Showing 3001 words to 6000 words out of 57328 words

Chapter 2 - Anya Baiwa Ce 1 Complete Hausa Novels.txt

30 Nov 2024

3913

taɓa mahaifiya ya fara mata nuni da hannu, Jakadiya sakin baki tayi tana kallansa sai kuma ta karya murya ta ce. "To banda abin ka Ƙanin Yarima ni yaushe na koyi maganar kurame wannan kam sai ranki shi daɗe...? Kallon da Fulani Zaliha ta wurgawa Jakadiya ne yasa ta ja bakinta tayi shiru.


Fulani Zaliha ta ce. "To banda abin ka Saif idan kuma yarinyar bata amince ba, ko kuma ita Yaya idan bata lamunce ba fa naji ance yanzu Baiwarta ce, nifa banasan abin da za'a zo ana ƙananan maganganu" Jakadiya tayi karaf ta ce.


"Sadaƙallahul azim Ranki shi daɗe haka za'ayi kawai tunda kowa ya sanki da tausayin talakawa." Fulani Zaliha ta kama hannun Saif ta ce. "Jakadiya ku taimaka masa mu wuce da ita."


Fualani Zaliha dasu Jakadiya suka wuce ɓangarenta suna riƙe da Maryo da har lokacin bata cikin hayyacinta, suna zuwa aka shimfiɗar da ita akan tabarama Jakadiya na ganin haka ta zame jiki ta wuce ɓangaren Fulani Maryama.


Jakadiya na zuwa sashen Fulani Maryama ta zayyane mata duk abinda yake faruwa Fulani Maryama taɓe baki tayi ta ce. "Cen sa ji da munafurcinsu daga yanzu ma na sallame ta dan naga alamar bazamu daidaita da ita ba." Fulani Maryama zayyawa Jakadiya duk abinda ya Boka ya gaya mata tayi ta ɗora da cewa.


"Jakadiya me ya kamata mu gudanar wa kike zargi a cikin waɗannan bayin anyi sababbin bayi ne ko iya baƙin sarki ne kawai?" Jakadiya tayi jim sannan ta ce. "Allah ya taimake ki ai sallamar yarinyar nan bai kamaki ba kuma ni dama cen akwai wacce nak zargi dan dai kawai kar nayi miki katsalandan ne amma ai dama biri yayi kama da mutum, ya za'ayi ki ɗauki wuƙa ki taɓawa cikinko ranki shi daɗe."




KU MUN AFUWA DA GAJEREN TYPING 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 PROMISE GOBE INSHA ALLAH 2 PAGES ZAKU SAMU.



_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI
[26/10/2021, 15:45] Ameera Adam🌚: 13...




Fulani Maryama a firgice ta ɗago da kanta tana kallan Jakadiya, da sauri ta sauko daga kan kujerar da take kai ta alfarma ta dafa cinyar Jakadiya ta ce. "Jakadiya me kike nufi kina nufin kinsanta amma kika bari nake zaune cikin dubu?" Jakadiya ganin yadda Fulani Maryama tayi a zuciyarta ta ce. "Yo dama ai komai nisan jifa ƙasa zai faɗo kuma duk nisan dare gari zai waye, Allah na tuba dama tunda naji labarin ɗan wajen Zaliha ya take ƙafarsa ai nasan tuni ginshiƙin dutse ta faso gi..." Jakadiya bata gama zancen zucin ba Fulani Maryama ta kwantar da murya ta ce. "Jakadiya ki mini rai ke nake sauraro" Jakadiya ƴar dariya tayi ta ce. "Fulani Maryama kenan Yaushe rabon duniya, da ayya-raye? Wai ni kike kwantarwa da murya haka lallai Duniya juyi-juyi kwaɗo ya faɗa ruwan zafi." Fulani Maryama fusata ta farayi ta ce. "Jakadiya saboda na zauna ƙugu da ƙugu da ke ba yana nufin ki ci duniyarki da tsinke a kaina ba. Me ake ciki? Wacece yarinyar a cikin gidan nan?" Jakadiya ta ce. "Maganar gaskiya Fulani ina zargin yarinyar can da ta bar wannan sashen naki saboda alamu duk sun bayyana daga yanayinta"


