Showing 24001 words to 27000 words out of 57328 words

Chapter 9 - Anya Baiwa Ce 1 Complete Hausa Novels.txt

30 Nov 2024

3904

"Duk wanda yace garinsu da nisa ba'a kama shi ya zuɓuce ba, idan bazaka iya wannan yaƙin ba ka sakar mini linzamim dokin bazai gagareni sarrafawa ba, kasan bahaushe yace me tsoron a mutu shi yake maho ni da ka ganni ba gudu ba ja da baya har sai na cimma buri na a gidan nan." Dukda suna cikin duhu hakan bai hanashi watsa mata muguwar harara ba, cikin zuciyarsa yana ayyana ta hanyar da zai ɓullowa lamarim Fulani Maryama ta ruwan sanyi yadda bazata fahimci indai ya sa gaba ba. Gyaran murya yayi a hankali yace. "Ragamar damisa a jaki da nisa, randar cikin ɗaka Allah ke baki ruwa. Fulani Maryama sarauniyar mata nina isa nace tazugen Sarki ya kunce ai duk inda kika saka ƙafarki kina ɗaukewa zan ɗora tawa. Me za'a fasa mutuwa ko hisabi?" Fulani Maryama tayi murmushi sannan suka ci gaba da ƙulle-ƙullensu daga ƙarshe kowa ya kama gabansa.


Washegari da sassafe Salman ya shigo sashen Mahaifiyarsa kamar wanda aka jefo shi daga sama ko sallama babu, hatta Bayin da suke cikin sashen ba ƙaramin razana suka yi da ganin yanayin da Salman ya shigo ba, da ƙarfin gaske ya bankaɗa labulen ɗakin nata ya shiga a lokacin tana kwance a kan gado ko sallar asuba batayi ba. Yana shiga ya ɗora ƙafarsa ɗaya a kan gado sannan ya sa hannu ya fara tashinta da ƙarfi, kamar saukar aradu haka ta tashi firgigit tana dube-dube. Wata uwar tsawa ya buga mata yace. "Mama wallahi ki kiyayeni babu ruwanki na gaya miki babu ruwanki, ki cire kanki daga cikin sabgar yarinyar nan idan ba haka ba wallahi zaki tsinci talatarki a labara, ina raba ki da kiwon kyalla kina akuya ta haihu muddin kika bari kika kaini bango wallahi zakiyi mamaki na gaya miki babu ruwanki da yarinyar nan amma kinƙi ji ko to shikenan jiki magayi maji ma gani an binne tsohuwa da rai, wallahi wani abu nake dubawa ina duba hallaci banasan na yi miki butulci, kinyi mini hallacin da ko Mahaifiyar da ta haifeni bata yi mini ba shiyasa nake ɗaga miki ƙafa amma bakya gani, ina ƙara jaddada miki da ko fita harkarta saboda mallakina ce idan kuma ba haka ba wallahi zaki sha mamaki. Akan Maryo babu wanda bazan iya ganin bayansa ba dan haka gwara ki shafawa ranki salama ki ga aurena da ita kamar yadda kika ɗauko da farko bansan ma akan wane dalili ne zaki juya mini baya ba alhalin kinsan nafi kusanci da ke, Mahaifiyata babu yaffa bata yi dani ba akan na rabu da ke amma na fifita ki akanta, sai da kika san sirrina zaki juya mini baya? Sam bazan ɗauki wannan ba dole cikin biyu a yi ɗaya zaɓi ya rage naki amma wallahi kika nemi ki kawo mini cikas akanta sai inda ƙarfina ya ƙare."


