Showing 48001 words to 51000 words out of 55893 words
Chapter 17 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt
murmushi kad'an yace"nama nefa kuma harna cinye".kuma daure fuska Ummi tayi tace"can kai ka sani,duk in da zaka nemo kaje ka biyata abunta yaro baka da aiki sai cin nama" kulan da Ummi ta basa a dole ya karba ya wuce gida baida niyar komawa wurin Annien ma gaba daya.
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
38
BAYAN WATA BIYAR
Kallonta kawai yake ji wani abu na tsarga masa rai kanta a duke cikin sanyin murya tace"Allah Ammi babu ruwansa,nice dai nace bana so naci gaba,Kara na ajiye shekarar in yaso next year sai in ci gaba"wani kallo Ammi ta jefa mata fuska daure tace"Amma ban taba sanin baki da hankali ba sai yau,me ke damunki Layan? To bari in fada maki ba'awa namiji haka in ma wani dadin baki ya maki kika yarda to kanki kika cuta kije ki canza shawara Dan bazan taba amincewa ki ajiye karatunki a daidai wannan lokacin ba"sannan ta mayar da kallonta kan Jabeer kallon tsab da tuhuma take binsa.ya wani zaro Ido alaman babu ruwansa sai kuma yayi kasa da kansa .ya Lula duniyar tunanin daya Sanya Layan cewa zata ajiye karatunta,shirye ta fito tsab cikin dogon riga baki ta yane kanta da mayafin ,lab coat ce a hannunta da katuwar school bag dinta sai laptop Wanda zuwan su Basma suka kawo mata jiya,sai fitar da wani sanyayyen kamshi takeyi,safkowa yakeyi daga stairs din da dan sauri da alamu fita yake son yi da kallo ya bita kafin yace"Ina zakije?"Dan waro manyan idanuwanta tayi tana karewa shigarta kallo sai kawai tace"Yaya makaranta mana mun kusa fara C.A kuma Allah ka duba aikin gidan tun asuba na Saka nose max Dina nayi ko Ina da kyau".kallon baki da hankali yayi mata tare da cewa"to sai ki zaba makaranta ko zaman gidan Jabeer danni bani ra'ayin wacce aka tursasani ta ansa sunan mata a gareni ta rika yawo a titi tana tallar jiki da gogayya da kartai wai sunan makaranta impossible".wasu irin hawaye ne masu zafi suka soma biyo kyakyawar bak'ar fuskarta ta lumshe Ido cikin kuka tace"Yaya Dan Allah,Ina son karatuna"...beko kulata ba tasan kuma idan zata kare rayuwarta a haka bazai taba cewa komin ba.jakarta ta dauka tayi ciki tana rushewa da wani matsanancin kuka Mai karya zuciya a nan tsakiyar dakin ta baje tana kuka tana kuma tunanin tsawon wata BIYAR da tayi a gidan kwata kwata babu abunda ya canza na zamantakewa a tsakaninsu kamar yarda yace yar aiki ce ita to har yanzu wannan sunan take ansawa ita ke gyaran ko Ina da duk wani aiki Wanda a yanzu har Mai gadi basu dashi duk tsawon dare ita zaiwa horn ta taso ta bude masa babu kalar aikin wahalan da bata yi ga wankin kayansa da guga data gama kwarewa girkinta ne kawai baya ci,sai kuma idan tayi laifi bazai taba Jira ba zata samu hukuncin kyakyawan Mari wani lokacin ma har fiye da haka,a yanzu nema taga ya daina dukanta sai dai tsabar tsawa da masifa ,wani murmushin takaici ta saki tare da cewa"har abada wahala ba zata taba sanyawa na gujeka ba Yaya Jabeer,har sai ranar da kai ka koreni da kanka ko wahalar ta zama silar rayuwata Amma soyayyarka Allah ne ya Sanya mun kuma zan jure duk wani yanayi domin na kasance tare da kai,na zaba zama da kai Yaya Jabeer n hakura da makaranta"...kallon Ammi yayi tare da dawowa duniyar tunanin daya Lula tace"Jabeer me yake damun Layan naga tayi wannan ramar haka?,bayan kullun kai da ita kalmarku daya everything is owk"...kasa yayi da kansa yace"Babu komai Ammi"tasan kome zatayi bazai Kara daga hakan ba cikin kakkausar murya tace"idan ma kana mata wani abunne kayi gaggawar sauyawa Dan wallahi idan na gane you will see