Showing 21001 words to 24000 words out of 57328 words

Chapter 8 - Anya Baiwa Ce 1 Complete Hausa Novels.txt

30 Nov 2024

3899

Jakadiya bayan sun gaisa, Jakadiya take kallon Inna Habi a watse. Ita kuwa bata lura da irin kallon da take mata ba yasa Inna Habi ta ce. "Jakadiya dama zuwa nayi naji ko da wanda yasan ɓangaren da Maryo take kwance naji ana raɗe-raɗin wai Uwar bayi na gurinta, shi ne nazo dan naji ko wata tasan gurin da take" Jakadiya ɗage hanci gefe ɗaya ta yi sheƙeƙe ta kalli Inna Habi ta ce. "Habi Kya tambayi kaza hanyar rafi ki tambayi agwagwa kisha labari, ni zane na fiku da zan fiku sanin ɓangaren da Maryo take? Duk fa tare muke da ku a cikin gidan to hana rantsuwa dai na je filin wasan al'ada ke baki je ba banda nan ina na leƙa? Ki tambayi wasu ƴaƴan masanan ko sun sani amma ba ni ba jikar Hudu"


Inna Habi bata ji daɗi ba sam a sanyaye ta miƙe tana kallan Jakadiya ta ce. "Allah ya baki haƙuri Jakadiya" Ai kuwa kamar ta watsawa Jakadiya ruwan zafi a zafafe ta ce. "Ki dai bawa kanku haƙuri Habi ku dai kuke cikin bala'i banda ma Allah ya fitar da ku amma bansan tsiyar da zaku samu ba idan Maryo ta kashe Takawa, kinsan dai har abada ba karagar Mulki ba ko sarautar Sarkin Dogarai bazaku samu ba." Inna Habi idanunta ne suka ci ko da ƙwalla zata fara tafiya wata matashiyar Baiwa ta ƙaraso gurin jikinta sanye da kayan bayi, kusan gware sukayi da Inna Habi da sauri matashiyar budurwa ta ce. "Wayyo sannu Inna ban sani bane." Inna Habi ta ce. "Ba komai yarinya" Jakadiya dake gefe ta ce. "Ina zaki lura yara sai tsinannaniyar rawar ya na balagaggen ƙadangare" daga Inna Habi har Baiwar babu wanda yabi ta kan Jakadiya. Inna Habi har tayi nisa Baiwar ta bi bayanta ta ce. "Inna naji kamar tambayar gurin da Maryo take kike yi ko?" Inna Habi ta ce. "Eh yarinya"


Baiwar ta ce. "Ɗazu naje gurin idan kina so sai na raka ki" kafin Inna Habi ta bata amsa Abu ta ƙaraso gurin da mamaki take bin Baiwar da kallo dan sam bata santa a cikin gidan ba, Inna Habi ta ce. "Na gode kuwa yarinya amma kamar ban waye ki ba" Abu tayi karaf ta ce. "Gaskiya nima a cikin gidan nan bansan ta ba ko kuma baƙuwa ce?" Baiwar murmushi tayi ta ce. "Eh baƙuwa ce sunana Hikbiyat" Inna Habi da Abu suka kalli juna suna maimaita sunan cikin haɗin baki. Basarwa tayi ta ce. "Yanzu zan kai saƙon fulani Zaliha na dawo idan nazo sai mu tafi." Inna Habi ta amsa tana godiya sannan Hikbiyat ta wuce.


Abu da mamaki ta ce. "Inna ina zaku je kuma?" Inna Habi ta ce. "Rakamu za ta yi Asibiti gurin Maryo" Abu washe baki tayi ta ce. "Kai amma naji daɗi wallahi, Allah sarki Maryo ko a wane hali take" nan take tausayin ƴar uwar tata ya kamata har idanunta suka ciko da ƙwalla.


