Showing 6001 words to 9000 words out of 55893 words

Chapter 3 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt

mik'a mata ya tashi zaibar parlon Momy ta rakashi da Harara tana jan tsaki zuciyarta na zafi....mayar da kallonta ga khalifa takwaran Daddy tayi tare da cewa"b'ace mun da gani ka baza kunne kaje ka kai rahoto to ka mayarda hankali kaga in banyi maganinka a gidan nan ba"..Aunty Amarya kam dake dining tana shirya culas yi tayi kamar bataji me suke fad'a ba...."Abba dan Allah yaushe Yayan zai dawo,ina kiran wayarsa amma bata tafiya"Basma ta tambaya.Murmushi Abban yayi tare da cewa"gobe insha Allah i war haka Lamin yana nan tare da mu,yace kada a fad'awa Mamana ne sai dai ta ganshi kawai".wani ihun Murna Muhibba da Basma suka saki a tare kowa da abunda yake fad'a.....A hankali take fitowa daga d'akin to make sure batayi wani sound da zaija hankalin Umma ba tace mata bata da natsuwa da hankali sanye take cikin atamfa royal blue da ash riga da sike dinkin yayi daidai da ita d'as ga dan karamin kugunta kamar an zana a cikin siket din scarf dinta a hannu sai ribbon ta taho tana tura baki,sosai tayi kyau dan Layan asalin y'ar gayu ce duk rawar kanta akwai shegen tsabta da iya kwalliya gaban Umma tayi raurau da ido kamar wacce zata fasa kuka har idonta ya tara ruwa tace"Umma please ki daure mun na kasa"from head to toe Umma ta bita da kallo tare da tab'e baki tace"as big as you are Layan kina 22 years kina university amma har yanzu baki iya daure gashinki ba?kin b'acemun a wuri ko sai nayi maganinki yanzu".with out second thought Layan ta b'are baki da sakin kuka,cikin Sauri Hydar dake dining yana cin abinci yana kuma kallon drama ya taso da Sauri ya janye Layan daga dukan da Umma ta kawo mata,aiko tana ganinsa ta kuma shashakwewa tana kiran Yaya hannunta ya kama yana fadin"Afuwan Ummanmu ba zamu sake ba,lallai yau ana so Abba yayi hukunci da kowa a gidan nan an tab'a Annie k'arama".ya k'are zancan yana dariya kafin suka fita daga part din zuwa na Annie acan ya zaunar da Layan yana tubke mata tulin sakalkiyar sumar kanta wacce ta sauka har bayanta yana kuma aikin lallashi...Annie dake kan abun sallah da carbaha a hannunta anata istigfari tayi saurin yaye Hijab din jikinta tare da kai k'arshen lazimunta tace"Kai Aliyu meka mata daga dawowarta makarantar ko hutawa batayi ba,me aka mata?"...."ita da Umma ne tana so ta daure mata gashi "...." Hubuhu duniya ke Laya meya kaiki wurin Fatima? Dama dai kinsan bayi maki zatayi ba,shiyasa nace zanje kauye wurin malaman Allah da Annabi bafa boka ba,danni bana bin la'anannun Allah,kawai dai suyi mana addu'a da bamu k'aik'ayi koma kan mashekiya dan tabbas ba banza ba yarda Fatima take maki kamar ba ita ta haifeki ba ,,,keni duniya ba tsoron Allah ba ruwana bama nufin kowa da sharri amma dole mu tashi mu k'are kanku wannan zamani duniya ba tsoron Allah ba tawakkali sam".......Zaune yake akan sofa ta babban parlon part din su na mazan gidan,sanye yake da farin 3quater sai white singlet k'ar tana nan kamar ba'a tab'a sakawa ba idanuwansa a lumshe sai tashin sanyayyen k'amshi yakeyi,waya ne kare a kunnansa da alama magana yake da wani mutun mai mahimmanci a rayuwarsa,kad'an yad'an saki fuskarsa alamun Murmushi tare da shafa tulin sumar kansa tare