the other side of me,Jabeer zakaga bacin ran da har abada baka taba sanin Ina dashi ba,so respect your wife kasan me kake yi"...bece komai ya tashi ya fita dan besan kuma mezai fadawa Ammi ba,shidai yasan babu wani abu da zai canza Layan daga kallon da yake mata,to bayan nan kuka besan me suke so yayi ba,a bangaren Annie yaci burki Yana Jin muryar Layan daketa tsandara kukan iskancin nata yanda yake fada shiru yayi Yana jin abunda Annie ke fada,cike da karadi take fadin"yau naga tashin hankali,Allah ya tsinewa bokon ,mecece wata bokon ?kardai maryam bakin ciki takewa Bukar ya samu ya aurar da ke,to duk Wanda ya sawa jikata Ido nidai bazance komai ba gashi ga Allah nan.yanzu kuma zanje naji me take nufi.tura baki gaba Layan tayi tace"ni dai na cewa nayi kije ba,kawai cewa nayi idan tazo kice nazan koma makarantar ba".Shikowar Jabeer ya katse mata sauran maganar,Layan Kam jikinta har rawa yake ta mike da fice da sauri daga parlon Annie,gwalo Ido Annie tayi tace"mezan Gani haka? Wanne mugun abun Kawa jikata ?shiyasa naga ta rame kamar kudin guziri"bece komai ba ya nemi wuri ya zauna Yana ci gaba da latsa wayàn shi.......part din su Muhibba ta nufa tun a parlo ta iske Ihsan zaune ta cab'a ado kamar wacce zata kar kasa,ga Momy Badiyya a gefanta sai washe baki takeyi ta cika mata gabanta da kuloli,Lamin Kam dake gefe kansa a kasa Yana aikin danna wa,kallon tsana Ihsan kewa Layan har bata son ganin yarinyar Sam,tun daga ranar farkon data ganta da Lamin ta kuma fahimci duk burinsa da farin cikinsa ya ta'allak'a ne akan yarinyar,Kara sautin karar gum din da take ci tayi,Layan Kam a hankali ta karaso cikin parlon cikin sanyi murya tace"Ina wuni Momy".gaba d'aya mommy ta juyo sai kuma ta tafa hannuwa tare da cewa"dama kin Saba gaishe ni ne da zaki zo kimun tsaye akai sai kace Mai cutar k'anzamau haka kika koma,a'ah to Allah ya rufa asiri"...cikin yatsine fuska ihsan tace"to Hajiya Ina tarbiya bare kuma a gaishe ki da ladabi,daga sama ma ba'a samota ba bare ayi kankanba".still Lamin yayi Yana karewa ihsan kallo sai kuma cikin kakkausar murya yace"mind you Ihsan kisan me kike fada,na dade da gargadinki akan duk wani abu daya shafi gidan nan,idan kuma kinki ji ba kyaki Gani ba"sakin baki mommy tayi sai kuma tace"tunda ga Rukayya an taba ko sallammme?"."to kya Kara fada mommy,Ina dalili nima yanzu ai na dade da zama ahalin gidan nan,abunda ya shafeka ai ya shafeni Lamin,Amma sai kaita yin wani abu kamar bakasan nice wacce igiyoyin aurenka ke akai ba".cewar Ihsan.layan Kam ko tsayawa ta karasa Jin zancensu bata yi ba ta wuce part din Aunty Amarya dan bata ma da lokacin Ihsan.....plate din gabansa ya ture alamun ya koshi kenan fuskarsa a sake yace to "Umma na koshi"jinjina kai tayi sannan tace to"madallah,ita Layan din bata maka girki a gidan ne".murmushi ya sakarwa Umman yace"tana yi Umma,kin dai san bana son wuce tayin abincinki ne,ita na rako ma wurin Ammi".kallonsa Umma tayi sai kuma tace "ince dai lafiya? Danni ko ganinta ma banyi ba".shiru yayi sai kuma yace"Ina fa zata shigo Umma,anata fama da ita wai sai ta ajiye school".sakin baki Umma tayi sai kuma tace"to Allah ya rufa asiri ya zaba abunda ke alkhairi,komai dai tayi ai kanta tawa, feature dinta zata duba tunda ba wani zata amfana ba,amma idan ta zaba hakan sai kowa ya Saka mata Ido tayi gaban kanta"jinjina kai yayi yace"to magana ta kare ai tunda har taje ta fadawa Annie".tab'e baki Umma tayi tace"taji dashi"ta tashi ta soma tattare kayan da Jabeer din yaci abinci dan ita har gobe bata masa kallon siriki tana nan tana masa kallon Jabeer dinta data raina tun baisan wanene shi ba.
RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
39
Cikin cool voice tayi sallama kamar wacce kwai ya fashewa a ciki haka ta tako tattausan carpet din dake malale a faffad'an parlo din nasu,bata ma San Daddynta ya dawo ba sai da ta d'aga kai taga ya tsura mata Ido,cikin sassarfa ta karaso in da yake a hankali ta silale ta zauna fuskarta kunshe da murmushi,sai dai Sam ba murmushin bai kayatar dashi ba,a kasan murmushin nata yake hango wata damuwa a kwance.gyara zaman shi yayi Yana ajiye jaridan hannunsa ya dawo da dukkan hankalinsa zuwa gareta yace"are you owk".samun kanta tayi da saurin d'aga kai bata yarda sun hada Ido ba tana boye hawayen dake kokarin zubowa a fuskarta,kallonta yake yi irin ramar da yaga tayi ,a hankali kuma yace"meke damunki Mamana?kina cin abinci kuwa?".Nan ma kai ta d'aga masa sannan a hankali tace"Daddyna lafiyana qlau,kwana biyu dai banji Dadi bane,amma Yaya ya duba ni".sosai yaji dadin abunda ta fad'a sai yace"kije kici abinci ki huta,idan zaku wuce Ummanki zata baki Sako,Naji kuma abinda Annie tace Allah yasa hakan shine Mafi alkhairi,be the best wife you can ne Daughter Allah ya maki albarka"...kanta a kasa take ansawa da Ameen tana kuma Jin tsananin son Daddyn nata Wanda bata da kamar shi duk duniya,cikin sanyi ta wuce dining a nan ta samu Umma itama dai kallon ta bita da shi ganin irin uban ramar da tayi sai dai bata ce komai tace"kije ki cire abayan,sai kizo ki dauki abincin,sakon Abbanki kuma na Saka maki a jakkanki da Jabeer ya kawo tun dazu"jinjina kai kawai tayi ta juya ,Umma tabi bayanta da kallo tausayin only child din ta na kamata da alama akwai damuwa a tattare da ita sai dai tasan idan zasu shekara tambaya ba zata taba fada ba,fatanta dai kawai Allah ya shiga lamurranta...lokacin data dawo dining din still tayi ganin Jabeer zaune a wurin Yana saving abinci Yana wa Umma magana,ganinta ya Sanya ya kashe mata idanuwa daya tare da cewa"karaso mana,tsaiwar na menene kuma?"ya kare maganar Yana langwabar da kai,Umma bata tanka ba dan tasan da Layan yake taci gaba da dauraye plate dake gabanta,runtse idanuwa da karfi Layan tayi tana Jin wani abu na taso mata,Inama inama,inama ace tsawon rayuwarsu Jabeer zai kasance a haka ba pretending a gaban iyayenta ba,da yasan yarda Allah ya jarabceta da tsananin soyayyarsa da duk bai aikata mata hakan ba,sai dai ba zata gushe ba tana rokon Allah ya karkato mata da hankalinsa,a hankali ta soma taka k'afarta izuwa dining din taja kujera ta zauna,cikin tattausan lafazi yace"ga abinci nan na zuba maki,kiyi ki cinye sai mu wuce gida is almost magrib".kai kawai ta gyada masa sai hawaye suka balle mata Wanda bata San daga Ina ba,wani irin daure fuska yayi ta kasan table din ya Sanya kafarsa dake cikin shoe ya take nata Yana jefa mata alamar gargadi da kwayar idanuwansa,idanuwa ta runtse tare da yarfa hannuwa tana Jin tsananin zafin takawan ta ratsata sai dai ba yarda ta iya,hannu bibbibiyu ta Saka tana dauke hawayen dake zubo mata cikin sanyin murya wacce ta dishe tace"kayi hakuri bansan sun zubo bane"sai a lokacin dayaga ta share hawayenta sannan ya daga mata k'afar......sai bayan sallahn magriba suka wuce gida sosai taji dadin kyautar da Daddyn ya bata kudi ne masu kauri duk da babu abunda zatayi dasu amma taji dadi.sai abunda Aunty Amarya ta bata magunguna ne na gyaran jiki murmushi tayi tana tuna me zatayi da wannan a gidan Jabeer zata iya cewa abinci ne kawai bata