Showing 51001 words to 54000 words out of 55893 words

Chapter 18 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt

ta dauki hankalinsa tace "tare da oga Ahmad muke ya shiga kitchen ne dauko ruwa"kafin ta karasa rufe bakinta Ahmad ya fito da wani Dan iskan Aski a kansa Yana tsotsar baki tare da fiddo harshe Yana fadin"how fa,Ashe baka gida ni kuma ban nema wayanka ba Dan so nake na baka surprise ".jinjina kai Jabeer yayi duk da yasan ada sam Ahmad ba haka yake ba amma a yanzu ya rasa meya shiga kansa har yayi sanadiyar sauyawar dabi'unsa gaba daya kikarin hadiye b'acin ransa yake tare da cewa"waya ce ka kawota gidana?".tage kafadunsa yayi alamar ko in kula yace"ita ta nuna tana so,ni kuma kasan bana son kwakwa,Husna kuma d'abi'arta ce ka sani to bana son damuwa shiyasa na kawota".lumshe idanuwansa yayi da matukar sauri ya budesu Yana karewa Ahmad kallo Wanda yake fadin"wow wow maa Sha Allah,kai man wacce kyakyawar beb ce a bayanka haka? Ko dai kaima ka soma d'anawa ne? Abeg ko saura ne ka barmun wallahi na kwadaitu kuma kasan sai na Dana ba komai zan Jira ragowarka"jikinsa wani irin tsuma ya soma yi har wani rawa rawa jikinsa keyi tsananin b'acin Rai na kuma hassalosa a matukar tsawace yake fadin"you idiot keep quiet,wane irin dabbanci ne wannan ka kwaso"ya kare maganar tare da cin k'walbar Ahmad da duka hannuwansa bibiyu Wanda besan lokacin da yakai gabansa ba.Layan dake tsaye tuni tsaiwar Jabeer tasa hantar cikinta kad'awa jikinta ya soma rawa da karfi ta kama hijab din dake jikinta ta rike da matukar karfi tana kokarin fasa maganganun Ahmad amma Sam ta kasa,Abu daya ke mata yawo a kwalwa kardai ace Yaya Jabeer mata yace bi? Kardai ace Yaya Jabeer mazinaci ne tayi saurin katse tunaninta da korar shaidan tana fadin "a'uzibillahi mishshaidanir raj'im"...bata San a fili tayi maganar ba sai da Jabeer ya tsura mata idanuwansa da suka soma canza launi a matukar tsawace yace"ubanme kika tsaya dauka a Nan? Wallahi idan na iskeki nan sai na karya wannan Yan iskan tsintsiyan kafafun naki da basu da amfani".da gudu ta kwasa tayi cikin dakinta tare da dannawa kofan key tana saune wani wahalallan ajiyar zuciya kafin daga bisani wani irin kuka Wanda bata San daga Ina ko meye dalilinsa ba ya kwace mata ta silale anan bakin kofar tana rairawa....Hannu Ahmad yasa ya kwace kwalwarsa yace"meye haka wai,daga magana sai ka hauni da zazzare Ido".hannu Jabeer ya kada a gaban fuskar Ahmad cikin zallar b'acin rai yace"ka sani wannan din da kakewa wani kallo matata ce,ta Sunna sadaki aka biya aka aura mun ita to ka dauke idanuwanka a kanta tun kan ayi mumunan Gani"...sakin baki Ahmad yayi sai kuma yace"to Ina ce baka son auren? Har yau kuma ka kasa karbarta a matsayin mata,to meye amfanin ajiyeta ka sawwake mata kabawa Mai rabo dama mana Aboki".Girgiza kai kawai Jabeer yakeyi baya so ayi b'atacciya ko wani abun Allah Wadai yasa ya kaiwa wani jadden table na glass dake daidai hanyar shigowa dining area duka da hannu tuni ya tarwatse flower vase dake gefe ya dauka ya kuma jifa dashi ita ta tarwatse hannuwansa ya Saka cikin gyararriyar sumarsa a matukar hassale yace"wallahi wallahil Azeem Ahmad zan iya illataka cikin gidan nan,ko na maka abunda har abada ba zaka mance wanene Jabeer ba,kazo ka kwashi wannan tsiyar kayan tarkacen naka kubar gidan nan tun Ina ganin sauran kima da darajarka a idona ,ko da bana son Layan ta haramta ga kowanne da namiji matsawar ni Jabeer Ina numfashi,kuma ita din dolena ce,dawainiyata ce kanwata ce matata ce jini na ce,hijabin aurena Yana lullube a kanta giyoyina ukku sun dade da zama garkuwa a rayuwarta ka fita tun kafin na canza zuciyata ayi b'atacciya nayi maka alkawarin ka Kara minti ukku a gidan nan,sai dai a fitar da kai amma badai ka sake amfanuwar kafafuwanka ba".jinjina kai Ahmad yayi tare da cewa"relax Aboki,yau har anyi macen da zata shiga tsakaninmu? Mecece mace har da zata Saka ka wulakanta ni haka,babu komai amma duka zakayi nadamar abubuwan daka fada lokacin da basu da amfani"Yana zuwa Nan ya Kalli Husna tare da cewa"beb let's go "be Jira cewarta ba yayi gaba abunsa.da gudu gudu ta kwashi kayanta ta mara masa baya Dan dama tun kallon Jabeer na farko komai a karfin hali take yinsa....Jabeer Kam kujera ya dafe dake dining din da k'yar ya zauna kansa na wata irin sarawa lokaci daya da k'yar ya dauki cup daya Gani Ahmad din na zuba lemo Mai sanyi a ciki ya soma kwankwada,sai da ya shanye tas sannan yayi wurgi da cup din ya dafe kansa da hannuwansa duk biyun Yana sauke ajiyar zuciya..


