Showing 51001 words to 54000 words out of 57328 words

Chapter 18 - Anya Baiwa Ce 1 Complete Hausa Novels.txt

30 Nov 2024

3906

na lura mafi rinjayen hallitarta daga ɓangarena ne na jinsin Jinnu, akan idon kowanne bil'adam ne zai ganta a matsayin mutum amma sam ba haka bane."


Mahaibish ta diro💃🏻 Su waye zasu biyo ni muje suna😜


_LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[22/11/2021, 15:13] Ameera Adam🌚: 33...




A firgice Kyauta ta ɗago da kai tana kallon Mardid hawaye na ci gaba da tsiyaya kamar wacce ta shiga gasar kwaranyar hawaye, wani abu ne ya tsarga mata a tsakar kanta da wani dunƙulallen abu mai ɗaci da tsaya mata a zuciyarta, wannan ne karo na farko da Kyauta tana ji rashin jindaɗin zamantakewarta da Mardid, yanzu ace ƴarta ta cikinta wai ta tashi cikin jinsin aljanu. Mardid ganin yanayin Kyauta ya canja yasa ya tsugunna kusa da ita yana tallafo fuskarta da tayi ja saboda kukan da tasha yace, "Kyauta! Ko bakiji daɗin kasancewarta haka ba?" Ɗagowa ta yi ta kalleshi idanuwanta na ci gaba da hawaye ta girgiza kanta, tana cusa kanta cikin jikinsa tare da fashewa da matsanancin kuka. Runtse idanunsa ya yi yana jin kukanta har cikin zuciyarsa, hannu yasa ya fara bubbuga bayanta kamar yarinyar goye, har sai da ta tsagaita da kukan da take yi sannan ya saketa ya ci gaba da cewa, "Na yi miki alƙawari zan kula da ku na tabbatar bazaki yi maraicin Kaka ba" Gyaɗa masa kai tayi sannan ya sa hannu yana goge mata hawayen idonta yace, "Yanzu ki tashi ki fita ki sanar musu da mutuwar Kaka idan yaso bayan an binne shi sai mu koma cen Masarautarmu da zama" wannan karan tashin hankalinta ya bayyana ƙarara a saman fuskarta har sai da ta ɗan firfito da manyan idanuwanta, ya fahimci halin da take ciki ba ƙaramin tausayi ta bashi ba dan haka ya tattaro jarumta yace, "Karki damu na tabbata babu wani abu da zai faru daku ki kasance jaruma me jarumta karki bari raunin zuciyarki ya yi tasiri a gangar jikinki." Gyaɗa masa kai tayi tana ƙoƙarin ɗauke damuwar fuskarta wanda tsanani damuwar tata ya ƙaryata haka. Kallanta ya sake yi a karo na babu adadi yace, "Je ki kirawo su lokaci na ƙurewa" ya ƙarasa faɗa yana ɗaukar Sarƙar da Kaka ya bashi. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fita tana zubar da ƙwalla, ta fara sanar wa tsirarun mutanen da suke kewaye a wurin. Tsohuwar da ta gyara Kyauta lokaci ɗaya ta ƙaryata dan gani take wannan kamar wasan yara ne, amma suna tozali da gawar Kaka ba ƙaramin sanyi jikinsu ya yi ba, kuka suke sosai dan Kaka na da matuƙar muhimmanci a cikin rayuwarsu, musumman ga Dattawan da ke rayuwa a wurin, matasan yanki ne basu ɗaukake shi kamar yadda iyaye da kakanninsu suke kallansa ba, duba da lokacin da girma ya kamashi ya tarkata kayan aikinsa wuri ɗaya ya daina duk wasu taimako da yake yi musu na bada magunguna, idan ba gani ya yi mutum na cikin wani irin tsanani ba.