Yana zuwa nan a zancensa ya fice daga ɗakin yana wani irin huci kamar kumurcin macijin da yake gabda kai mummunan sara. Tsoro, mamaki, fargaba haɗe da tashin hankali ne suka yi caraf suka samu gurbin zama a cikim zuciyarta haɗe da sassan jikinta, da ya sanyaye kamar wacce aka zarewa laka. Tun da ta ƙurawa bayansa ido bata ɗauke su daga kallon ƙofar ba, bawaye take yi bibbiyu wani irin tsoron Salman na ɗarsuwa a cikin zucuyarta, gabaɗaya kanta kullewa ya yi ta rasa gane inda maganganun Salman suka dosa, a hankali ta furta. "Yau me yake faruwa da Salman ne ko sauran matan Sarki ne suka fara sa masa hannu, me yake faɗa haka ne akaina ina mahaifiyarsa amma yana ce mini wata ce mahaifiyarsa anya so suke su rabani da shi ba sannan su haukatar mini da shi, duk rashin kunya da rashin mutumcin Salman har ya kai yazo ya tashe ni har gadon baccina ya yi mini wannan tijarar? To wai ma ya akayi yasan da na tattauna maganganu akan yarinyar cen? Na shiga uku wai me yake shirin faruwa da ni ne?" Fulani Maryama kamar taɓaɓɓiya haka ta dinga surutai babu kai ba fasali tana daga zaune daga ƙarshe ta yanke shawarar ziyartar Boka Marduska ko zai bata mafita. Baccin da ya gagari idanunta kenan jiki a mace ta miƙe ta fita ta ɗauro alwala sai a lokacin ta gabatar da sallar asuba.


Bayan kwana biyu Jikin Maryo ya yi kyau sosai dan tana cin abinci kuma har ta warware tana takawa da ƙafafauwanta, Inna Habi duk yadda take fushi da Maryo hakan bau hanata siya mata abubuwan da Likita ya zayyana mata ba, idan wanda zata siya ta girka ne tana siya ta dafa ta bawa Abu ta je ta kai mata. Duk yadda ta ƙaugauta ta ƙara ganin jikin Maryo danne zuciyarta tayi dan ta nuna mata kuskurenta, cikin kwana biyu Inna Habi ta rame ta lalace kamar ita ce mara lafiya, ƴar sana'ar kwalliyar dokin da take yi tana siyarwa gabaɗaya ta watsar da ita saboda rashin kwanciyar hankali. Babu wanda ya tambayeta dalilin yawan damuwarta da ramar da tayi saboda kowa gani yake rashin lafiyar Maryo ne ya jefata cikin wannan halin. Kwanan Inna Habi uku da zuwa aka sallamo Maryo daga asibiti, Uwar bayi ji take kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda farin ciki, tun daga farkon shigowarsu gidan Maryo ta fara wurga Idanu tana kalle-kalle kamar wacce abin ta ya ɓata take nema ruwa a jallo. Da yake tare suke da Abu ta lura da yanayinta nan take tausayi da mamakin ƴar uwarta ya kamata dan duk wanda ya fahimci Maryo ya san ta zurfafa cikin zazzafar soyayya, ta wani gefe kuma za'a iya kiranta da makauniyar soyayya. Har suka ƙarasa hanyar sashen Bayi Maryo bata daina waige-waigen da take yi ba, suna shiga ciki aka fara turuwar shiga gurin su Inna Habi. Masu zuwa dubiya dan Allah da masu zuwa ganin ƙwaƙwaf sai turuwar shiga suke yi, Bayan an lafa da zuwar musu Maryo cikin jin kunyar Inna Habi ta ce. "Dan Allah kiyi haƙuri Inna" Fuska a tamke Inna Habi ta ce. "Haƙuri da me?" Maryo ta sunkuyar da kai ta ce. "Akan abin da ya faru" Inna Habi ta watsa mata mugun kallo tana jin ɗaci a zuciyarta ta ce. "Maryo bani zaki bawa haƙuri ba kanki zaki bawa Allah ya gani duk wanda ya zageni akanki ban yafe ba, na baku tarbiyya dai-dai gwargwado meye bana muku? Me yasa zaki kai kanki ga ɗan sarki alhalin kina ƙasƙantacciya mara galihu, kina tunanin idan kika ce kina da cikin Ɗan Sarkin nan zasu yarda, wai bakya banbace matsayinki da nashi ne shi fa Ɗan Sarki ne ke kuma Baiwa ce." Maryo ta sunkuyar da kai cikin ladabi ta ce. "Inna ni ba Baiwa ba ce shi ma yasan da haka, kuma munyi alƙawarin aure da shi nasan zai yi murna da abun cikina. Babu wanda zai ƙi amincewa da abin da yake cikina tunda Sarki Mahaifina ne Inna kina ganin akwai me ja..." Cikin takaici Inna rufe Maryo da duka saboda wani ƙululun baƙin ciki da ya tokare mata zuciya, cikin kukan baƙin ciki Inna Habi ta ce. "Maryo yaushe kika fara hauka ban sani ba? Anya kuwa kina cikin nutsuwarki kinsan me kike faɗa kuwa a wane dangin kika haɗa jini da Takawa, tunda haka kike gani yafi ga fili ga me doki zamu ga wanda zai yi nasara tsakanin ke da shi" Inna Habi ta ci gaba da magana cikin kuka me ban tausayi. "Maryo na ci buri akanku amma lokaci ɗaya kin wargaza min shi yanzu da wanne ido zan kalli mutanen gidan nan? Tun baki fita daga masifar da kike ciki ba kin janyo min wata, a da ina shedar ku amma a yanzu Allah ɗaya zaku gaya mini ke da ƴar uwarki na aminta, kin dasa mini zargi a kanki dangane da laifin da ake zarginki da shi, Allah ka na ganin halin da nake ciki ka kawo min mafita." Gabaɗaya jikinsu ya yi sanyi Abu ma banda hawaye babu abin da take yi, Maryo ta raɓe gefe guda itama sai hawaye take gogewa.


