Showing 1 words to 3000 words out of 55893 words
Chapter 1 - RUHIN JIKI BOOK PART 1 BY JORDERH .txt
*RUHIN JIKI!!*
*JORDERH MAJIDADI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
All thanks to Allah SWT for the privilege to start this book,special greetings to my siblings ,cousins and My lvly fans that have waited so long for Majidadi,and now am back da wani saban salon,I know u will luv it,cos I am in luv with it too...abun fa ba wasa,kudai ku biyo muji ya zata k'are salon na dabanne.😘😍😀
BISMILLAH
Page 1
Sauti ke tashi da hayaniyar y'an Matan a cikin babban parlon Wanda yaji kayan more rayuwa kallo d'aya zaka masa ka tabbatar an narka dukiya a parlon..Doguwar cikinsu siririya ko kad'an bata da jiki black colour ne skin dinta irin mai silb'in nan tana da long face ,wacce komai na jikin fuskar ya dace da muhallinsa.tsantsar kyau da yarda fuskar ta wadatu da bakin gashi sidik a duk in da ya kamata she's the real Definition of beauty..magana take yayinda gefan kumatunta suka lotsa shiya kara fito da kyawunta white teeth dinta suke anan jere ras take fadin"Muhibba wallahi Anni ta fito zata ci k'aniyarki ne,mukam nan karki janyo mana ita.ki mayar mata da fura"Su ukku ne a parlon sa'annin juna sai dai su farare ne tas wacce aka kira da muhibba ta tsuke bakinta tare da fadin"ke LAYAN haka kike, in ba ke zaki fad'a mata ba to ina zata gane? Kinsan tana gani zata ce Yaya ne ".Duka a cinya Basma tawa Muhibba tana hararenta tare da zaro ido tace"to kisa a kashe mu da ranmu , kinsan halin Yaya a gidan nan amma zaki jawo mana jangwam? To wallahi sai dai kiji ke da shi." Murmushin bosawa Layan tayi tace"lallai yau banga gidan kwana a gidan nan ba ni Layan d'akin Ammi zan gudu ni kam."Dariyan shakiyanci Muhibba tayi tare da cewa"Au yau kuma Layan? Ke da Habibin naki? Farin cikin rayuwan ki?" Da sauri Layan ta yunk'ura tare da rufe bakin Muhibba tana jujuya dara-daran idanuwanta masu matuk'ar girma da haske cikin cool voice tace" please mana "tana kare. Maganan tare da raurau da ido alamun zatayi kuka...kallonsu kawai farar Dattijuwar take tsaye a entrance na parlon farace sosai duk da yanayin tsufan daya bayyana a jikinta amma wanke take tas tasha sabuwan atamfanta ko ina a jikinta k'al-k'al fuska babu fara'a ta k'aro tana bin cup din furan dake hannun Muhibba da kallo cikin mitsi-mitsi da ido tace"Amma wallahi kin cuci kanki Mubabbi,ke da Allah,yanzu furar tawa zaki shanye? Ko da kudin waccan narkekiyar matar na had'a na siya ne? To Wanda yayi na gari yaga na gari dan uban mutun kuma ki sani da Amadu kike kuma a gabanki zai biya kudin tashi barmun d'aki mai kama da zabiya kawai". Had'e fuska Layan tayi tace"Anni meyasa kike haka wai?".. " A kul na haneki ,bansan tsirfa tunda ban kasa da ke ba kina fama zok'ai-zok'ai to kiyi ta kanki"......Daga sama har k'asa Ammi kebin Veer da kallo she was speechless. Cikin sanyin murya kamar mai rad'a yace Am-mi please".kuma daure fuska Ammi tayi"hala na fara wasa da kai Jabeer?, ka daiji abunda na fada" ta k'are maganan tana kai mug din tea a baki ajiye mug din tayi ta dauki handbag dinta d eyeglasses dinta with car key tace "I'm going to office".. Cikin sanyin murya yace" Allah ya tsare".Da gudu Layan ta shigo part din tare da mak'alk'ale Ammi tana turo d'an karamin pink lips dinta gaba" har so nawa zan fad'a maki ki daina yin gudu a gidan nan iyee Layan?"