Showing 39001 words to 42000 words out of 57328 words
bata ta ciro tana rungumeshi tana sauke ajiyar zuciya akai-akai. Idanu ya zura mata yana kallo shi kaɗai yake jin zuciyarsa babu daɗi, cikin zuciyarsa yake jin kamar bai mata adalci ba gani yake kamar yaso kansa da yawa, kamata ya yi ya keɓence shi da ita ya ji tw bakinta tun kafin ya taho da ita tunda zaman aure ba na mutum ɗaya bane. Miƙewa ya yi jiki ba ƙwari ya zagaya ta ɗayan ɓarin ya kwanta yana lumshe idanu.
Inna Habi ta jima a gurin ban da Kuka babu abin da take yi da ƙyar Abu ta ja hannunta suka wuce cen sashensu, bayan tafiyarsu babu daɗewa Fulani Maryama ta aika wata Baiwarta kiran Inna Habi, Inna Habi bata ɓata lokaci ba ta ƙarasa cen sashem Fulani Maryama. Cikin girmamawa ta russuna gaban Fulani Maryama ta ce. "Allah ya taimakeki ya kara miki lafiya ance kina nemana" Fulani Maryama da farincikinta yaƙi ɓoyuwa saboda tafiyar Maryo ta ce. "Tsohuwa sannunki, ni ya sunanki ne?" Inna Habi ta ƙara russunar da kai ta ce. "Allah ya taimakeki Suna na Habiba" Fulani Maryama ta ce. "Habiba kece Takawa yace zaki dawo sashena da zama ko?" Inna Habi da gyaɗa kai ta ce. "Nice ranki shi daɗe" Fulani Maryama ta taɓe baki tana ƙarewa Inna Habi kallo dake rakuɓe a ƙasa cikin tsummokaran kayanta ta ce. "Me ya sa tuntuni baki ɗebo tsummokaranki kin dawo nan ba? Salan Takawa yace bana farinciki da dawowarki? Anya ma kuwa zamu wanye lafiya kuwa? Ace tun daga yanzu kin fara ƙoƙarin haɗa mini tuggu" Ita dai Inna Habi shiru tayi gabanta na faɗuwa dan Allah ya sani ba ƙaramin tsoron Fulani Maryama take ba, tun kafin ta haɗawa Maryo wannan tuggun dama cen jininsu bai haɗu ba, murya na rawa ta ce. "Tuba nake Allah ya taimakeki" Fulani Maryama bata amsa ba ta ce. "Ga ɗakince na daga jikin soro sai ki gyarashi za'a kawo miki wasu kayan sawar dan bazan iya zama da ke da waɗannan tsofaffin kayan uniform ɗin naki ba." Inna Habi cikin rawar jiki ta ce. "Godiya nake Ranki shi daɗe, Allah ya taimakeki ya ƙara nisan kwana Zuma kike me farar saƙa ba'a miki lasa ɗaya, Zinariya kike a cikin Mata tauraruwa mai walƙiyar alkairi, babu wata Fulani a gabanki ke ɗin ce dai me dogom zamani. Allah ya raya Yarima mai jiran gado Sarkin gobe da yardar Allah." murmushi Fulani Maryama tayi dan a duniya babu abin da Fulani Maryama ta fi so iri ka wasa ta, duk irin ɓacin ran da take ciki nan take zaka ganta cikin walwala bare a wannan lokacin da ji take kamar wacce aka yiwa albishir ɗin shiga aljanna. Gyara zama tayi tana buɗawa tana daidaita zaman alkyabbarta cikin isa da ƙasaita ta ce. "Habiba anjima ki zo ki karɓi kyautar alkaki da maɗi" russunawa Inna Habi tayi ta ce. "Ina godiya ranki shi daɗe Allah ya ƙara girma" tana gama faɗa ta miƙe ta fice daga gidan tana mamakin hali irin na Fulani Maryama, cikin zuciyarta take ayyana tabbas dole ta san irin zaman da zatayi da Fulani Maryama, dan ta lura mace ce mafaɗaciya uwa uba kuma makirci da iya kissa da kisisina.
