Showing 33001 words to 36000 words out of 55893 words
Chapter 12 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt
isa ,ita watace to wallahi wallahi kinji na rantse a ranar zata san nima ba a banza nake b,yar banzar kaina ce duk kyaleta nakeyi"..
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
26
Layan kasa rike dariyarta take duk da tana jin hakan sam bai kamata ba ko dan darajar su Muhibba amma sam ita Momy bata a lamarinta, hakanan Allah bai had'a jinisu ba,daurewa tayi tace"Annie ta wajena yanzu dai ya isa haka ni dai ba ruwana kinsanta yanzu tana ji kowa sai yaji a gidan nan,bari ma ni kitchen zanje Ammi ta sani girki tana dawowa banyi ba kuma nasan sauran"....mitsi-mitsi da ido Annie tayi tace Laya "nifa ba kanwar uwarki bace bare ta ubanki,da nayi magana jira kike akan Badiyya ki taka mun burki,kul na haneki da shiga lamurana idan ba haka ba wallahi wallahi kinji dai na rantse zaki kwashi kashinki a hannu,in dai Badiyya ce kici gaba da wani kakkareta ina nan zata kullo maki wata tsiyar tunda baki san ciwan kanki ba,tashi ban wuri tun kan nayi kukan kura a kanki". Wani Dariyan Layan ta matse ta fice da gudu tasan ta yita a gaban Annie zata sha terere ne....kallonta kawai Lamin yakeyi Dariyan sosai ya mata kyau ga dimples dinta da suka lotsa sosai gaba daya gani yake ta wani canza mai har wani kyalli kyalli takeyi ga fatarta tayi fayau kamar ba Layan ba,kullun ji yakeyi a ransa kamar ana kara mashi sonta,he wish Momy bata saka baki a aurensa ba,da yanzu Layan za'a aura masa ba Ihsan ba,amma duk da haka bai cire rai ba jira kawai yake bayan biki ya lallabi Momy ya auri Layan dan baya jin xai ita ci gaba da rayuwa da wannan soyayyar tata mai matukar wahalar da zuciya,he can't take it any longer zuciyarsa zata iya fashewa a ko da yaushe haka yake ji,runtse idanuwansa yayi yana jin sanyi a zuciyarsa na ganinta da yayi,itama da gudunta ta karaso in da yake tana cewa"Yaya",.idanuwansa da suka soma canza launi ya bude ya zuba mata su amma bece komai ba,cikin dauki tace"yau Annie tace zatayi maganina zan kwashi kashina a hannu".yadda take describing yarda Annie ta mata shi kadai ya bashi dariya badan yaso ba ya dara yace" da kika mata mene?,na dai san u and Annie 24/7 alkawarinku na nan"...."hmm not any longer kwannan nan naga hari take kokarin kaimun".murmushi yayi sai kuma yace"zaki raka ni unguwa Lil".waro ido tayi tace"sure Yaya,bari na daurawa Ammi girki sai muje".jinjina kai yayi yace"muje na tayaki" daga haka ya kama hannunta zuwa kitchen din,all the work sunyi shi a tare ne suna yi suna labari ,daga karshe ya jingina da cabinet yana kallon yarda take aiki dan girki is her favorite, ta iya sosai ,bata wasa da girki,shiyasa kowa a gidan rububin tayi girki ko kad'an ne,sai dai favorite Yayan nata ko kad'an baya iya kallon abunda ta dafa ma bare kuma har yaci kullun gani yake jagulgulo takeyi.ajiyar zuciya Lamin ya sauke yace"lil idan akai aure zaki koma gidana,I don't want miss this delicious girkin naki gaskiya".washe hakoranta tayi tana dariya tace"ah Ammi ba zata bari ba,u know idan na dawo school ni nake mana girki,da kula da gidan".Sallamar Ammi a kitchen din ya tsayar da surutun Layan da sauri ta ajiye spoon din hannunta da take juya orange juice ta ruga ta rungume Ammi cikin cool voice tace"you're welcome Ammina".kafin ta karb'a handbag dinta da laptop dake rike a hannunta,Murmushi Ammin tayi ta shafa kanta tace"ya aikin" ta ansa da alhmdllh kafin tayi hanyar waje zuwa bedroom din Ammi.sai a lokacin Ammi ta gaisa da Lamin sannan suka fito tare ya zauna jiran Layan...kallonta sama har k'asa Ammi tayi tace"zuwa