..rau rau tayi da ido kamar wacce zata fasa kuka tace"Ammi..."Bana so naji komai kinji ma na fad'a maki,Sam na hanaki tsokanan fad'a a gidan ,dama wannan ne shirin school din naki?"Ammi ta k'are maganan da alaman tambaya.hawaye ne suka kawo fuskar Layan cikin sanyinta dan duk rigimarta da tsokanarta akwai sanyi tace"Ammi Yaya Jafar ne kuma yasa Driver ya tafi dasu Basma school an barni"..Agogon hannunta ta kalla kafin ta mayar da kallonta ga Layan tace"and I'm late too,bazan iya jiranki ba kije ki karasa shirin Yayanki ya ajiyeki,shima ki masa rawan kai ai kinsan sauran" Ammi bata jira cewarta ba ta juya ga Veer tace"drop her at school" tana zuwa nan ta fice tana gyara lab coat din jikinta dan ta kusa latti na zuwa asibitin...ko kallon in da take Veer beyi ba,hasalima kamar bada shi Ammi tayi magana ba,hankalinsa sosai ya tattara akan waya yana pressing,ganin Haka Layan ta k'arasa a tebur din idanuwanta a k'asa kamar wacce k'wai ya fashewa a ciki taja chair zata zauna tana fad'in "ina kwana Yaya". Be amsa ba saima d'agowa yai yana watsa mata mugun kallo ganin tana neman zama kallon data fahimci yana mata ne yasa tayi saurin marairaicewa idanuwanta na tara ruwa tace"da break zanyi ban karya ba". Wani wawan tsuka Veer yaja tare da kuma tamke fuska a fusace yace" barnan ko na karya maki wannan sololon k'afar naki ".Da gudu Layan tayi hanyar d'akinta dake part din.haushi da takaicin rawar kan Layan ya kuma kume Veer na sakalci irin nata wanda ko tafiya bata iya yi sai gudu...a daidai corridor Layan tawa kanta masauki kafin ta daidaita tsayuwanta a hankali ta leko Veer dake zaune still yana aikin pressing phone tuni wani murmushi ya kwace mata zara-zaran siraran hannuwanta tasa tare covering long face nata a hankali tana jin wani dadi da sanyi suna ratsata ganin yana kallon agogon hannunsa tasan time ya ibar mata kuma tasan idan ya cika ko zata mutu bazai tab'a kaita school ba.Da hanzari ta fad'a d'akinta ta sanya k'aramin hijabinta na school sannan ta ratayo bag dinta ta fito ,baya parlon saurin zaro ido tayi tare da cewa" Kai Yaya!"sai kuma ta kwasa da gudu a parking space ta same shi yana kokarin bud'e mota beko nuna yasan alaman akwai zuwan mutun a wurin ba....har cikin school ya kaita ,yana kallon malaminsu dake tambayarta "why is she late". Juya ido kawai take without noticing wani abu taji muryar Veer kamar mai rad'a yana fadin" just furnish with some work ko duka gobe ba zata sake ba".ko kad'an Layan bataji mamaki ba dan ba yau ya saba kaita school yasa a mata duka ba.maimakon taji haushi sai kawai ta saki murmushi tana k'arewa Yayan nata kallo kafin cikin sanyi tace"Allah ya tsare Yaya na gode".ko bi ta kanta beyi ba ya juya ...aiko sosai Teachernsu ya bata dama gwani ne a mugunta...parking ya gyara tare da fitowa kai tsaye ya shiga gidan Aunty din nasa babu kowa a parlorhad'u..Maid dinsu daketa faman goge goge a parlor ga kamshi d sanyayan AC na tashi ,sai a lokacin ya samu nutsuwa da farin ciki Dan wani k'unci ke mamaye shi idan yana zama inuwa d'aya da Layan baya son Fadannan na Ammi shiyasa yau kawai ya daure ya kaita school.. Kujera kawai ya samu ya zauna tare da sauke idanuwansa suna anan kamar mai kama da jin bacci yana kuma tauna red lips dinsa a hankali ga kuma hannunsa a cikin tulin gyarariyar sumarsa wacce ke shek'i ta wadatu da kamshi.Gaishesa Maid din tayi tare da wucewa dan Sanar da Ummi kanwar Baban