Showing 57001 words to 57328 words out of 57328 words
Maryama bata tanka mata ba itama ta fisge ɗankwalin kanta sai ga wani irin farin gari na marmashewa. Jakadiya dafe ƙirji tayi ta ce, "Maryama! Yoo ai nawa shafar mai ne a haka kike zuwa shimfiɗar takawa gari na zuba? Wai ma kuwa ya kuka ƙare da takawa nasan dai har yanzu ba'a ce bai shafo hallitar kanki ya ji yadda kanki ya koma ba"
Juye-juye yake ga gumi yana tsattsafo masa ta ko'ina, firgigit ya farga daga mummunan Mafarkin da yake yi bakinsa ɗauke da Addu'a. Kallanta ya yi har yanzu bacci take miƙewa ya yi jiki ba kuzari ya faɗa banɗaki ya ɗauro alawa zai wuce masallaci, har yaje bakin ƙofa ya dawo ya fara bubbuga fulonta yana tashinta, ganin bata tashi ba har zai iya rasa jam'i yasa ya fice da niyyar idan ya dawo ya tashe ta. Fitarsa harabar gidan ya hangi taron jama'a zagaye a wurin kamar zai wuce sai ya hangi Ƙaninsa Sulaiman, yafito shi ya yi da hannun alamun yazo nan take ya ƙaraso wurinsa. Maleek ya tambayashi, "Me yake faruwa ne naga mutane da yawa.?" Mamakin fuskar Sulaiman ne ya ƙaru, ya juya yana nuna masa wurin sannan yace, "Yaya Me babban ɗaki aka gani zaune a wurin" Wani kallo Maleek ya wurga masa yace, "Baka da hankali, shirmen naku har kan Mai babban ɗaki shekarar baiwar Allahr nawa ta rasuwa ina jin tun baka da wayo ta rasu ka ce mana ita ka gani a zaune, ya akayi ka santa?" Sulaiman yace, "Wallahi da gaske haka naji su Baba Ciroma suna faɗa..." Maleek bai gama jin maganar Sulaiman ba ya hango Mahaifinsa da wata tawaga sun nufi hanyar da mutane ke tsaitsaye.
Ina muku fatan alheri🥰 Mu haɗe a comments🤾🏻♀️
LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KI ACOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._