Showing 54001 words to 55893 words out of 55893 words

Chapter 19 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt

asibiti a masa kwaje kwaje "..."Dan Allah Fatima yanzu abunda akawa yaron nan daidai ne? Ke zaki dauka idan Laya akawa?,wacece wata Ammi ni dai kawai idan wani abu ya samu jikana Mai tsananin biyayya bai taba fada na fada ba to wallahi ba yafewa zanyi ba shara'ace har gaban Allah dama waccan kodaddiyar matar tashi ta soma hada kayanta dan bam na fashewa ita da BADIYYAa sai dai su nemi wani gidajen auren"...Momy BADIYYA Kam ko bin takan kalaman Annie ma batayi ta fado parlon a rude cikin matukar tashin hankali tana kallon Lamin yarda ya koma ,lokaci daya duk ya gama fita a hayyacinsa,kuka ta sakin tare da fadin"wannan wanne irin ciwo ne ni Badiyya,Allah ka tashi kafadun yarona,aniyar kowa ta bisa,tunda aka ga yayi aure na nunawa tsara shikenan ya tsole idon kowa,innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"ta kuma fashewa da kuka tayi zaune tare da kama hannun Lamin Wanda ba'a sakawa drip ba.Girgiza kai Abba yayi cike da takaici sai dai bece komai ba,Dan yasan muddin ya bude bakinsa ba abu mai dadi zai fito ba Sam ya rasa meke shiga kan Badiyya at times ma baya gane in da ta dosa wani abu ya hadiye Mai d'aci yana mikewa yabar wajen,ganin yabar wajen Momy tace"to zaman me kuma marar lafiya irin wannan yake yi a gida? Gaskiya mu wuce da shi asibiti yaga kwararrun likitoci".tab'e baki Aunty Amarya tayi tace"sai ruwa ya kare dan Ammi ta gama dubasa komai da za'a masa kuma an gama tsarawa a asibitinta".wani irin kankance Ido Momy tayi tace"to badai jinin Badiyya ba wallahi,idan Jabeer ne wancan tabbataccen marar kunyar ta zauna tana kallonsa a wannan halin? To ni zan kai Dana asibiti dan Sam ni banma yarda da karatunta ba,haka kawai yarona yaje ya salwanta".sai lokacin Annie ta dauke kallonta daga Momy Badiyyan sannan tace"to ko Ahmadu ubansa bai isa ba bare ke kayan karere,anan Lamin zai zauna kuma anjima a kaimun shi asibitin Maryam nayi jiyyar kayana ubanda bai zuwa can shi ta dama".Daga haka ba Wanda ya kuma cewa komai,Dan Sam Momy mutuwar zaune tayi tasan tanayin ba daidai ba yanzu Annien zata fatattaketa ta hanata ganin Lamin din ma gaba daya,ita kuma ba zata iya dauka ba,the only favorite child dinta da take matukar so Yana cikin wannan halin ace bata tare da shi sai tarkacen kishiya da Sako Ina bazai yiwu ba.
*RUHIN JIKI*


_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*___________________________________*




