Showing 36001 words to 39000 words out of 57328 words
ba ƙaramin kyau da kwarjini ya yi mata ba sai dai fuskarsa a murtuke take babu alamun fara'a ko kaɗan. Goge hawayenta ta fara yi sannan ta fara takawa a hankali tana murza ɗan yatsan hannunta, sai da ta matsa gabda shi ta miƙa masa hannunta tana zubda ƙwallah murya na rawa ta ce. "Dan Allah koda bazaka tuna ni wacece a gurinka ba ina san ka kama hannuna ka sumbace shi ko da sau ɗaya ne a wannan karan ko zan ji daɗi. Wannan zoben da ka bani ne dan Allah kayi mini kallan rahama ko naji daɗi acikin zuciyata ta yadda zan ginga tuna irin kallon da kayi mini." shiru ya yi yana kallanta cikin zuciyarsa yana cewa. "Wannan wacce irin mayyar yarinya ce haka?" Kuka take sosai ta tsugunna a dai-dai ƙafafuwansa ta haɗa hannuwanta guri ɗaya alamun roƙo ta ce. "Nasan kana jin abin da nake ji a cikin zuciya inda haka ba bazaka taɓa zuwa gurin nan ba, dan Allah karka juya mini baya indai zaka amshi soyayyata a shirye nake na bijirewa umarnin Mahaifina da Mahaifin Maleek saboda ni ba matarsa bace." kukanta ne ya tsananta tana yi ƙirjinta na wani irin suya sannan ta ci gaba da cewa. "Wallahi ni ba ta shi bace kaine nawa kaine wanda na aminta da shi kaine wanda mukayi alƙwari tare duk wuya duk rintsi bazamu gujewa juna ba amma me yasa zaka yi mini haka, nice wacce ka sadaukar da komai naka akaina nice wacce aka azabtar da kai akaina nice wacce take ɗauke da cikinka Ɗanka ko Ƴarka, dan Allah ceci rayuwa wallahi bazan iya jure rashinka ba" wannan karanma kukanta ne ya tsananta nan take ta ƙware tare da fara wani irin tari tana fesar da jini daga bakinta, zaro ido ya yi yana mamakin kalaman da take faɗa ko kaɗan bai ji tausayinta ko ɗar a zuciya ba har sai da ya ga ta fara aman jini, sai da ta tsagaita sannan ya ciro wani ƙaton ƙyalle ya miƙa mata. Sororo ta tsaya tana kallansa da mamaki murna ce ta kamata a tunaninta ya fahimci abubuwan da take gaya masa da sauri ta karɓa ta fara goge bakinta, sai da ta gama sannan matsa gabda da shi tana wara hannuwa alamar zata rungumoshi.
Da sauri ya ja baya bata damu ba ta ƙara matsowa ta fara jikinsa tana sauke wata irin ajiyar zuciya tana runtse idonta ta fara hango rayuwar da suke gudanarwa, da sauri ya yakice ta yana kifeta da wani irin mari kafin ta dawo hayyacinta ya ƙara ɗauketa da mari, ba marin ne ya ɗaga mata hankali ba illa rabata da jikinsa da ya yi shine babban abin da ya sa ta cikin damuwa. Hancinta ne ya fara ɗigar da jini hawaye na zuba daga idonta, da sauri ta riƙe hannunsa tana ja suka nufi hanyar rafin da take hangowa sai da suka je bakin rafin ta nuna masa tana cewa.