Veer mai rasuwa zuwan shi.a hanya suka had'u ...da Kallo Ummi ta bishi tare da cewa"kai da nace ka kwana ka'ki and now meye na zuwa mun da sassafe?".sai ka kallesa sosai zaka ga alamun sakin fuskarsa alamun murmushi sannan yace"ina kwana".harararsa Ummi tayi tace" ba wannan na tambaya ba".sosa kai Yayi yace"na sauke wacce ugly monster ne a school".without second though Ummi ta kwashi pillows na kusa da ita ta jefa masa su a fuska ,fuskarta tana nan a d'aure tace"iskancin naka yana nan ashe Jabeer? Har yanzu baka daina cewa Layan wannan sunan ba,to wallahi ahir dinka da ni.yanzu zanci k'aniyarka a gidan nan,kai da y'ar uwarka wannan wacce irin bak'ar rayuwa ka dauka wa kanka? To daga Mahaifinka har mahaifiyarka dai ba haka suke ba,kuma Umma da Abba basu cancanci kak'i jininsu haka ba".kallon Ummi kawai yake can dai ya mik'e ko sallama babu cikin tsawa Ummi tace"karna sake ganin k'afarka kuma harsai kayi hankali"ko juyowa beyi ba ya fice yana jin dama be biyo ba...Annie ce zaune a k'atuwar darduman data baxa a tsakar parlon nata ga carbaha a hannunta tana ja ansha gogggen sabon Hijabi ala lazumi ta d'aga kai tana k'arewa Jabeer kallo Wanda ya shigo tare da kwanciya a chair ya lumshe ido.saurin karasa lazumin tayi ta iso wurinsa tana binsa da kallo kafin tace"kai Jabeeru a wurin aikin sojan ne aka kore ka? Naganka haka kamar Wanda aka saukarwa da mutuwa?shiru ba amsa".wani kallo Annie ta jefa masa cikin shaushin shareta da yayi tace" to kaita yi wannan bak'in halin naka ko shi yasa Janar yake ko wa oho maku a maka tsinannan duka a kawo mana kai kaca-kaca muhau jinya da kashin kudi.to wallahi kada ka janyo mana inmu ka raina to can akwai hukunci sai ka kama kanka ah'to".idanuwansa da suka soma canza launi ya bud'e yana bin Annie da kallo bece komai ba ya kuma rufesu..
Comment and share kada Ku bari a wuce Ku mutanena .
Oum Aryaaan.....
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
page 2
A gajiye suka shigo daga school din kai tsaye Layan part din Annie ta tafi in da duk yawancin rayuwarta anan take yi,duk yarda Annie keda rigima amma tana tsananin son Layan Wanda asalin sunanta Maryam sunan Annie ne da kuma y'arta wato Ammi mahaifiyar Jabeer taci.kallon Basma Umma tayi tace "ina kuma Layan din ta wuce? ". Zama a d'aya daga cikin Sofa's din parlon tayi tare da cewa " ina fa Umma kinsan ta wuce wurin Annie ne"."oya maza kije ki cire Uniform din lokacin Islamiyya yana k'urewa"....kamar ko yaushe tun daga waje take k'wala kiran "Annie,Annie nikan ina kika shige Annie gani na dawo daga makarantar" she was speechless a tsananin tsorace take waro manmanyan idanuwanta tare da langwab'ar da kai a k'asa.tuni sakakken yalwataccen sumar kanta ta zubo a bayanta tare da bajewa a duka fuskarta .cikin jin zafin fusgarta da Veer yayi cikin shak'ak'en murya tace"wallahi Yaya ban ganka ba,ban kula da kai b..."sauran maganar ta mak'ale sakamakon kyakyawan marin da Veer ya wanke fuskarta da shi.iya k'arfinsa yasa hannu tare da ingijeta daga jikinsa da take shirin fad'owa.a can jikin TV stand kanta ya bugu ta sakin wahalliyan k'ara kad'an dan tasan baya son ihu ko kad'an."innalillahi wa'inna ilaihir raju'een Jabiru,Jabiru kana tsoron Allah kuwa,ni na tabbata ka mutu a haka wuta can Allah zai maka masauki,kashemun y'ar zakayi to wallahi bari maryam ta dawo kai ko darajar sunan da taci ma ba zaka tausayawa yarinyar nan