*JORDERH MAJIDADI*






End of part 1




Tunda ya kwanta bacci bashi ya Farka ba sai wurin 12pm cikin sanyin jiki da karyewar zuciya ya tashi zuciyarsa da zantuttuka iri iri,Sam ya rasa in da ya dosa sai tuna irin bannar daya tabka wa karamar yarinyar yake yi,Sam baya son ko hada idanuwa da ita,abu daya ya sani Yana Jin wani nauyi a kasan zuciyarsa sai dai ya kasa fassara hakan da komai.cikin sanyi jiki Dana kafafu ya mike kai tsaye ya nufi kasan benen dan zuwa dubata,dakin ya shiga a hankali kwance take tayi rub da ciki da alama tayi kuka ne harta gaji baccin ya dauketa a haka ,shi kansa yayi mamakin irin zafin zazzabin dake jikinta har duvet din data rufa,tashi ta yayi tare da bata tea din daya hada cikin sanyin murya tace"zanyi fitsari"bece komai ba,be kuma kalleta ba yadai jinjina mata kai.tana safko da kafufuwanta ta saki wani wahalallan kuka tana kaiwa ta duke a wurin ,tana sauraron irin zafin azabar dake ratsata kamar ana yayyanka kasanta haka takeji,sauke ajiyar zuciya yayi Dan yasan shi kansa beje mata ta sauki ba ya mike ya dauketa cak zuwa toilet kafin ya dawo bakin kofa zaman jiranta,sai da ta karasa sanna ya dauketa zuwan gefan bed din ya zaunar da ita,kad'an tasha tea din sai drugs dinta da yake bata.cikin sanyin murya yace"ki hada kayanki a jakka Ina zuwa yanzu".be Jira cewarta ba ya koma d'akinsa kaya ya had'a a karamin jakka da duk wasu takardunsa da yasan zai bukata ko a Ina sannan ya shiga yayi wanka a gurguje cikin minti 20 ya shirya cikin kananun kaya da sukayi masifar karbarsa sosai ya fafeshe jikinsa da dad'an turarensa masu matukar kamshi da Jan hankali.jakkar ya sak'alo a kagadarsa ya safko tare da shiga dakin layan.sai dai me Taurus ya tsaya Yana karewa dakin kallo Babu kowa sai cup din daya bari a hannunta,karasa yayi cikin zuwa toilet nan ma babu komai a ciki,jakar kafadarsa ya sauke a tsakiyar dakin ,cikin natsuwarnan tasa ya fito ya dudduba ko Ina a parlo har kitchen Amma Babu Layan Babu alamarta ,kai tsaye gate ya nufo ya zagaya har backyard amma babu kowa,gateman daya kawo 2days baya ya karasa ya sama.da sauri Yana gaishesa cike da girmama,kasancewar tsohon ya Dan manyanata yasa Jabeer gaishesa kafin yace"Baba ko akwai Wanda ya fita daga gidan nan?"Jin jina kai Baba yayi cikin tabbatarwa yace"Babu Wanda ya fita Ranka ya dade,kuma tunda safiya tayi nake bakin gate din nan,amma ba Wanda ya shigo ko ya fita"sai lokacin ya soma Jin hankalinsa na tashi gaba daya yama rasa abun cewa cikin rashin kwarin jiki ya koma ciki wurin daukar jakkarsa yaga farin takarda anyi rubutu layi biyu an ajiye a gefan gado,cikin sauri ya karasa Yana saukewa rubutun manyan idanuwansa da suka soma canza launi ya kallah *kada kuce zaku matsanta da nemanta,Dan har abada tayi maku nisan da ba zaku taba ganota ba,tana tare da ni* kamar idanuwansa zasu fado haka yake kallon rubutun ko kuma zaiga layan din a ciki tuni kansa ya matukar sarawa zuciyarsa ta tsinke amma d'aya ke masa yawo a kansa shin waye ya dauki Layan?ba ansa yasa ya Saka papern a aljihu ya dauki key din motarsa ya wuce gida.kamar Wanda beson taka k'asa haka ya shiga part din Umman ya zube a kujera tun gate Yana Jin karadin Annie amma ya boye ta bayan motoci ya shigo nan ya zauna tare da dafe kansa dake barazanar tarwatsewa,yafi minti 30 sannan Umma ta fito daga bedroom dinta turus tayi ta tsaya rike da baki tace"son yaushe ka shigo? Aida kaimun magana kasan in Daddynka baya nan na shiga cikin nan nakan dade ban fito ba"Ganin har lokacin bai juyo ba kamar yarda ya Saba da yarda yake zama kamar an dasasa a wurin yasa ta karaso da sauri tana tambayarsa ko lafiya.shiru baice komai ba sai dai kansa dake kasa har lokacin ya kasa kallon Umma bare ya samu kwarin gwaiwar yi mata magana,cikin sanyin murya ta soma da fadin"kayi hakuri kaji son,komai yake faruwa ka kaddara Yana rubuce ne cikin kuncin kaddararka,wannan nuna b'acin ran da fushi babu abunda zai kawo sai wani damuwan kuma na daban".sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke ,ya rasa ta Ina zai fara shi dai Sam bai iya karya ba,kuma baya kwana kwana a magana cike da rashin kwarin gwaiwa ya mikawa Umma takardar dake hannunsa content din ciki ta karanta ta kuma maimaitawa sai kuma tace"wacece kuma son?"kasa magana yayi tare da yin kasa da kansa sai kuma