki ci ,bazanyi nema a waje nazo kuma na kare a kitchen ba".wayoyinsa dake a kujeran ya kwasa yayi sama ko ansa thank you din da take fada masa beiyi ba ya haye stairs abunshi........tun Kiran sallahn farkon na asuba ta Farka wanka tayi tare da dauro alwala ta dawo ta shimfida sallaya tayi raka'atanil fajir tana ta zaune har aka kira asubahi sannan tayi sallah ,ta Saka Riga marar nauyi ta feshe jikinta ta turaruka masu Dadi ta soma gyaran dakinta sannan ta wanke toilet ta Saka turaren wuta ta fito waje tana kokarin Saka hulan kanta suka kusa cin karo da Jabeer Yana dawowa daga masallaci,ko kallonta beyi ba ya rab'a ta gefenta zai wuce cike da sanyin nan nata ta bude baki zatayi magana saurin d'agaata hannu yayi tare da cewa"karki cika mun kunne da wannan rashin natsuwar taki tunda asuba"be bata listening ear ba kuma yayi wuce warsa ciki.jiki a sanyaye ta karasa fitowa parlon.nose max dinta ta dauko ta Saka da bucket da mop ga tsintsiya da faka tana tunanin ta Ina zata fara kuma".tana ta tsaye tana kyab kyabta manyan manyan idanuwanta,kamar zatayi kuka haka ta taka tana kuma tina gargadin da yake mata a jiya,amma haka nan ta daure ta hau stairs din daidai kofar dakin da take kyautata zaton nan ne d'akinsa ta soma kwankwasawa a hankali gaba daya tsoro ya gama cikata kamar k'afarta ba zata dauketa ba,har sai da ta cire ran zai bude kofan tana niyar juyawa taji alamun tafiyarsa wani irin daskarewa a wurin tayi dana sanin zuwa wurin lokaci d'aya ya dirarta kamar zata saki fitsari,suna yin ido biyu ta lumshe idanuwanta da sauri ta soma ja da baya.shikam mamaki ne ya kashe sa gaba d'aya watau yarinyar nan dan tana Jin an daura masu aure har ta kuma rainasa kenen? Be isa ya Saka doka ta bi ba kenan Aiko zata gane kuranta,wani kwafa ya saki ganin tana yin baya yace"billahil Azeem idan kika gudu sai na karkaryaki a gidan nan ,uban me ya kawo ki nan?"...saurin zaro idanuwanta tayi ganin irin seriousness dake fuskarsa,da k'yar ta hadiye yawun daya taru a bakinta na tsoro tasa dogayen hannuwanta ta rike k'asa doguwar rigarta kwarai kamar zata b'alla ta kasa cewa komai sai girgiza kai da takeyi kawai....wani zuciyan ne ya kuma kume Jabeer yayo kanta bejira komai ba ya kwasa mata wani lafiyayyen mari cikin takaici yace"wato rainin har yakai haka tsakani na da ke,ni da gidana ban isa na Saka doka ba ki bi,ubanme kika ajiye a nan jarababbiya kawai, monster to sai dai kici kanki a gidan nan"...wasu hawaye ne masu zafi suka soma zaryar sauka a kuncinta wasu na bin wasu ga hannunta dafe da kuncinta Wanda sahun yatsunsa suka fito radau radau a jiki,kasa cewa komai tayi ganin Yana neman yowa kanta yasa tayi baya da gudu tare da sakin Kara tayi k'asa a garin tsallake stairs ta fad'i a wurin ta soma gangarowa harta karaso kasa gaba d'aya wani irin wahalalliyar Kara da bata fita sosai ta saki tare da cewa"wayyo Annie na wayyo Ammina mutuwa zanyi,bayana ya kare,Yaya,Yaya"....Jabeer dake tsaye ya kura mata Ido harya mance Rabon da yayi mata irin wannan kallon siririn tsaki ya saki wani takaici na kumeshi ganin da gaske ta kasa tashi yasa ya karaso wurin tare da cewa"gobe ma idan halinki ne gulma kya Kara hawa "hannu daya yasa ya d'agota ta saki Kara tare da mak'alk'aleshi ta fashe da kuka tana fadin"Yaya k'afarta ta karye wallahi bazan iya takawa ba wayyo Allahna "ta kuma sakin wani kukan,hannu yasa ya bige mata baki cike da takaici yace"kimun shiru ko inyi maganinki a wurin nan,sakaryar yarinya kawai".duk yarda yaso ya banbareta daga jikinsa kasawa yayi Dan riko tayi masa bana wasa ba,tsuka yaja sannan ya dauketa kamar yar baby ya wuce dakinta da ita,a gefan bed ya dungurar da ita Yana jefa mata harara ita kuwa bata San Yana yi ba sai aikin kuka da take yi,fitowa yayi daga dakin ,d'akinsa ya koma ya dauko man zafi ya dawo ya duka daidai k'afarta,kokarin janye kafar takeyi yaja tsuka fuska daure yace"idan na tafi ke kike da asara ba ruwana"be Jira cewarta ba ya fizgo kafar da karfi Murda kafar yayi ya gyara targaden data samu ya shafa mata man zafin ya mike ya fita,ransa fal takaici .hawaye mararsa dalili suka soma zarya akan fuskar Layan daga haka har bacci ya kwasheta.Jabeer Kam Yana fitowa ya dauki su tsintsiyan yayi shara yayi mopping har plates da ya Gani a ajiye duk ya wanke ya gyara ko Ina Dan shi ya tsani k'azanta be kuma iya zama in da take.sama ya koma ya sake yin wanka ya kwanta baccin gajiya.
