Showing 42001 words to 45000 words out of 55893 words
Chapter 15 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt
General wato mijin Ummi shima da mutanan sa ga kuma manyansa na wurin aiki da abokanan aikinsa,wara idanuwa yayi sosai ganin Ahmad,Ahmad babban abokinsa ne kut da kut wani lokacin ko bacci baya rabasu course ne ya fita dashi ko jiya sunyi waya amma sam bai sanar masa yana dawowa ba,sallah aka fara gabatarwa kasancewar kowa yasan da daurin auren yasa mutane zama.anan akayi shela aka soma daura aure..kamar statue haka Jabeer ya tsaya Yana sauraren sunan da ake fada ,tunani yayi ko mai shelar beji daidai ba,sai kuma ya Kara Jin sunayen har cikin tsakiyar kansa.An daura auren JABEER ABUBAKAR SADEEQ da amaryarsa MARYAM ABUBAKAR SADEEQ (LAYAN) sai LAMIN AHMAD tare da amaryarsa IHSAN MUH'D akan sadaki naira dubu dari bibiyu lakadan ba ajalan ba,shi da Lamin bansan waye yafi shiga rudu ba a wannan lakacin,tsoron Lamin dama Jabeer ne mijin da Abba ya zab'awa Layan ya akai sukayi wannan aikin bayan sun san tashin hankalin dake baibaye da hakan Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un kawai ya samu bakinsa da maimaitawa Yana d'aga hannu da k'yar Yana ansa gaisuwar masu yi masa Allah yasa alkhairi Yana yaken dole...Jabeer Kam wani butum butumi ya zama ko kad'an ya kasa motsawa daga in da yake,shi kansa bazai iya fada maka a wacce duniyar yake ba,Abba ne ya karaso ya Saka duka hannuwansa duk biyun ya dafa kafadunsa da suka gama jikewa da zufa jagab ya d'agasa Yana sakin murmushi tare da fadin "yau burina ya cika Jabeer,Allah yasa alkhairi ya Baku zaman lafiya karka damu kanka zan maka bayanin komai kuma insha Allah watan wata rana Jabeer zakayi alfahari da wannan auren za kuma ka gode mun ko bayan ba raina "kallon bakin Abba kawai yakeyi amma sam kunnuwansa duk irin hasashen da yake yowa da kuma karfin ji da Allah ya masa ya kasa jiyo ko fahimtar abunda Abban ke fada kallonsa kawai yake yi Yana Jin wani irin mumunan tashin hankalin dake rubtowa a bisa kansa yarda kasan am dauko duka duniya an daura masa a kai haka yake Jin kwatankwacin nauyin da kansa da kuma idanuwansa dake neman rufesa sukai masa,a hankali ya tattare busashen yawun da yayi saura a bakinsa ya had'a tare da lasan tattausan lab'ab'ansa da suka yakune suka bushe a cikin sakanni sannan ya lumshe Dara daran idanuwansa Wanda suka sauya launi zuwa launin ja suka kuma Kara girma alamar mamallakinsu yayi nisa da duk wata natsuwa daga gangar jikinsa da ruhinsa,Abba ya damka hannunsa ana Lamin sannan ya wuce cikin jama'arsa .shidai Jabeer tun daga wannan lokacin bai furta ko kallama d'aya ba,haka zalika baya fahimtar komai ake cewa,Jin kansa na neman tarwatsewa yasa ya silale yayi cikin gida zuciyarsa na lugude da fama da madaukakin tashin hankalin da bai taba shiga ba tsawon rayuwarsa....sakin k'walbar turaren hannunta tayi take ta fad'i k'asa ta tarwatse ta fashe turaren ciki kuma ya malale,da kallo kawai take bin su Muhibba da ko wanne a cikinsu yayi cirko cirko,cikin dakusashen murya tace"kunji Mai kunne na ya jiyo man kuwa Basma?"Layan ta kare tambayar tana tsaresu da manya manyan fararen idanuwanta Wanda kwallin Kajol ya Kara kawatasu da addo na daukar hankali .jinjina kai dukkansu y'an matan dake d'akin suka yi kafin Asma'u tace"an daura