ina kuma ?".."nima dai yace zan rakasa kawai ne Ammi,dan Allah kada kice bazanje ba".Layan ta kare maganar da alamun ban tausayi...kallon Agogo Ammi tayi kafin tace"kada kuyi magriba a waje".daga haka ta wuce tana rage kayan jikinta zata shiga ban d'aki,da long ash hijab Layan ta fito a har k'asa kamar yarda ta saba shigarta..."Yaya bari na karashe juye farfesun Ammi a collar"bata jira cewarsa ba ta shige kitchen din ta dauki coller making very careful ta samu ta juye farfesun cat fish din daketa tashin kamshi sunsha hadi,ta rufe colarn ta goge da tissue ta dauko ta ajiye a dining sannan ta fito suka fita....as always kamar yarda ta saba gaba daya tafiyan bata bar bakinta yayi shiru ba labari kawai take bashi cike da kuruciya shikam dariya da murmushi kawai yake yi sai ansa mata da yakeyi in ya kama,gaba daya farin ciki ya gama cikasa,tun tafiyar Jabeer bega tayi farin ciki irin na yau ba,gaba daya sai yaji yau din ta zamar masa special day ,A daidai wani tankamemen gate yayi parking ,gate man ya leko ya tabbatar da waye sannan ya bude masu suka shi,da kallo Layan tabi babban compound din da kallo ba laifi gidan yana da girma sosai amma bekai nasu ba sai dai gidan ya tsaru kallonsa tayi kafin tace"gidan waye muka zo Yaya".yana pressing phone dinsa yace "zata zo yanzu ki ganta". A kunne ya kara wayar.Ihsan dake zaune tsakiyar babban bed din dakinta tana ta daddaga wasu English wears da suka siyo da Husna ta juyo da kanta taga Wanda ke kiranta,dandanan fara'a ya cika fuskarta ba wani bata lokaci ta dauki wayan tace" Baby ka iso?".lumshe ido Lamin yayi yace"ina jiranki a waje".be jira amsarta ba ya kashe wayar .ba dadewa sai ga Ihsan ta fito daga entrance na gidan sanye da tsadaddun English wears dinta Riga da wando sai hula a kanta,sosai kayan suka mata kyau ta taho tana chewing gum a bakinta,kai tsaye driver seat ta nufa ta kwankwa glass din,zuge glass din lamin yayi dan danan uban kamshinta ya cika wurin sai dai tana sauke idanuwanta akan Layan ta wani daure fuska kamar taga mutuwarta,ta koma gefe taja ta tsaya tana wani cika da batsewa,kallon Layan Yayi yace"ki sauka ki gaisheta".kafin tayi magana kuma ya bude motar ya sauka.vividly take tuna irin rashin mutuncin da tayi mata ranar da taje gida gaishe dasu Annie,run daga ranar kuma taji gaba daya Ihsan din ta fita daga ranta,bata son musu da Yayan nata yasa ta bude motar ta fito fuskarta adan sake ta zagayo in da suke,ko kad'an baya tsaya duba yanayin Ihsan ba tace"good Evening ".wani wawan kallo Ihsan ta bita dashi sai kuma tace" yauwa sannu" daga haka ta kuma take fuskarta,Layan kam mota ta koma dan bama zata iya jurewa kallon da Ihsan ke binta dashi ba,Wanda ta kasa gane manufarta.kallonta Lamin yayi kamar mai irgan abu yace"me yasa zaki ansa mata a haka Ihsan,baki san sisterna bace?"..."kar kace zaka mun masifa a kanta Lamin,kasan nasan wacece ai,bata yimun ba,ba kuma zaka tursasani nayi alaka da ita bane tunda ba Momy ta haifeta ba,ina dalili duk in da zaka je tana biye da kai,kai kuma kaita rawar kai kana wulakanta ni a kanta to wallahi bazan dauka ba tun wuri kara asan abunyi"ta kare maganar tana tauna gum din bakinta yana kara...cike da mamaki Lamin yake kallonta sai dai bece komai ba ya juya ya barta nan a tsaye ya shige motarsa ya tada yabar gidan.ko kadan be canza fuskarsa ba hasalima a yanzu shi yake jan Layan da labari har ya tsaya yayi mata siyayyan da ya saba mata duk date kafin suka wuce gida....Ihsan kam fuuuu ta wuce cikin gida kamar zata tashi sama tana jin zuciyarta na tafarfasa kamar zata fasa kirjinta ta fito dan takaicin irin walakantata da Lamin yayi.