Tana fita kai tsaye sashen su na bayi ta wuce, babu ɓata lokaci ita da Abu suka haɗa kayansu suka fara yi wa sauran Bayin da ke sashe sallama. Masu taya su murna suna yi masu kuma jin haushin haka sama-sama suka amsa sallamar ta su, dan a ganinsu ya za'a ce su Inna Habi da suke ƴan baya-baya ace har sune suka samun wannan matsayin na ɗaga likafarsu har aka ƴanta su. Abu da Inna Habi lokacin da suka zo mararrabar sashen matan Sarkin Aminullah da ƙwallarsu suka rabu. Inna Habi ce ta rungumo Abu ta ce. "Abu na cucemu na tarwatsa mu lokaci ɗaya dan Allah yanzu meye fa'idar haka, banyi haka saboda wata manufa ba ko dan ba ni na haifi Maryo ba. Na yi haka ne kawai dan ganin na nema mata mafita daga tsananin soyayyar da ta faɗa ta gaibu mara amfani, yanzu babban tashin hankalina idan suka fahimci yarinyar nan na da ciki bamusan me zasu ce musu ba, ko a mafarki kina ganin mun isa mu ce musu cikin Ɗan Sarki Aminullah ne" lokacin da Inna Habi ta zo dai-dai nan a zancen ta faɗa tana ƙasa da murya. Abu ta goge hawaye ta ce. "Inna kin yi kuskure ko kaɗan banso kika amsa cewar Maryo matarsa ce ba." Yanzu fa ba'a ɗaura musu aure da Maryo ba yanzu wanne irin zama yasu yi da ita. Inna kin fi kowa sanin wacece Maryo da kanfiya akan abu idan ta kafe babu me canja mata ra'ayi, kinsan tun da ta kallafawa zuciyarta soyayyar Saif wallahi babu mai canja mata da wani" Inna Habi sai lokaci ta farga dan tasan halin Maryo sarai. A tsorace ta ce. "Wallahi Abu na sani nasan Maryo tana cen" sai kuma ta fashe da kuka ta ci gaba da cewa. "Ina tsoron kar ciwonta ya tashi wallahi nasan wacece Maryo" Ganin Inna Habi na niyyar rikicewa yasa Abu ta ce. "Inna ki kwantar da hankalinki kinsan fa tun da Maryo ta ce taji ta gani zata bisu babu abin da zai faru da bazata zauna da su ba kinsan idan duniya ce zata haɗu a kanta babu wanda ya isa yasa ta bisu, idan ma kuma ta bisu kinsan ko baɗaɗe ko bajima sai ta dawo. Karki ɗaga hankali nasan tana cikin ƙoshin lafiya, kedai ki bita da addu'a da fatan alheri." Inna Habi ajiyar zuciya ta sauke da jin maganganun Abu, babu ko tantama maganar Abu na hanya babu wanda ya isa ya tilasta Maryo akan abin da bata yi niyya ba, da wannan tunanin Inna Habi ta ɗan samu ƙwarin gwiwa sai dai har lokacin cike take da zullimin halin da Maryo take ciki. Inna Habi da sauri ta yiwa Abu sallama akan sai sun dinga haɗuwa, dan tana tsoron karta ɓata lokaci ta ƙara laifi agun uwar ɗakinta tun da ta samu ta goge wancen da tayi na baya.
Abu da sallama ɗauke a bakinta ta shiga sashen Fulani Zaliha, Bayinta ne suka amsa sannan suka yi mata jagora zuwa rumfar Fulani Zaliha. Abu na shiga ta russuna ƙasa cikin girmamawa ta ce. "Barka da hutawa Ranki shi daɗe" Fulani Zaliha da murmushi ta amsa ta ce. "Barka dai" Abu ta ce. "Dama ni ce..." Katse ta Fulani Zaliha ta yi da. "Ke ce sabuwar ƴar da nayi ko" Abu ta gyaɗa kai tana murmushi ta ce. "Ni ce Ranki shi daɗe" Fulani Zaliha ta ce. "Ya sunanki" Abu ta ce. "Suna na Abu" Fulani Zaliha ta ce. "Wane irin Abu ƴata daga yau na soke sunan nan kin koma Zainab" Abu cikin jindaɗin tarbar da ta samu ta ce. "Godiya nake ranki shi daɗe Allah ya ƙara girma da jinkiri me amfani Ubangiji ya ƙara lafiya ya raya Yarima Saif." Ba ƙaramin daɗi Fulani Zaliha ta ji ba ta ce. "Ameen, daga yau ki ɗauki Saif kamar yayanki ki dinga kiranshi da Yaya Saif" Abu ta ce. "Insha Allah ranki shi daɗe" Fulani Zaliha kallan Baiwa Salima tayi ta ce. "Ku kaita ɗakinta da aka gyara mata a haɗa mata ruwan wanka ta gyara jikinta." Abu godiya ta ƙara yi sannan ta miƙe suka wuce sabon ɗakinta.
