Showing 36001 words to 39000 words out of 55893 words
Chapter 13 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt
kawai yayi,sanin halinsa yasa bata ja da tsayi ba tace"muje kaje kayi wanka sai ka fito kaci abinci".bin bayanta yayi zuwa parlon basu samu kowa ba hakan yasa ya fice daga wurin....hawaye take matsa kallonta Ammi tayi tace"bana son sakarci ki tsaya naga hannun ko kinji ciwo a wani waje,a ina kika fad'in?".k'ibk'ibta ido tayi kafin tace "a d'akin Umma ne ina saka turaren wuta"... " sai kuma aka ce ba zaki natsu kiyi abu a hankali ba ko Daughter yanzu kiji kukan da kike yi kin bige hannu".Sallamar Jabeer yasa Ammi yin shiru tana binsa da kallo sai kuma ta girgiza kai tana had'e fuska tace"kai kuma daga ina? Daga zuwanka harka illata mun y'a Jabeer? ".cikin sauri Layan ta daga ido tare da cewa" Ammi bafa shi bane,faduwa nay.....".kin rufamun baki ko sai hakoranki sun zubo a nan wajen ,tunda ke baki san ciwan kanki ba,to duk a tare zan hadaku nayi maganinku".Da kallo kawai Jabeer yabi Ammi sai kuma yace"itace tace naji mata ciwo Ammi"...."Jabeer wallahi idan baka fita idona ba zanyi maganinka a gidan nan waye besan muguntarka ba? To wallahi kayi na farko kayi na karshe in ba haka ba zaka hadu da b'acin raina bana wasa ba,na gaji da wannan halin naka marar tushe".Sunbure baki Layan tayi kamar ta fasa ihu haka takeji Ammi ta kalleta fuska a daure tace"nawa Babanki magana ranki ya baci ko Maryam? To tashi fita mun a d'aki dukanku bana bukatarku a nan,ranar da kika fara amincewa da zalincin Jabeer a kanki kyace na fada maki"..turo bakinta tayi gaba ta tashi ta wuce d'akinta dake part din.."Ammi tasan ko zasu kwana a nan bazai fada abunda ya hadasu ba,kasa yayi da murya yace "Good afternoon".. Shiru tayi sai kuma tace" Afternoon,look Jabeer this should be my last warning going to you ,daga yau har a daura auren gidan nan bana son wani abu ya hadaka da Layan,billah duk idan ka kuma dukanta ko wani abu haka kasan ni kayiwa,kuma zanyi Fushin da ban tabayi da kai ba,you can leave "..kasa yayi da kansa sai dai bece komai ba ya tashi a fita a part din yana jin dama bezo yau din ba,daga zuwanshi akan yarinyar can an fara damun rayuwarsa...kallonsa sama har kasa Momy tayi kafin ta fara tafa hannuwa tace" Jabeer yanzu harka shigo gidan nan amma sai ka gaba zagaye ko ina mu bamu samu darajar da zaka iya shiga ka gaishe mu ba? Waye babba a gidan nan? Kazo kayi zaune labcece gidan mutane amma gaishe mu ya gagareka?"Shidai bedai ce komai ba kamar bazai kulata ba sai yace"ina wuni"kallon sama da k'asa ta masa a tsawace tace"ban wuni ba,ban wuni ba nace Jabeer,dama ai ba tarbiya ta ishi maryam din ba bare kuma kai ta dauraka a in da ya dace".Runtse idanuwansa yayi da sauri da suka soma canza launi ,sunan Lamin kawai yake masa yawo a kai yasa kawai ya gitta Mommy ya wuce bece komai ba,wannan aibata masa mahaifiya da takeyi duk yana daya daga cikin abubuwan dake hanasa zuwa gidan gaba daya baya tunanin bayan auren Lamin zai kuma dawowa gidan da wuri,waya ta ishesa ya gaishe da kowa in ba haka ba zai iya canza zuciyarsa ya aikata abunda kowa zai iya dana sani.tsaki yaja tare da buka kofar dakinsu daya shiga yasan zai samu dakinsa yarda yake so matsawar Umma na rayuwa a cikin gidan,bata barin d'akinsa ko Abincinsa a hannun wani,yana shiga ya murzawa kofar nashi key,wani Dadden kamshi ya ziyarci hancinsa ya lumshe idanuwansa ya bude ko boot dinsa bai cire ba ya fada akan lausasan bed dinsa da yasha sabon bedsheet kamar wani d'akin mace ya lumshe ido yana jin zuciyarsa na sauka a hankali a hankali