ba? Duka duka nawa Laya din take"sai kuma ta fashe da kuka tana nufo in da Layan ke kokarin tashi..cikin jin jiki take fadin"Annie ki barsa dan Allah,ban gani bane n dora masa jakkan school dina,basai kin fad'awa Ammi ba"."ke rufemun baki yaune Jabiru ya fara cin zalinki a gidan nan?".k'arar bud'e k'ofa yasa duka suka mayar da kallonsu a wurin..Jabeer ne ke barin parlon hankalinsa kwance kamar Wanda beyi komai ba...Annie ta kama Layan zuwa bedroom dinta tana ta sababi..tsuke fuska Layan tayi duk da yarda fuskarta ta haye ga shatin hannun Jabeer kwance a fuskarta sannan tace"wai Annie meye naki a ciki,ina dai ni ya doka bake ba? Kuma nace abar maganar nan dan Allah".sake da baki Annie tabi Layan da kallo ta saki dariyan bosawa tace"tabdi jam.in ke lalacewa ta same ki to banda ni wallahi wallahi kinji na rantse ni banyi gantalewar da zan saka ido ina kallon Jabiru yana abunda yaso a gida ba".Bata ko kula Annie ba ta kwashi bag da hijab nata tayi bedroom tana tura baki,ita ko kad'an bata ga laifi a abunda Yaya Jabeer ya mata ba.....sallama yayi ciki ciki tare da k'arasawa kusa da Ammi ya zauna kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace"Ammi kin kira".banza tayi masa har sai da ta karasa cike paper's din da take dubawa sannan ta cire white eyeglasses dinta tare da ajiye pen din hannunta kafin tace"so nake naji me layan ta maka ka mata wannan dukan harda buga mata kai da bango"waro ido Jabeer yayi kamar zaice wani abu sai kuma yayi shiru."I think ka kurumce anyway let me drop this in your head,na rabaka Layan tunda bakai ka haifeta ba,to banga dalilin treating dinta da kakeyi haka ba,tunda kai baka da kunya da kara,tashi ka bani waje"lumshe idanuwansa yayi cikin cool voice yace"kiyi hakuri Ammi"ko kulasa batayi ba ta kwashe kayanta ta bar masa parlon As if zai gano wani abu a jikinta haka ya bita da kallo..d'akin da Layan take ta tura ta shiga Muhibba ta samu da cup a hannu ga Layan jingine da bed sai tura baki takeyi ..."kin bata maganin?"kallon Ammi Muhibba tayi kafin tace"to Ammi wai bata sha".karasa shigowa tayi cikin d'akin cikin daure fuska tace"bansan iskanci halan na fara wasa da ke?"rau rau tayi da ido kafin ta karb'i maganin tana hawaye tasha da kyar sannan tayi saurin daukar Shayin da Muhibba ta kawo mata tun dazu ta banzatar sai yanzu take sha.tab'e baki Ammi tayi ta fita ta bar masu d'akin....sosai Jafar ke dariya harda rike ciki yana kallon yarda Annie ta dage tana nuna masa yarda Jabeer ya dodoki Layan..."ah to ni lalacewata bata kai nan ba Jahwaru niko jiki har rawa yake na isa sashen maryam da ta dawo aiki na sanar mata abunda wancan yaron yayi na kara da cewa maza tasa ya hada inasa-inasa ya kama hanya ya tafi gidan ubanshi mu bamu gayyar tsiya ko nayi ba daidai ba? Saboda Allah ai zalinci babu kyau ko?,Allah sarki Laminu ni nasan da yana nan duk ba haka ba,yo yana kusa waya isa ya saka Laya kuka?".....Da safe ba laifi zazzabin ya saki Layan har tayi shirin zuwa school da yake tana karantar medicine ne tana shekara ta biyu,Muhibba kuma law in da Basma ke karantar Entrepreneur dan tana sha'awa kasuwanci sosai kuma shine abunda familyn su sukafi yi sai dai da yake gidan y'an boko ne yasa suka tara ma'aikata da makaranta da dama a gidan...kai tsaye tana fitowa main ginin gidan ta nufa in da nan ne Asalin gidan ,gidan Alhaji Ahmad Wanda suke kira da Abba kenan kuma shine yaro