Fulani Maryama ta ce. "Da gaske kike faɗa?" Jakadiya ganin ta zurma Fulani Maryama ta shige yasa ta ɗaga kanta da sauri ta ce. "Ko ke baki dubi yanayinta ba? Haba ai duk me hankali ya dubi yarinyar nan yasan ba ita kaɗai bace. Kina ganin yarinya da ido a tsaitsaye kamar kamar Inuwar soja ai ko ba'a faɗa ba biri yayi kama da mutum" Fulani Maryama ta jinjina kai jiki a sanyaye tana nazari sannan ta ce. "Wacce hujja kike da ita da zai tabbatar mana da ita ɗince Jakadiya?" Jakadiya tayi yaƙe a fili saboda Allah ya sani ita kanta ta faɗa ne kawai bata da wata hujja hasalima ta faɗa ne dan ta ƙara ɗagawa Fulani Maryama hankali ta ce. "Eh man baki ga yarinyar sam bata da tsoro ba, ɗazu a gabanki fa makaran jikinta suka make ta gaskiya nidai ina da shakku akanta." Fulani Maryama ta ja guntun tsaki ta ce. "Wannan bai isa ya ban tabbacin ita bace ni nafi zargin a cikin sabbabin bayin da akayi ne makon da ya gabata, saboda sai bayan zuwansu haka ta faru da wancen tsinannan yaron." Jakadiya jim tayi tana nazari sannan ta ce. "Ehto mutum baya ƙin ta mutane yanzu ki barmun komai a hannuna zan yi ta shige da fice har na samo miki gaskiyar labari inyaso sai a tashi tsaye a san abinyi" Fulani Maryama har lokacin bata cikin nutsuwarta ta miƙe ta koma mazauninta na farko sannan ta gyaɗawa Jakadiya kai." Sallama Jakadiya tayi mata sannan ta tashi ta fice zuciyarta fes dan ko banza ta san Kwanciyar hankali yayi ƙaura agurun Fulani Maryama.


Fulani Zaliha zaune take a gefen Maryo da har lokacin batasan waye a kanta ba, addu'a take ta tofawa Maryo har ta fara jin saukin jikinta. Miƙewa tayi zaune jiki ba ƙwari gabaɗaya ta haɗa uban gumi, a hankali take ƙarewa gurin kallo har ta sauke idanuwanta akan Fulani Zaliha da itama kallon nata take yi. Maryo sunkuyar da kai ƙasa tayi ta ce. "Barka da hutawa ranki shi daɗe" Fulani Zaliha ta dafa kaɗarta bata amsa ba ta wurgo mata tambaya.


"Ya kike jin jikin naki?" Maryo ta ce. "Da sauƙi" Fulani Zaliha ta ce. "Ki dinga yawaita addu'a kinji kuma karki dinga zama babu ɗankwali." Maryo ta gyaɗa kai sannan ta ce. "Insha Allah zan kiyaye ya shugabata" Miƙewa tsaye Maryo tayi Fulani Zaliha ta ce. "Ina zaki haka?" Maryo ta russuna ta ce. "Allah ya taimakeki Fulani Maryama ce ta aiko kira na" Fulani Zaliha ta ce. "Ki tsaya kiyi sallar magriba inyaso kya je kiran da take miki" Maryo bata musa ba ta miƙe ta ɗaura alwala tana mamakin mutumci da karamcin wannan matar saki, tana cikin wannan tunanin ta ga Fulani Zaliha ta miƙa mata wani abu kamar mayafi amma ba mayafi bane kuma yana da kauri sosai kamar bargo ta ce. "Ga wannan kiyi sallah da shi" Ta karɓa tana godiya cikin girmamawa sannan ta ta tayar da sallah.