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
29
*Masoya ina bada hakuri ,to gashi dai Jorderh ta dawo akan makamar aiki insha Allah cikin kwanakin kad'an zamu karasa ayi hakuri da uzururikan da suka sha gabana,na gode maku da jimurin bibiyata,masu waya masu text duka ina godiya can't luv u less Allah yabar tare,yau dai inji ruwan comments ta ko ina su tashi kaina,nasan kuma page din zai kayatar daku kamar yarda aka saba.*
Hangangan haka Annie ta wake kofar dakin Jabeer tana wani kyab'e baki kamar taga kashi a d'akin kafin ta saka kai tana rabka sallama.Jabeer dake kwance har lokacin be tashi ba tun shigowarsa gidan ya ware manya manyan idanuwansa da sauri kasancewar ciwan kan dake damunsa,akan Annie ya sauke idanuwansa sai dai ya kasa cewa komai sai binta da kallo yake,Annie tace"to tashi Allah ya kamaka yanzu Jabeeru ni,ni nan ni Maryama dana haifi uwarka naci fitsarinka naci shegen kashinka mai doyi ni ka gagara shiga ka fad'awa dawowanka gidan nan? Akwai ubanda ya rainan mun kai ko ya haifa mun maryama din,kul na haneka to ko marigayi Allah jikansa Sadeequ ko kara na ajiye baya tsallakawa ba ruwana bare kuma na masa sharri,amma yau d'aya samb'al ka labce a d'aki,to ko dai bak'in halinka yasa an koroka daga aikin sojan ne mu shiga ukku?"...A hankali Jabeer ya mike zaune cikin sanyin murya yace"kinzo kin cika mun kunne ina bacci,lafiya?"...wani gwalo ido Annie tayi kafin tace"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,harda rashin kunya ka koyo a wannan karon to nace uwarka ke cika kunne badai ni ba,wallahi Jabeeru kasan nasan kan tsiya daidai da kowa nake".Murmushi kawai yayi ya mike ya sofa rage uniform din jikinsa,kyabe baki Annie tayi ta fice tana sababi,duk yarda Lamin zuciyarsa ke a cunkushe days din nan da kunci amma dariya yakeyi harda kwanciya da rike ciki kan tsiyar da Annie tawa Jabeer,tsaye Jabeer yayi kamar wani statue sai kuma yace "kilan baka da lafiya ko?". Wani dariyan ne ya kuma tunkuro Lamin yace" wallahi kai zan cewa marar lafiya,anya Jabeer basai na dubaka ba,ba maka duban k'wak'wab at 32 ace ko budurwa baka taba yi ba? Baka ma maganar aure,dole na duba ko mata maza ne".wani wawan suka Jabeer ya kawowa Lamin da sauri ya goce yace"tabdi waye xai tsaya ka masa wannan dukan naku na mararsa imani? The great barrister zakawa wannan cin fuskar? Kuma ai gaskiya na fada zanwa Annie bayani dallah dallah a bin cika mana kai,kasan ko gidan redio albarka"yana kaiwa nan ganin Jabeer yayo kansa yasa yayi waje da gudu yana kuma sakin dariyar daya Dade beyita ba,wayarsa ce ta fara ringing ya Ciro daga aljihu ya duba ganin sunan Ihsan yasa ya dauka,yana daga wayan tace"Lamin gaskiya na gaji da wannan walakancin da kake mun,tun karfe nawa mukace zamu fita amma har yanzu ban ganka ba,ko su kawayen nawa basu da darajar da zan gayyacesu ne? Kuma kasan ina neman bazaiyiwu kace wai aurenmu ba za'ayi shagalin komai ba sai kace zan auri liman? As big as I I'm sam ka canza tunani,saboda kaga na nace sai kai amma bai cancanta na rika samun out comes daga wurinka irin haka ba haba Lamin".sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke, shikam har ya gaji da complain na Ihsan sam komai nata a baki