Hikbiyat na shiga sashen Fulani Zaliha ta faɗa ɗakin Saif a lokacin yana zaune yana shan fruit hankali kwance, har ta shiga ɗakin ta gama tsayuwarta bai san da wani mai numfashi a gurin ba, ta jima a tsaye a kansa sannan ta juyo ta fice. Bata jima ba ta ƙarasa cen sashen Bayi ta yi wa su Inna Habi magana. Irin kallon da yawancin mutanen gurin suke binta da shi yasa ta fara shan jinin jikinta, a gurguje ta nemi su Inna Habi da su fito ta yi musu rakiyar dan batasan ko kaɗan a samu matsala. Suna fitowa suka nufi asibitin da yake daga gidan Sarki zuwa asibitin Murtala babu nisa da ƙafa suka tafi suna tafe suna hira, Hikbiyat haka ta saki jiki da su kamar wacce ta shekara ɗari da su, a cikin hirar ne ta fara bugar cikinsu akan lamarin Saif basu wani bata amsa yadda take buƙata ba saboda basa shiga ɓangaren Matan Sarki idan ba da wani ginshiƙin abu ba.Suna Ƙarasawa asibitin tuni anyi sallar magriba a gefen ƙofar shiga ɗakin suka samu su Uwar Bayi suna sallah, Hikbiyat ce ta fara ƙoƙarin shiga ɗakin wani securitie ya taso yana mata magana domin a wannan lokacin ba lokacin ziyartar marasa lafiya bane. Kwantar da murya ta yi cikin roƙo ta ce.


"Dan Allah ka taimaka wannan mahaifiyarta ce tun da aka kawota asibiti bata samu ganinta ba" Tamke fuska ya yi yace. "Ke banasan sakarci ai kun san doka ce ko Malama ku zo ku wuce."


Hikbiyat fakar idonsu Inna Habi tayi ta hura masa iska a fuska, Kamar wanda aka matsawa remove haka ya juya ko kalma ɗaya bai ƙara furtawa ba.Ta juya ta kalli su Inna Habi ta ce. "Inna kuzo mu shiga."


A dai-dai lokacin su Uwar bayi suka idar da sallar, da fara'arta ta fara yiwa su Inna Habi sannu da zuwa saboda dama tun tuni suke fargabar shiga gurin Maryo dan basu san abin da zasu gano ba." Gabaɗaya suka ɗunguma suka shiga Hikbiyat na gaba suna biye da ita a baya. Uwar bayi da mamaki ta kallo Hikbiyat ta ce. "Yarimya ke kuma wacece dan ban wayeki ba" Hikibiyat bata waiwaya ba tace. "Dama ba lallai ki waye ni ba dan ba zamanki nake yi ba."


A hassale Uwar Bayi ta ce. "Ke yarinya karki nuna mini tsageranci dan wallahi tsaf nayi jika da ke" babu wanda ya tankawa Uwar Bayi ita dai Inna Habi babban burinta ta shiga ta gano halin da Maryo take ciki. Shigar su ɗakin daga cen nesa da su kan sauran gadajen, waɗansu marasa lafiya ne guda huɗu, sai da Inna Habi ta yi musu ya jiki sannan suka wuce gadon Maryo.


Tana kwance idanunta a lumshe kamar me bacci, kana kallanta zaka fahimci zallar ramar da tayi ta rame sosai ta yi wani haske daga wuyanta sai ƙasusuwa.Suna zuwa da sauri Abu da Inna Habi suna rungume ta Inna Habi harda ƙwallarta, a hankali ta buɗe idanunta ta sauke su akan Hikbiyat da ke tsaye tana kallonsu cikin tausaya saboda irin soyayyar da suke nunawa Shugabarsu. Inna Habi ce ta ɗago ta kalli fuskar Maryo zata yi magana Maryo ta rigata.


"Inna yaushe kuka zo?" Abu ta turo baki cikin zolaya ta ce. "Au Inna kiɗai kika gani baki ganni ba ko? Lallai Maryo ba amana a tsakaninmu bari na tafi kya nemi wata ƴar uwar ba ni ba" Maryo ɗaga kai tayi ta kallo Abu cikin so da ƙauna ta ce. "Ni na isa wallahi sharrinki ne kawai Abu amma kinsan ko cikin dabbobi Zaki shine sarki dan haka Inna cen kan gaba kafin ke" Uwar bayi ido ta zura mata tana mamakin yadda ta ga Maryo ta ware tana maganar masu hankali, Inna Habi ta ce. "Maryo ya jikin naki" Maryo ta ce. "Da sauƙi Inna amma kaina na yawan ciwo kuma wallahi ina yawan jin tsoro" Inna Habi ta ce. "Ki daina jin tsoro kinji ƴata insha Allah babu abin da zai faru sai alheri." Maryo idonta ne ya ciko da ƙwallah ta ce.