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
37
A hankali ta soma bude rinanun idanuwanta Wanda suka kumbura saboda uban kukan da taci soma zagaye dakin tayi kamar Mai bitar abunda ya sameta dafe kanta tayi tare da fadin"ash wayyo Annie na,so take ta tashi amma abun ya faskara kamar ance ta juya sukayi Ido biyu da Jabeer Wanda ke tsaye jikin kofar,siririn tsaki ya saki tare da karasowa ciki dawowarsa daga masallaci kenan,kamar Mai counting steps haka ya karaso ko kallonta baiyi ba ya janyo hannunta ya taimaka mata daidai kofar toilet din ya tsaya ya bude mata kofar a hankali tace"na gode"d'age kafadunsa yayi alamar ko in kula ya dawo gefen bed side drawer ya zauna Yana pressing phone dinsa tare da taune jajayen lips dinsa Wanda hakan ya dade da zama d'abi'arsa Yana ta zaune harta fito ba laifi tana takawa a hankali alwala tayo ,abun sallah ya shinfid'a mata ya ajiye mata hijab yayi gaba abunsa.wani sanyayyen murmushi ne ya kubce mata sosai taji dadin kulawar daya bata,ko ba komai ya nuna ita wani naauyi ce a wuyansa kuma da alama Yana kokarin ganin ya fita hakkinta,ba dan badan ba da tace ita ciwan ma alkhairi ya zamar mata,sai dai bata fatan haka,kamar kullun kamar ko yaushe yau ma addu'a ta samu kanta dayi masa sosai har fiyema data kullun,tana ta zaune kan sallayan ya shigo hannunsa dauke da takeaway da ruwa ya ajiye mata kusa da ita cikin kausasshiyar murya yace"ke kina jina"juyowa tayi in da taci karo da fuskarsa kamar jadarin gabas dake dab da tsinkewa da ruwa kasa tayi da kanta bata ce komai ba dai.cikin deep voice yace"zan fita,salan garin wannan rawar kan naki ki kuma turgude kafar,na maki alkawarin ba abunda zan iya maki,tunda rashin natsuwa ke damunki"be Jira cewarta ba ya fice abunsa duk da bataji dadin maganganunsa ba amma dai haka nan ta daure ta lallaba ta shiga bayi wanka tayi ta dawo ta Saka kaya marassa nauyi sannan ta zauna tana cin abincin daya ajiye mata cike da walwala da Jin Dadi,haka nan take Jin zata iya zuwa ko wanne stage danta kasance da Jabeer din Babu abunda ke dawainiya da ita sai tsananin soyayyarsa dake sake bijiro mata ta ko wacce fuska.....zaune yake yaki furta komai Yana kallon TVn dake Aiki a dakin ,da sauri Annie ta ajiye bowl din soyayyen naman dake hannunta sai tirin kamshi yake taja da baya sannan tace"la'ilaha'illah,kai Bukar ya tafi yabar jaraba a Doron kasa,yanzu Jabeeru da na Fadi na zubar da hakwara sai dai ka cuceni ka cuci y'ay'ana ka barsu da zaryar neman magani,to saboda Allah ba,kazo labcece ka girkemun a daki ,kayi auren ma ba'a huta ba".idanuwansa yakai sosai akan naman sannan cikin sanyin murya yace"zuwa fa nayi na gaishe ki duk kwarki ta dameni"sosai Annie ta washe baki ta zauna tana gyara daurin dankwali tace"Allah sarki mutumin kirki,ni wallahi dama nasan sai kasha wuya na zama babu ni Jabeer,shikam wancan Mai kama da uwarsa ta aura masa zabaya uwar jaraba kaga ko kafarsa bamu sake Gani a gidan nan ba wallahi Jabir,to dama wake gare ni banda kai din,nace zanje gidanka amma Bukar ya hana wai ba yanzu ba,to ni dai bazanyi musu dashi ba Dan nasan Maryam ce ta tirashi sai wani bubudawa takeyi ita ta aurar da kai da waccan figaggiyar ban dai ce masu komai ba".ta gefan idanuwa Jabeer ke karewa Annie kallo murmushi kawai yayi yace"gobe ki shirya zanzo ja dauke ki da kaina,yanzu zan tafi".washe baki Annie keyi sai