yake kamar tana jira"look Ihsan,ni bana bukatan yin komai a aurena,idan zakiyi ban hanaki ba amma count me out dan bazanje ba,ki fada ko nawa kike so zan tura maki ki shirya,maganan fita kuma ina da wani uzirin ne Driver xai zo ya same ki kuje"be jira cewarta bama ya kashe wayan shi dan yasan karshen zancen wani ihun ne zata kuma tarara masa a kunne.......kansa a sunkuye bedaice komai ba Ummi tace"yau naga lalata Jabeer in tambayeka kuma kamun shiru?".kallon Ummi kuma yayi can dai harta fidda ran zai amsa yace"nifa bata mun komai ba,Allah ne kawai be hada jininmu ba".."amma ai ya hadu dana iyayenta ko?,ko kunya bakaji ko yaushe kana manne dasu,sun tsaya maka kai da fata ,baka taba kukan maraici ba,amma y'arsu ta gagareka kulawa,dazun nan Amminka ke fadamun abunda kawai yarinya a hannu kuma a cikin parlon uwarta,anya Jabeer rayuwa zata tafi a haka kuwa? Anya kawa kanka adalci kuwa? ,Jabeer ina guje maka ranar dana sani ranar da zakayi kuka babu mai taimakawa,ranar da zaka so wata ta soka ta taimaka maka kamar Layan din amma babu ,kayiwa kanka adalci ka sassauta zuciyarka ka daina kuntatawa yarinyar nan,so ba karya bene,in kana tunanin Allah ya daura maka kiyayyarta kuma kana jin ba zaka iya dainawa ba,to itama ka tausayeta Allah ne ya jarabceta da sonka kuma har abada tana backing dinka tana bukatar damar rike hannayenka kuyi tafiya da zama na har abada,kuma zaka ce na fada maka wannan even when k'asa ta rufe idona Jabeer "Da sauri ya dago kansa ya dubi Ummi sai dai bece komai ba,maganganun ma ji yayi sun ishesa baya son ji ya juya yace" zanje na gaishe da Hajja"..."Allah ya tsare idan kaje ka gaishe ta,kuma baka mun maganar hutun naka ba" .phones dinsa yake kwasa yace"na dauka kamar yarda kika ce amma sati biyu dai na samu saboda wani aiki da yake tunkaromu"..."Allah yasa hakan shine mafi alkhairi ka gaishe da Hajjan"...sallama sukayi kafin ya fita ya wuce gidan Hajja a mota yana tunanin what's so special about Monster da kowa ke nanan da ita,shidai yasan banda hauka rawar kai da rashin natsuwa da mugunta bata da wasu nagartattun halaye bayan wannan,to shi ina ruwansa da ita ko harkarta baya ma shiga,ko abu ya mata to ita ta kawo kanta,saboda kyamar zama da ita da yakeyi ma yasa sam baya son zuwa gidan ,sirirn tsaki yaja a fili yace"ya bakin fuskarta ya bakin halinta,stupid gal"A haka ya shiga gidan Hajjan tuni ya manta duk wani damuwa da bacin rai daya kwaso,lallai zaici gaba da addu'a Allah ya dube shi ya karawa Hajja lafiya da tsawon kwana dan Hajja wani bangone garesa abun jingina....."Ban gane kace harda su Maryam za'aje kai lefe ba Yallabai?saboda ni bani ga kowa? Duk yan uwana da kawayen nawa sai suyi zuru,ina da wa'anda zasu kai basai sun bisu ba gaskiya"Mummy Badiyya ta kare zancen da alamun b'acin rai a tattare da ita...kallonta kawai Abba yayi da kausashiyar murya yace"Badiyya let me send this warning to you,daga yau na kara yanke magana kika ja da ni zakiyi mamaki na,kinsan kuma bana magana biyu,ki kuma gwadani kiga idan ban juya wannan auren da kikewa ba,lefe Maryam da Amarya da Sadiya su shirya su kai ya isa bana son gayya".yana zuwa nan ya sauki eye glasses dinsa ya saka ya soma karatun jaridar shi.har wani shidewa Mummy takeyi dan takaici tace"zasuje da kawayena su biyu,ba zasuji dadi ba dan harna sanar dasu tun farko,ni bansan meyasa komai zan fada zakace neyi ba,alhali da ba haka kake mun ba".Abba dai bece komai ba can dai yace'ina so in huta ki rufemun kofar".be jira cewarta ba ya kwashi tarkacen shi yayi bedroom da takaicin Mommy Badiyya cike a rai yana tunanin ko yaushe zata girma har tayi hankali