Bayan an binne Kaka Mardid ya ɗauki Kyauta suka koma cen Masarautarsu ta fararen aljanu dake ƙarƙashin ƙasa, lokacin da suka shiga hannunsa rungume da Muhaibish Kyauta na miye da shi a baya gabanta sai faɗuwa yake. Yana shiga fadar ya gansu a tsaitsaye wasu na zaune sai dai ga dukkan alamu fuskarsu babu walwala wanda yake nuni da cewar suna cikin gagarumin ɓacin rai, dama ya tabbata sai sun ji labari tun kafin isorwarsu saboda yadda suke bibiyar rayuwarsu, Mardid jinin jikinsa yasha dan tabbas yanayinsu baya rasa nasaba da shi, Mardid ne ya gaishesu cikin girmamawa ganin yadda ya yi yasa Kyauta itama ta gaishe da su. Babu wanda ya tanka mata hasalima gabaɗaya a wurin uku ne suke zaune cikin siffar bil'adam, gabaɗaya sauran jama'ar wurin a rikiɗe suke cikin siffarsu da Jinnu. Wannan sam bai dame ta ba saboda ta yi sabo da ganin wannan hallitun nasu tun tana ƙarama amma wannan yanayin nasu ba ƙaramin razanar da ita ya yi, har sai da tsoronta ya bayyana a fili ƙarara. Mardid ne ya fara takawa wajen Yayan Mahaifinsa dake kwance cikin siffar dorinar ruwar da kan Jaki sai wasu tsili-tsili ƙafauwansa masu kama da ƙafafun zakaran hausa, yana zuwa ya miƙa masa Muhaibish cikin ladabi yace, "Kyauta ta haihu ga yarinyar na saka mata Suna Muhaibish, amma a gafarceni na yanke hukunci ba da saninku ba" A firgice ya ɗago yana kallonsa, wagegen bakinsa ya buɗe me matuƙar muni ya furta, "Muhaibish?" Gyaɗa masa kai Mardid ya yi a ƙufule Junduru ya miƙe yace, "Dole a canza sunan yarinyar nan bazai taɓa yuwuwa a kira ta da suna kamar wannan mai matuƙar muhimmanci ba" Kyauta da ke gefe da ba ta san ma'anar sunan ba amma ko da ba ta san me sunan yake nufi ba, ta fahinci sunan me muhimmanci da matuƙar amfani ne a gurinsu, dan ta tabbata da banzan suna ne baza su taɓa ƙorafi akai ba tun da ta san ba ƙaunarta suke ba, kuma ta san bazasu ƙaunaci abin da ya fito daga jikinta ba.


