Showing 27001 words to 30000 words out of 55893 words
Chapter 10 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt
bakinsa yayi shiru ya soma laluben wayar Abba yana dauka ya mika mata,ansa sallamarsa tayi kafin tace"karfe nawa zaka dawo?".cike da girmamawa yace"da yamma ne Annie"...."to yau dai ba batun yamma in ka dan samu sarari karka taushe hannu ina nemanka,maganar bata waya bace gaskiya"....Annie ta fada...Dan Jim Abba yayi sai kuma yace "wani abun ya faru ne Hajiya?"..." Babu komai sai alkhairi kaidai kawai kazo"..da to ya ansa sannan ya kashe wayar...k'asa Momy Badiyya ta duka tana gaishe da Annie tsuke fuska tayi kadaran kadahan ta ansa gaisuwar kafin tace"so nake naji Badiyya meya hanaki shigowa gaishe da Hajja?",..wani abu Momyn ta hadiye da kyar kafin tace"ban samu labarin zuwanta bane da wuri sai yanzu Ahmad karami ke fadamun.".."duka dai ya rage naku,mai son zaman lafiya dai yazo ya gaishe da matar nan salin alin cikin mutunci kamar in da suke mutuntamu danni bazan kwashi rashin zaman lafiya da zumunci mai kyau ba tun da duk an zama daya"..."kiyi hakuri Annie zamu shigo yanzu"...bata kuma bi ta Kansu ba tayi waje abunta tana gyara rikon wayarta...A parlon ta samu Umma da warmer's guda biyu ta kawowa Hajjan suna gaisawa dan harta zuba mata farfesun catfish a bowl da karamin spoon ta bata ,ita kuma tana zaune wurin kafarta...."sannu da kokari yar albarka,Wato dai kinsa ta riga fara cin abincin sashenki".Murmushi kawai Umma tayi tana gaishe da Annie tace"ai nasan Hajja da son kifi ne kamar Jabeer shine Layan na fadamun na daura mata kuma tadanji dadin bakinta"..."sosai kuwa yar albarka Allah ya wadata naku yaran ya masu albarka ya basu ikon yi maku,kamar yarda kuke dawainiya da mu,na gode sosai Allah ya jibanci lamuranki".da Ameen duk suka ansa sannan suka ansa sallamar Momy Badiyya dake shigowa fuska a dan daure,nesa da Umma ta zauna kafin tace"Hajja barka da zuwa,mun sameku lafiya,ya karfin jiki kuma?"."lafiya alhmdllh,ya naku gidan da iyalin"...alhmdllh kawai Momyn ta fada sai kuma ta mike tace"to a gaida gida Hajiya zan fita ne nace bari nazo mu gaisa"...godiya sosai Hajja ta mata sannan ta fita,ba Jimawa ma Aunty Amarya ta turo da Warmer's na abincin Hajjan sannan itama tazo daga baya suka gaisa...slowly yake tafiyan kamar baya son taka k'asa ya tura main Door ta babban parlon ya shiga bakinsa dauke da sallama.in ba ka saurara ba ba zakaji me ya fada bama.looking everywhere amma parlon so silent babu abunda ke magana sai babban plasma TV dake ajiye a tvstand sai karan AC kuma zama yayi a daya daga Sofa's na parlon yana shafa cikinsa sai kuma a hankali yace"Ummana we're are you".to two minutes ya tashi heading to the dining table area kawai tsaye ya wuce kitchen zai dauka ruwa marar sanyi.A nutse kuma hankali kwance duk wannan shirmen babu shi take soya favorite Noodles dinta cikin kwan data hada a gas Allah Allah takeyi ta karasa ta wuce wurin Hajja dan har ranta da zuciyarta take jin soyayyar matar,kashe gas din tayi ta dauko plate da fork ta soma juyewa..at all bataji shigiwarsa bama,duk da yaji zafin ganinta shima amma ko kallon in da take bai kuskura ya sakeyi ba dan sai da ya shigo gaba daya sannan ya lura tana kitchen din.ruwan ya dauka ya juyo zai fita Yaga ta kuresa da dara-daran fararen manyan idanuwanta masu daukar ido da hankali,bece komai ba duk yarda zuciyarsa ke azalzalarsa akan ya mammareta ya wuce amma the other side yana