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
30
Murmushi kawai Daddy yayi yace"to why not ka barta ta saka wa'anda take so su kai lefan Yaya? Kasan maryam ma ba son shiga sabgoginta take ba tun ba yau ba,ba wani abun zaka duba ba kuma illa dan ayi hidimar nan lafiya a kare lafiya tashin hankalin ba dadi"."bawai naki bane Sadeeq abubuwan Badiyya sun fara mun yawa ne a gidan nan,kullun idan ana biyeta har yaushe zata san ta girma?,beside ma auren nan gaba daya itafa ta takurawa yaron nan sai anyi shi ina ake haka fisabilillahi"...jinjina kai Daddy ya kuma yi yana kallon Yayan nashi yace "da dai anyi hakan Allah ya rufa asiri insha Allah komai zai wuce ". Da ameen kawai Abba ya ansa bai kuma cewa komai ba kuwa ya tashi yabar parlon dan yana da in da zaije Daddyn ya tsayar dashi akan maganar kuma yasan kararsa Momy Badiyyan zata kai ba ko kunya kuma a wurin kaninsa,shikan yaga ranar da Badiyya zatayi hankali tana girma tana cin kasa.....d'ad'aga kayan lefan akeyi kwanin burgewa kowa na jinjina kai ganin yarda set na boxs din suka hadu kowa ya yabawa Lamin kam kowa yasan Ihsan ta samu miji na kece raini,duk wani magana da akeyi tana gefe a chair tana kuma kallon kawayenta dake kallon kayan suma suna yabawa sai wani bubud'a hanci takeyi tana jin kanta a sama ita babu ya ita,kallon Husna tayi tace" sai yau na kara tabbatarwa Baby na sona,ya fitar da ni kunya na dauka yarda baya son kashe kudi to bazaiyi abun kirki ba duk da wayayye ne".murmushi Husna tayi tace"kema da gangan tunda kinsan ai sirikarki da son iyayayi da nuna tafi kowa ai ba zata bari ayi abunda ba dai dai ba,Dan wallahi karfinki a gidan nan kab itace wannan mijin naki da shegen taurin kai kamar mutanan farko".tsuke fuska Ihsan tayi rai b'ace tace"dan na baki fuska kuka bashi ke nuna ki walakanta mun miji ba,gaskiya kisan abun rika fada in ba haka ba ki rika jina dib ba wani out come wallahi,haba kamar jira kikeyi".Husna dai batace komai ba ta juya taci gaba da kallon box's din da ake harhadawa tunda an gama daga duk wani abu dake ciki sai kace za'a bude wani shago......Shafa kansa tayi cike da kewa da tsananin soyayya tace"rayuwa sai hakuri Jabeer,ina so duk halin da ka tsinci kanka karka manta da Allah duk wani rintsi shi ya kaddara maka kuma zai baka mafita ka zama mai hakuri a ko da yaushe,kada kuma ka zama mai garaje ko saurin yanke hukunci a al-amuran rayuwarka,duka duniyan nawa take? In yau mune gobe bamu bane,ina fada maka wannan ne wata kila dan yau nake da dama wata ranar bazan samu lokaci kamar haka ba,ka zama mai gaskiya da rungumar duk abunda kaddara zata baka kai dai kayi kokari ka furta alhmdllh a ko wanne hali Yarona"..Manya manyan idanuwansa ya daga yana kallon Hajja sai kuma ya rike hannuwanta sosai cikin nashi kamar wani karamin yaro yace"Haba Hajjana dan Allah ki daina sai nake ganin kamar bankwana kike mun,idan babu ke ina zai zama mafakata kenan? Bana tunanin zuciyata zata iya daukar rashinki Hajja"...Murmushi mai matukar kyau Hajja ta saki tace"Ayya Jabeer in yanzu mutuwa tazo garemu ai batayi sauri ba ,idan kuma ta tsaya batayi jinkiri ba,idan mutuwa tazo dole mu ansa kiran mahaliccinmu ,fatanmu dai