rasa ba a gidan Jabeer da duk wani abubuwan bukatar rayuwarta sai dai bayan nan bata da wani saurin Karin bayanin fada,abun yayi mata dadi lokacin da ya canza akalar motar tasa zuwa gidan Hajja,sosai hakan ya mata dadi har yaso bayyana a fuskarta,Hajja badai kirki ba mata Mai karamci da sanin ya kamata kowa nata,sosai take Jin dadin zama da matar dan dolema ka karu ka kuma kwashi darussan rayuwa.tun a mota ya mata kashedin salan taje ta rika masa sakarci da rashin wayanta data saba.kas tai da kanta karon farko maganar na mata ciwo a ranta,sai dai bata ce komai ba ta bude motar tabi bayansa kamar wacce kwai ya fashewa a ciki....Hajjan na kishingide Jamila Mai aikinta tana shafa mata man zafi a kafa kasancewar ciwon kafan da take dashi ya soma tashi kwana biyun nan,da madaukakin farin ciki take masu lale tare da cewa "ai na dauka maryama kin manta da ni,kullun sai dai Yayanki yace kina gaishe ni amma na kasa ganin kafafuwanki a gidan nan"Murmushi Layan ta saki wani sanyi na ratsata ta karasa ta karbi man zafin daga hannun Jamila da suke gaisawa ta duka tana fadin"Ashe zan iya mantawa da kaina Hajja,kwana biyu ban samu sararari bane shiyasa amma kullun kina makale a raina"sannan ta soma shafa mata man zafin a hankali yarda zata ji dadi,kafin tace"Ina wuni Hajjiya,mun sake ku lafiya,ya jiki jikin?"jinjina kai Hajja tayi kaunar yarinyar na sake ratsata tace"alhmdllh Maryama, alhmdllh,jiki Kam yanzu sai mu Saka tsare da ke nan zaki gane irin kafin dana samu"duka suka Saka Dariya banda shi ogan daya hakimce Yana latsa waya kamar Wanda akawa dole zuwa gidan.kallonta Hajja ta kuma yi sannan tace"maryama ajiye man nan haka kije kitchen ki haduwa Yayanku tuwo Yana nan dazun nan na tuka shi".da to ta ansa ta mike ta fice.a matukar mamakance Hajja ta kurawa Jabeer Ido cike da taraddadi tace"Muhammad Jabeer lafiya kuwa? Meya samu yar mutane haka? Wacce iriyar rama tayi haka?kardai kace mun har yau ka kasa rike amanar da kowa ke danka maka,kardai kace mun ka zama daya daga cikin masu cuzgunawa matansu idan dai ko haka ne Allah Yana kallonka ba kuma zai taba yafe maka ba Jabeer".warwas yaji shi duk wani abu daya ebo ya nema ya rasa rarraba idanuwa ya soma yi sai dai kanshi tsaye yace"ko kusa Hajja ban rageta da ci ko Sha ba ko sutuura,sai dai har yanzu na dauketa a matsayin matata na kasa isa wannan bigirin na kasa aminata da wannan Hajja,ni saboda Allah a raba ni da wannan dawainiyar haka"...dakuwa Hajja ta masa tace"karbi nan ungu naka nace,maras kunyar banza,har yau kai baka San gatan da Maryam ta maka ba? To Ina so ka sani har bayan raina Babu Wanda zai raba wannan auren JABEER in ma zaka dawo a hankalinka to Kara ka dawo,ka koyi zama da ita,kai kardai ka zama cikin butulun mutane Wanda basa mayar da alkhairi da alkhairi ko bayan ranmu na dauka jinin Sadiqqu da Fadima sunfi gaban hakan Jabeeru a wurinka,to ka tattara kafufunka kabar mun nan kada na sake ganinka har sai ka shirya tsakaninka da matarka ,idan kuma ka cutar da ita ka sani Allah subuhanahu wata'ala Yana kallonka kuma shi yasan irin hukuncin da zai maka"shigowar Layan yasha Hajja yin shiru ta kuma saki murmushi tace"Mika masa yaci ku tashi ku wuce,ki rike mijinki da kyau Maryam Allah yayi maku jagora ya jibanci lamurranki Allah ya maku albarka baki daya"da Ameen ta ansa ta Mika masa abincin a gabansa,duk yarda yake son abincin kasa ci yayi wasa yayi dashi kawai ya tashi yace su wuce gida.
RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
40
Tun a mota tunani kawai yake yi maganar Ammi da Hajja sai yawo suke masa a kwakwalwar kansa Sam ya rasa me zai aikata,har gobe kuma bai iya Jin zai karbi Layan matsayin matar aurensa in dai wannan dalilin daya hanasa sonta na ci gaba da wanzuwa a doron kasa,satar kallonta yayi yaga yarda ta lafe jikin kujeran motar tamkar wata marar Rai,kamar wacce take jiran kiris ta ruga a guje,ya sani tabbas shine silar gigita duniyarta zuwa wannan matakin bai San kuma zuwa wanne lokaci zata bar bigiren daya daurata ba,matukar tsoronsa take yi duk lokacin da ta kasance a tare da shi dalilin irin marin daya dakko Yana mata,Amma Sam tun tuni yayiwa kansa fada na daina dukanta duk yarda take matukar son shi amma ya zama abun gudu gareta,wani yawu Mai masifar d'aci ya hadiye Yana dubanta yarda ta kuma takurewa tana kallon hanya yarda kasan yau ne ta fara ganin titin,har suka karaso gida wannan tunanin bai bar zuciyarsa ba,motar Ahmad daya Gani a gidan ita ta tabbatar masa yana gidan kenan,Dan tun wancan satin da Yana wurin aiki yaso yazo ya shaida masa baya nan ya bari sai zuwa wani satin hakan tasa ya masa zuwan bazata bai ko sanar dashi zasu zo gidan ba....Yana tsayawa da motar cikin sanyin nan nata Wanda Jabeer bai taba gani ba ta bude motar ta sauke dogayen fararen kafufuwanta Wanda yanzu yanayin rayuwar da take ciki ya Kara Saka su wata sabuwar ramar motar ta rufe tabi bayansa kamar wacce bata son taka k'asa,Yana zuwa ya bude gidan suka shiga,tsaye yayi cak na wasu seconni b'acin Rai na kokarin mamaye sauran salamar daya soma samu da tarin matsalolin rayuwarsa Husna ce,Asma'u ce Gani yake kamar gizo yake yi ta kwabe mayafinta tana dining tana jera abinci yarda kasan gidanta ko gidan wani shakikinta,tana ganinsa ta wani kashe Ido tare da yauki na daukar hankali ta fara takowa cikin shigarta ta Riga da Wanda Wanda suka matukar d'ameta sai fitar da masifaffan kamshi take yi kanta Babu ko hula sai mayafin data ajiye ,k'afarta takalmi ne masu matukar tsini tana taku daidai,ta karaso cikin ainihin tsakiyar parlon.da karfi Layan ta runtse Ido tana ambatar innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,a'uzubikalmatillahi tammat min sharri ma kala'qa tana kokarin danne wani azabar wutar kishi dake kokarin taso mata,wani dunkulen abu takeji yazo ya tare mata makoshi gaba d'aya...saurin bude idanuwanta da har sun soma sauya kala tayi tana kure Husna da manya manyan idanuwanta tana kare mata kallo da son ganin in da abun zai tsaya.dab da Jabeer ta tsaya fuskarta kunshe da murmushi tace"barka da dawowa my man,tun dazu muke tsumayenku amma shiru,sai dai kasan bazan taba gajiya da jiranka ba,da kuma Ina so in ga kanwata"wani b'acin rai ke kai kawo a kwalwarsa kokarin cooling temfer dinsa yake yi da duk addu'ar da tazo bakinsa idan ba haka ba kusa yasan tsab zai iya illata yarinyar mutane Wanda kowa ba zaiso yaga abunda zaije ya dawo ba.fuska a daure cikin kausasshiyar murya yace"keda waye?" Farr ta kuma yi da idonta da suke can ciki ita a dole