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
27
Yacce kasan wata zautacciya haka Ihsan ta shigo cikin d'akinta ta ibe hulan data rufe tulin sumar gashin data kara aka mata kalaba ta watsar gashin ya zubo a bayanta duk ACn dake aiki a dakin amma wani irin zufa ke tsatsafo mata ga wani irin nauyi daya danne mata zuciya, kallonta Husna tayi sai kuma tace"waike lafiya? Lamin din bezo bane?"hannu ta daura a kai sai lokacin ta samu hawaye suka zubo mata tace"na shiga ukku Husna,wallahi in dai ina ganin Lamin da yarinyar can zuciyata bugawa zatayi,wallahi sonta yakeyi babu komai a kwayar idonsa sai tsantsar soyayyarta,I can't any more zan iya haukacewa wallahi,na hakura da Jabeer amma bazan kuma rasa masoyi na biyu ba wallahi"...Dariya Husna ta saki tace"yanzu akan wata kike wannan tashin hankalin Ihsan?wallahi na raina wayonki da ajinki,me akayi akayi wata mace ,ni idan ni keson namiji ko uwarsa wallahi sai dai hange bare wata kanwarsa "wani kukan Ihsan ta kuma saki tana fadin"na lura baki da hankali Husna baki san mena gani bane,Lamin kuma ba irin duk mazan da kike tunani bane" Mom da Aunty Jamila dake tsaye a Kansu basu sani ba,Mom ta kyab'e baki ta karasa shigowa cikin dakin,da Gudu Ihsan ta karasa ta rungume Mom tana gunjin kuka tana fadin"wallahi Mom ni baxan iya zama da kishiya ba,mom zuciyata zafi takemun na tsani ganin yarinyar nan amma kullun tana tare da shi,yanzu haka fa da ita yazo mun ya barni tsaye a walakance Mom"Dagota Mom tayi daga jikinta cikin zafin nan nata tace "ke ni bansan sakarci da rashin wayau karma ki karasa Hassalani,ki kwantar da hankalinki yadda nake gidan Ubanki ni kadai ga Yayarki har mijinta ya rasu bata da kishiya to ba za'a fara a kanki ba Ihsan,ki nutsu kisan abunda kikeyi bana son kukan nan naki,yanzun nan zan kira uwarsa wallahi duk Wanda yaci tuwo da ni miya miya yasha"tana kaiwa nan ta zame jikinta ta fice a dakin.Aunty Jamila ce ta kamata ta zaunar da ita sai tabara takeyi da koke koke......parking yayi a in da ake parking luck ya sakawa motar Layan ta juyo da manya manyan idanuwanta tana dubansa cikin cool voice tace" Yaya".bece komai ba ya kama duka hannuwanta guda biyu cikin nasa cikin sanyin murya yace"Layan please I'm sorry for what happened earlier".tab'e baki Layan tayi sai kuma tace"I didn't complain Yaya,wani abun ya faru ne?".Dungure mata kai yayi sai ta saki dariya kuma,shagala yayi da kallonta har dariyar ta lafa mata sannan yace"u look beautiful, I mean, kimun alkawari Layan".ido ta waro tace"alkawari kuma Yaya?"gyada mata kai yayi yace"just at any cost kiyi backing dina Layan,just believe me goyon bayanki da yardarki shine abunda kawai nake bukata lil."jinjina kai tayi sai kuma tace"Yaya aikai bakayin abunda ba daidai ba,I trust you,insha Allah in Allah ya bani iko".back seat ta yunkura ta kwashi ledojinta ya bude mata lock din ta fita ,yakai musan 5 minutes zaune a motar ya jinginar da kanshi ya lumshe ido sai kuma ya bude ya fito.....Momy kam ta Gaza zaune ta gaza tsaye wani irin tashin hankali ke dawainiya da ita,tunda ya shigo da mota a gidan take jiran fitowarsa duk da tasan abunda Hajiya Sha'awa ta fada mata wai Lamin nasan Layan tasan bamai yiwuwa bane har bayan ranta,ranta tafarfasa kawai yakeyi da kyar ta iya controlling kanta ta hana kanta fita waje tayi maganin Layan din ,tana ganin Lamin ya nufo part din su ta koma ta zauna a gefe bed tana cika tana batsewa.so silent ya iska parlon Momyn kai tsaye bedroom