Da daddare Sarki Aminullah na turakarsa a kwance, shi kaɗai ne ranar da yake sanarwa da Jakadiya baya buƙatar kowacce mace daga cikin matansa ta ziyarce shi, ban da juyi babu abin da yake yi tunanin abubuwan da suka faru a ranar yake yi. Tabbas akwai abubuwa masu rikitarwa fuskar Maryo ce take ta yi masa gizo a ido, ya rasa wane dalili ne yasa ya kasa cireta daga zuciyarsa kukan da take yi ba ƙaramin taɓa masa zuciya yake ba, runtse idonsa ya yi bacci ya fara fisgarsa kamar almara haka yake jiyo sautin kukanta, firgigit ya yi ya buɗr idonsa yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. Gyara kwanciya ya yi babu jimawa bacci ya yi awon gaba da shi. Mafarki yake wani matashin saurayi ya tunkaroshi gadan-gadan da makami zai kashe shi, yana dubawa da kyau sai ya lura da Ɗansa Salman ne nan take suka fara kokawa ba ƙaƙƙautawa. Daga cikin mafarkin ya hango fuskarta tafe akan doki har ta ƙaraso gurinsu tana zuwa ta shiga tsakiyarsu ta kalli Sarki Aminullah ta ce. "Ya kai Mahaifina wannan faɗan sam ba naka bane ka barni da shi wannan ba Ɗanka bane maƙiyinka ne" tana gama faɗa ta juya gurin Salma suka ci gaba da fafatawa da faɗa, Sarki Aminullah tsaye ya yi yana kallan ikon Allah cikin rashin nasara Salman ya sareta a hannu ta durƙushe a gurin, ganin haka yasa ya koma gurin Sarki Aminu da niyyar halaka shi nan take suka fara faɗa amma har wannan lokacin Salam bai yi nasara akan Sarki Aminullah ba. Firgigit ya fara bakinsa ɗauke da salati buɗe idon da zai yi ya ga Salman tsaye a gabansa. Nan take gabansa ya yi mummunan faɗuwa saboda abin da ya faru a cikin mafarkinsa.
Washegari bayan Maryo tayi sallar asuba ne ta samu ta ɗan koma bacci saboda rashin baccin da bata samu tayi ba, sai kusan goma ta tashi a lokacin taruwar jinin hannunta ya fara bajewa Bayin da suke sashenta ne suka haɗa mata ruwan wanka, bayan ta fito tana gaban madubi ya shigo ɗakin da sauri Maryo ta janyo mayafi tana rufe jikinta, girgiza kai ya yi yana mamakin yaushe ta fara kunyarsa haka matar da har ya haihu da, ficewa ya yi daga sashen gabaɗaya. Yana fita bai tsaya ko'ina ba sai sashem Mai martaba dan dole ya sanarwa masa halin da ake ciki, ko dan saboda a tashi tsaye da neman magani.
Maryo na gaban mudubu taji kanta ya sara mata ta jikin window ɗakinta ta fara jin iska na kaɗawa, a gaggauce ta sa kaya ta ɗauko abayar da aka ajiye mata ta saka bakin window taje ta tsaye tana ƙarewa gurin kallo lokaci ɗaya ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ƙyallen nan ta janyi tana goge hawayenta sai da ta gama gogewa sannan ta miƙe ta fice daga ɗakin. Bayinta ne suka fara bin ta a baya nan take ta dakatar da su sannan ta ci gaba da tafiya, duk inda tafi Bayi ne ke russuna mata wasu kuma suna bin ta da kallo tana wucewa kaji ƙananan maganganu suna tashi. Tana wucewa bata tsaya ko ina ba sai bayan ɗakin me babban ɗaki, durƙusawa tayi a gurin ta fara haƙa gurun da wani ɗan ƙarfe daga cen nesa bayi da sauran dogarawa ne suke leƙenta, sai da ɗanyi haƙa me zurfi sannan ta ciro wata sarƙa da tai datti cikin jar ƙasa, da sauri ta sa kayan jikinta ta fara gogewa tana ɗago katon kwaɗon sarkar wani babban tambarin masarauta ne a jiki, ƙare masa kallo tayi ta rushe da matsanancin kuka, sai da tayi me isarta sannan ta miƙe zata koma sashenta daga bayan Jakadiya Muna ta ce. "Shukra lafiya kuwa me kike haƙawa haka" Maryo kusan mutuwar tsaye tayi ta juya a hankali dan jin muryar me yi mata magana, da gudu ta tafi ta faɗa jikinta tana cewa.
