Showing 9001 words to 12000 words out of 55893 words

Chapter 4 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt

har abada banga ranar da zaki daina shirme ba a haka kullun girma kike k'ara yi,look at your body"....k'ank'ance ido Annie tayi tare da cewa"A'a Fatima inma na maki Allah ya isa to tsab ta zauna,wannan wacce irin rayuwa ce? Ace y'ar daka haifa ma ba zakayi mata magana cikin salama da kwanciyar hankali ba? A'a tunda nake wallahi,dole na tashi tsaye na shiga malamai badai boka ba danni ba ruwana da sabon Allah wallahi,amma dole a nemo kaikayi koma kan mashekiya ko kin sawa ranki salama ki daina gantalewa ki rike y'arki da zuciya d'aya".tura baki gaba Layan tayi tana k'arewa jikinta kallo,long robber trouser ne a jikinta sai rigar har rabin cinyarta mai hannun vest amma shine Umma take complain akan shigarta to itakam batasan me zana sakawa ba ,kallon da Umma ta kuma binta dashi yasa ta juya zata bar wujen.Abba yace"zo mamana! "Sannan ya juya ga Umma yace" Ayi hakuri Hajiya faty nasan bata San da dawowar Yayanta ba aida ta shirya tunda wuri"k'asa Umma tayi da kanga sai yanzu kuma wata irin kunya ta rufeta takaicin Layan ne ta kasa d'auka har ya sakata yin magana,a hankali ta zame tabar wurin.Mommy Badiyya dake can gaban Apartment dinsu tayi mutuwar tsaye ganin irin rungumar da Layan tayiwa Lamin takaici kunci duk sun gama kasheta a wurin.she's just helpless kawai taja tsaki kamar zata tsinke harshenta ta shige ciki kamar zata tashi sama......b'ararrajewa yayi a parlor yana kwasar hadaddiyar miyar zogale da Masan da Annie tayi masa da kanta wacce tasha manshanu sai zuba kamshi takeyi,tare sukeci da Layan yayin da Annie ke gefe hannunta rike da robar man shanun tana kora masa bayani na komai ke faruwa a gidan ko abu d'aya bata iya ta b'oye ba...tura baki Layan tayi tace"ke Annie duk yaushe Yaya Veer din yamin haka? Ke komai yayi ni gaskiya bana son kina mun wannan abun,in ma ya daka ai ni dolensa ce kuma komai zai mun ba Wanda zaice danmi"...wani kallo Annie ta bita dashi sannan cikin takaici tace"tashi ki fita,in dai Jabiru ne gaki gashi,ina nan zaki zo ki sameni,yarinya kamar kun had'a dangi da mayu,ina amfanin duniya ka so Wanda baya sonka? Ranar da zai maki dukan mutuwa ki dawo babu ruwan Mairo ,in dai na haihu na gama shiga tsakaninki da wancan labcecen marar imanin tashi tashi kada nima zunubi ya shafeni kibar gidan nan,tunda ba waccan figaggiyar ta ginamun shi ba,gaki nan kin kwaso rashin auki kina tafiya kamar iska zai kwashe"...sosai Lamin ya fad'ad'a fuskarsa da fara'a yace"a'a Annie ba ayi haka ba,in dai Layan ce ke da kanki zakije biko".."meye wata Laya? Na had'a me da ita banda na haifi Abubakar".murgud'a baki Layan tayi yare da mikewa