Sarki Aminullah murmushi ɗauke a fuskarsa yace. "Gaskiya Yarima naji daɗin wannan maganar da ka zo mini da ita, dama ina gabda im zaɓa maka mata a cikin ƴaƴan abokai na sai gashi Allah ya tarfawa garinka Nono." murmushi Salman ya yi ganin Mahaifinsa ya yi na'am da maganarsa farad ɗaya. Sarki Aminullah yace. "A cikin gidan nan take" Da Mamaki Takawa yace. "A gidan nan kuma? Ƴar wajen Ciro ma Hajara?" Salman ya girgiza kai yace. "Maryo ce a cikin Bayin gidan nan take..." Bai ƙarasa faɗa ba daga bakin ƙofa suka ji ance. "Ƙarya kake ka sauya zancen ka domin ni ba Baiwa bace." Sarki Aminullah ido ya zura mata yana kallon kayan jikinta sannan ya fara maimaita kalmomin da ta faɗa a hankali." Maryo bata saurare su ba ta tako a hankali ta zauna a ƙasa gefen sa na dama ya yinda Salman yake gefensa na hagu. Cikin izza ta ci gaba da magana, "Baba ka ja masa kunne ko da wasa kada ya kuskura ya ƙara ambatona da Baiwa, haba Baba kamar ka manta wanene shi kamar ka manta ta'addancinsa har ka amince masa ya shigo fadarka. Wallahi har abada bazan aureshi ba." Salman sunne kai ƙasa ya yi yace. "Idan wancen karon nayi kuskure wannan karon dan Allah ku bani dama, dan Allah Mai martaba karka hana ni ita idan ka hanani komai zai iya faruwa" Sarki Aminullah shiru ya yi yana bin su da kallo dan gabaɗaya kansa ya kulle, ya rasa wacce irin magana suke yi ita kanta Maryo fa ta tako ta shigo gurinsa ya rasa wanda ya bata damar shiga alhalin tana matsayin baiwa.


Maryo a hassale ta ce. "Tashi ka fice mana idan ba haka ba ranka zai yi mummunan ɓaci. Mai martaba kana jin abin da fa yake faɗa wai komai zai iya faruwa, kaga kuwa bazai taɓa saduda ba ni babu wanda nake so nake ƙauna sai Saif." Kamar daga sama suka ga shigowarsa da mamaki Sarki Aminullah ya kalli Saif dan ya manta rabonda ya sa shi a idonsa, Maryo na ganin Saif ya shigo ta miƙe da sauri ta ƙarasa gurinsa tana kama hannunsa ta ce. "Dan Allah Saif ka gayawa Mai martaba halin da muke ciki, ka gaya masa ni kai nake so ba Salman ba ka tuna masa da alƙawarin da ya ɗauka akanmu, ka gaya masa da bakinka Salman mayaudari ne bazai taɓa sake halinsa ba..." Tun bata ƙarasa magana ba Saif ya kifeta da wani irin gigitaccen mari ya nuna ta da ɗan yatsa yace. "Ki kama kanki banasan shirme da rashin hankali" Yana gama faɗa ya wuce gaban Sarki Aminullah.