*RUHIN JIKI*


_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*___________________________________*




*JORDERH MAJIDADI*






41


Cikin shiga ta alfarma Hajiya sha'awan ke safkowa daga matakalar benan har ta karaso cikin babban parlon nata cike da farin ciki tace"a'a Hajja Badiyya Ashe kece,shine zasu barki a nan ba'a karasa da ke bedroom ,kinsan duk sabbin masu aiki ne a gidan".itama Momyn murmushi tayi tare da cewa"naga bansan yarinyar data sauke ni a nan din ba ai"Sam Hajiya sha'awa sai ta fasa zama tace"muje daga ciki,Dan naga alamar bakinki da motsi Hajiyata"Saman suka koma cikin makeken bedroom din Hajiya Sha'awa sai ka kallah tsayawa fadan irin kyansa da abunda aka jere a ciki bata lokaci ne dukiya dai tayi kuka harta gaji a gefan wasu matsiyatan sofas dake cikin dakin suka zauna kafin kace me an cika gaban Momy da kayan motsa baki,ruwa Mai sanyi kawai tasha sannan ta sauke ajiyar zuciya.cikin tattara hankali Hajiya Sha'awa wato mahaifiyar Ihsan tace"yau kuma meke damunki? Ina ga kin gama cikar burinki tunda dai wannan yarinya bata auri lamin ba".wani kallo Momy tawa kawar tata kafin tace"nikan Ina zan cika buri bayan Maryam da abunda ta Haifa suna shakar munfashi cikin walwala da Jin Dadi? Nifa wallahi bana Jin ma Aunty Amarya kishiyata akan yarda nake Jin kishin Maryam da Fatima sune duk ummul aba'isin duk shiga wani kunci nawa,kin ha kuwa bazan taba bari masu hankalin ya kwanta ba,so nake wannan auren da suke tutiya suke ganin sun kulla ya zamar masu ciwan Ido,ya zamar masu bala'in da zai kawo karshen su,Kinga sai suje su karata da iskancinsu dama wannan yaron Mai zubin maguzawa ba son auren yake ba har yanzu,duk da naga yarinyar ta fige ba kwanciyar hankali a tattare da ita hakan bai ishe ni ba wallahi Sha'awa".murmushi sosai Hajiya Sha'awa ta saki Mai ma'anoni da yawa tare da cewa"duk farrakun da kika masu bai isa ba kenan? Ni har yau na kasa ganin yarinyar nan dan na dade da ganin ma tawa Autata Ihsan tsaye a Ido,kuma itama nasan tabbas da nata Shirin ba zata zauna ba,to ko wajen mutumin nan zamu koma?".girgiza kai Momy tayi tare da cewa "wannan aikin kai da kai ne bana bukatar malami a ciki sukam sun gama nasu,Amma tabbas bazan taba zuba idanuwa ba har sai duniya ta gama yiwa wad'an nan maciya amanar juyin waina ta gama masu daurin huhun goro,zan San abun yi".jinjina kai Hajiya Sha'awa tayi taci gaba da cewa"tabbas na sanki ba zaki zama sakarya a lamurranki ba amma Ina mai kara jaddada maki ki Nemo kudi kizo ki rufe bakin waccan tsohuwar da gidanku kuma gaskiya aiki mijin nan naki na bukatar service Bangea alamar abubuwan na tafiya kamar a waccan shekarun ba".tsuka Momy Badiyya taje tace"to Ina zasu tafi daidai wannan tsohuwa da kike Gani tsaye take akan y'ay'anta da kuma wannan shaidanun jikokin nata,bata Jin kowa a Rai kamar yarda take jinsu,Kara ma Hydar shima na hannun damanta ne tunda bakin hali Babu irin uban Wanda bai iya ba,Allah da ba'a gida na haifesa ba tsab zan ce canza mun shi akayi,Ina nan Ina zuba Ido da Jin ta Ina zai ballo tashi Sabon rikicin Dan na fara Jin yarinyar Ummi Fatima kanwar uban Jabeer Asma'u take ko ubanwa wai ita yake nema,zanga ta in da zai kunce mun zani a kasuwa shima".Rike haba Hajiya Sha'awa tayi tare da girgiza kai cike da takaici tace"to gaskiya lamari ya karasa lalacewa wai yaushe Rukayya har kikai sanyin da lamurra suka gama kwabe maki haka? Gaskiya da sakal,in m kudin me baki dasu ni zan bada wannan cin fuska har Ina".....Tagumin dake fuskarta ta cire tare da kuma Saka hannu ta yaye uban blanket din