"Kalli nan shin baka ga abin da nake gani ba? Shi ka manta ƙoramar da muke gudanar da soyayyarmu, ka manta a nan gurin na sanar da kai abin da yake cikin cikina, ka manta irin albishir ɗin da kayi mini nida abinda zan haifa." hawaye ne ya ci gaba da tsiyaya daga idanunta ta ce. "Karka manta nan gurin anan ne aka tarwatsa farincikinmu dam Allah karka bari wannan karan suyi galaba akanmu" Kallan ramin gurin da yake cike da tarin bola ya yi sannan ya kalli Maryo yace. "Waɗannan abubuwan da kika faɗa a cikin nan abun ya faru?" da sauri ta gyaɗa kanta. Jinjina kai ya yi ya ja dogon tsaki sannan yace. "To banyi mamaki ba wataƙila aljanune kikayi rayuwa da su a cikin wanan ƙatuwar bolar amma ba ni ba" yana gama faɗa ya fisgi hannunta suka koma cen inda suka fara tsayawa da farko sannan ya wurgar da ita da ƙarfi har kanta ya bugu da jikin bishiya ya fashe ya kalleta a fusace yace. "Wannan ya zama karo na ƙarshe da zan gargaɗeki wallahi-wallahi kika ƙara yi mini makamancin irin wannan saina karkaryaki na watsar, banz karya banda mace mara aji kina da aure me zaki yi da wani namijin Allah ya tsareni daga kaidinki." Yana gama faɗa ya juya ya nufi hanyar cikin gari dan dama ganyen magarya yaje cira ya haɗu da ita, fasa cirar ganyen ya yi koma gida rai a ɓace. Maryo kuka ta rushe da shi a gurin kamar ranta zai fita fuskarta tayi jawur ta kumbura kamar wacce ta kwana ta wuni tana kuka, ƙyallen da ya bata ta rungume tana jin wani irin sanyi a zuciyarta. Sai da ta yi kuka mai isarta sannan ta miƙe ta nufi cikin gari tana haɗa hanya.
Maryo duk daɗewar da tayi tana zuwa gurin da ta bar bayin da suka zo tafiya da ita a inda ta barsu a nan ta samesu, gaba ta wuce suna biye da ita a baya har cikin sashen Fulani Maryama. Lokacin da Maryo ta shiga kallo ɗaya ta yi wa Fulani Maryama ta ɗauke kanta gefe, Jakadiya da wasu bayi ne suka ɗauki Maryo aka shiga wani ɗaki da ita dan shirya ta. Fulani Maryama da har lokacin cikin jimamin sabon labarin da ya zo mata take yi ta kalli Fulani Fahima ta ce. "Nifa har yanzu mamaki nake ace wai Shukra ita take rayuwa a gidan nan batare da wani ya sani ba sai yanzu" Fulani Fahima ta ce. "Yaya Maryama kenan kinmanta yadda auren Maleek ya kasance kina ganin yarinya ƙwaƙwaran zaman wata biyar ba muyi da ita ba fa. Kinsan fa ko lokacin da ya zo mana da ita cikin jikinta ma ya girma, kinga kuwa ta ya za'ai wani ya santa a nan mu kanmu a waccen masarautar ba kowa ya santa ba" Fulani Maryama tayi zuru kamar me nazari a gefe guda kuma farinciki ne mamaye a zuciyarta tun da tasan ko ba komai zasu rabu da alaƙaƙai, babban farincikin ta da Salman bazai samu Maryo a matsayin matar aure ba. Ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "To Allah ya bada zaman lafiya gaskiya yarinyar akwai hankali" cikin jindaɗin addu'arta Fulani Fahima ta ce. "Ameen bari na zagaya gurin su Yaya Bilkisu na dawo"