Daga Sarki Aminullah har Salman kallon mamaki suka bishi da shi jin wai yau da bakinsa ya furta magana, a gefe ɗaya kuma Salman yaji zuciyarsa fes har da sakin wani malalacin murmushi, ya saci kallon Maryo da ta sandare a tsaye yana kashe mata ido ɗaya. Maryo daskarewa tayi a tsaye riƙe da kumatu ga wani irin hawaye na bin fuskarta, ganin kukan zai ci ƙarfinta yasa ta juya ta fice da sauri.


Tana zuwa bakin ƙofa suka yi gware da mutumin har ledar hannunsa na faɗuwa, da sauri ta tsugunna ta ɗauka ta miƙa masa muryarta na rawa ta ce. "Kayi haƙuri." ta raɓa ta gefensa ta fice. Bin ta ya yi da kallo har ta ƙurewa ganinsa gabansa na ci gaba da faɗuwa a hankali ya furta. "Me ya take yi a nan? Dama duk tsawon shekarun da ta ɗauka bata tare da ni tana gidan nan ina ta kai mini ƴan tagwayena, me yasa tayi kamar bata sanni ba? Why Shukura laifin me nayi miki kika nesanta da ni..." Bafaden da ke tare da shi ne yace. "Yallaɓa mu ƙarasa gurin Mai martaba" Sarki Aminullah tun daga nesa da ya hango shi ya ya faɗaɗa fara'arsa yana cewa. "Marhabun lale da babban baƙo amma gaskiya ka Shamma ce ni Son"


KUYI HAƘURI DA TYPING ERRORS BANYI EDITING BA.


TO FA KU KAFTA🤣🤣🤣🤣🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️ ANA WATA GA WATA


AMUN AFUWA GOBE BA LALLAI NA SAMU DAMAR TYPING BA WALLAHI SABODA WANI UZURI AMMA IDAN NA SAMU SUKUNI KO BA YAWA ZAKU JINI👏🏻


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_
[08/11/2021, 17:22] Ameera Adam🌚: 23...




Baƙon da Sarki Aminullah ya kira da Son ya nemi kan wata lallausar dadduma ya zauna, har lokacin waigen bakin ƙofa yake da alama hankalinsa ya karkata acen. Saif da bai wani waye shi ba yace. "Barka da zuwa ya hanya?" Sai a lokacin ya juyo da kallansa ya amsa da, "Alhamdullah" sannan ya mayar da kallonsa ga Sarki Aminullah yace. "Abba barka da hutawa da fatan mun same ku lafiya?" Sarki Aminullah yace, "Lafiya ƙalau Son ya hanya?" yana shirin bashi amsa Salman yace. "Ɗan uwa ya hanya?" Baƙon yace. "Lafiya ƙalau yasu mama" Salman ya amsa da, "Lafiya ƙalau" Baƙon yanasan ya tambayi yarinyar da ta fita yana shakkun kar aga zaƙewarsa. Ƙarfin hali ya yi yace. "Salman lafiya naga kamar baiwa ce wacce ta fita, ta fita da kuka?" kafin Salman ya yi magana Sarki Aminullah yace. "Maleek rabu da sakarcin yaran nan shirmensu ne kawai suke yi" Maleek ba haka yaso ba yaso ace ko yaya ne ya ɗan ji wani abu game da yarinyar dan tabbas babu ko tantama wannan Shukura ce. Saif ne ya miƙe zai fita Maleek yace. "Ranka shi daɗe wannan kamar Saif amma..." tun bai ƙarasa faɗa ba Salman yace. "Eh kwantacce ba ka ga dai Allah ya yi har ya miƙe ga baki ya samu" Da tsananin mamaki Maleek yace. "Da gaske ya samu lafiya gabaɗaya?" Sarki Aminullah da har lokacin shi kansa cike yake da al'ajabi ya gyaɗa kai yana murmushi, mamaki yake sosai yadda kayi Saif ya warke daga ƙasan zuciyarsa yaji wani irin farinciki da ya rasa dalilinsa. Saif murmushi ya mayarwa da Maleek sannan ya wuce saboda ba wani sanin ƴan uwan Mahaifinsa ya yi va saboda kodayaushe yana gida gurin mahaifiyarsa, dama Salma ne ɗan zaman fada shiyasa duk wasu ƴan uwa da baƙin Sarki babu wanda bai sani ba. Musamman da ya kasance kowa yasan shine Yarima magajin masarauta hakan yasa duk inda Sarki Aminullah zai sa ƙafa tare suke zuwa. Abu ɗaya mutanen garin suka riƙe wato albasa batayi halin ruwa saboda ta kowacce siga Salman ya sha bam-bam da mahaifinsa, mahaifinsa mutum ne me adalci da sanyi hali, kyautatawa tausayi tare da taimakon talakawa, ya yinda Ɗansa Salman yake da halaye akasin haka.