aurenki ne da Yaya Jabeer yau burinki ya cika ".wara idanuwa tayi kamar Mai son Karin bayani sai kuma wasu sanyayyen hawaye suka soma gangarowa akan kyakyawar fuskarta,dandanan taji wani sanyi na ratsata,irin sanyin data dade tana farauta da nema,kamar an zare k'aya a abu haka taji wani malolon kullutu daya dade dayi mata wurin zama a zuciya Yana dargajewa tuni ta nemesa ta rasa,ba shiri ta tafi sujudur shukur ,sijjadan godiya ga Allah buwayi gagara misali Mai cire rayayye a matacce matacce a rayayye,a sujadan kuka ya kwace mata,cike da kallon tausayu duk suke binta kafin Aminata da Muhibba suka dagota suka zaunar da ita a gefen bed.....Annie Kam Kabbara kawai take saki ta rasa in da zata Saka ranta,ta rasa meke gareta yau ta bayar raji Dadi,kukan farin ciki ta saki tare da cewa"ko yau Allah ya karbi raina ni maryama burina ya cika,Allah kai ka kaddara auren Nan,Banga ubanda ya isa ya hanasa wanzuwa ba,da Yan naki da Yan naso duka dai Allah yafi karfinku sai kowa ya rungumi kaddara yau dai Mai ciwon cuta da bak'ar kala ta samu mijin kera sa'a Ina Badiyya tayi kukan Jin kunya? Taki Allah ya so yau ga ranar mayar da murtani"duk hali irin na Annie kyauta ta dinga yi abunta har zannuwan sakawanta sai da ta bayar ta kuma bude kofar d'akinta baja-baja bata tsegumi wa kowa....."Ashe auren kuma biyu aka daura bana Lamin kad'ai bane"Hajiya Nana ta tambaya.tabe baki Momy Badiyya tayi wacce ta gama haduwa cikin tsadaden leshinta tace"auren cushe ba,to ko angon da amaryar yanzu suka San da daurin auren kamar yarda kuma kuka samu labari,ni dai can dasu gada tunda sauran cuta bata mak'alewa y'ay'ana ba"rike baki Hajiya Nana tayi sai kuma tace"to godai a zamanin mu ba'ayu haka ba,har Yan atamfofin nan da kayan shafa ake kawowa na fitar biki".Dariya Momy Badiyya ta saki tace"to namu auren dai daga maggi sai kuka,aini zanga yarda wannan drama zata kaya a gidan nan wallahi ".ko karasa rufe baki batayi ba khalifa ya shigo da gudu Yana fadin "Aunty Amarya,Aunty Amarya kuzo Kuga kayan Yaya Layan akwatina kawai ake safkewa daga manyan motoci wai kayan lefenta ne na aurenta da Yaya Jabeer"sak Mommy ta juya tana bin bayan khalifa da kallo sai ya zama kamar magana yake jefa mata ji tayi kamar wani Mayen karfe na janta har tana tuntube tayi waje cikin gate din gidan.mota hud'u ce,Ummi ce ta fito da few of her friends Wanda daka gansu kasan sunci sunsha sun kuma tada kai da nera dan tayi kuka a jikinsu boxes ne jere a tsakiyar tankamemen gate din gidan har 24 set biyu sai manya manyan bags guda biyu daka kallesu kasan tsadaddune ,mutane keta dauka ana shiga dasu part din Annie Dan anan ta tubure a kawo mata kada a kai wani wuri ayi sata,a Nan kuma tasa a tsakar gida a bude lokaci daya kowa ya Gani Dan tace rufesu zatayi a daki ba dalili a samu masu Yan hali a kwashewa Laya kaya.kowa sai dai yace Masha Allah a kayan ko Gold's kala hud'u ne a ciki Dandanan Annie ta bawa Ammi su ta adana kowa sai da ya jinjina irin kokarin su Ummi Babu Wanda ya taba tunanin Rabin haka Layan zata samu daga garesu a yanayin yarda auren yazo kai ko falle ba Wanda yayi tunanin za'a kawo mata.da k'yar Mommy Badiyya ta taka tabar in da take lab'e Dan kin fitowa tayi tasan tsab Annie zata fara yab'a mata magana da kuma habaicin data Saba,in kuma ta gaji kai tsaye ta kama sunanta.