Mardid ya kalli kawun nasa da tsananin mamaki yace, "Saboda me za'a canza sunan?" A hasaale Junduru yace, "Saboda sunan me tsarki ne dan haka bazamu yadda ka banzatar da sunan ga wata bil'adam cen mara galuhu ba, kuma kai kanka ka sani ba kowanne yaro ne yake cin wannan sunan rayuwarsa ta ɗore ba, ka sani kuskuren tsinuwa na bibiyar me sunan nan me yasa zaka janyo mana jafa'i cikin ahalinmu, ka san tarihin Muhaibish tun daga farko har ƙarshe. Ka karanta yadda Boka Bugudur ya kuskurewar bakinsa har ya tsine mata, kanasan tsinuwar bakinsa ta sauka akan ƴar ka ne? Ko kuma so kake tsinuwar ta waiwayo har cikin ahalinmu? Sam ba zai taɓa yuwu ba! Dole ma a canza mata suna" Mardid wannan hakan bai ɗaga masa hankali ba ya gyara tsayuwa yace, "Ina ji a jikina wannan Jaririyar bata daga cikin waɗanda Tsinuwar Boka Bugudur zata hau kanta, ina ji a jikina daban take da sauran ƴaƴa. Jarirai da dama sun rasa rayuwar su da dama wasu ma daga ranar da aka ambace su da Sunan Muhaibish kwana ɗaya basa ƙarawa suke mutuwa, amma wannan bazai karya mini gwiwa ba domin na tabbata akwai wani al'amari ɓoyayye dangane da rayuwarta, amma ka gafarceni Kawu idan maganata ta sosa maka rai" Ai kuwa kamar jira suke haka suka yo masa caaa kowa da abin da yake gaya masa, ban da zagin Kyauta babu abin da suke yi da aibanta ta. Ɗaukan ƴarsa ya yi ba tare da yace musu uffan ba ya riƙo hannu Kyauta da take kuka suka wuce cen sashensa. Suna shiga Kyauta ta saki kukan da take riƙewa tun daga cikin fadar ta su, kallanta ya yi yana jin wani irin babu daɗi aransa, janyo hannunta ya yi ya zaunar da ita yace, "Kiyi haƙuri! Dama nasan haka sai ta faru saboda ba ƙaunarmu suke ba" Kyauta ta kalleshi da jajayen idanuwanta ta ce, "Ka san da haka me yasa zaka saka mata sunan da zai zame mana matsala gabaɗaya, kana ji fa yace mutuwa yara suke itama so kake mu rasata, daga haihuwa ko zafin haihuwarta bai gama sakina ba? Wai ma wacece wannan Muhaibish ɗin da ambatar sunanta na ga duk ya firgita su, wacce irin tsinuwa ce Bokan ya yi mata, baka gudun tsinuwarsa ta shafi zuri'armu gabaɗaya? Gaskiya ka sauya mata suna saboda banasan na zama silar rabuwar kawunanku, gani zasu yi nice nake saka komai tun da dama ba ƙaunata suke ba." Yana gama sauraronta ya sakar mata wani lallausan murmushi kamar babu wani abu da yake damunsa sannan yace, "Ki kwanta ki huta kina buƙatar hutu saboda jikinki babu ƙwari" wani irin haushi ne ya kamata nan take hawaye ya ci gaba da shatata, kallansa ta yi ta ce, "Babu wata nutsuwa da zan iya samu matsawar baka sanar da ni ainihin waɗannan tambayoyin da nayi maka ba" Ganin da gaske take yasa yace, "Muhaibish wata shuɗaɗɗiyar shugabarmu ce, zamu iya kiranta ta uwarmu gabaɗaya a Jinsin Aljanu. Wani abun ta aikata wanda mu mun ɗauke shi a matsayin gagarumin abun kunya, ku kuma a jinsinku wannan abin da tayi ba komai bane. Hasali ƙiyayyar da ƴan uwana suke miki akwai wani ɓurɓushin dalili da suke kallo yasa suka ɗora miki wannan karan tsanar, wanda ya faru ne sanadin ƙaddarar Muhaibish. Macece da wannan tsayuwar tawa bazata wadatar da ni na baki ainihin labarin halayenta na gari ba, sai dai wani kuskure da ta aikata tsakaninta da jinsin bil'adam yasa Babban Bokanmu na wancen ƙaranin ya fusata har ya tsine mata, wannan tsinuwar ce take bibiyar duk wanda ya saka wa ƴarsa suna Muhaibish. Na san zakiyi mamaki yadda jarirai suke mutuwa amma ba'a daddara wasu suke ƙara saka sunanta, labarin me tsayin ne akwai ɓoyayyun al'amura dangane da ita. Sannan bayani ya gabace mu cewar za'a haifi Yarinyar da zata ci sunan Mahaibish matsawar ta haure kwana da wuni bayan raɗin sunan batare da ta mutu ba, wannan yarinyar ita zata kasance Muhaibish ta wannan ƙarnin, bazan ce miki komai akan baiwar da yarinyar zata taso da ita ba, matsawar ya kasance Muhaibish ɗinmu ce. Ina ji a jikina ita ɗin ce ma saboda mafarkan da na dinga yi a cikin bacci na, ki kwanta ki huta kina buƙatar hutu" Kyauta kamar wacce aka zarewa laka a jiki haka ta zaunn daɓas tana tunanin wannan rayuwa da zasu fuskanta. Tana shirin kwanciya ta ji dirowar tafkeken wani tsuntsu a tsakiyar bukkarsu me ɗauke da kawuna biyu, a razane Kyuta ta ja da baya Mardid ya haɗe fuska dan ganin yadda suke neman tsoratar da matarsa. Kafin ya yi wani yunƙuri Tsuntsun ya fara magana cikin harshen jinsin su, "Ka gaggauta fito da matarka domin gabatar mata da wankan al'ada na masu jego ita da ƴarta" ƙirjinsa ne ya buga har sai da yaji ƙafafuwansa suna neman kasa ɗaukansa, "Ta ya zasu ce agudanar mata da wankan al'ada bayan sun san ba jinsun su bace? Anya ba da biyu suka yi hakan ba tun da sun san ba za ta iya ɗauka ba?" Yana cikin tunani ya kuma riskar maganar tsuntsun yana ci gaba da cewa, "Idan kuka ɓata lokaci kasan hukuncinta" yana gama faɗa ya bi ta jikin bukkar ya fice.