ta fice tabar d'akin...k'asa k'asa Annie tayi da murya tace"to ko ni fa,na samu na korata da kyar kullun saita shanyemun fura yanzu meye amfanin haka."Dariya kawai Lamin yayi ya tashi ya tafi part dinsu,da sallama ya shiga parlon Mama Badiyya ba kowa sai Muhibba da Ahmad dake game a tab.Da gudu Ahmad yaje ya rungumesa yana kuma masa oyoyo,shafa kansa yayi yana jin dadin samun kowa da yayi lafiya kafin ya kalli Muhibna tare da ansa sannun da take masa yace "ina Mommy?" "Tana bedroom yanzu ta dawo daga wurin Abba"... Bece komai ba ya wuce tura k'ofan yayi tare da sallama ya shiga ya zauna a gefen bed,sai da ta gama wayan da take yi sannan ta juyo ta kallesa cikin tsabar takaici tace"sai yanzu kayi lokacinmu Alhaji? Na dauka ai kana can wurin ita uwar taka,ko ka taba ganin Jabeer yayi tafiya ya sauka a bangaren nan,sai kai da baka San kishin mahaifiyarka ba anya Lamin,anya dai rayuwa zataje a haka,to bari kaji wannan karon a shirye nake da kai duk wani abu da kasan kanayi billah wannan karon bazan dauka ba ,ka gama daukata y'ar banza ,kaji yarda ka tsaya yarinyar can sauran cuta ta wani makalkaleka ko kunya bakaji ba,to inma kana da intention na wani abu na fada maka tun wuri ka tsayar dashi dan zanyi mugun sab'a maka wallahi zanga ko Fatiman ko Maryam ciki idan akwai Wanda yamun goyon cikinka ko nak'udarka". K'asa da kai Lamin yayi yasan komai zai fad'a mata ba zata tab'a yarda dashi ba, in fact ya gaji da duk wannan issue's din yana son hutu da kwanciyar hankali cikin cool voice yace"kiyi hakuri Mommy insha Allah zan kiyaye"."yadai fi maka,zakaci abinci ko shima an hanaka kaci?".murmushi kawai yayi tare da cewa"babu abunda zai hanani cin dad'an girkin Mamana nayi kewarsa sosai zanci komai kika bani Mommyna".ya k'arashe zancen yana rike hannayenta,murmushin itama tayi sannan suka fito zuwa dining ta fara loda masa abubuwan data dafa da hannunta domin shi,Dan duk yaranta Allah ya daura mata matukar son Lamin bata iya jure komai a kansa bare kuma har ace tayi fushi da shi....."I beg live me ka dawo zaka cika mun kunne".janye duvet din da Jabeer ya rufa Lamin yayi cikin tsokana yace"malam dallah tashi kazo ka mana kwance ga Miemie tana ta kiranka".mikewa sosai Jabeer yayi tare da dafe kansa yace"Ya Allah,,Lamin ko baka da d'aki a gidan nan ne?".Murmushi ya sakar masa tare da cewa"ina da,amma nazo maka labarin matanka ne".sound seriously Jabeer yace'tashi ka fita"."au labarin Miemie da husna ne baka so".pillows dake kusa dashi ya jefawa Lamin kafin ya kwanta tare da rufe idanuwansa yana jin kansa na barazanar tarwatsewa lallai dole kuwa yayi saukon komawa aiki bazai iya kwasar takaicin Lamin ba.Dariya sosai Lamin ya shek'e da kafin ya fita yana tsokanarshi......