tuna gargadin Ammi bayan ya ajiye ta office data ce masa yarta na gida idan ta dawo ya tab'a lafiyarta kuma zaiga the other side of her..."yaya aida sai kace na kawo maka ruwan,Umma na wurin Annie bari na kawo maka abincin tayi saving naka a warmer,ta karashe maganar tana ajiye fork din hannunta.wani abu mai daci daya tsaya masa a makoshi ya hadiye da kyar,yana jin bak'ar kiyayyar da wutar zuciyarsa ke rura masa from no where, can cikin makoshi yace"wallahi monster if u there make that mistake na zuwa dining can you will regret in all your life time,idiot mayya ".bottle watan daya dauka kawai ya juya ya jefa mata shi a k'afa ya fice da sauri dan zuciyarsa fada masa kawai takeyi ya karkaryata ko yaji saukin kiyayyar da yake mata a zuciya.sosai yake regretting na shigowa part dinma gaba daya,baisan dalili ba bai kuma daga ina ba amma tabbas yasan dai ya tsani yarinyar fiye da duk wani abu da yake ki a doron duniya,idan ya ganta ji yakeyi kamar his life come to and end.gaba daya ji yayi gidan ma ya masa zafi baiji sassauci ba sai da yabar gidan kafin ya samu peace of mind....karamar kara Layan ta saki ta durkusa tana shafa kafarta in da ya jefeta saboda zafin daya ratsata sai kuma kawai ta saki murmushi ta mike ta dauki noodles dinta da drink ta wuce dining din tana tura baki dan tasan ko da wasa ba kuma zai kara zaman part din ba tunda yasan tana ciki....
Share fisabilillah
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
22
Babu dadewa Abba ya shigo gidan,part din Annie ya nufa direct be tsaya kiran kowa ko jin me yake faruwa ba a gidan,tunda ya kira Aunty Amarya kuma ta fada masa Hajja ne kawai taso amma gidan lafiya qlau.to ya yarda kuma ya amince akan Jabeer ne ko kuma makamancin hakan shiyasa bai bata lokaci ba cikin ladabi da mutuntawa ya zauna a kasa ya gaishe da Hajja tare da Annie da suke zaune a wurin.kafin ace komai Annie ta dubi Muhibba da Basma tace"to Ku tashi zamuyi magana.kafin kuma na fara jin ana tanbele da gararamba da abunda aka saurara a duniya, bare wancan da jira takeyi"Ganin Abba a wurin babu Wanda yace komai a cikinsu kai tsaye suka bar wurin....nisawa Hajja tayi kafin tace"Alfarma nazo nema,nasan bani da iko ko damar tursasawa amma nazo ne da kokon barata da kuma tunanin hakan shine mafita wacce ko bayan ranmu zamu kwanta cikin salama da kwanciyar hankali,ina fatan zan samu wannan abun da nazo nema,sanin kanka ne Ahmad Jabeer da Maryam basa shiri kuma ni da kai da duk Wanda ke rayuwa dasu bashi da kwakwaran hujja ko makamar dazai fada wacce ta zama sanadiyyar faruwar kiyayyar nan,duk da hali irin na Jabeer yaci ace sunfi kowa shakuwa da Maryam amma hakan bata faru ba,ko Baku fada ba Ku iyayene kuma ba zaku taba jin dadin irin yarda suke rayuwa ba,wannan ne Dalilina na son nemawa Jabeer auren Maryam idan har hakan bazai zama da cutarwa a gareku ba,insha Allah kuma wata rana zakuyi alfahari da hada wannan auren".jinjina kai Abba yayi without second though yace"Hajja kinfi karfin komai a gidan nan,muma kasanki muke zaki iya yanke hukunci a kanmu kuma ta zauna ,da mu da abunda muka mallaka duka zaku iya yin hukunci dashi Hajja,duk abunda kuka yanke mu masu biyayya ne"...sosai Hajja taji dadin maganganun Abban cikin dauki da tsananin jin dadi tace"Allah yayi maku albarka baki daya,Allah ya cika maku burikanku na alkhairi baki d'aya"Annie na washe baki kamar sabuwar Amarya tace"Ameen ameen ya rabb,to amma kuna gani wannan yaro yasan