Allah ya mana arzikin kyakyawan karshe ,mutuwa dole ce"Bai kuma cewa komai ba ya soma sauke ajiyar zuciya kawai amma gaba daya ya rasa sukunin zuciya sai wurin karfe tara na dare da Daddy ya kirasa sannan yayi sallama da gidan Hajjan ya tafi.ko da ya shiga parlon Umma anan ya samu Lamin shima zama yayi tare da cewa"Ina wuni Daddy "cike da soyayya da kulawa Daddy yace" lafiya qlau my son,ya aikin yaka baro Hajjan?"da alhmdllh ya ansa yana yin kasa da kansa.bags manya guda biyu Daddy ya dauko daga gefansa ya tura masu tare da cewa"ka kayanyakin da zakuyi amfani dasu a fitar biki nan,sai Ku duba abun da babu sai kuyi magana ko kuma za'a karo"Murmushi Lamin yayi tare da cewa"mun gode kwarai Allah ya saka da alkhairi Daddy ai nasan komai ma akwai a ciki".Dan shafa kai Jabeer yayi fuskarsa a sake yace"Allah ya kara budi Daddy,amma ni da ba ango ba".Dariya Daddy yayi ya tari maganarsa yace "Babban Abokin ango ma ai angone,ina so ne in ganku komai iri daya kun fito gonin Sha'awa yan samarina,su Hydar ma dai su ukku ga nasu can"... Sosai sukaji dadi sukayiwa Daddy godiya sannan suka dauka zuwa part dinsu a parlo suka baje kayan tsadaddun shadda,da voyels na maza ne iri da kala har kala goma ga hula da agoguna da turaruka hatta da boxers da singlet sai da Daddy ya zuba masu a ciki,dinkin ya dinku dan kab family din su a RASHEED MAKERA FASHION DESIGN suke dinki ma'ishi Wanda sai wane da wane ke samun dinki a can ko wanne b'angaren na dinkin maza da mata babu wanda basayi kai harma da kayan mazan suna siyarwa ka zaba a dinka maka daidai da ra'ayinka kuma a tura maka ako ina a fadin Nigeria gamai bukata ga number su 07047230000.....A gajiye lis su Layan suka shigo gidan musamman ita da ko kad'an bata jurar wahala danma Ammi na tare dasu da wallahi tuni gudo wa zatayi lalle ne aka cancad'a mata ja da baki ga kitso yan yarfa mata duk da ita ba gwanar yin kitson bace sam,Muhibba kam da Basma dasu Asma'u sai washe baki sukeyi dan dama sun saba kwalliyarsu irin haka,itakam tafi kowa jigata saboda rashin sabo.kai tsaye toilet ta wuce bayan ta rage kayan jikinta ta zubar a tsakar dakin nata,wanka tayi da ruwa mai zafi sosai sai kallon kanta takeyi a madubi sai kace wata sabuwar Amarya ga fatarta sai wani glowing na musamman takeyi yarda ta samu gyara da kulawa sai fitar da wani sihirtaccen kamshi takeyi mai masifar dadi da jan hankali sosai taji dadin jikinta ta fito ta saka wani sakalken dogon rigan material mai kallon purple hula ash ta saka sosai ta haska kamar ba ita ba,kamar ka saceta ka gudu,sai lokacin ta kwashe kayan data zubar tana gudun Ammi ta shigo ta samu kayan a haka,kai tsaye dining ta wuce sakwara ne akayi da miyar egusi,kad'an ta iba a plate ta zauna ta soma ci a hankali dan wani irin masifan yunwan da take cinta abun ba'a cewa komai,ga gidan duk ya cike da baki dan yau sora kwana biyu ne biki,kara b'angaren Ammin shine ma ba mutane sosai, da sallama ya shigo parlon amma in ba kana kusa da shi ba sam ba zaka ji meya fada ba ,da sauri ta ajiye spoon din hannunta taso tana ansa sallaman tare dayi masa sannu da zuwa.idanuwansa ya runtse da karfi yana kokarin calming kansa down dan yana son ya cika umarnin da Ammi ta basa,amma ya rasa dalili yarinyar yarda kasan Mayya haka take sata barinsa ko kadan.cikin cool voice tace"Yaya ina wuni sannu da shigowa.kana son wani abunne?"layan ta fada tana tsuresa da idanuwanta