Comment and share
Ouhm Aryaan.


*RUHIN JIKI*


_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*___________________________________*




*JORDERH MAJIDADI*






Page 8


Dedicated to Nasrullah.




Da kallo kawai Ammi ta bita har tazo ta wuce zuwa bedroom dinta,tsaye tayi tana kallon Basma da Muhibba dake zaune a bed suna sakin shewa da alama labari sukeyi.shiga tayi tare da jan pillow ta kwanta tana kallon sama ba tare data kulata ba..."yauma an dab'a ko? Har abada ba zaku daina wannan rigiman ba Idan zaki sakawa zuciyarki salama k'arama ki saka mata,ki fita daga hanyar Yaaya Veer wallahi tun kafin wahala ta kaiki kushewa"Basma ta k'are maganan tana kallon Layan...sanyayyar ajiyar zuciya ta saki tana mayar da kallonta akan Muhibba data d'auka da cewa"nima dai kullun na fad'a mata amma yarda kika San kullun k'ara ingizata akeyi,ni nama rasa wannan tsana ta menene marar dalili Sam bansan asalinta ba bare mafari,to k'arama ki sawa ranki salama".wani murmushin takaici Layan ta saki tare da mikewa zaune tana k'are masu kallon da manya manyan idanuwanta duk su biyun cikin cushewar murya tace"lallai har yanzu Baku san menene so ba,kiyayya bata hana kaso Wanda kake so,haka Allah ya k'addaramun shi ya sanyamun soyayyar Yaya Veer a jinina da duk wani b'argo na jikina,duk ranar da kuka ga na daina san shi to kusanya a ranar duk wata jijiya ta jikina ta daina aiki,a ranar zuciyata ta dainawa gangar jikina aiki,kuma tabbas a ranar ranar raina yayi bankwana da gangar jikina,Dan haka Ku daina wahalar da bakinku Dan ko kasheni yaya Veer zaiyi wallahi bazan tab'a daina sonsa da son kasancewa tare da shi ba."tana kaiwa nan tasa hannu tare da share hawayen daya soma bin fuskarta ta mike da sauri ta wuce zuwa toilet tare da bude fanfo tana sakin wani kuka Wanda bata san dalilin zuwansa ba,itadai wani kewa da k'unci kawai takeji yana taso mata kawai tana jinta she's not complete, ba kuma tasan abunda zai iya cike mata wannan gurbin ba.....sanyayyar ajiyar zuciya Ammi ta sauke wacce ke tsaye kofar bedroom din na Layan tun shigowarta ta mara mata baya amma ta tsaya danjin abunda suke tattaunawa.hannu tasa ta shafi fuskarta tana zancen zuci lallai akwai sauran aiki a gabansu tun Layan tana 2years da ance waye takeso zatace Jabeer kowa yana dauka shirmenta ne da kuma irin yarda take son shige masa ashe abun babba ne har yanzu akwaishi har haka,lallai wankin hula yana Neman kaisu dare,duk muguntar da Veer yakewa Layan tun tana mitsitsiyarta hakan besa ta tab'a gudunsa ba har Allah yasa ta mallaki hankalin kanta......bedroom din ta tura tare da kare masa kallo kwance yake rubda ciki idanuwansa a lumshe kamar mai bacci sai dai tasan ba baccin yakeyi ba yana jinta,sanyayyan kamshi ne kawai ke tashi a d'akin ga ko ina Need kamar d'akin mace,sanye yake da white 3quater sai white singlet da alama hutawa yakeyi,k'arasa shiga d'akin tayi tare da saka hannu ta tab'a gadon bayansa.A hankali ya soma bud'e idonsa kafin ya idasa waresu gaba d'aya akan Ammi wacce tadan sunkuya a gabansa...d'an sakin fuskarsa yayi kamar yayi murmushi cikin Cool voice yace"Ammiiiina aida kin aika nazo".ya kare zancen yana gyara xama kusa da ita a gefan bed...tsura masa ido tayi kamar mai son karanto wani abu ,sunkuyar da kansa yayi sai kuma yace"ki gafarceni Ammi in ma wani wani laifi a sani na ko akasin haka,ina neman yafiyarki kuma insha Allah na za'a sake ba"...kama hannuwansa duk su biyun Ammi tayi tare da kallonsa cikin ido tace"ko kusa Jabeer ,babu abunda kamun komai na umarceka kana kokarin yimun biyayya akansa sai dai akan abu d'aya Wanda na kasa tankwara zuciyarka a kai kuma kasa kasa yimun biyayya akai why?"...kallonta kawai yayi tare da sauke ajiyar zuciya yace"what's it is Ammi".Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace"Akan y'ata Layan Jabeer".Dandanan dan sakin fuskar da yayi ta gushe yarda kika san an aiko masa da sakon mutuwa lokaci d'aya hannuwansa ya zare daga rikon da Ammi ta masa tare da shafa fuskarsa amma bece komai ba."menene dalilinka na tsanar Layan? Meta aikata maka har haka Jabeer? Layan fa jininka ce yar wa'anda suka reneka suka daukeka tamkar Dan da suka haifa,Daddynta ya hanaka kukan rashin mahaifi Jabeer amma meyasa kiyayyarka ta bayyana akan y'arsu kwara daya tilo Wanda nasan sai dai suyi maka kawaici akai Veer"Ammi ta k'are maganar...Runtse idanuwansa yayi tare da cewa"Ammina Dan Darajar Allah ki daina ambatamun sunanta a nan,bana son ji,ni bana da wani dalili kawai I hate her with passion nothing more nothing less,kawai bana sonta a al-amurana ne"..."Amma kasan wannan ba d'abi'ar musulmi na kawarai bane? Kuma ba shine tarbiyar daka samu ba?"."yes I know" ya katse Ammi Wanda da alama zuciyarsa harta soma hawa Wanda daba Ammi bace a gabansa da yanzu wani zancen ake ba wannan ba"sannan yaci gaba da cewa"kiyi hakuri bazan iya son abunda na taso da kiyayyarsa bane tun asali ,bazan iya tursasa zuciyata ba".daga haka kuma yayi shiru,duk maganar da Ammi keyi beko d'ago kai ba bare tasa ran zai ansata,tasan kuma bazai kuma yin maganar ba,in dai akan wannan maganarne itace ma yake Dan tsayawa yana yiwa doguwar magana haka sai kuma Lamin,so da dama tana binsa ta zafi zafi ko ruwan sanyi ko wa'azi amma hakan bata tab'a sauya zani ba in dai akan lamarin Layan ne.shiru itama tayi ta kallesa tare da tashi kuma ta fita ta bar masa d'akin..kusan cin karo sukayi da Momy Badiyya dake rike da womer da alama kuma d'akin Dan lelen nata Lamin ta nufa,cikin ko in kula Ammi tace" barka da gida".A dakile kamar wacce akawa Dole Momy tace" sannu,nace kuma sintiri ya kamaki a part din nan ne ko kinyi ajiya ne?,a iya sanin kowa dai bakya zuwa nan,ko wancan d'an naki agola kafi Dan masu gida daya gagari kowa bakya zuwa wurinsa sai dai ya iskeki to kuma yau zuwan na menene?"....Murmushi kawai Ammi tayi dan ita bata shakkar kowa sai dai Momy tana cin albarkacin Dan uwanta nodding kai kawai tayi tace "kya iya shiga ki duba".sannan tabi ta gefanta ta wuce.Mommy tsaye tayi bata bita ba dan sarai tasan wacece Maryam bata daukar warkinta yanzu tayi mata kaca-kaca ta kama gabanta kuma Annie ta daure mata k'ugu kwafa tayi ta wuce ciki fuuuu tana kwala kiran sunan Lamin.jin shiru yasa ta wangale kofar bedroom dinsa amma wayam b'ab'atun da takeyi yasa Jafar ,Hydar duk fitowa daga d'akinsu Hydar yana cewa" Momy lafiya?"ko kallonsa batayi ba ta wangame d'akin Jabeer lallai ilaika kuma anan ta samu Lamin tsaye a kan Jabeer dake zaune ya dafe Kansa da hannuwansa,karasowa ciki tayi tare da cewa"me Maryam tazo yi wurin nan?"kallonta yayi sai kuma yace"Layan?" Wani banzan kallo ta watsa masa tace"zanci k'aniyarka a wajen nan Lamin mecece wata Layan,Maman wannan nake magana"ta k'are zancen tana nuna Jabeer da hannu.Girgiza kai kawai Lamin yayi tare da cewa"to ai ni banma san Ammi ta shigo nan ba"...hanya ta nuna masa,ganin baida niyar wucewa tace"dan kaza kazanka zo wuce,Wanda besan ciwan Kansa,Maryam da abunda ta haifa har abun sone ? Ta dalilinta har saki saida na samu a gidannan amma kullun kana gindinsu".....Annie dake tsaye bakin k'ofa tayi wata kwafa tare da cewa"tabdi jannan Ahmadu ya auro masifa a wannan Family"ta kare zancen tare da jinjina kai sannan ta ajiye basket din data ciko da kuloli sannan ta kalli Mommy tace"wallahi Badiyya idan baki canza hali ba zan nuna maki nima y'ar banza nake,kinsan zanyi maganinki me akayi akayi wata Badiyya da zaki zo ki b'ata mana Family kin cinye komai kin tada komar kin koma kamar tsohon buhun masara to wallahi ahir dinki da rabamun jikoki,maza zo kibar wurin nan kafin inyi da Wanda ya ajiyeki danni nafi karfinki kin sani"....Takaici yasa Momy barin dakin da sauri kamar zuciyarta zata buga dan takaici......