da cewa"Owk Allah ya kawo ka lafiya ,nima kai nake jira na wuce hutuna ya k'are"banji me aka ce masa ba sai naga ya ajiye wayar tare da tsurawa silin ido kamar mai son gano wani abu.....Shigowar Daddy parlon Annie yasa duk suka mayar da hankalinsu a kanshi banda Annie data wuce kitchen dan daura girki dan ita Sam bata fasa girki ba,ko yan aiki a sashenta bata so.cike da girmamawa Hydar ya gaishe da Daddy tare da Jafar Wanda yake shigowa yanzu,kallon Layan Daddy yayi tare da cewa "naga motar Yayanki yana gida maza kiramun shi bana so na makara kuma ". Sai da gabanta yayi tsananin bugawa saboda tsorata duk da yarda take cike da zakun da buri da muradin ganin kyakyawar fuskarsa sai dai bata so taje ko dan tattalin farin cikinsa Wanda ta sani yana ganinta komai sai ya dagule,sai dai ko da wasa ba zata tab'a gujewa aiken Daddyn ba,Dama Annie an kusa tasan ba zata tab'a bari taje ba.kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta mik'e tana d'aura dankwalinta ta fice daga d'akin zuwa madaidaicin part din nasu..cike da tsananin tsoro fargaba bawai na dukan da zai iya mata ba a'a sai na bata son taga b'acin ransa wannan shine abu mafi wahalar da zuciyarta ta rasa meyasa tun tana jaririyarta har kawo yau tana rayuwa ne da so da kuma farin cikin Yayan nata a rayuwarta tabbas duk ranar rabuwarta da shi tayi imani cewa a ranar rai zaiyi bankwana da gangar jikinta a ranar duk wata jijiya ta jikinta da zuciyarta zasu gaza su kuma kasa d'aukar d'awainiyar gangar jikin nata.dan haka tuni ta sallama Jabeer shine rayuwarta ko da kuwa zai ringa yankan naman jikinta ne...tura parlon tayi sai dai ba kowa.dib dib dib haka zuciyarta ke bada sautin bugawa a hankali ta soma saka doguwar kyakyawar k'afarta wacce tasha ado da Jan lalle sannan ta taka zuwa kofar d'akinsa Wanda yake jingine Dana Yaya Lamin..A hankali tayi knocking kofar to make sure batayi sound da k'arfi ba gudun kada ya balbaleta da masifa duk da tasan akanta ne kawai zuciyarsa ta fiye hawa,jin ba'a ansa ba yasa ta kuma knocking can ciki ciki yace"come in".hannunta har kyarma yake ta samu ta bud'e tare da shiga ta tsaya a bakin k'ofar sosai ta rike hannuwanta tare da runtse idanuwanta Wanda take kallon k'asa cikin sanyin murya tace"Yaya Daddy yace kazo yana sauri ne"....Jabeer dake kwance rubda ciki ya bada kofa baya ya juyo da wani irin speed bakinsa har rawa yake cikin tsananin tashin hankali yace"you again?".waro dara daran fararen idanuwantayi ta d'agosu suka had'a ido.cikin k'araji Jabeer yace"innalillahi wa'inna ialaihir raju'un,sai dai kici kanki mayya kawai"kafin ya safko daga bed din jikinsa har rawa yake ya k'araso tare da d'auketa da gigitaccwen mari ya bud'e kofa ya ingizota gaba d'aya iya k'arfinsa baya ko tunanin irin fad'uwar da zatayi,jikinsa har rawa yake...Da k'arfi Layan ta runtse ido dan ta riga ta sadak'as yau saita karye k'ugu sai kawai ta jita a jikin mutun ,Aunty Amarya ce ta tareta sosai Layan ta k'ank'ame Aunty Amarya tana karanto duk wata addu'ar da tazo bakinta....kallon Veer kawai Aunty Amarya keyi ko kad'an batayi mamaki ba dan tasan zaiyi fiye da haka ma "ka kyauta Jabeer ka kashe Layan a gidan nan ka huta kawai,tunda kai bakasan kara da kawaici ba". Tana zuwa nan taja hannun Layan suka bar part din...