Bayan ta idar da sallah ta naɗe abin da tayi sallar da shi ta miƙawa Fulani Zaliha tana zabga godiya, Murmushi Fulani Zaliha tayi bata karɓa ba ta ce. "Ki tafi da shi ki dinga sallah" Maryo tsugunnawa tayi tana godiya da sauri Fulani Zaliha ta ɗagota ta ce. "Godiyar ta isa haka. Amma zan roƙe ki wata alfarma" a firgice Maryo ta zaro idanuwanta tana shirin magana Fulani Zaliha ta ci gaba da cewa. "Ba wata alfarma bace so nake duk lokacin da kika yi sallah kiyi wa ɗana addu'a kice Allah ya bashi lafiya ya dawo kamar yadda kowa yake" Idanun Fulani Zaliha ne suka kawo ƙwallah Maryo ta lura da haka nan take taji tausayinta ya kama ta, saboda babu wanda baisan labarin Saif ba a cikin gidan. Ko kai baƙo ne bazaka rufa kwana biyu a gidan ba sai an kwashe labarinsa a baka, dan haka ne ya faru da su a washegarin ranar da suka zo Jakadiya ta kwashe labarin Saif ta basu. Maryo ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Insha Allah nayi miki alƙwari kuma zai samu lafiya da yardar Allah. Amma Ranki shi daɗe ba naji ana ta ce wa ya warke ba" Fulani Zaliha tayi murmushi ta ce. "Alhamdullah a ranar da kika kawo mun saƙon gurin Delu Dillaliya bayan fitarku babu jimawa Allah ya bashi lafiya ƙafarsa ta samu lafiya garau yana takawa, saura idanunsa da bakinsa kawai ya rage kuma hakan ba ƙaramin daɗi yayi mini ba" Motsi suka ji daga bakin ƙofa suna kallan gurin suka ga Saif ne ya shigo da alama daga masallaci yake. Nan take wani abu ya tsargawa Maryo gabanta sai faɗuwa yake, kafe shi tayi da kallo yadda yake tafiya kai ka rantse yana gani da idanunsa, tunda ga idanunsa nan a buɗe tar sai dai ganin da baya yi. Wani irin so da ƙaunarsa ne suke fusgarta har ta shagala da kallansa ta manta a gaban wacce take. Muryar Fulani Zaliha ne ya katse ta ce mata. "Yauwa ni ya sunanki ne?" Maryo ta ƙara sauke ajiyar zuciya a karo na biyu ta ce. "Sunana Maryo" Fulani Zaliha ta ce. "Masha Allah suna me daɗi to shikenan je ki kinji Allah ya ƙara miki lafiya" Maryo ta russuna tana godiya sai a lokacin Saif ya fahimci da wacce Mahaifiyarsa take magana. Alamu ya fara mata da hannu yana tambayarta yarinya da suka shigo da ita ce ta ji sauƙi har take magana?" Nan take mahaifiyarsa ta yi masa bayani yadda sukayi da Maryo. Duk wannan jawabin da Fulani Zaliha take wa Saifa Maryo ta tattara hankalinta gabaɗaya ta ɗora akan sa, har sai da Fulani Zaliha ta lura da irin kallon da Maryo take wa Saif, gyaran murya tayi a hankali sannan Maryo ta dawo cikin nutsuwarta ta gaida Saif cikin wata irin murya da batasan ma tana da ita ba sannan ta yi wa Fulani Zaliha sallama ta fice.


Maryo kai tsaye bata wuce ko ina ba sai sashen Fulani Maryama lokacin da ta shiga duhun magriba yayi sosai, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga sashen. Fuska babu walwala Fulani Maryama ta kalle ta ba tare da ta amsa sallamar ba, Maryo na shirin magana ta dakatar da ita.


"Ta shi ki fice mini daga sashena bana buƙatar ƙara ganin ki indai bani na aika kiranki ba" Jiki a sanyaye Maryo ta tashi har zata fita Fulani Maryama cikin tsawa ta ce. "A ina kika samu wannan abun na hannunki"rissiawa tayi ta ce. "Fulani Zaliha ce ta bani Allah ya taimake ki" A zabure Fulani Maryama ta ce. "Me ya kaiki sashenta kina matsayin baiwata?" Maryo ba ƙaramin tsorata tayi da yanayin da ta ga shugabarta ta shiga ba, jikinta har rawa yake bakinta na karkarwa ta ce. "Wallahi nima farkawa kawai nayi na ganni a gurinta shine da nayi sallah ta ce na tafi da shi" a hargitsi Fulani Maryama ta ce. "Kin haɗu da Saif?" Maryo ta ce. "Eh da zan fito ya shiga" Wani kukan kura Fulani Maryama tayi ta danƙo wuyan Maryon ta maƙure mata wuya ta ce. "Ƙanwar uwarki ce ko ta ubanki da zaki dinga shiga sashen nata?" Maryo sosai ta tsorata ga shaƙewar da Fulani Maryama tayi mata har idanunta sai da suka firfito nan ta ke ta fara tarin wahala, kanta ne ya sara idanunta suka fara canja launi jini ne ya fara ɗiga daga hancinta. Saboda masifar da ta rufe idanun Fulani Maryama bata lura da halin da Maryo take ciki ba sai bambamin faɗa take tana ranƙwashinta haɗe da dungure mata kai, kamar wacce aka haɗawa lantarkin wuta ta fara zuƙar jinin jikinta haka taji wani irin shocking a jikinta, cikin tsananin azabtuwa tayi wurgi da Maryo tana ja da baya haɗe da mayar da numfashi da ƙyar.