Comment and share
Ouhm Aryaan
RUHIN JIKI*


_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*___________________________________*




*JORDERH MAJIDADI*






Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Eu8jhXno1XdCkcuKbtprEg




Page 9




Tsab tsab ta fito cikin shigar Doguwar riga na material mai budad'en wuya sosai rigan ya zauna a siririn jikinta ga fuskarta data kuma yin fayau sai daukar ido takeyi,mini hijab ta saka white tare da dauko lab coat dinta da school back ta dauko eye glasses dinta kenan ta juyo suka kusa cin karo da Muhibba,"Malama yada shigowa ba izini haka sora kad'an na zunduma da gudu ".tab'e baki Muhibba tayi tare da cewa" to inafa zan tsaya daukar izini aina dauka kina nan kina bitar karatun da babu ranar bada haddarsa bare kuma a samu riba,shiyasa nazo tashinki dan kada kiyi latti muma ki janyo mana,dan Basma tana da CA yau".kallonta kawai Layan tayi cikin cool voice tace" to naji".ta k'are zancen tare da daure fuska.murmushi Muhibba tayi tare da karbe school bag din nata tace"haba y'ar Abba ina mai bada hakuri,ke kanki kinsan takaicin sakamakon ki a lamarin nan ne yake kuma lassala ni nake neman maki mafita".wani murmushi mai wuyar fassara Layan tayi kafin ta zuba dara-daran kyawawan idanuwanta akan Muhibba kafin tace"in dai hubb'a sanki na neman rabani da Yayane kada Allah ya nuna mun ranar wannan taimakon naki,several time ,day and night zanci gaba da fad'a maku babu abunda zai iya rabani da soyayyar Yaya Veer sai dai mutuwa! Ranar da numfashina zai bar gangar jikina to ina mai tabbatar tafi, bankwana da jikin.,ina matukar sonsa idan ina tare dashi ko ina kusa da inda yake kawai nake samun natsuwa,kuma ina addu'ar Allah ya nuna mun ranar da Yaya Veer xai fahimci irin abunda yake damuna harya tallafe ni"...."you serious y'an mata? You mean kina jiran wannan ranar ne? To idan kin manta bara na tura maki Yaya Jabeer shine mutumin da besan menene shauki ko soyayya ba,shine mutumin da baisan ya akeji dan ganne da alak'a ta jini bama bare soyayya,dama kin tuba ko me zakiyu bazan gaji da fada maki gaskiya ba kuma dan ni na fiki jin zafin abunda ke faruwa da ke,kuma zanta rokon Allah ya yaye maki"Basma tare maganar wacce shigowarta kenan....tunda ta taho ya k'ureta da idanuwa hankalinsa gaba d'aya ya gama komawa kanta duk wata natsuwa ta gama kaura daga gangar jikinsa,takunta yake kallo yacce kasan d'awaisu na rangaji haka Layan ke doso su Wanda tun kafin ta ido turarenta ya sanar dasu zuwanta,a hankali cikin kasaita tana tafiya cikin nutsuwar nan nata wacce ba kowa ke fahimtar tana da wannan sirin ba...wani irin kyau haka yake ganin kullun tana k'arawa a idanuwansa,Momy Badiyya data dauki Irish zata saka a baki ta buga fork din da table tana dan gyaran murya,cikin sanyi Lamin ya dauke idanuwansa Wanda harsun soma canza launi ya lumshesu a hankali tare da shafa tulin sumar kansa cikin zuciyarsa yana fadin "*Allah Kaine Allah,Allah kaima jarabeni da soyayyar Layan a raina, Ya Allah Kaine buwayi gagara misali ina rokonka daka nuna ikonka ka mallakamun Layan a matsayin matata kuma mafakar sirina!*"...Fuskarta kawace ta murmushi ta k'araso kusa da Abba tare da dukawa tace"Abbana ina kwana". Hannunta ya kama ya d'agota tare da fadin" lafiya lau Mamana ,kin tashi lafiya".k'asa tayi da kanta tare da cewa "Alhmdllh"." Me kuma ya had'aki da Annie yar gidan Annie yau tun asuba take mitar kwana biyu yau baki shigo ba"..tura d'an karamin hakinta tayi Wanda yasha ado da white lipglose "Abba ai korata tayi " Dariya kawai Abba yayi be kuma cewa komai ya yaci gaba da cin abincinsa.kallonta ta matar wurin Momy da Aunty Amarya ta gaishe su Wanda Momy da kyar ta iya ansa gaisuwar shima ganin Abba yana wurin...bayan kujeran Lamin ta koma tare da daura hamnuwanta akan kafadunsa tana fadin"Good morning"...wani irin sanyi da natsuwa suka dirar masa lokaci d'aya cikin cool voice dinsa mai dadin sauraro yace"sai yanzu kika ganni?"shagwabe fuska tayi kamar zatayi kuka ta saka hannayenta duk biyun ta kama kunnuwanta alaman ban hakuri sannan ta kwashi jakanta ta baza da gudu.besan sanda murmushi ya subuce masa ba ,sai kuma ya kawar da kai.....Tsaye yayi yana karewa Annie kallo zaune a can edge na kujera hannunta da carbaha hawaye ne ke fita a idanuwanta sai kib-kibta ido takeyi taba kallon Jabeer daya ki cewa komai yana pressing phone as if babu shi a parlon.wani kwafan bosawa Annie ta kuma yi tana had'a ido kuma da Lamin sai ta fashe da kuka.da sauri Lamin ya karasa ciki yana tambayar lafiya,gefan zani Annie tasa ta goge hawayenta tace"dama ka rabani da Jabiru babu abunda na had'a dashi,dole ma yabar mun d'akina tunda babu abunda na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login