a hankali yace"LAYAN ".jinjina kai Umma tayi tare da waro idanuwanta Wanda zamu iya cewa a wurinta Layan ta gado girman idanuwa sai kuma a hankali ta fara furta"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,Allahumma ajirni fi musi bati wa'akilibni Khairan minha"sai kuma ta mike tsaye tana kuma kallon papern dake hannunta cikin sanyin murya da sarewa Jabeer ya fara fadin"kiyi hakuri Ummina,kiyi hakuri Ummina na kasa rike amanarki gare ni".komawa tayi ta zauna kusa dashi ta shafa kansa tare da cewa"har Abada zuciyar Ummanka ba zata tana zarginka da kasa rike amanarta ba ,sai dai nasan akwai wani al-amari Mai girma dake niyar tunkaro mu,fatana kawai ka jure ka kuma ci gaba da kasancewa Jabeer dinka gudun magauta suyi nasara da rauninka,duk da nasan baka son Layan amma nasan ba zaka taba bada kofar cutarwarta ba Son".waya ta d'aga tayi Kiran Aunty Amarya da sanar mata abunda ke faruwa,cikin kankanin lokaci maganar ta karade gidan gaba daya har su Ummi sunji Dan a rikice ta biyo hanya iKon Allah ne kawai ya kawota gidan.......tsit parlon yake baka Jin motsin komai sai karar kukan Annie sai kuma ta saki salati da fadin"na ga rayuwa ni Maryama,naga tashin hankali ni maryama meya faru da jikata,innalillahi wa 'inna ilaihir raju'un Jabeeru duk in da ka kai Mani jikata ka fito da ita in ba haka ba hukuma ce zata rabamu"sai kuma ta fashe da kuka.cike da karfin hali Daddy yace"Annie Dan Allah kiyi hakuri kibar kuka insha Allah Babu abunda zai samu Layan,addu'arki kawai take bukata,Babu kuma abunda ya alakanta b'acewar Layan da Jabeer ,kinsan bazai taba salwantar da matarsa kuma kanwarsa ".wani irin zabura Annie tayi ta mike tace"kai dai Bukar bakaji Dadi ba,wallahi baka ji Dadi ba,Allah ya wadaran naka ya lalace Sam dama kai baka da zuciyar Imani da tausayi,bana son wata magana Abu daya nake bukata shine naya Laya cikin gidan nan,kuma daga nan wannan kaddarar auren ya kare"....Jinjina kai Ammi tayi tare da share hawayen da suka zubo mata itama ta mike tare da cewa"nima Ina bayan Annie,duk in da Jabeer ka kaimun yarinya ka maidota kafin dare idan ba haka ba kuma duk abunda kake bukata zaka samu,zaka samu b'acin ran da baka taba tunani ba wallahi"cak Annie ta tsaya da kukan da takeyi sai kuma tace"ke Maryam ya haka? Karki Saka mun jika a haki,kowa dai yaci kansa Allah na tare da jikana,Ina zaikai wannan yarinyar da kowa zai Saka mun shi gaba"kai tsaye Annie ta kama hannun Jabeer ta mike ta wuce da shi tana banbami da fada.Girgiza kai Abba yayi tare da anbaton"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,I don't know what to do "...share hawaye Umma tayi cike da karfin hali tace"idan duk kuka zargi Jabeer to kuma tantama da irin tarbiyar Dana basa kenan,Jabeer bazai taba cutar da Layan ba ni nayi Imani da hakan,sai dai a bincika wani wurin,tabbas akwai abunda ba daidai ba,Amma Dan Allah kada ku zargi yarona akan abunda bashi ya aikata ba"tana kaiwa nan ta mike tabar masu parlon...ajiyar zuciya Ummi ta sauke tare da cewa"ya kamata dai mu Sako hukuma a ciki,danni kaina ban yarda Jabeer zaiyiwa Layan wani abunba kuma....bayan wani lokaci....gaba daya duk in da ake Saka rai na ganin Layan babu ita babu alamarta,gaba daya rayuwa ta gama canzawa a gidan ta maye gurbin da tashin hankali da dunbin damuwa da kowa ya kasance a ciki sabanin Momy Badiyya da kowa ya kasa gane in da ta dosa Dan ko a kwalarta a cewarta ma a daina damunsu yarinya ta tafi yawon ta zubar dinta amma azo a wani damu mutane,ko kuma a bincike mijin nata Shi yasan in da ya kaita Dan wannan uwar dukiya da yake da ita ma ai abun a bincika ce,sai da Annie ta mata wankin babban bargo sannan aka Dan samu saukin habaice habaicen da takeyi.......






*To jama'a ku biyo ni danjin ya zata kasance,shin menene makomar Jabeer? Ina Layan?shin Lamin zai tsallake daga ciwan daya damesa? Shin menene fassarar maganganun Momy Badiyya? Shin ya rayuwar Ammi zata kasance Babu yarta a kusa da ita,kudai ku biyo ni domin Jin ya zata kasance,insha Allah bada jimawa ba zamu saki sauran kuma a complete dinsa idan yayi ready zan sanar maku sai dai part 2 din na kudi ne akan naira 300 kacal ki biya Kisha karatu lafiya cike da kwanciyar hankali.07033636337 ku biyo ni danjin ya zata kasance.*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login