maganar xai yarda kuwa?".sanyayyar ajiyar zuciya Hajja ta sauke tace"bana so cikin yaran nan ko daya su san da batun Hajiya Maryama a bari har sai an daura auren sannan a masu duk bayanin daya dace,a lokacin su san muke iko dasu,dan kinsan idan anbi ta nasu ba zamu taba samun abunda muke so ba"..."Allah yasa hakan shine mafi alkhairi ya tabbatar mana da dukkan haske da gyaruwar ko wacce b'araka insha Allah da anjima san hada iyayen nasu na masu bayani yarda duk kika fada Hajja".cike da farin ciki da jin dadi Abba yabar parlon Annie dan sosai har ransa ya gamsu da shawarar Hajja Wanda be taba kawowa ransa tunanin hakan ba......."sannu Mrs Jabeer karewar soyayya,iska dai tana wahal da me kayan kara banga alamar nasara ba bare kuma za'a tsira,dan Allah ki sawa ranki salama dan Allah"Muhibba ta fada tana gyara zamanta akan makeken gadon Layan din dake part din Ammi.kyab'e baki Layan tana hararar Muhibba tace "idan har ba zaki yi mun fatan alkhairi ba,to kara kiyi shiru dan banga alamar nisan tafiyar da nayi hargaginki ko surutunki zasu dawo dani baya ba,komai lokaci ne kuma zaki fada da bakinki,Yaya Jabeer mallakina ne kuma zai soni is just a matter of time just wait and see"..... Dariya sosai Basma tayi tace" to Allah ya tabbatar da alkhairi sarkin soyayya ni dai na kagara a daura auren nan in dai rabonki ne ko ma huta da daure fuska a gidan nan" .......sanye take da material dinkin bubu mai dan fadi ta kashe dauri a gaban goshi,sosai fuskarta tasha make-up sai fitar da sihirtaccen kamshi takeyi ga chewing gum tana taunawa k'as k'as daga ita sai kawarta Humaira wacce kusan shigarsu iri daya ne itama siririyarce kamarIhsan.Humaira itace kawa daya tal ga Ihsan ,parking motar tayi a cikin babban parking lot na gidan kafin ta kwashi hand bag dinta da wani siririn mayafi data sako a motar dan gaishe da sirikan nata.kayan jikinta ta kuma kallah ta saki siririn tsaki tace"Wallahi sam gaba daya rigar nan ta takura mun dan dai ance harda kakarsa zan gaida da me zai sakani wannan shigar kamar a wani kauye".Dariya Humaira tayi tace"to tunda kina son Lamin kam ai biyayya ta zama dole,tun da kakar ai itace komai a gidan...."bari duk zanyi maganinsu da wannan Dan uwan nasa da bashi da magana sai tashi,ni gani ma nakeyi an danka komai a hannunsa ne an barmun Lamin din a baya,bayan shi bama gidan ubansa bane,wallahi duk zan zama daidai dasu".wani irin takaici ne ya kuma kamata kafin ta karasa fadan abunda zata fada ta turawa Lamin da Layan idanuwa Wanda suke fitowa daga part din Umma.murmushi sosai kwance a fuskar Lamin yana kuma dungure kan Layan dake sanye da long blue black hijab har kasa da littafai a hannunta da alama masallaci zata shiga ta bada karatu...bata kuma wani tunani ba ta balle murfin motar ta fito tana kuma daure fuska da kare masu kallo....kai tsaye wurin motar shima ya nufa Layan din na binsa a baya tana korafi akan bai fada mata zuwan Ihsan din ba,da fara'a fuskarta ta karaso ta kama Hannun Ihsan tace"sannu Aunty you're highly welcome, duk da Yayan nawa bai sanar mana da zuwan ki ba,ko kuma mu ya kawo mu".Kadaran kadahan Ihsan ta kirkiro murmushi bata dai ce komai ba sai ta kuma juya kallonta ga Lamin tace"Honey kace mun baka gida kuma,kasan naso kazo ka taho da ni "...." Yanzu ma shigo nima na dauka ma har kinzo kin tafi ai,anyway ki karasa ciki wurin su Momyn".Layan dai bata yarda ta bita part din su Momy ba "au ba zaka rakani ba Baby" ta kare maganar a shagwabe.kallonta yayi sai kuma ya dauke kai tare da cewa"zanje na duba Annie ne,zan shigo"be jira cewarta ba ya kama Hannun layan sukayi part din Annie,da kallo kawai take binsu tana kisisima abubuwa da dama a kanta....kusan cin karo sukayi da Jabeer dake shirin fitowa fuskarsa a hade kamar ko yaushe, kallon Hannun Lamin yayi dake rike dana Layan sai dai bece komai ba ya rabasu xai wuce,janyo shi Lamin yayi yace"c'mon,ni zaka fara ignoring Mr man?"