Comment and share
Ouhm Aryaan
07033636337 WhatsApp only


*RUHIN JIKI*


_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*___________________________________*




*JORDERH MAJIDADI*




Page 6






Kai tsaye part dinta tayi da Layan ta baya ma suka shiga dan Sam bata son wani yasan abunda yake faruwa Bare a sakata gaba da tambaya.har bedroom ta kai Layan ta zaunar da ita a gefen bed ta tsaya tana k'are mata kallo.k'asa Layan tayi da kanta hawaye masu zafi suka soma rige-rigen sauka a fuskarta duk yarda take k'ok'arin da son ta mayar dasu amma hakan ya faskara,siraran hannuwanta da suka sha ado da Jan lalle da bangles ta daga tare da k'are fuskarta duka dasu tana sakin kuka Marar sauti..Basma ce ta shigo d'akin tana k'wala Aunty Amarya kira sororo ta tsaya tana k'arewa Aunty kallo da kuma Layan dake kuka cikin sauri ta yunk'ura zatayi kan Layan Aunty tace"don't you try that,maza fice mun a d'aki,idan kin fita kuma naji labari a gaba"sunburar baki Basma tayi tare da cewa"Amma Aunty"."au bakiji mena fad'a ba kenan,in maimaita kaina?".Aunty ta katseta .shiru tayi ta fita tabar d'akin ...zaman kusa da Layan Aunty Amarya tayi tace"ya isa kukan haka Daughter bana son Amminki ta gane kinyi kuka kinsan hankalinta zai tashi ,shawara d'aya zan baki ki guji duk abunda zai had'aki da Jabeer batun yanzu baki Layan tun kina zanin goyonki kinsan manufar Jabeer a kanki to ki taimaki rayuwarki ki nisanta kanki da shi,kuma hakan baya nufin ki daina ganinsa a matsayin Yayanki a'a sai dan ki guje masa fad'awa fushin iyaye sanin kanki ne duk ranar daya maki duka to Ammi tana fushi dashi ke kuma nasan ba zaki so hakan ba.dan Allah Layan ki guji duk abunda zai had'aki dashi ,mu had'u mita masa addu'a Allah ya sassauta masa wannan tsanar da yake maki wacce bata da makama bare tushe babu kuma Wanda yasan dalilinta bare muce ga k'arshenta"....Layan kasa fadin komai tayi sai kai kawai data girgizawa Aunty tare da k'ak'aro Murmushi tana zancan zuci taya mutanan gidan su zasu San ba zata tab'a iya nesanta kanta da Jabeer ba,ilahirin rayuwarta ta ginu ne a tsananin son Jabeer da bautatawa sonsa ko da ace a kullun yankan naman jikinta yake yi bata tab'a jin zata bar sonsa kamar yarda yake jin har abada bazai tab'a daina nuna tsana da kyara gareta ba,ta tabbatar duk ranar data rabu da Jabeer to ranar ne ranar mutuwarta ko tantama batayi ranar rai da ruhi zasuyi bankwana da gangar jikinta,firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data lula sanadin tab'ata da Aunty Amarya tayi murmushin ta kuma yi mata tasa hannunta tare da shafar fuskarta da tayi sakayau bak'inta sai k'yalli yake da sulb'u kafin ta shiga toilet ta wanke fuskarta kamar yarda Auntyn ta umarceta sannan ta samu damar fitowa daga part din zuwa babban parlo.Da gudu Khalifa yaso ya rungumeta cike da tsananin so da k'auna da yakews yayar tasa dan duk gidan babu Wanda khalifa yake matuk'ar so kamar Layan da Jabeer yace"Yaya Layan ina kika shige duk gidan nan bakya nan har Daddy da Yaya Jabeer sun fita tare,Yaya yace zai siyamun chocolate ".Murmushi ta sakar masa kafin tayi magana kuma Momy Badiyya ta rigata da fad'in 'kai Khalifa bana son surutun banza da wofi maza zoka nemi wuri ka zauna,ke kuma ki shiga kitchen ki taya su Ladi aiki kina mace har kinje university ace baki iya komai ba harkar kitchen sai zaman banza da neman magana ,da daukar rahoton gulma"... Kwab'e fuska Layan tayi kamar zata saki kuka tace" Momy kin manta ne? Kinsan bana iya shiga kitchen bana iya yin aiki".'rufemun baki amma aikin iya gulma ba? To maza tashi mai Asthma karya kije maza,in an maki aure ubanwa zai na maki aikin? Cavage da su carrots zaki yanka mun kota nan a k'aru da ke"...sakin hannun Khalifa tayi ta tashi jiki a sanyaye ta nufi kitchen tana aikin turar baki......Tunda tayi sallar asuba ta koma ta kwanta bata cewa komai ta zurfafa dogon tunani Wanda ita kanta bata San iya lokacin data d'auka tana yinsa ba tun tanajin hayaniyar y'an gidan da suketa kai kawo a ko wanne part girke-girke da gyaran gidan kawai akeyi sai kace zasuyi bak'i har ta daina jinsu ,Muhibba ce ta shigo d'akin da Annie tare da tapping long legs na Layan tace"ke madam bacci ba zaki tashi ba? Ko irin ma ki tambaya meke faruwa da gidan amma ke ko a jikinki sai bacci da tunani marar amfani".tura baki Layan tayi tare da kuma Jan Duvet ta