Ɗagowa tayi ta kalleshi dan bata fahimci wane irin wankan al'ada ne suke zancensa ba, tausayinta ne ya kamashi yana jin anya zai iya ci gaba da zama a cikin masarautarsu kuwa, tuno halin da Mahaifinsa yake ciki da wasiyyar da Kaka ya bashi ya yi, nan take hankalinsa ya ƙara tashi. Katse masa tunani tayi da cewar, "Mu je kiran da suke mana banasan ka ƙara laifi a wurinsu." Motsa bakinsa ya yi a sanyaye yace, "Kyauta ba za ki iya ba, sam ba za ki iya jurewa ba saboda ba al'adarku bace." Murmushin ƙarfin hali ta ƙaƙalo ta ce, "Ka daina tunanin akwai wani abu na daga al'adarku da zai gagareni tun da ni na amince zan iya zama da kai" Ta ƙarasa faɗa tana riƙe hannunsa suka nufi hanyar waje har lokacin hannunsa na rungume da Muhaibish. Suna fita cen farfajiyar masarautar cike gurin yake maza da mata manya da yara, wani fili aka zagaye wanda wata ƴar ƙoramace a tsakiyarsa. Ruwan jawur yake da wasu ɗaiɗaikun korayen furanni, gefe waɗansu irin duwatsun ne masu ruwan zaiba sai wani farin yashi da yake ta walƙiya yana ɗaukan ido.


Kyauta da take jinta cikin ƙwarin gwiwa suna zuwa wurin taji gabanta na faɗuwa, karɓar Muhaibish Luliya tayi ta ɗaga sama sannan ta damƙi yashin ta birsine ta da shi gabaɗaya, kuka take tsalawa kamar ranta zai fita. Duk yadda Kyauta taso dakewa ji tayi ta kasa, cikin kuka ta kalli Mardid da ya sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "Ka karɓo min ƴata wallahi kasheta za su yi" girgiza mata kai ya yi yace, "Babu abin da zai yi mata wannan kukan da take yi yana da nasaba da ɗigon jinsin jikinki, sai dai tsorona bansan yadda naki wankan zai kasance ba" Shiru tayi zuciyarta na bugawa tsakanin uwa da ɗa sai Allah, Kyauta ji take inama wankan yashin da suke wa Muhaibish ta karɓeshi ya dawo kanta. An ɗauki lokaci me tsawo ana yiwa Muhaibish wankan al'ada da kala-kalan kayan al'adarsu sannan aka kira Kyauta, tana zuwa da ƙarfin tsiya suka dannata cikin wannan ruwan ƙoramar, wata irin azababbiyar ƙara ta ƙwallah saboda azabar da ruwan yake yi mata a jiki. Jikinta ne ya fara sauya launi zuwa baƙi-baƙi nan take fatarta ta fara darewa. Mirdad na ganin haka ya bazama da gudu da niyyar ciro Kyauta da sauri ƴan uwansa suka shatalo shi suka danne shi suna cewa, "Yadda ake wa matanmu babu abu ɗaya da za'a raga mata."




😥Akwai tausayi wlh


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[23/11/2021, 18:54] Ameera Adam🌚: 34...