"Inna kuma kun yarda zan iya cutar da Sarki, wallahi ni bansan komai ba aike na fa kawai Fulani Maryama tayi ta yaya zan iya cutar da Mahaifina" Inna Habi ta ce. "Dai-dai da ƙwayar zarrah ban taba gasgata maganar ba saboda nasan irin tarbiyyar da na baku tun kuna ƙanana, Allah ya dubi lamarinmu ya ga baki da haƙƙi a ciki tun da Allah ya kuɓuto da ke. Wani bawa ne yayi gasar ƙira a ƙarƙashin buƙatarsa shine yace a fito da ke." Maryo ta runtse ido ta ce. "Inna ko da bai fito da ni ba nasan zan fito kuma dan Allah karku kasankance da shi." Inna Habi bata bi ta kan zancen Maryo ba dan ta mata uzurin wasu maganganun nata ko harda zafin ciwo. Abu da ke gefe ta ce. "Amma Maryo gaskiya idan aka sallamo ki sai kin yi taka tsantsan saboda mugu baida kama." Maryo ta ce."Haka ne Abu amma bansan ribar da zasu samu a kaina ba, bayan ni ɗinma jinin masarautar ce" Inna Habi ganin ba su kaɗai ne a gurin ba yasa ta ce.


"Ba komai Maryo Allah dai ya kyauta ya kuma kiyaye gaba."


Maryo ɗagowa tayi ta kalli Hikbiyat ta ce. "Ya ake ciki ne" Hikbiyat russunawa tayi ta ce. "Shugaba babu wani abu me muni da ya faru yana cikin ƙoshin lafiya" Maryo wani malalacin murmushi ta saki ta ya bawa su Inna mamaki, da mamaki Inna Habi ta ce. "Maryo dama kinsan yarinyar nan ne?"


Maryo ta ce. "Na santa Inna Baiwata ce" Cikin haɗin baki gabaɗaya mutanen gurin suka furta. "Baiwarki" Cikin rashin damuwa da yanayin da suke ciki ta ce. "Eh" Uwar bayi kuwa ta ce da wa Allah ya haɗa ta inba da Maryo ba.


"Yau naga faɗin rai irin na talaka kina baiwa har ki dinga ƙafafar kina da baiwa, kai Allah wadaran naka ya lalace ashe shiyasa kike yunƙurin hallaka Takawa..." Wani mugun kallo Maryo ta wurgawa Uwar bayi tun bata ƙarasa maganarta ba taja bakinta ta tsuke.


Inna Habi ta dafa kafaɗar Maryo ta ce. "Maryo dan Allah ki dinga kiyayewa, mu zamu wuce kar dare ya yi mana Allah ya baki lafiya." Maryo ta ruƙo hannun Inna Habi ta ce. "Inna wallahi na gaji da zaman gurin nan" Abu ta ce. "Insha Allah kwana kusa za'a sallame ki kinji." Idanunta ne suka ciko da kwalla Inna Habi na ganin haka ta kauda kanta gefe ta miƙe ta yi mata sallama Abu ma sallama ta yi mata har zata tafi Maryo ta ruƙo hannunta ta ce. "Maryo har yau bai zo ya duba ni ba alhalin yasan harda nauyinsa nake tafe, da shi nake kwana nake tashi bansan a wane hali yake ba." Abu sunkuyowa tayi dan kar sauran mutanen su fahimci inda zancen su ya dosa ta ce. "Wa kenan wai kina nufin Saif?" da sauri Maryo ta ce. "Eh shi bai zo gurina ba Abu, dan Allah idan kun koma kije ki sanar da shi halin da nake ciki wataƙila bai sani ba"