da Lamin ya rufe jikinsa har kai,Babu abunda yake yi sai rawar sanyi,yau kwana hud'u kenan Yana kwance a haka kuma ya hana a sanarwa kowa kuma yaki zuwa asibitin, kallo d'aya zaka wa Ihsan kasan tsananin damuwa da tashin hankalin ciwan mijin nata sun gama fita da ita a hayyacinta,ko Mai baya iya ci komai yaci sai ya amarya hawayen dake idanuwanta ta share tare da cewa "wallahi ni dai na gaji Baby,bazan zauna ciwo ya Kashe mun kai ba,kaki zuwa asibiti yanzu nan kuwa zan kira Mommy ko kuma ka tashi mu tafi can gidan kawai asan nayi,Dan ba zamu Kara kwana a haka ba .sake lumshe idanuwa Lamin yayi Yana Jin karadin Ihsan din har cikin tsakiyar kansa sai dai bai ce komai ba,uban dukan gidan da akeyi yasa Ihsan zabura da sauri tace fadin"waye kuma wannan,daga Ina?"Jin ba za'a daina dukan ba yasa ta Kalli agogo ko 8 na safe bai karasa ba cike da masifa da b'acin Rai kuma ta fice fuuuu zuwa kasan taga uban waye ke mata wannan dukan....Annie dake waje ta kuma takarkarewa zata gabzawa kofar duka aka bude da karfi a irin fusacen nan,gwalo idanuwa Annie tayi tana karewa Ihsan kallo daga ita sai wata yar fingilar sleeping dress wacce ko gwaiwa bata sauka ba,sai kuma ta washe baki tace"Kisha iskanki hankali kwance ai ana zuba zafi,nima da shimi nake wuni Ina Shan iska".Basma dake bayan Annie rike da katuwar kula ta boye dariyar da takeyi.Annie bata ko kulata ba ta rab'a ta gefan Ihsan ta shige cikin parlon tare da cewa"wannan yaro Lamin na biyo,tunda nake bai taba mun haka ba gaskiya,Danshi duk yafi yayan Ahmadu hankali da biyayya Amma na jishi shiru kamar an Aiki bawa garinsu yasa na biyo sahu naji ko kece kika hanasa fita ko kuma wani abun aka masa a gidan uban nasa,Dan Sam ba zan ragawa ko ubanwa keda hannu na hana jikana zuwa gida ba,Sam ba haka Lamin yake ba"ta kare zancen tana zama a daya daga cikin parlon.duk da Ihsan taji haushin zuwan sassafen da Annien tayi masu sai dai ta wani bangaren taji Dadi Dan tasan zata taimaka a ciwan Lamin,wannan ciwo da ita ta kasa gane kansa, murmushin yake Ihsan din ta saki tace"bari na canza yanzu zan dawo Hajiya"sai lokacin Annie taga Basma tsaye a gefen kujera,tsuke fuska Annie tayi tace"kufa yayan Amadu matsalarku kenan Sam Baku San Ina ke maku ciwo ba,ki zo gidan Lamin Amma ki rabe kamar wata bakuwa ubanwa ya isa ya hanaki yin yadda kikaga dama gidan Yayanku? To ni gulma ke bani so,in kuma haka wannan kodaddiyar uwar taki ta turoki kimun to maza yanzu sai in Maida mata ke,danni wallahi Laya ta fiye mun kowa a gidan nan,mu kashe mu rufe Babu Wanda yasan me muke ciki,kai Amadu dai ya haifawa kansa".tsuke fuska Basma tayi ta dawo kusa da Annie ta zauna.Ihsan Kam sama ta wuce ta shiga dakinta a gurguje ta watsa ruwa ta canza kayan jikinta zuwa atamfa dogon riga ba laifi wannan ta Dan saki bata kamata ba,kallabin ta daura ta fito zuwa dakin da tabar Lamin,Yana nan a yarda ta barsa karasawa tayi kusa da shi hannu ta daura a goshin shi still taji akwai zafi sai kuma tace masa"Grandma tazo,zaka iya saukowa ?"sai a lokacin ya bude idanuwansa Wanda suka gama sauya launi gaba daya suka kankance ya zuba su akan Ihsan sannan ya fara kokarin mikewa,jallabiya ya Saka ba tare da yace komai ba ya nufi kofa Yana dan Jin Jiri....wani irin kwalalo idanuwan Annie tayi a matukar tsorace da kuma firgice ta furta"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Laminu Kaine?"wani iri fari da yayi ga tsananin rama sai kace Wanda ake Iba ,shidai bai ce komai ba ya karaso cikin parlon ya zauna Yana kallon Annien dake ta faman tafa hannu cike da al'ajabi