ta mike bari na baka dambun da nawa Laya ka kai mata ko taji dadin bakinta wannan aure ai mutu ka raba Rukayya na can hassada zata kashe ta dazu na leka na mata tas nace wallahi idanuwanta su fita akan jikata ko kuma hukace zata rabamu".Shiru Annie tayi tana karewa parlon kallo ba Jabeer ba dalilinsa ba kuma bowl din namanta data ajiye ,wani salati ta saki ta jikinta har rawa yakeyi ta yo waje tana cewa"ku tare mun shi,Jabeeru ya zama jaraba,dama kada a Kara shigowa gidan nan a mana katangar karfe innalillahi wa'inna ilaihir raju'un "sai ta fashe da kuka kawai tayi part din Annie tana matsar kwallah a daidai kofa ta hangi Jabeer yana rufe motarsa yaja da gudu yayi baya gateman ya bude masa ya fice yabar gidan.wani dukan kofan Annie keyi tana kwalawa Ammi kira,da sauri Ammi ta ajiye Documents din da take sakawa a laptop dinta ta cire eyeglasses dinta ta taho da sauri ta bude kofar tana fadin "lafiya Annie".wani kallo Annie ta watsa mata sai kuma tace zuwa nayi ki fada mun ko Bukar uban Jabiru nawa yabar mun gado da zai mutu ko kuma idan kin Saka sisi kin siyomun naman da Kika taras Amadu ya siyomun Ina soyawa"ta kare maganar fuska a daure.girgiza kai Ammi tayi tace "kiyi hakuri Annieeya faru"...Annie ta rufe Ido tare da cewa"wallahi wallahi tsakani zaki mun da Jabeer kuma dama duk gidan ubanda ya kaimun nama na yau ba sai gobe ba a dawo mun da nama na,ko in tashi hankalin kowa a gidan nan".dafe kai Ammi tayi tana son bawa Annie hakuri amma tayi ficewarsa,karasawa tayi a table din da take aiki ta dauki wayarta ta soma Kiran number Jabeer,Yana Driving yaga Kiran Ammi dama yasan za'ayi haka,murmushi kawai ya saki ya kashe wayar gaba daya ya ajiye yaci gaba da driving dinsa Yana cin naman Annie daya dauko.kai tsaye gidan Ummi ya wuce da sallama ya shiga parlon ya zauna ,Ummi Kam fitowarta daga kitchen kenan Asma'u a bayanta suka jera wormer 's din hannuns sannan ta karaso parlon tana cewa"Asma'u ki sakawa Layan abinci idan yayanku zai tafi ya wuce mata dashi shi dai nasan idan ba niyya yayi ba he's always owk daukar magana kawai ya Saka a gaba".kallon Ummi kawai yayi yace"Ina wuni"tace"lafiya qlau ya iyali?"sai tambayar tayi masa wani iri ya kasa cewa komai,kallonsa kawai Ummi tayi sai kuma tace"iKon Allah,Jabeer ko har yanzu baka da iyalin ne?".shiru bece mata komai ba.kasa da murya Ummi tayi tare da cewa"Jabeer kana da ilimi daidai gwargwado you have to know what you're doing,koma me zai faru yanzu Layan nauyinka ce idan ka cutar da ita Allah Yana kallonka idan ka gyara duka kanka kaiwa,ka dauki kaddara,ko ba komai Allah ya rubuta sai ta kasance a mazaunin matarka,so kaji tsoron Allah".shi dai bece komai ba Yana shafa kansa can kuma yace"zan wuce dama nace bari nazo na gaishe ki ne"karar wayarta yasa ta juya tana daukar wayàn dake kusa da ita,tana dauka Ammi bata tsaya sun gama gaisawa ba tace"Ina Jabeer,dama ki fada masa duk in da yake ya dawo wa uwata da abunda ya dauka mata,I don't wante disrespectful da yake nuna mata,wallahi zanyi maganinsa saboda raini ni ko ganinsa ma banyi a gidan ba Ashe ya shigo"..."ayi hakuri insha Allah zak kira shi".sannan ta ajiye wayàn fuska a daure tace"me kaje ka daukanwa Anni?har yau dai ba zaka girma ba ko Jabeer".daure fuska yayi yace"ta ganni a Ina? Ko gidan banma ke ba".kallon ka raina mana hankali Ummi ta bisa da shi sai kuma ya saki