*Inga ruwan comments sai muci gaba da tafiya yarda aka Saba,idan naji shiru kuma zakuji shiru ,ahtou Dan ba zaku barni a gantale ba*
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
34
"Kiyi sauri ki shirya ki fito Abban suna parlo suna jiranki"Ammi ta fad'a tana mikawa Layan babban milk mayafinta wacce lokaci d'aya jikinta yai sanyi ganin da gaske yau kuma barin gidan zata yi,bata tab'a tunanin zataji wani abu ba idan ta kasance a matar Yaya Jabeer dai gashi daga jiya da aka daura auren zuwa yau kwata kwata ta kasa sukuni ta rasa inama zata Saka ranta.Mayafin ta karba kamar wacce bata da lakka sannan ta zira flat shoe dinta shima milk colour tabi bayan Ammi wacce tuni tama bar part din.Annie ce ta turo kofar da karfi tace"Laya zaman me kikeyi?kinsan mijin nan naki burkeken mota yama fishi tabbas amma kike nan kin shanyamu parlon Amadu kamar wasu gantalallu".kasa Layan kawai tayi da kai bata ce komai ba tabi bayan Annie wacce keta zuba kallo d'aya zaka mata kasan tana cikin tsananin farin ciki kamar wacce akayiwa bushara da gidan aljanna....da sallama ta shiga parlon ganin Hajiya Badiyya a zaune yasa ta daure fuska ta dawo da baya ta rike hannun Layan a cikin hannunta taja ta suka shiga ta samu kujera ta hakimce.a kasa kusa da ita Layan din ta samu wuri ta zauna tanayin kasa da kanta wani hawaye na taruwa a idanuwanta.....Abba ne yayi gyaran murya ya Kalli Direction din da Jabeer ke zaune tamkar an ajiye gawa a wurin ,tunda Lamin ya janyo shi suka shigo da k'yar ya iya gaishe su ya zauna ya dukar da kanshi baya um baya um'um."Jabeer yau Allah ya nufa ka zama magidanci ,Layan dai kanwarka ce ka riketa amana ka kula da ita ,kai kafi kowa sanin condition dinta,kayi hakuri nasan mun maka laifi amma hakan shine kawai mafita da kuma cikar burin ko wannan mu,nasan bazan samu matsala da kai ba Jabeer ka kula bani da abunda zance maka bayan wannan,insha Allah Mamana nasan ba zaka samu matsala da ita ba ta kowacce fuska,Allah yayi maka albarka"jinjina kai kawai Jabeer yayi kansa a kasa cikin cool voice and deep yace"Abba Babu laifi tsakanin iyaye da yaronsu,duk yarda kukayi da rayuwata bazan biyaku ba Abba"Wani murmushi Momy Badiyya tayi kafin carab tace"to Jabeer adai rika kulawa,kasan yaran yanzu ba wani abun kirki suka iya tsinanawa ba an kula da yaro ya ya kare bare kuma wannan da uwarka ta Riga ta gama sakalkaltata,Allah dai ya rufa asiri amma kam akwai aiki gabanka"wani wawan kallo Ummi da tun safe tazo gidan ta soma jefar Momy Badiyya dashi kafin tayi magana kuma Annie tayi mitsi mitsi da Ido cikin daga murya tace"yau naga abunda ya ishe ni,Amadu ka kwaso wa kanka bak'ar tsiya,wacece wata Badiyya Allah ma tuba bare kawai .ki fita idona,bakinki ya fita akan jikokina idan ba haka ba kuwa ran uban kowa zai b'aci a gidan nan,wallahi wallahi zakiga tsiya zakiga rashin arziki,duk tsiyar da kike shukawa yau zanyi maganinta a gidan nan."kasa da kai kawai Lamin yayi bayan ya gama kallon Annie sai dai bece komai ba amma komai Momy zatayi uwa uwace dai baiji kuma dadi ba Sam..Abba ne ya Kalli Daddy yace"y'allabai ko kana da abun fad'a ne,ga yaran naka?".Murmushi kawai Daddy yayi yace"ai ka gama fadan komai Yaya Allah yayi masu albarka baki daya ya basu zaman lafiya,shima Lamin din ya kamata yau yaje gida shikenan anyi an wuce wurin,Allah kuma ya cida Yan baya"kowa ya ansa da Ameen......wani irin kuka Layan ta saki lokacin da Abba ke kokarin sakata motar da sauri ta rungume Abba iya karfinta tace"Abba Dan Allah ni dai zan koma wurin Ammina,ni