*RUHIN JIKI*


_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*___________________________________*




*JORDERH MAJIDADI*




42




Cikin sanyin da mutuwar jiki ta mike daga jikin kofar kai tsaye bathroom ta wuce ta yi wanka tare da dauro alwala tayi sallan isha'i dake kanta ta dade zaune a sallayan kafin a hankali ta mike danji takeyi gaba daya kirjinta na cunkushewa kamar numfashinta na son daukewa lotion dinta ta shafa da turare sannan ta samu rigan bacci marar nauyi silik white colour p kawai ta Saka ta zura rigar a daddafe ta isa a bed din ta kwanta tana sauke numfashi tare da lumshe dara-daran idanuwanta Wanda suke hasko mata abunda ke faruwa a dazu ga tunanuka iri iri dake neman wargaza mata kwakwalwa ta shafe tsawon lokaci a haka tana tubka da warwara da tunanin wani b'igiri kuma wannan rayuwar zata kaita ? Menene kuma ke rubuce a shafin kaddarar nata? Abu daya dai ta sani duk tsawon zama da tsawon lokaci ba zata iya daina soyayyar Jabeer ba,wata Kila sai ranar da ruhi zaiyi ban kwana da gangar jikinsa,lokacin da ko wacce gaba a jikinta zata daina aiki ,tabbas idan soyayyar Jabeer zata iya kasancewa cikin zanen kaddarori to tabbas zata ce ta hadu da tata kaddarar mai matukar wahalar cinyewa sai dai tana fatan kada ta gaza ko samun rauni a wannan tafiyar.Hannu tasa tare da shafo hawayen dake gangarowa a gefan idanuwanta sai kuma ta tashi zaune da sauri Jin an turo kofar dakinta,wani irin luguden duka zuciyarta keyi kamar zata fasa kirjinta ta fito dan tsananin tsabar tsoro da k'yar ta hadiye yawu tana niyar kwara ihu ya kunna wutan d'akin tuni haske ya gauraye ko Ina ,ganin Jabeer dake da kofa ya lumshe idanuwansa ya Sanya tsoronta dan raguwa kafin cikin mutuwar jiki tace"Yaya kana son wani abu ne?"ganin beda niyar ansata yasa itama yin shiru tana karewa yanayinsa kallo,sai dai bata ce komai ta dukar da kanta kasa.Cikin tangadi da tunzurawan zuciya ya karasa gefen bed din ya zauna Yana dan cicije lip's tunda yake yasan Yana kasancewa a yanayi irin haka lokuta daban daban to amma na wannan lokacin karara yaga kasawarshi ga wani irin juyi da yake ji kamar Wanda ya dirka kayan maye,a hankali ya dafe kansa ya kwanta a gadon Yana kokarin hana kansa abunda ke Shirin faruwa,wani irin tsikararsw da mararsa tayi yasa ya birkito da Layan gaba daya ta rikoto akan jikinsa ya kuma kankameta kamar Wanda za'a kwacewa,wani irin yamutsata yakeyi kamar zata guje masa,da aika mata da salo kala -kala masu wuyar fassaruwa da b'acewa a zuci,zaro manyan manyan idanuwanta tayi Wanda harsun tara ruwan hawaye Jin irin sumbar da yake aika mata dasu ta ko wanne gaba na jikinta tana kuma sauke numfashin wahala dan rikon dayayi mata yafi karfin kwarin k'ashinta,bata gama tsurewa ba sai da ya lalubi bakinta dib kakejin ta sai faman raba Ido,daga nan kuma wasan ya