duk'unk'une kanta kamar zata saka kuka dan duk jikinta ciwo yake yi saboda tsaiwanda tasha jiya na yanka Cavage ga hannuwanta duk sun d'ura ruwa cikin cool Voice tace"please Muhibba allow me dan Allah"...."to ki zauna kyayi takaici ke kad'ai a d'aki"...Annie dake jikin k'ofa tsaye ta k'washe labile tace"Amma in nace zanyi maganinku aga kamar cin zalinku zanyi.Mahibba na hanaku shigo mun d'aki idan nayi gyara,kuna da d'akin nan naga kuma waccan Narkekiyar tana da nata d'akin itama to bansan me kika manta ba da kika tahoman kika tile kamar shirgin doya,to wallahi zakuga tsiya tashi fita tunda ba gadona kikeyi ba".kyab'e baki Muhibba tayi tace"shi mutun sai rakad'i in banzo nan ba ina zanje,daga na shigo d'aki ki sanyani gaba."kanne ido Annie tayi tare da cewa "hmmm huuumm ni da d'akina? Nace ko d'akin Amadune kona Badiyya?" Ki tsaya ni da ubanki zanyi Ku baku isheni kallo ba". Ganin Annie na neman fita yasa Muhibba rigata ficewa tana kwashewa da dariya dan tasan sarai tana fita to wurin Abba zatayi kuma tsab zaiyi maganinta ta sani.....Gaba d'aya Ahalin gidan marigayi Alhaji Sulaiman Bulasawa dattijon Arziki Wanda ya mutu yabar tarin alkhairai da zuri'a a doron k'asa.jere suke reras a babban compound na gidan tun daga kan Anni har zuwa kan Khalifa Layan ce kawai babu a wurin...kowa ka gani fuskarsa dauke take da madaukakin Murmushi tsananin farin cikin da suke ciki ya kasa b'oyuwa kowa ya cab'a Ado musamman Momy Badiyya wacce tayi shiga cikin wani dangan les daga hannuwanta zuwa wuya da kunne ko ina yaji d'anyan gold sai fitar da sihirtaccen kamshi take yi tana ta ware hakoranta Wanda hokorin makka ya masu ado....Jabeer da Jafar,Hydar da Faruk su sukaje taro Lamin a filin jirgi.get din gidan aka wangale take wasu ratsa ratsab rides guda biyu suka sako kai na gaban Faruk ne a mazaunin driver sai Jafar a gefansa sai Hydar a baya.mai bi masu kuwa Jabeer ne a matsayin driver sai gefansa wani matashin saurayine da zasuyi agemate da Jabeer din...A tare zaratan samarin suka taho sai d'aukar ido sukeyi..wani kyakyawan farin dogon saurayi Wanda kusan komai nasu d'aya da Jabeer ya sako k'afarsa daga cikin motar kafin ya fito gaba d'aya sosai naga tsananin kamarsu da Jabeer sai dai yafi Jabeer haske ,Jabeer kam ya fisa kyau,sanye yake black suit sai inner fara yayi matuk'ar kyau da haskawa kamar shiya halitta kansa.Jabeer kam sanye yake cikin long black trouser sai long sleeveless black colour itama da bakin takalmi velt da jacket dinsa duk brown sai fitar da sihirtaccen kamshin nan nasa mai wuyar barin zuciya yakeyi gashin kansa sai d'aukar ido yake yi saboda tsananin gyaran da kulan da yake samu a kullun,tsadaddan Gucci agogon hannunsa ya kalla tare da dan waro idanuwansa da yada'an lumshe yana kuma rike briefcase din da Lamin ya kefo masa,"au ni zan maka daukar jakkan ma"..Dariya Lamin ya saki tare da cewa "to mene amfaninku badan kumin haka kukaje d'auko ni ba".. Tab'e baki Jabeer yayi tare da cewa" sure Papa"sosai Lamin ya saki dariya tare da zagayowa ya rungume Jabeer sosai a jikinsa cikin tsananin k'auna yace"I missed you so much Buddy".bige masa hannu Jabeer yayi tare da hararansa kafin yaja hannunsa suka nufi y'an gidan...da gudu Basma da Muhibba sukayo Kansu tare da ruk'unk'uke Yaya Lamin fuskarsu ta gagara daina sakin Murmushi.sakin Hannun Lamin Jabeer yayi tare da k'arasawa wurin su Daddy yana gaishe su Dan harya fita basu had'uba...tare dasu Basma ya k'araso wurin ya duka ya gaishe da Abba da Daddy a tare suka d'agosa tare da rungumesa suna welcoming nasa,Annie ya fara gaisarwa ta washe baki tana fad'in "yauni Maryama saina taka rawa,jikana na Allah da Annabi Wanda baya cin zali ya dawo,maza ka gaishe su Dan bangarena nan ne masaukin baki".. Ta k'are maganar tana kallon Jabeer kyab'e fuska yayi duk da yasan da shi take sai yayi kamar besan ma tana yi ba.Ammi ya fara gaisawar ,sosai ta rike hannunsa tana masa sannu d zuwa kafin ya gaishe da Momy wacce tuni fara'ar fuskarta ta gushe ganin ba wurinta ya fara zuwa ba shikan gani yayi Ammi CE kusa dashi ,ciki ciki Mommy ta ansa kafin ya juya ya gaishe da Umma da Aunty Amarya yana rike da hannun Ahmad yace" nikan da sake banga Lil sis ba"..."komu nan ba mutane bane bari muyi saurin tafiya sai ka nemi wacce kaga tafi dacewa ta tareka"Mommy ta fad'a tare da juyawa ta nufi part dinta....