....Dan waro manyan idanuwamsa yayi sai kuma yace"ni ban ganka ba".murmushi Lamin yayi tare da cewa "oh I see,ina Hajjan ko harta koma nabi da rabon addu'a a yau?"...." Abba ya saka Hydar ya mayar da ita".be kuma tsayawa ba yaja hannunsa ya wuce da sauri,yana jin wani takaici na taso masa na kallon da wancan Monster din take binsa dashi dan idan ya tsaya xai iya illatata da shegen dukan da kowa xaiyi nadama...itakam Layan da manya manyan idanuwanta Wanda suke nan farare tas ta tsura masa su ko kiftawa batayi harya wucewa ganinta,Hannun Lamin yayi tapping a face dinta yace"Yaya dai? Wannan kallon fa Lil sis?".Murmushin ta saki tace"babu kai Yaya,naso na gaishesa ne amma nasan as always ba ansawa xaiyi ba"...."you not worry about him,I assure you one day one time Jabeer xai maki dariya zai soki xai kuma kiraki lil sis insha Allah,ki tsaya ki gani".....wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta from no where tunda take babu Wanda ya taba bata kwarin gwaiwa akan Jabeer ji tayi aduk duniya tana kuma kara jin girma da son Yayanta Lamin shine daya dake fahimtarta a ko wanne hali ,duk taje ta dawo kuma xaiyi backing dinta,cikin sanyin murya tace"thank u so much Yaya".Murmushi ya mata yaja hannunta suka wuce wurin Annien kawai.
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
23
Gyaran murya Abba yayi yace"kamar yadda na taraku ba wani abu bane illah ina son sanar da Ku insha Allah in 2weeks time za'a daura auren Jabeer tare dana Dan uwansa Lamin Wanda duka kunsan da shi"....."y'allabai wanne Jabeer din dai? A tunanina Lamin kawai za'a aurar a gidan nan,Jabeer bai gabatar da wacce yake so ba,to kuma kace zaka hada"Momy Badiyya ta fada.kallonta Abba yayi sai kuma yayi murmushi yace"ni na zab'a masa,ba yanke shawarar aurar da Mamana ga Jabeer".....Aunty Amarya tace"Layan dai Yallabai?".jinjina mata kai yayi yace"ita ma fada kuma na zaba masa,ina fatan kuma hakan bazai janyo komai ba sai gyaruwar duk wani abu da muke tunaninsa ba dai dai ba".......Duk maganganun da akeyi Annie tana kallonsu ne kawai bata ce komai ba,Umma ma da Ammi ba Wanda ya tanka Momy Badiyya ta saki wani Murmushi can tace"lallai wannan gaggarumin abu ne,ina Jabeer ina Layan? Layan ina taga lafiyan zama da Jabeer ,sanin kanka ne kuma ba jituwa tsakaninsu ,kara dai a duba maganar nan,Jabeer ba abunda zaiyi sai illata yarinyar can,ita kuma gata duk cuta sauran ciwo,a barta tayi karatunta shima kuma naga bai sanya niyar aure ba,bare kuma ace za'a masa dole".Sosai Ammi ta shaka haushi duk ya cikata bawai kuma dan Momy ta saka Jabeer ba kawai irin yarda ta muzanta Layan ne bai mata ba,kasa daurewa tayi tace"Halan ita mai cuta ba'a aurenta? Beside ma ki fada mun wanne irin cutar ne kuma kika Santa da shi? Insha Allah kuma haka za'ayi auren su zauna da juna cikin kwanciyar hankali dan banga alamun in da wata damuwar zata bullo ba"....."to ke bakiga dama Dan naki kamar kin gaji dashi bane? Aini Murna ma ya kamata na maki da yanzu Cikin nawa yaran za'a