dinta ya bude yanayin daya ganta zaune yasa ya karasa ciki da sauri ko noticing Hydar dake shigowa parlon na beyi ba,kai tsaye gabanta ya karasa yace"Momy lafiya? Wani abun ya faru ne?".kwafa tayi tace"uban meyema be faru ba,wallahi wallahi Lamin na kusa maka baki ka lalace kowa ya huta,Lamin ni zaka walankata ka zubarmun a daraja a idon duniya? Ace ban isa da kai ba? Akan waccan y'ar iskan Layan? Yau sai dai ka zaba ko ni ko Fatima zanga idan ita ta haifarmun kai"...innalillahi wa inna ilaihir raju'un kawai Lamin ke maimaitawa be taba jin maganganun da suka masa nauyi ba a kai irin yau cikin shakewar murya yace"kiyi hakuri,kiyi hakuri Momy bani da kamarki duk duniya ,Momy na maki biyayya ne zan auri Ihsan badan type dina bace,Momy ina san Layan Momy ina Santa hakan kuma bawai yana nufin bijirewa umarninki bane,ki yafe mun bayan auren Ihsan zan auri Layan,Momy rayuwata zata rushe idan na rabu da it.....".."kayi mun shiru marar zuciya da Sanin ciwan kai, babu Wanda ya isa Lamin ko bayan raina ka auri jinin Fatima sai tsinuwata ta bika ,har abada bani ba jinin Fatima ".turo kofar dakin Hydar yayi idanuwansa jajir yace" you can't say this Momy ,kin yarda ki tarwatsa rayuwar danki akan wani dalili da kiyayya marar amfani,Momy you can't do this to him wallahi in dai harke kika haifesa ,aduk cikinmu wa yake maki abunda yake maki Yaya Lamin ne cancanci haka gareki ba".Abba ne ya katsesa da fadin"tayi masa haka mana saboda cikar burinta da muradinta mana Aliyu".gaban Momy sai da ya fadi sosai amma ta dake tana girgiza kafa jin muryar Abba kamar daga sama,kallonsa ya mayar kanta yace"yace sai dai kiga lalacewa a wani wurin Badiyya amma ba akan son dina ba,ni na sani wannan auren ke kika kullasa amma ina so ni sani idan yanzu Lamin ya canza ra'ayi babu Wanda ya isa ya aura masa yarinyar da baya so..let me make this clear to you bancin na yanke hukunci akan Layan da a yau zan daura aurenta da Lamin kina tsine masa kuma kema a bakin naki auren,kullun girma kikeyi amma kina cin kasa sai yaushe zaki san ciwan kanki ,to ina tabbatar maki albarkacin yaranki kike ci da yanzu nayi maganinki"kuka Momy ta fashe dashi tana cewa"dama ni kullun cikin laifi nike ,ka tsaya kana walakanta ni gaban yarana".da sauri Lamin ya karasa gabanta yana fadin"kiyi hakuri Momy insha Allah hakan ba zata sake faruwa,kiyi hakuri"..."ki kallah da idonki amma wannan yaron shi zuciyarki keson lalatawa kinji kunya Badiyya"yana kaiwa nan ya fice,Hydar ya bisa a baya......"kwanciyar me kike mun a nan Laya? Sharafa nakeyi ,yau naga lukutar masifa ni Maryama".tura baki Layan tayi tace"ke Annien nan sai mutun na tunaninsa kizo ki tsorata shi,shara da tsakar daren nan,nifa nan cite ciye zanyi abuna ".kwalo ido Annie tayi sai kuma ta fizgi ledan dake gefan Layan ta duba kwalo ido tayi ganin gasheshen kaza dasu chocolate kala kala sai ice-cream,kanne ido tayi tace"gidan ubanwa kika samu? Badai fita kikayi ba Laya,yau na shiga ukku na taba ganin biki saura kwanaki ana gantali a titi?". Murtuke Fuska Layan tayi tace"to ai Yayan ne ya siyo mun,gidan amaryarsa ya kaini,ni za'a daurawa aure da zaki ce kada na fita ikon Allah". Tuna katobarar da take son yi tayi sai kawai ta saki murmushi ta bude ledan ta yagi gasashiyar kazar ta saka a baki tace"yaro man kaza yaro yaro ne" sai kuma ta zauna a kujera tana b'are kazar tare da cewa"tashi ki dauki kasanki kada ma kice da cuta a lamurrana,ni kam nafi son komai gaskiya da daskiya".