Maryo ce aka fito da ita cikin shiga ta alfarma sanye take da alkyabba silva da ratsin ja, ba ƙaramin kyau tayi ba sai zuba ƙamshi take kamar wacce aka ciro daga cikin kwalbar turare, gashin kanta aka wanke aka gyara kamar bashi ba. Fulani Maryama ba ƙaramin razana tayi da ganin irin kyawun da tayi tai ba, suna haɗa ido gabanta ya faɗi. Jakadiya sai sunne kai ƙasa take lokaci-lokaci taje tamke kanta dan kar ɗankwalinta ya zame ta sha kunya. Kai tsaye fadar Sarki Aminullah aka wuce da ita sai dai har lokacin fuskarta sata koma dai-dai ba saboda irin kukan da ta sha, babu yadda basuyi da ita ba akan ta bada ƙyallen hannunta amma fir taƙi babu yadda suka iya haka suka haƙura suka ƙyaleta da shi. Suna shiga aka zaunar da ita a gaban Sarki Aminullah da Sarki Abdallah, zamanta babu daɗewa su Inna Habi suka shigo bayan zaman su Fulani Fahima ta shigi fuskarta ɗauke da murmushi. Sarki Aminullah ne ya fara magana. "Assalamu alaikum. Dukan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin talikai, mun godewa Allah da wannan al'amari ya faru har gashi Maleek da iyayensa zasu koma da matarsa wato Shukra. Amma ke Habi muna so muji alaƙarki da Shkra tunda Maleek ya shaida mana cewar akan idonsa aka kashe mahaifiyar Shukra wannan dalilin ne yasa har ya ceci Shukra daga ƙarshe kuma har Allah ta ƙaddara ta zama matarsa?" Cikin Inna Habi ne ya kaɗa saboda ko kaɗan bata taɓa zatan zata iya fallasa wannan sirrin a gaban Maryo ba amma babu yadda ta iya idan tace ita ta haifeta zasu ce ina shedarta ita kuwa bata da wata shaida. Gyara zama tayi tace. "Allah ya taimakeka a hanya muka haɗu da ita ganin haka yasa na riƙe ta itama ta zama kamar ƴata saboda gujewa faɗawa cikin ruɗin zamani" Sarki Abdallah yace. "Ina ƴan biyun da ta tafi da su?" Inna Habi shiru tayi dan batasan me zata ce ba." Maryo tayi karaf ta ce. "Duka Allah ya yi musu rasuwa" lokaci ɗaya suka nuna jimami sannan aka yi musu nasiha sosai daga ƙarshe Sarki Aminullah yace an ɗaga likafar su Inna Habi sun tashi daga matsayin Bayin zuwa ƴaƴan cikin gida. A dai wannan lokacin ne ya zartar da cewar zaman Inna Habi zai koma Sashen Fulani Maryama yayinda Abu zata koma sashem Fulami Zaliha da zama. Daga ƙarshe akayi addu'o sannan suka rufe taron Sarki Aminullah da iyalansa suka fita da jiyyar tafiya Masarautar su.
Maryo jikin Inna Habi ta faɗa tana wani irin kuka mai tsuma zuciya haka itama Abu, da ƙyar aka cire Maryo daga jikinsu suka wuce da ita bakin mota. A dai-dai nan gurin Salman ya ƙarasa gurun fuskarsa ɗauke da murmushi ya miƙawa Maleek hannu yace. "Shar kake yau sabon Ango ina ta ya ka murnar samun Shukra Allah sanya alheri" Maleek ya yi mamakin yadda Salma ya sake masa fuska saboda yaga rabuwar baram-baram suka yi, shima mayar masa da martanin murmushi ya yi sannan yace. "Ameen ya rabbi Ɗan uwa, kaima ya kamata kayi gaggawar fito da mace ko mu kaɗa maka gangar gwauro" Salman ya saci kallan Maryo cikin zuciyarsa yace mata. "Amaryar Maleek ki shirya takaba, babban albishiri tuni Furzaan antura masa matar da zai aure dole dai ni ɗin nine mijinki" Maryo ta watsa masa harara ta mayar masa martani da. "Maleek bazai mutu ba sai dai kai ka muti saboda zuciyarsa me kyau ce, Kaidinka zai koma kanka domin Furzaan ni kaɗai ce ta shi bazai taɓa auren wata ba, kuma zai yi biyayya ga Maleek domin ko kaɗan banjin haushin abin da ya yi ba wataƙila yana da gaskiya bansani ba ko na taɓa rayuwa da shi a baya." Maleek ne ya ce. "Salman kayi shiru hirar ce baka so?" Fulani Maryama tayi karaf ta ce. "Maleek kaga kaja matarka ku tafi karka biyewa wannan sakaran" Maryo yana buɗewa ƙofa tana ɗaga kai ta hango Saif dake hango su yana zaune a cikin rumfa nan take ta fara zubda hawaye, jiki babu ƙwari ta shiga motar su Inna Habi na ɗaga mata hannu suna kuka, Sarki Abdallah ne ya yiwa Sarki Aminullah sallama sannan motocinsu suka tashi suka nufi garin Adamawa.