Comment and share
Ouhm Aryaan


*RUHIN JIKI*


_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*___________________________________*




*JORDERH MAJIDADI*




Page 7




K'asa da kai Lamin yayi yana tunani jiya i yau dai kenan,har yanzu gidan nasu na nan yarda ya barshi kenan tsawon lokaci,wannan yana d'aya daga cikin abunda yasa yake son barin k'asar kodon ya samu kwanciyar hankali da sukuni a zuciyarsa...A cikin bacci kamar ance ta tashi ta mik'e tsaye tare da yaye labulayen window na bayan d'akin Annie sosai ta waro manya-manyan idanuwanta Wanda bacci ya kuma k'ara masu girma,hannu tasa ta shafi tulin uwar sumar dake cikuikuye cikin ribbon kafin wani kyakyawan Murmushi ya sub'uce a fuskarta ji tayi ta nemi duk wani ciwo na jikinta ta rasa without second though tayi wajen bedroom din da gudu cikin sauri ta tura k'ofar part din Annie Lamin kawai idanuwanta suke gano mata tseye sukayi kowa yana kallonta cikin sauri ta rungume Lamin tana sakin wani sanyayyan murmushi cikin farin ciki tace"I missed you so much Yayana,shine baka fad'a...."sauran maganar nata ya mak'ale idanuwanta suna saukan akan kyakyawar farar fuskar Veer duk yacce yayi kicin kicin da fuska hakan be hanata hango sanyayen kyau da yayi ba,his nose,his brown shining eyes,his white teeth dake zagaye da cute lips the way he stand ,the best of all his cool walking and body structure cikin sakanni duk ta kare masa kallon nan kasancewar siririn tsakin daya saki ya wuce part dinsu zuciyarsa na cunkushewa da wani irin tsabar takaici har wani d'aci d'aci yakeji a makoshinsa yarda kasan ya soma dukan Layan haka zuciyarsa ke raya masa har sai ta daina numfashi yasan idan ya tsaya wurin komai zai iya faruwa yasa ya wuce kawai Dan yarda kasan Monster haka yake bin duk mumunar fuskarta da kallo.da sauri ya rintse idanuwansa Wanda suka soma canza launi ajiyar zuciya ya soma saukewa lokacin daya shiga d'aki yanajin all the world na masa wani irin zafi.....Da kallo Umma kebin jikin Layan da kallo takaici da kunya duk sun gama rufeta har gobe Layan batajin magana ba zata daina shiga a haka ba,kasa hakuri Umma tayi tace"ke har gobe yaushe zakiyi hankali Layan? Kin wuce kinbar wurin nan ko saina rufeki da duka a wajen nan sakarya kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login