Kafin Maryo takai ga faɗuwa ƙasa Salma da ya shigo ɗakin ya taro ta ta faɗa jikinsa, wani irin yar yaji tun daga tafin ƙafarsa har zuwa tsakiyar kansa. Maryo lumshe ido take tana buɗewa saboda yanayin da take ciki, cikin zuciyarta ta fara karanta wasu ayoyin cikin kur'ani da ta sani. Ba ta jima a haka ba ta fara jin jikinta ya fara koma mata dai-dai, a hankali ta fara ƙoƙarin zame jikinta amma fir Salman yaƙi sakinta sai bin ta yake da wani irin mayataccen kallo mai wuyar fasaltuwa, muryar mahaifiyarsa ya riska tana cewa. "Salman wannan yarinyar ce wallahi babu ko tantama banayi ita ce" Salman da har lokacin riƙe yake da Maryo yace. "Wace ce itan me tayi miki?" Sai a lokacin Fulani Maryama ta fahimci ta so tayi suɓutar baki ta wayance da cewa. "Sheɗaniyar yarinya ce so ake a haɗa baki da ita a cutar damu alhalin tana matsayin baiwa ta."


Salman bai bi ta kan maganar Mahaifiyarsa ba yasa hannunsa ya goge mata jinin da ke hancinta, fuskarta ya ƙarewa kallo yana jin wani abu na fusgarsa akanta, kayan jikinta na Bayi ya ƙarewa kallo a hankali ya furta. "Sam baki cancanci zama haka ba" ya faɗa cikin wata irin kasalalliyar murya.


Fulani Maryama da bata fahimci inda zancen Salman ya dosa ba ta ce. "Banda abin ka mugu yana da kama ne har gane mutumin arziƙi ake a haka" Maryo kiciniyar ƙwace kanta ta farayi sai da ya ga dama dan kansa sannan ya sake ta yana binta da wani irin kallo haɗe da lashe baki. Yana sakinta ta fice da gudun gaske jikinta ta ko'ina rawa yake yi." Salman takawa yayi ya tsaya gaban Mahaifiyarsa da har lokacin tsoro ne ƙarara shimfiɗe akan fuskarta, ƙerere ya tsaya yace. "Ke ya akayi kika gane za'a haɗa baki da ita a cutar damu?" Fulani Maryama ta ce. "Wallahi Saif wannan yarinyar ba alheri bace a zamantakewarmu da ita." Guntun tsaki ya ja yace. "Wai ke tambayar da ake miki daban amsar da kike bawa mutane daban wai ma me kika yi mata naga jini a hancinta dan nasan halinki?" Idanu Fulani Maryama ta zaro tana maimata tambayar da Saif ya yi mata a fili sannan ta ce. "Saif yarinyar nan Baiwa ce fa akanta har kake tsareni da tambayoyi" Wani kallo ya watsa mata yana wani irin murmushi da bai san lokacin da ya sake shi ba sakamakon tuno fuskar Maryo da ya yi, ido ya zurawa Mahaifiyarsa yace. "Ke kike ɗaukanta a matsayin Baiwa amma ni matsayin da na bata yafi wannan a gurina saboda ina jin wani abu da bantaɓa jinsa ba akan wata ƴa mace dukda kinsa dai ba yau na fara tarawa da mata ba, nayi mu'amala da mata kala-kala amma babu wacce na tsinci kaina a yanayin..." A zafafe Fulani Maryama ta kife Salman da wani gigitaccen mari cikin masifa ta ce. "Saif ni kake gayawa haka baka da mutumci ashe ban sani ba, ni kake gayawa kana tarawa da mata saboda ka riƙa..." Salman da sauri ya ture hannunta yana wani irin huci da muzurai yace. "Wallahi karki ƙara ɗora hannunki a kan fuskata idan ba haka ba zakiyi mamaki, kuma wannan yarinyar nan son ta nake kuma ba soyayyar da zan watse da ita ba son da zan aureta saboda ina san ta haifa mini ƴaƴa kyawawa masu kama da ita." yana gama faɗa ya fice ko waiwaye bai yi ba, Fulani Maryama zaro ido tayi tana bin bayansa da kallo sannan ta rushe da wani irin mahaukacin kuka.