Magariba liƙis suka sauka a Masarautarsu kafin zuwansu anshirya musu tarba da kayan ciye-ciye kala-kala, Maryo wucewa da ita akayi sashen Fulani Fahima ruwan wanka aka shirya mata sannan ta shiga tayi wanka ta ɗauro alwala ta fara gabatar da sallolin da ake bin ta, bayan ta idar aka shirya mata kayan ciye-ciye a gabanta amma gabaɗaya a ciki lemon inibi kawai ta iya ɗauka ta sha daga haka ta ce musu ta ƙoshi, basu takura mata ba suka ƙyaleta. Kan shimfiɗa ta alfarma aka kai Maryo gurin baccinta Maryo tun da ta kwanta ta kasa runtsawa banda hawaye babu abin da take yi har gari ya waye.
Washegari Tun da gari ya waye Fulani Fahima ta fara haɗawa Maryo kayan gyara na mata kala-kala, saboda ta ce bazat tare ba har sai bayan sati guda da zuwansu. Maryo babu yadda ta iya haka take turawa tana ci wani taci ya zauna wani kuma ta amayar da shi. A ranar da ta cika kwana bakwai da gidan da daddare aka shiryata cikin rantsattsatsun kaya masu kyau sai zuba ƙamshi take, har sashen da aka ware gurin zamansu da Maleek aka kaita tana shiga ta samu bakin gado ta zauna gabanta na dukan uku-uku. Cikin shauƙin ƙauna da kewar matarsa ya tako ya ƙarasa gurinta yana zame mata alƙyabbar dake jikinta, sanye take da wata doguwar rigar mai adon duwatsu an naɗe mata gashin kanta ba ƙaramin kyau tayi masa ba. Kiss ya manna mata a goshi sannan ya ce. "Shukra nayi kewarki na tsawon shekaru dan Allah nan gaba karki ƙara hukuntani da irin wannan hukuncin domin ba zan iya ɗauka ba" Maryo shiru tayi har lokacin gabanya faɗuwa yake, miƙewa ya yi yace. "Tashi ki ɗauro alwala mu gabatar da Nafila domin wannan ranar jin ta nake kamar sabon ango ya zama wajibi mu godewa Ubangiji." Kama hannunta ya yi ya nufi banɗaki da ita sai da ya tura mata ƙofar ya ce ta shiga. Tana shiga ta fara alwala ta ga hannunta ya yi wani irin bau dai-dai gurin da ya riƙe mata hannu nan take ta ga jini na tsatstsafowa daga gannun, ruwa ta sa ta wanke sannan ta fara gabatar da alwala. Bayan ta fito sallah suka gabatar ya jima yana addu'a sannan ya fara ciyar da Maryo naman ƴan shiloli, sau biyu kawai ta karɓa ta ce ta ƙoshi dan har lokacin hannunta raɗaɗi yake mata. Bayan sun kammala koma Maleek ya riƙe hannunta suka koma saman gado cikin kewarta ya miƙa hannu ya fara shafa mata fuska cikin so da ƙyauna. Lokaci ɗaya ya ga ta yi wata girgiza harsai da gadon da suke kai ya motsa. Ɗaya bayan ɗaya ya dinga ganin me siffar Maryo na tashi daga jikin tana dira a kusurwar bango harsa da guda biyu suka fita daga jikinta, Maryo ce ta miƙe ta dira ƙasa itama ta koma kusurwar bango ta tsaya, ɗayan kusurwa da ta rage babu kowa ya ga alamar inuwar namiji a atsaye. Ta farkon ce ta fara cewa. "Muhainish ba matarka bace" sai ta biyun ta ce. "Kalimsiyat ba matarka bace" sai ta ukunsu ta ce. "Rayzuta ba matarka bace, sauran duk suna da mazajensu dan haka nima ga mijina nan" ta faɗa tana nuna inuwar dake jikin ɗayar kusurwar bangon.
KARFA KU SHIGA RUƊU IDAN KUN TUNA BAYANIN BOKA TUN A SHAFI NA UKU DAMA YACE SHUƊAƊƊUN RUHIKAN ƳAƳAN SARAKUNAN ALJANU NE ZASU TASHI KARSHE SU YADA ZANGO AKAN TA UKUNSU, DAN NAGA KAMAR WASU SUN RIKITA DA LABARIN HARDA MASU CEWAR KO WANI LAIFI SUKA AIKATA😂😂 SAM BA HAKA BANE KU DAI MUJE ZUWA MU HAƊE A COMMENTS🤾🏻♀️
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[13/11/2021, 19:30] Ameera Adam🌚: 27...