canza daga ita har shi basu Kara sanin in da kansu yake ba......Can wurin 3 na dare ya soma bude idanuwansa da dafe kai Wanda yake Jin ya masa nauyi amma kuma yau din sai ya kasance Yana jinsa Saka yau ,a hankali komai daya faru ya soma dawo masa a kwakwalwa kamar bitar karatun safe da matukar karfi ya mike Yana ambaton innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,hasbunallahu wani'imal wakeel,ya kare tare da waro idanuwansa a deep light din bedside lamp dake kunne sosai kansa ya daure da ganin in da yake da kuma irin katobarar daya aikata,kallon cute long chocolate baby face dinta yake yi ko Ina duk jirwayen hawayen daya gama bushewa gata can a gefen cikin yanayi na Suma.A nitse ya mike ya shiga toilet ya gyara jikinsa yayi wanka da kyau ya gargasa jikinsa danji yake yi wani zazzafan zazzabi na bin ko wacce gaba ta jikinsa dan harya fara rawar sanyi da k'yar ya kuma hada wani ruwan masu dumi yazo ya dauketa kamar ya dauki yar baby saboda rashin nauyi kai tsaye cikin ruwan ya tsundumata,wani wahalallan Kara ta saki da muryarta data gama disashewa dan tsabar kuma,zafin da taji shi ya farfado da ita daga suman data yi,kankame Jabeer din tayi tana sakin kuka dason mikewa cikin dakiya ya kuma dannata a ruwan fuska a daure da Jin duk ya gama muzanta yace"keep quiet,Allah yasa naga kin tashi a ruwan nan,kiga yarda zan b'allaki har a rasa me Dori"..Layan Kam bata ma fahimtar abunda yake yi kukanta kawai takeyi sai kuma tsananin tsoron Jabeer din daya gama lullubeta Dan tiryan tiryan wahalar data kwasa a hannunsa ke dawo mata gaba daya ta idasa firgicewa.ko kallonta beyi ba so ukku Yana canza mata ruwa sannan ya taimaka mata ta fito,wani doguwan rigan ya bata ta canza ya bata dugs sannan ya zaunar da ita a soma ya gyara gadon tas ya canza bedsheet sannan ta kwanta ya lullubeta yaje ya kwanke zanin Dan duk zazzabin da yakeji bazai iya barin zanin a haka ba,a daddafe ya karasa ya wuce d'akinsa ya kwanta sai dai ya nemi bacci ya rasa Yana ta kwance har akai Kiran asuba bai iya fita masallaci ba a nan yayi sallan sai kuma wani nauyayyen bacci ya daukesa............girgiza kafa kawai Annie keyi sai kuma cikin masifa tace"yau naga bala'i wacece wata BADIYYA da zata tsaida mutane har yau bata dawo daga gantalinta ba,jikan nawa zaku bari a walakance haka cikin cuta? Ni Sam ban ganewa wannan abun ba,Kara azo asan nayi tunda akai auren nan jikana ya birkice azo ayi zaman metin idan auren ne baya so wallahi wallahi ko sakan bazai Kara da wannan auren da aka rasa gabansa da bayansa ba wallahi".kallon kasan Ido kawai Ihsan kebin Annie da shi sai dai ganin Abba dasu Aunty Amarya yasa bata ce komai ba.numfashi Umma taja tace"kiyi hakuri Annie wannan ruwan daya kare tunda Ammi tace idan ya kare za'a Kaisa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login