jajibawa dan naga kamar neman kai ake da ita"Momy ta fad'a.....wani kallo Annie tabi Momy Badiyya da shi sai kuma tayi dariya irin ta basawa tace"hmmmm wallahi wallahi Badiyya ke ko ba y'ar arziki bace,ban taba ganin marar mutuncin tukekiyar mata irinki ba,ace bakinki baya haila baki da katsari ko kadan? To ke duk yarda Ahmadun ya dauko ki a gantale bamuji kyama ko nuna bakin ciki ba muka rikeki muka maida ke mutun har kin zama haka ki had'a komai ba gida?to ki sani har gobe zaman Sadeequ kikeyi a gidan nan da darajar y'ay'anki idan kin manta ni bari in tuna maki,Jinin Sadeequ kam yafi gaban ki wallakanta shi,in banda Jabeer din akayi niyar aura mata bana so Hajja ta dauke ni mutuniyar banza da tuni yau a Pamilyn nan an shaida auran Lamin da Layan,to mu ba mutanan banza bane,ahir dinki nasan duk me kike kullawa idan kuma kin musa kici gaba kiga idan Lamin ya auri wannan higaggiyar aljanar yarinyar da kuka lika masa"....Tunda Annie ta fara tijararta Momy tayi kasa da kanta shab ta manta Annie ba wurin tsabar kishin ance za'a hada auren tare dana Lamin ne yasa ta tanka amma batayi tunanin wannan tereren daga Annie ba....maganar Annie ta dawo da ita hayyacinta tana fadin"Aure insha Allah babu fashi za'a daura,kuma kada naji ko na gani na wani ya fadawa yaran nan,muna da hikimarku na boye ,duk kuwa Wanda naji maganan ta bangarensa to ni da kaina zanyi hukunci kuma Wanda ba zaiwa kowa dadi ba,musassan ke Badiyya da bakinki ya iya yin abunda ba'a umurce shi ba,to tun wuri ki kiyaye ni".ta kare maganar tana nuna Mommy.k'asa tayi da kanta tace"insha Allahu Annie za'a kiyaye"a haka taron ya tashi kowa da abunda ke ransa.Umma kam kanzil bata ce ba har akayi aka gama kamar bata a parlon,da aka sallami kowa kuma tabi hayan Ammi suka wuce....."ina gaya maki rashin mutuncin da take mun a gidan nan kenan,bana da ikon fadan ra'ayina ko wani abu sai ta fara mun terere kamar wata karamar yarinyar"Momy ta fada tana sauraran wayarta.Dariya Hajiya Sha'awa tayi tace"ni ai bani ganin laifin kowa a gidan nan Badiyya sai ke, kuma tsakani da Allah ya kamata ki mike tsaye,bazai yiwu na bada y'ata a gidan da sirikarta ta kasa mallakar kowa ba,kin san dai wacece Ihsan bata son ganin wani a samanta,ni ai k'arama da aka sanya auren nan,tunda tun dawowarta na lura yarinyar nan bata sonta kinsan dai mutuniyar"....nisawa Momy tayi tace"kinsan nima duk wani abu daya shafi Fatima ba san shi nake yi ba,amma na godewa Allah tunda ba yarana aka likawa ba,dan shine abunda na zan taba yarda ba kam duk me zai faru"...."ki daina wannan maganar Hajiya Badiyya,ki cire kudi ki cire tsoro ki biyawa kanki bukata,wallahi wallahi kinji na fada maki idan kikaje wurin nan ba Ahmad ba har Ita Annien take ko wa sai yarda kikayi da ita ni ba gani da nawa mutumin ba tuni nayi maganin komai,ni bazan iya jurar duk wannan CeCe kucen da kike iya dauka ba"Hajiya Sha'awa ta fada.nisawa Momy tayi tace"to nifa ba tsoro nake ba,kawai dai kinsan yanayin komai kakeyi kana tuna mutuwa da tsoron Allah dai,amma komai zai zama tarihi duk zanyi maganinsu daya bayan daya".A haka dai suka kare wayar kowa da abunda yake sakawa....tab'e baki Ihsan tayi wacce ke sauraren conservation din Mom dinta da Momy tace"hala wannan Dan jin kan sojan za'awa aure?"..."eh shine za'a aurawa yarinyar da kika zo kina complain a kai.na rasa irin son da sukewa wannan yaron"....tuno kyakyawar fuskar da Jabeer Ihsan tayi yasa kyakyawan murmushi subucewa