Mardid da ƙarfi ya shiga fisgewa yana ambatar sunan Kyauta amma bahaushe yace, "Sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi." Mardid yana ji yana gani haka Kyauta ta ci gaba da kwarara ihu wanda da alama tana yin sa ne ba tare da tana cikin hayyacin ta ba, Bayan an fito da ita daga cikin wannan ƴar ƙoramar jikinta gabaɗaya ya yi wani fatsi-fatsin baƙi ga fatar jikinta duk ta daddare, ko numfashi da ƙyar take sauke shi sabida wahala idanunta arufe suke jikinta duk ya saki kamar wacce babu sauran numfashi a jikinta. Kwantar da ita suka yi sannan suka ɗauko farin yashin nan suka fara fursuna mata a jikinta, a zabure ta miƙe ta zuba a guje cikin fitar hayyaci tana ta zabga gudu tare da kwarara ihu me ban tausayi. Gabaɗaya kallon gurin da tayi suka yi suna ƙyakyacewa da wata irin dariyar mugunta, Mardid na ganin haka ya zabura cikin ƙaraji yana kwalla ƙara tare da ambatar sunan Kyauta, suna hango ta har ta nufi wajen wani murgujejen dutse kai tsaye ta faɗa kai kanta ya bugu da dutsen ta faɗi cen gefe a sume kanta da hancin ta na zubda jiki. Ɗaya daga cikinsu suka ta sa da sauri ya je ya ɗaukota ya dawo da ita wurin da aka fara kwantar da ita, rirriƙe ta suka yi suka ci gaba da shafe mata jiki da farin yashi. Azabar zafin da ya ratsa cikin jikinta ne ya farfaɗo da ita daga dogon suman da tayi, a zabure ta miƙe wannan karan ko kuka ta kasa yi sai binsu take da wani irin kallo kamar mai taɓin hankali, wani garin koren ganye suka fara fesa mata nan take ta kuma kwanciya jikinta na wata irin karkarwa kamar me jin sanyi. Sai a lokacin suka saki Mardid wanda yake kwance a gurin rai a matuƙar ɓace, da gudu ya tafi gurin ta yana kururuwar kiran sunanta amma ko kallan gurin da yake bata yi ba saboda batasan ma abin da yake faruwa ba. A haukace ya ɗauketa be tsaya ko ina ba sai cen sashensa ya kwantar da ita, yana ƙare mata kallo da yadda jikinta ya saluɓe kamar wacce aka tsoma a cikin tafasashen ruwan zafi. Saboda tsabar firgice ya manta da Muhaibish da ke cen a hanunsu, hannuwansa ya kalla yaga fatar jikinta ce manne akan tafin hannunsa gurin da ya ɗauke ta, rushewa ya yi da kuka yana buga ƙasa tare da jin ƙiyayyar ƴan uwansa a zuciyarsa, sai dai yasan ko yana hauka bazai iya ja da su ba saboda sun fi ƙarfinsa. Ganin kukan bazai fissheshi ba yasa ya miƙe ya bazama tsinkar ganyayyakin da zai haɗa mata magani da shi, ya daɗe da fita sannan ya dawo ya fara murza ganyayyakin a cikin ruwa yana yayyafa mata. Wani irin gurnani take yi tana girgiza kanta, sai dai anci sa'a jikin nata ya daina karkarwa sai wani irin gumi da yake karyo mata, saboda yawan gumin har ɗiga yake a ƙasa kamar tsamowarta kenan daga ruwa. Yana nan zaune yana kallon halin da take ciki Ɗan ƙanin Mahaifinsa ya shigo hannunsa ɗauke da Muhaibish, a fusace Mardid ya karɓeta ya rungume yana kuma fashewa da matsanancin kuka. Kuka ta fara yi ya rasa yadda zai yi mata ruwa ya ɗauka ya bata ta sha sannan ya kwantar da ita ta ci gaba da bacci.


Kyauta sai da ta kwana biyar a wannan halin batasan wanda yake kanta ba, a kwana na shida ne ta farfaɗo lokacin Mardid na tsugunne yana shafa mata maganuguna, suna haɗa ido daɗi ya kama shi har sai da yaji kamar ya rungumeta, sai dai da ya tuna raunin jikinta yasa ya sakar mata murmushi yana mata sannu. Bata amsa masa ba ta yunƙura ta tashi zaune tana bin jikinta da wani irin kallo, sai a lokacin komai ya dawo mata hawaye ta fara yi cikin sanyin murya Mardid yace, "Sannu ya jikin?" Sam bata ji me yace ba sai dai ta ga yana motsa baki, a hankali ta buɗe baki ta ce, "Ina Muhaibish?" Motsa baki ta ga ya yi sai kuma ta ga ya nuna mata cen gefe da ta hango ta tana bacci. Cikin damuwa ta ce masa, "Ni fa bana jin ka bana jin abin da kake faɗa naga dai kana motsa baki."


Mardid ya zaro ido yace, "Kyauta bangane bakya ji na ba har yanzu bakya jin abin da nake faɗa?" Ganin ya daina motsa baki yasa Kyauta ta kuma cewa, "Ban san me ya samu kunnuwana ba amma banajin komai" daga wannan lokacin Kunnuwan Kyauta suka daina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login