Maryo wani irin kuka take mai taɓa zuciyar mai sauraro, duk inda ta gifta kallanta ake yi saboda hawayen da ke zuba bibbiyu a idanuwanta. Bata tsaya ko ina ba sai cen cikin daji-daji hanyar da tayi shiru sabida rashin mutane da ke bin hanyar duk kuwa da kasancewar a cikin gidan Sarkin ne, cem bakin bishiyar tsamiyar da ta saba zama tace ta zauna ta haɗa kai da gwiwa tana ci gaba da rusgar kukanta saboda yadda zuciyarta ke yi mata ƙuna. Sai da tayi mai isarta sannan ta goge hawaye ta ɗago a hankali tana furta. "Me yasa zaka yi mini haka? Me yasa zaka guje ni a lokacin da na fi kowa buƙatarka?" Hannunta ta ɗago tana kallan zoben dake jikin ɗan yatsanta ta ce. "Ashe zaka iya manta alƙawarin da muka ƙulla da kai me yasa haka idan wasa kake mini ka farka dan Allah" tana rufe baki kamar wacce aka ce ta juya daga cen tsallaken bishiyar ta hango wasu mace da namiji suna wasanninsu sai dai sun jiya mata baya yadda bata iya ganin fuskoki su, sautin muryoyinsu ta fara ji tare da wata irin sarewa mai tashi a tsakiyar ka, a hankali ta miƙe zata ƙarasa gurinsu sai dai tana miƙewa ta hange su suma sun tashi sunyi gaba suna suna ci gaba da wasanninsu. Maryo batayi ƙasa a gwiwa ba ta cigaba da binsu suna gaba tana binsu a baya har sai da suka yi tafiya mai tsawo, sannan ta hango hangesu sun nufi wani kogi itama batayi ƙasa a gwiwa ba ta nufi hanyar kogin. Kamar daga sama taji kiran da wasu Fadawa suke mata hannuwansu ɗauke da wasu manyan itatuwa wanda da alama bishiya suka saro a gurun. Ƙiƙam ta tsaya tana kallonsu ɗaya daga ciki yace. "Ke Maryo kanki ɗaya kuwa me ya kawo ki cikin wannan dajin da rana tsaka" Maryo dai har lokacin bata tanka musu ba. Ɗaya daga ciki ne ya ƙarasa gurin ya fisgota da ƙarfin tsiya ganin taba gabda da nufa bakin wani rami da babu komai a gurin sai tarin bolar da ake zubawa a gurin.


Murya a raunace ta ce. "Ganin nayi suna tafiya shiyasa na bi bayansu wallahi kamar nasansu ji nake kamar nice tare da Furzaan kuma sai suka faɗa cikin kogin cen" Ɗayan Bawan ne ya yi mata kallon baki da hankali yace. "Ramin bolar ne ya miki kama da kogi kina cikin hankalinki kuwa?" Ɗayan da ya ƙarewa Maryo kallo yace. "Kai Bulama riƙo hannunta mu ƙarasa ciki kawai" ba musu suka wuce Maryo na biye da su har lokacin bata daina waige ba har suka ƙarasa cikin jama'a. Sai da suka shiga cikin mutane ya saki hannunta sannan suka wuce gidan bayi suka tura Maryo sannan suka wuce kai itacen da suka ɗauko.Maryo ɗakinsu ta shiga kamar koyausne zaune ta ga Inna Habi ta zuba tagumi ga hawaye na bin fuskarta ɗaya bayan ɗaya, Inna Habi gabaɗaya ta rame ko abincin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login