Wani kallo Abu take mata na lallai baki da hankali sannan ta ce. "Maryo kanki ɗaya kuwa? Kinsan dai kowa yasan zarginki ake akan ƙoƙari kisan Mai Marataba, wai kin manta Saif ɗan Sarki Aminulla ne? Me yasa kike so ki yaudari kanki da soyayyar wanda ba lallai ma yasan kina yi ba?" Maryo idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta ce. "Ki daina faɗin haka Abu wallahi masoyina ne ki duba zoben da ya bani fa, wani abu da baki sani ba ina ɗauke da junan biyun shi ta yaya zaki ce baisan da ni ba?" Zaro idanu Abu tayi har tana ƙwarewa da wani irin wahallalen yawun da ta haɗiya, Dai-dai lokacin Inna Habi ta ƙaraso jikinta har tsuma yake saboda jin abin da Maryo ta faɗa. Uwar bayi da suka kai baki ƙofa a hassale ta ce. "Habi nifa banasan a dinga kwan gaba kwan baya ko inbarki ke zaki ƙarasa jinyar ta"


Inna Habi bata saurari Uwar Bayi ba tayi ƙasa da murya ta ce. "Maryo me bakinki yake faɗa?" A firgice Maryo ta ɗago ta fara kame-kame dan bata yi tsammanin bayan Abu ba wani zai ji wannan maganar ba. Sunkuyar da kai ƙasa Maryo tayi ta ce. "Ki gafarce ni Inna amma munyi alƙwarin aure da shi..." kafin ta rufe baki tuni Inna Habi ta ɗauke ta da wani gigitaccen mari. Da sauri Hikbiyat ta taso cikin tsawa Maryo ta dakatar da ita. Hawaye bibbiyu ne ke sauka akan fuskar Maryo haka daga ɓangaren Inna Habi da Abu. Abu cikin kuka ta ce."Maryo me yasa? Me yasa zaki yarda da zaƙin bakin namiji me yasa kike ƙoƙarin kai kanki inda Allah bai kaiki ba ina ke ina Ɗan sarki? Kar dai ace abin duniya ya fara rufe miki ido?" Maryo banda hawaye babu abin da take yi Inna cikin fushi ta juya ta fice zuciyarta na ƙuna. Tana fita harabar asibitin ta ga Uwar Bayi a tsaye da wani mai fararen kaya da alama likita ne, Uwar bayi na hango Inna Habi ta ce. "Zo zo zo Habi dama likita ne yace zai mini bayanin abubuwan da ƴarki zata dinga ci, tun da yace dole cimarta ta yanzu ta sauya wataƙila zaki iya jurar siya tunda naji yace harda ganyaryaki da sauransu." Gaban Inna Habi ne ya faɗi ta ƙarasa gurin Likitan kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki.




WOLLAH SARKI AMINULLAH SAI YA KARƁIN JIKA ƊA A GURIN BAIWARSA TABBAS AKWAI ƘURA 🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️




_LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._




_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[04/11/2021, 18:37] Ameera Adam🌚: 22...




Likitan ya juya akalar tsayuwarsa zuwa fuskantar Inna Habi yace. "Sannu Inna" Inna Habi ta saki yaƙe wanda yafi kuka ciwo ta ce. "Yauwa Likita ya masu jiki?" Likitan yace. "Da sauƙi! Dama wani ɗan bayani ne zan ƙara muku dangane da abubuwan da ya kamata yarinyarku ta dinga ci saboda yanayin jikinta" Inna gyaɗa masa kai tayi ya ci gaba da cewa. "Tana buƙatar abinci masu gina jiki da ƙarin jini saboda yanayinta ya matuƙar bamu tsoro danma Allah yasa anshawo kan matsalar da tuni wani zancen ake ba wannan ba" Likitan ya jima ya yiwa Inna Habi bayani daga ƙarshe ya yi musu sallama sannan ya wuce ofis ɗinsa. Jiki babu ƙwari Inna Habi ta yiwa Uwar Bayi sallama sannan suka wuce gida ita da Abu zuciyarta cike da saƙe-saƙe iri-iri.