dai na fasa tafiya Dan Allah"wani irin kuka takeyi Mai ban tausayi,barin da taga Basma da Muhibba na tayata kukan Aunty sai lallashinsu take yi....tab'e baki Annie tayi kafin tace"nifa bana son sanabe da shiririta Ahmadu kasa yarinya tabi mijinta su wuce ka tsaya wani lallab'ata salan Yan hassada su fito,dama haka jiya ta tara narka narkan mata kamar aladu,kai Badiyya wallahi akwai shahararriyar tab'ab'iya"ta kare zancen tana dariya.tura baki gaba Muhibba tayi bata dai ce komai ba..Layan dake kusa da Lamin ta kamo hannunsa tana cewa"ni dai Yaya a barni nan".murmushi yayi ya leko ta gefan Abba yace"be the best wife you can be lil,kiyi biyya, wishing you a peaceful marriage life Dear"a hankali ya zare hannunsa be kula kowa ba yabar wajen cikin sauri.Abba Kam mota kawai ya Saka Layan ya rufe,ya dafa kafadar Jabeer yace"kuje kawai nazo gidan".jinjina kai Jabeer yayi Wanda ya zama kamar wani kurma ya masu sallama ya zagaya ya shiga motan be kula Annie daketa washe baki ba yaja motar yabar gidan..."to Ahmadu yaushe zanje? Kasan Laya sai da rarrashi kafin ta Saba gashi ba cikekken lafiya gareta ba".sunkuyar da kai Abba yayi yace"idan ta kwana biyu sai kuje dasu Basma Annie"rike haba Annie tayi sai kuma tace"shikenan daga Laya ta tafi zaka fara hadani da wannan gandama gandam yayan naka da basu da niyar aure? A'a ni maryama a barshi kawai Aliyu ya kaini,yo Ina ni Ina wannan yaran"bata ce komai ba tayi gaba abunta tana surutu kasa kasa.Ummi da Ammi da Aunty bangaren Umma suka nufa zaune suka sameta a parlon tana kallon Sunna TV da sallama suka shiga,da fara'a sosai Umma ta tarbesu Ummi tace"ba zama nazo yi ba,na biyo ne inji meya hanaki fita rakiyar y'ar tawa?".murmushi sosai Umma ta saki sai kuma tace"to Ina ruwan uwar miji da rakiyar mata? Ni ta 'Dana nake yi Kam"...Dariya dukkansu sukayi,mikewa Umma tayi ta cika masu gabansu da kayan drinks da abinci sumata fira abunsu......Tunda suka shiga motan wani takaicin da kunci from no where Jabeer ya soma ji Yana tokare masa zuciya har d'aci d'aci yakeji a makoshi.a matukar tsawace yace"Billah idan baki rufemun wannan Dan iskan bakin naki ba zakiga karshen iskanci da munafurci a motar nan.shashasha"rasa abun fad'a yayi ya Saka dayan hannunsa yana cakuda sumar kansa ya danna motar da gudu...tsoro sosai ya shiga Layan lokaci daya,irin tsoron da bata taba ji na Jabeer ba tuni ta takure wuri daya tana rarraba Ido cikin mayafi......tunda suka shigo unguwar tasan unguwar na masu da shi ne,a jikin gate din wani madaidaicin gida ya tsaya Yana horn,gateman yazo ya bude Yana gaishesa suka shiga gate din zai iya daukar mota biyu zuwa ukku .parking yayi be kulata ba ya bude motar ya fice abunsa da sauri itama ta bude tabi bayansa, entrance din gidan yaje ya Saka key ya bude ya suka shiga,maa Sha Allah gidan well furnished three bedroom with two parlo sai kitchen da dining.sosai gidan yayi matukar kyau yadau hankalin Layan tsarin gidan kawai ta kallah tasan aikin Ammi ne,a nan first parlo ta rakube bakin kofa wani tsawa da Jabeer ya mata bata San ta mike ba da sauri hawaye na rige rigen saukowa a idonta murya na rawa tace"Ai bansan Ina ne d'akina ba...kallon tsana ya watsa mata yace"see duk in kika kuskura naga wannan shegen kafan naki Mai kama da tsintsiya a sama wallahi sai na karyaki.up stairs nawa ne,ki kare ratuwarki a kasa".be Jira cewarta ba yayi sama abunsa one bedroom ne a sama da tailet sai babban parlo a can.komai dama choice dinsa ne aka zuba a sama yayi wani irin kyau so maa Sha Allah.....