Maryo ilahirin jikinta rawa yake tana tafe ko kallan gabanta ba ta yi saboda tsoron abin da Fulani Maryama tayi mata, tana gabda shan kwanar katangar sashensu taci karo da wani matashin har kusan gware suka yi, da sauri Maryo ta ja da baya tana ƙwallah wata irin gigitaciyyar ƙara. Dariya ya bushe da ita sannan ya janyo hannunta yana cewa. "Ke meyasa kin fiya tsoro ne?" Sai a lokacin ta sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya tana kallan fuskarsa da matsanancin mamaki sakamakon hasken farin watan da ya gauraye filin gurin. Ganin irin kallon da take masa babu ko ƙiftawa yasa hannu a saitin fuskar ta, a hankali ta janye idanunta suna haɗa ido ya sakar mata wani tattausan murmushi, sunkuyar da kai tayi saboda wani kyau da kwarjini da ya ƙara mata sai kuma taji kunyarsa a hankali ta ce. "Dama kana magana ne?" Murmushi ya yi yace. "Gashi kuwa kinji" Bin gefensa tayi zata wuce ta ce. "Na maka murna"


Janyota ya ƙara yi har sai da ta faɗa jikinsa yace. "Bani Hannunki" Da sauri ta tashi daga jikinshi ta ce. "Ni ka daina taɓa ni banaso haramun ne" Kafeta yayi da ido yace. "Ni ba haramun bane a gurinki dan Allah ki tuna Rayzuta ni Fauzaaan mijinki ne, kuma karki bari wani ya ƙara taɓaki bayan ni idan ba haka ba zai mutu naga wancen Ɗan Sarkin yana rawar kai akanki" Zaro idanu tayi tace. "Ɗan uwan naka zaka kashe? Dan Allah ka bari karka kashe shi" Murmushi ya yi yace. "Ni ba Ɗan uwana bane, to shikenan bazan kashe shi ba amma sai kin bani hannunki" Har lokacin a tsorace take saboda kalmar kisa da taji ya furta, jiki a sanyaye ta miƙa masa hannu.


Wani irin zobe ya zura mata a hannu mai wani irin gwamammun rubutu da babu wanda zai gane me aka rubuta ajiki, ya zura mata a hannu nan take taji kanta ya sara daga cikin kunnenta taji wasu irin maganganu, lumshe ido tayi tana bin kalmomin da bakinta kamar ta taɓa saninsu a baya tana cikin haka daga cen taji muryar Abu da Dije suna ƙwala mata kira, da sauri ta buɗe idonta kallanta yayi yace. "Maza kije ga su Abu cen ƙarasowa." Jiki a sanyaye ta wuce inda take hango su Abu har ta ƙarasa gurinsu bata daina murza ɗan yatsan da zoben yake jiki ba.


Dije ce ta fara magana ta ce. "Maryo tun ɗazu nake nemanki" Maryo ta ce. "Wallahi naje kiran shugabata ne" Dije wucewa tayi ta ce. "To nima bari na ƙarasa Fulani Bilkisu na kira na" Abu ce kawai ta iya amsa mata Maryo har lokacin tana cikin wani irin yanayi.

Abu fisgar hannun Maryo tayi ta ja ta cen gefe tayi ƙasa da murya ta ce. "Ke Maryo ke da waye kike a tsaye a gurin cen?" Maryo ta ce. "Saif ne Ɗan wajen Fulani Zaliha" Zaro ido Abu tayi tana waige dan kar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login