Washegari gidan Sarki ya roraye yawancin baƙinsa kowa ya koma garinsa. Sarki Aminullah yana cikin Fada a zaune Fadawansa na gefe waɗanda suka haɗa da Ciroma, Galadima da su Wambai harda su Waziri. Cikin girmamawa Ciroma yace. "Allah ya taimake ka mun aika akira yaron yana tafe." Sarki Aminullah ya amsa cikin izza irin ta jiƙaƙƙun jinin sarauta." Ana cikin haka Zulik ya shigo fadar jikinsa sanye da kayan Bayi, daga cen gefe ya zauna ya gaishe da Mai Martaba cikin ladabi. Sarki Aminullah yace. "Yaro wasu ƴan tambayoyi zamu yi maka muna fatan zaka bamu haɗin kai." Zulik ya amsa yana me russunar da kai ƙasa.


Sarki Aminullah yace. "Burin duk wani jarumi na gidan nan yaci wannan gasa saboda ya samu sukunin dukiya daga garemu, amma wani abun mamaki sai gashi kai ka samu damar amma ka ɓige da nemawa waccen yarinyar mafita ko meye dalilinka? A binciken da akayi mana an tabbatar mana da babu wanda take tsayawa da shi da sunan saurayi bare mu ce ko kai saurayinta ne, hasali ma an sanar da mu cewar a ranar da ka fito wannan gasar a ranar ne aka fara ganinka a cikin gidan nan, meye gaskiyar lamari shin meye alaƙar dake tsakaninku?" Zulik yace. "Allah ya taimake ka duk abin da ka faɗa haka ne, amma ni na taimake ta ne ba dan komai ba sai saboda Allah tunda na sami labarinta nake ji a jikina yarinyar bazata iya aikata abin da ake zarginta ba, sai dai idan maƙarƙashiya aka ƙulla mata, Allah ya baka yawan rai ka duba lamarin sosai kai ne Ubanta Mahaifi kada yankewa ƴarka hukunci daga baya abin ya dame ka" Duka mutanen Fadar ido suka zuba masa suka kallo hatta Mai martaba ido ya ƙura masa sosai yana auna maganar da ya faɗa yana ɗora ta a mizani, numfasawa Sarki Aminullah ya yi bai wani ɗauki maganar Zulik da wata manufa ba saboda yawanci haka bayin suke faɗa masa shine Uba kuma Mahaifinsu mai share musu kuka, jinjina kai ya yi yace. "Haka ne! Magana ai ta ƙare sai fai zamu sa masu leƙen asiri au lalubo mana gaskiyar lamarin. Daga haka aka sallami Zulik ya fice. Bayan fitarsa Sarki Aminullah da fadawansa suka ci gaba da tattaunawa.


Wata fuska na gani ɗaya daga cikin Fuskokin da akayo zaman fadar da su cikin dare ya nufi soron tsakiya fuskarsa ya yane ta da wani baƙin ƙyalle, yana tsaye a soron sai kaiwa da kawowa yake dan gudun karna samu matsala shirin su ya lalace. Kamar munafuka haka take tafe tana sanɗa ta ƙaraso gurin tana ganin sa ta ce. "Zakaran dawaki kukanka ba alheri ba." murmushi ya yi kamar bai ji zafin kalmarta ba yace. "Fulani Maryama kenan Baƙon munafuki bana mutum ɗaya bane, haka nan ƙadangaruwa bata ramin banza sai dai idan ƙwai zata zuba." Fulani Maryama ta taɓe baki ta ce. "Ɓoyayyar fuska kenan kasan fa Kuwwa da kuwwa bata korar Buzu kuma ko a cikin tumaki rago ke zuwa fada." Mutumin da ta kira da ɓoyayyar fuska yace. "Wanda za'a kashe dan an rataye shi ai ba komai bane, a juri dai zuwa rafi wata rana tulin zai fashe." Fulani Maryama ta gyara tsayiwarta ta ce. "A dana wannan kalaman naka wata ƙila zasu amfani a gaba amma me ake ciki yanzu?" Ɓoyayyar fuskar ya kwashe duk abin da ya faru a fada ya gaya mata, baƙin ciki haɗe da tashin hankali ne ya turniƙeta a fili ta furta. "Lallai kuwa tsugunne bata ƙare ba dan dole kuwa mu ɗauki mataki akan wannan yaron saboda yarinyar nan karta fallasamu." Ɓoyayyar Fuska yace. "Maryama ki bi komai fa a sannu dan ba kowanne nama ne yake ciwu ba wani idan ka ci shi kwanan keso zaka yi." Harara ta watsa masa tace.


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login