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
35
Da asuba a sanyaye yake fitowa daga Saman kamar baya son taka k'asa kamar zai wuce sai kuma ya Kalli corridor in da jerin well furnished two bedroom ji yakeyi kamar ya wuce ga kansa dake masa wani irin ciwon Dan kwana biyu kenan ko bacci baya yi,karasawa yayi babban ciki ya bude a Yana leka kansa a ciki,Jin motsin ruwa a bathroom yasa ya gane harta tashi kenan,siririn tsuka yaja sannan ya rufe mata kofan ya wuce masallaci.....Layan Kam tunda ta karasa sallan asuba take nan zaune akan sallayan tana lazimi ga wani irin juyawa da cikinta yakeyi gaba daya yunwan ta gama galabaitar da ita har bata gani da kyau.a daddafe ta samu tayo wanka tazo ta bude press kallon kayan kawai takeyi dan babu abunda babu a ciki Wanda zata bukata inner wears ta xaro ta Saka ta samu wata saukaken dogon riga ta Saka marar nauyin lite blue turare ta samu ta fesa ta dauki hula tana tura dogon gashinta a ciki Wanda tunda Ammi ta kaita saloon bata kuma yarda ta taba gashin ba,gefen 🛏️ ta dawo ta zauna tana wani kyabe baki kamar zata saki kuka,.mikewa kuma tayi ta zura slippers dinta tayo hanyar waje.kad'an ta bude kofar ta leka babu kowa sai karar Ac a parlon ,a hankali ta janyo kofan to make sure batayi wani sound ba tasan yanzu Yaya zaice tayi hauka wani irin zazzaro manya manyan idanuwanta tayi waje a matukar tsorace ganin Jabeer kwance sanye da jallabiya fara k'yal sai tashin kamshin turarensa perlon yake yi gaba d'aya...cikin cool voice yace"kici kanki ,idan baki daina kallonta haka ba sai na kwakwale wannan idon".da sauri ta marairaice tayi k'asa da kanta kamar zata fasa kuka cikin wahalliyar muryarta da yunwa ta gama cinyewa tace"Yaya wallahi yunwa nake ji".ta karasa zancen siraran hawaye na zubowa a fuskarta.bude idonsa daya dan canza launi yayi da sauri ya ware su kanta sai kuma ya mike zaune gaba daya Yana jifanta da wani mugun kallon with much expression a fuskarsa calmly yace"to yi maza zoki cinye ni kinji".duk da kallonta b'ata masa Rai yakeyi Amma haka ya tsureta da Ido cikin takaici yace"let me make it clear to u,idan kika kuma Saka ni a sabganki gidan nan,dama ki fara neman gidan ubanda zaki buya billah zan kaklaryaki in zubar,in kuma ni na zama kitchen sai in Gani".turo Dan karamin bakinta tayi sai kuma ta rushe da kuka gaba d'aya kamar wacce aka aikowa da Ammi ta mutu,yunkurawan da Jabeer yayi yasa tayi Shirin kwasawa a guje sai kuma Jiri ya ebeta ta zube anan wajen.tsaki ya saki beko kalleta ba ya haura sama Yana Jin idan ya tsaya wurin zai iya illatata da shegen dukan da ba'a taba mata ba,lallai shi zata rikawa iskancin da takeyi a gida?in ko haka ne da matsala zama inuwa d'aya garesu ya haramta dan bazai dauka ba....da k'yar Layan ta ta dafa daya daga sofa ta parlon tayi wurin dining anan ta bude kofan kitchen, kitchen din babba ne sosai babu abunda babu a ciki sai karamin kofa a wurin tana lekawa taga store an jibge uwayen buhuhunan abinci da kwalaye babu abunda babu a store din.cikin sauri ta kunna gas ta daura karamin tukunya ta Saka ruwa kad'an kafin ruwan yayi ta ebi kayan shayi a cup,kamar Mai yunwa ta juye ruwan shayin ta kada ta koma dining ta shanye tas ta zauna tana sauke numfashi,ta soma tunanin tunda aka fara Shirin bikin nan bata wani ci abun kirki ba shiyasa yunwa ta kusa haalakata sai da taji ta dawo daidai sannan ta kuma komawa kitchen din.Irish ta dauka a bowl ta zauna ta fere ta kuma kunna gas ta zuba man gada