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
28
Yau ya kama bikin sora kwana biyar cif,A hankali ya fito daga cikin motar da Hydar ya daukosa daga Airport, sanye yake cikin complete uniform dinsa kaki ,sosai kakin ya masa kyau ga wani irin haske da fuskarsa ke kuma sakarwa sai dai ya dan fada kad'an kasancewar ayyukan da suka saka shi gaba,k'atuwar Jakkan goyonshi Hydar ya dauko yana kuma masa sannu da zuwa ga kuma Faruk da Jafar da suka karaso suma, jinjina kai kawai yake yi ta haka ya amsa gaisuwarsu ya taka zara-zaran k'afufuwansa yana tafiyar nan tasa ta zaratan mazaje ,part din Annie ya kallah sai dai sam baya son fara shiga wurinta dan gajiyar daya ibo hutawa kawai yake son yi,kai tsaye part din Umma ya wuce,da sallama a bakinsa ya tura main entrance na part din ya shiga in ba kana kusa dashi sosai ba ba yarda za'ayi kaji,babu kowa a parlon sai k'afar Ac da wa'azi dake tashi a sunna TV Wanda plasma TVn data kusa mamaye bangon d'akin take fitar da sauti babu abunda parlon yake fitarwa sai kamshi mai tsananin dadi Wanda lokaci daya ya saka shi lumshe manya manyan idanuwansa da suka dan rage girma .da gudu ta karasa zuba turaren wutan a borner data jona tana yaryarfe hannu tare da kiran sunan Umma tana turo baki cikin cool voice dinta da baya fita sosai kasancewar muran da take fama da ita kwana biyu,Baya baya ta soma yi with out her notice tayi ta zame a tayil tayi baya zata fad'i sosai ta runtse idanuwanta har hawaye ya kawo a idon tana tunanin ta ina zata fara jin radadin azaban zafin in da zata bugu.sai jinta tayi ta fad'a jikin mutun a duk tunaninta Yaya Lamin ne sai dai jin kamshin dadden turarensa Wanda bata iya mantawa ya kaiwa hancinta ziyara cikin hikima ta kuma saka hannuwanta ta mak'alk'ale shi,a Daidai nan kuma Umma ta fito daga kitchen rike da plates da spoons zata ajiye a dining saurin dauke idonta tayi ta koma kitchen da sauri bata ma son su ganta.Zaro ido Jabeer yayi yasa hannu ya kwace gaban rigarsa data rike,tuni zuciyarsa ta fara azalzalarsa ji yakeyi kamar an jona masa shocking iya karfinsa ya goce daga jikinta ya saketa akan tile ,wani siririyan kara ta saki lokacin data saka hannunta ta fad'a a kanshi tare da fadin"Yaya hannuna ya kare,wayyo Allah Ammi wayyo Allah Anniena".ta kare zancen idanuwansa suna ciccikowa da hawaye suna safka a fuskarta.ko kallonta beyi ba ya wuce cikin parlon yana jin zaman parlon ma gaba daya yana neman gaggararsa dan tsab zai karyatan da gaske sai ta samu kiranshi da wani Yaya can data kwallafawa bakinta,tsaki ya saki ya karasa kitchen in da yake jin motsi fuskarsa a dan yake yace"Umma"juyowa Umma tayi cikin da farin cikin ganin yaron nata tace"oyoyo my son sannu da zuwa".murmushi ya dan saki ya karaso tare da kama Hannun Umman ya durkusa yace"Ummana ina wuni,na same ki lafiya?".gashin kansa ta tsafa da yake nan a gyare tas sai tashin kamshi take tace"alhmdllh sannu da zuwa".gyad'a mata kai