Maleek ja ya yi da baya cikin tashin hankali, binsu yake da kallo ɗaya bayan ɗaya jikinsa ban da karkarwa ba abin da yake yi. Inuwar da ke kusurwar bangon ce ta fara takawa a hankali zuwa gurin Maryo dake kusurwar kudu, dafa shi tayi ta ce. "Ashe kana tare da ni kake ƙoƙarin juya mini baya?" Maleek zaune yake yana kallon ikon Allah. A hankali ya fara karanta ayoyin tsari yana tofa musu nan take fara bajewa ta jikin bango suna ɓacewa, Inuwar da ke jikin bangon ce ta bi ta jikin bango ta ɓace itama Maryo ta yanke jiki ta faɗi a gurin. Ajiyar zuciya Maleek ya sauke yana runtse idanuwansa, a hankali ya miƙe ya ƙarasa bakin gurin da Maryo take kwance ya sa hannu ya ɗaukota ya ɗora ta akan gado sannan ya koma banɗaki ya ɗauro alwala ya fara gabatar da sallar nafila. Maryo ba ita ta farka ba sai cen tsakiyar dare jikinta banda raɗaɗi babu abin da yake yi, daga ɓangaren Maleek shima hannuwansa ɗaɗi suke yi masa Kamar yadda jini yake kwanciya a jikin Maryo haka shima hannuwansa suka yi jawur da taruwar jini, ita kuwa Maryo jikinta har tsatssafar da jini yake yi a hankali take kai hannu tana sosa jikinta ganin haka yasa hankalin Maleek ya tashi, ƙarasawa ya yi gurinta yana mata sannu idanunta cike da hawaye ta ɗago ta kalleshi ta ce. "Jikina zafi yake yi mini dan Allah ka daina taɓa ni" Ba ƙaramin tausayi ta bashi ba saboda yadda take maganar zaka fahimci daga cikin zuciyarta maganar take fitowa. Yana san ya janyota jikinsa ya rarrasheta amma yana tsoron taɓa ta saboda yadda shi kansa jikinsa yake masa raɗaɗi bare kuma ita da har jini yake fita daga jikinta. Fuskarsa ɗauke da damuwa yace. "Shukra!" Ya faɗa yana kafeta da dara-daran idanuwansa, ɗauke idanuwanta tayi saboda ba ƙaramin kwarjini ya yi mata ba, hasali wannan shi ne karo na farko da ta kaɗaice da wani Ɗa namiji a rayuwarra, sunkuyar da kai ƙasa tayi tana tuna soyayyarta da masoyinta nan take ta ci gaba da zubda hawaye. Hannu ya miƙa zai rungumota sai kuma ya fasa ya ci gaba da magana yana kallonta. "Shukra yaushe kika gamu da wannan lalurar, tun da nake da ke ban taɓa ganin haka daga gareki ba. Dubi hannuwana" ya faɗa yana nuna mata hannuwansa da suka yi ruɗu-ruɗu musamman da yake farin mutum hannuwan sukayi jawur kamar ka taɓa jini ya zuba" Maryo shiru tayi tana jinsa daj ita kanta bata taɓa fuskantar haka ba ko dan ita tunda take idan aka cire Saif babu Namijin da ya taɓa riƙe ta har ya kai ga ya rungumeta. Ɗagowa tayi tana kallonsa har lokacin hawaye be kwance a fuskarta, karantar yanayinta ya yi cikin wata irin murya yace. "Shukra me yasa bakiyi farincikin dawowa gareni ba? Tun da muka haɗu a koyaushe babu abin da nake gani a fuskarki sai hawayen baƙin ciki, Me nayi miki ne? Ko bakyasan ci gaba da zama dani?" da sauri ta ɗago da kanta tana kallansa kamar zata amsa masa sai kuma ta girgiza kanta tana ci gaba da hawaye. Shiru ya yi yana nazari sannan yace. "Shikenan ki kwanta ki huta" kwanciya tayi ta rumtse idonta tana jin zuciyarta na yi mata suya, lokaci ɗaya tunanin Saif ya faɗo mata haka ta ci gaba da hawaye. Ƙyallen da ya