na farko a wurin Annie Wanda yake da 2wifes Hajiya Badiyya wacce suke kira da Momy itace ta farko tana da yara hud'u Lamin shine babba Wanda Barrister ne yaje wani course a Uganda shiyasa baya nan sai Hydar shi kuma Dan kasuwa ne sai Faruk yana karatu sai Muhibba Auta,sai Hajiya Aisha wacce suke kira da Aunty Amarya tana da yara ukku Jafar Wanda tare aka haifesu da Hydar shima kuma Dan kasuwa ne dan komai tare suke yi sai Basma sai Ahmad takwaran Daddy Wanda suke kira da khalifa yana JS 2.Sai Alhaji Sadeeq Wanda shi ne ke biwa Abba suna kiransa Daddy matarsa d'aya Hajiya Fatima wato Umma yarinyarsu d'aya wato Layan..Sai Ammi maryam takwarar Annie wacce itace Auta kuma y'a Mace tilo a wurin Annie tayi Aure ta Auri Alhaji Sadeeq Dan gaske hamshakin mai kudi Wanda a garin kano da kewaye suke alfahari da shi,shekararsu sha shidda da aure sannan ta haifi Jabeer .mahaifiyarsa da kanwarsa Hajiya Fatima Ummi su kadai suka rage masa itama tana aure a nan kano Allah yawa mijinta rasuwa tun Jabeer na da Shekara biyar Biyar kuma har yau bata kuma yin aure ba ta dawo gida ta zauna a part din da yayunta suka gina mata a cikin gidan.... A parlo ta samu Mummy da y'an aiki suna had'a dining sunkuyar da kanta tayi k'asa kafin tace"ina Kwana Mummy"sai da Mummy ta kare mata kallo daga sama zuwa k'asa kafin ta tab'e baki tace"lafiya" bata kuma cewa komai ba tayi hanyar stairs a tsawace Mummy tace"kije sama kiyi mene? To Alhajin be tashi ba jiya be shigo da wuri ba,kar Wanda yazo cikinku kuma ya damesa"kallonta kawai Layan keyi amma bata ce komai ba ta fita tana tura baki xuwa part din Ummanta da sallama ta shiga jiki a sanyaye,kallonta Umma tayi kafin tace"lafiya kika shigo mun d'aki a haka ko tun safe halin zaki fara?"..cikin shagwab'a tace"naje ganin Abba shine Mummy..."bata k'arasa ba Umma ta datseta ta cewa"bani wuri da wannan sakalcin naki baya k'arewa har yau naga ranar da zaki girma shi Wanda ya shagwab'aki ya tafi ya barmu da ala k'ak'ai a gida"..tura baki taci gaba da yi ta fito parlo ganin Jabeer yasa tayi saurin k'asa da Kansas cikin in ina tace"ina kwana Yaya"siririn tsaki ya saki har zai koma baya sai Umma ta fito hannunta rike da plate da spoon "a'a Son harka fito,k'araso ka karya dama yanzu nake tunaninka a rai". Kallonta ta mayar kan Layan" kije ki d'auki me zaki d'auki saura a tafi a barki kice kinyi latti".hawaye ne suke son zubowa a idonta da k'yar ta mayar da su ta wuce d'akinta Wanda sai ta mance rabonta da shi dan tafi zama a part din Annie ko Amminta dan mutane da yawa suna dauka Layan ce Ammi ta haifa ba Jabeer ba...sosai ransa ke kunci da kyar yake shan kunun gyad'an da Umma ta zuba masa haka kawai yaji komai ya fita a kansa da kyar yasha kad'an duk da kowa yasan a gidan abincinsa hannun Umma yake ko part din Annie shi mutun ne mai kyankyami ba komai d ya fito daga hannun kowa yake iya ci ba,Sallama yawa Umma ya fita yabar gidan gaba d'aya ko zai samu saukin abunda yake ji...
Comment and share
Oum Aryaan.
*RUHIN JIKI*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*___________________________________*
*JORDERH MAJIDADI*
Page 3
Driving yake amma zuciyarsa wani iri take masa har wani tashi tashi takeyi dan tsabar takaici da kuncin ganin Layan da yayi duk lokacin da zaiga yarinyar takan dagula masa lissafi ta tab'arb'arar masa da duk wani farin ciki nasa da take tattali juya kan motarsa yayi zuwa