"Didi dama kina nan" Jakadiya kallan gefe da gefe tayi dan ganin wacce ta kira da Didi amma bata ga kowa ba, sororo tayi tana bin Maryo da kallo, ita kuwa bata damu da irin kallon da Jakadiya take mata ba ta ce. "Didi kinga sarƙarki Dan Allah karki bari su ƙara kwace miki wallahi wannan karan bazamu juri haka ba" Jakadiya zaro idanu tayi tana ƙarewa sarƙar kallo dan har ga Allah ita kallan sarƙar ma tsoro yake bata. Maryo bata bi ta kanta ba ta zura mata ita aka sannan ta ɗora da cewa. "Wallahi duk wanda ya yunƙurar rabaki da sarƙar nan sai na kashe shi kowanene shi." Nan take cikin Jakadiya ya kaɗa tsoro ya kamata, suna nan tsaye Maleek ya ƙarasowa Maleek yace. "Jakadiya ashe kuna tare da Shukra na neme ta ban..." wata uwar tsawa Maryo ta buga masa ta ce. "Mahaifiyata ba Jakadiya bace. Ka kiyaye harshenka idan ba haka ba zan datse maka shi" Jakadiya ban da gumi babu abin da take Maryo ta ce. "Ko ba yanzu ba ki sanar da ni ga duk wanda ya nemi ci miki zarafi domin wannan karan kinfi ƙarfin ƙasƙanci" Maryo na gama faɗa ta wuce gaba daga Jakadiya Muna har Maleek ido suka zura mata, da sauri ya bi bayanta yana cewa. "Mu je Mai martaba ne yake nemanki" Maryo ta juyo fuska a ɗaure ta ce. "Ko bai neme ni ba dama zanje domin ina ji a ajikina yana tare da Jullifat kuma idona idonsa wallahi sai dai gawarsa. Maryo haka ta ci gaba da tafiya kamar wacce zata tashi sama kai tsaye fadar Sarki Abdallah ta nufa tana zuwa ko sallama babu tayi musu ƙerere a tsaye, Waziri dake gefe yace. "Ke gidanku baki ga gaban wanda kike bane?" A hassale ta kalleshi ta ce. "Dama nasan banza bata kai zomo kasuwa, naji a jikina kana nan kuma wallahi yadda ka wulaƙanta Mahaifiyata sai ka wuƙanta." Galadima da shigowarsa kenan yace. "Subhanallah ke me nake ji haka?" Maryo juyowa tayi idanunta suka kawo ƙwallah tana haɗa hannuwa biyu alamun roƙo ta ce. "Ya kai Mahaifina banasan ka hana ni abin da nayi niyya haƙurinka ne ya basu damar aiwatar da duk abin da suka yi akanmu, dan Allah karka ce mini a'a" Tana gama faɗa ta damƙi wuyan Waziri ta ɗaga shi sama nan take ya fara kakari, sa gudu dogarawa bakwai suka yo kanta da niyyar ƙwatar Waziri, da hannu ɗaya ta hankaɗe su lokaci ɗaya suka yi baya suka faɗi ko motsi basa yi.
NASAN KUNGA KURA KURAI AMUN AFUWA PLS
TO FA KU MU KAFTA🤾🏻♀️
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[14/11/2021, 13:18] Ameera Adam🌚: 28...
Hankalin Sarki Abdallah ba ƙaramin tashi ya yi ba hatta sauran fadawan da suke cikin fada tsoro ne ya kama su, Maleek zaro idanu ya yi dan ko kaɗan bai taɓa tsammanin lamarin nata ya kai ga haka ba, Waziri tun yana cikin hayyacinsa har ya fara fita ban da kakari babu abin da yake yi, Galadima da sauri ya ƙarasa gurin yana cewa. "Ke wai me kike yi haka ne ya kike shirin aikata kisa kai ne?" Sassauta riƙon da ta yi wa Waziri ta yi ta ce. "Dan Allah ka ja bakinka kayi shiru karka hana ni abin da nayi niyya" tana gama faɗa ta kuma cakumar wuyan Waziri Maleek ne ya ƙarasa gurinta yana ƙoƙarin kwace shi daga hannunta, kallonsa tayi da runannun idanuwanta ta ce. "Ka matsa daga nan banasan laifinsa ya shafeka" Galadima na ganin haka da sauri ya matsa suka ci gaba da kiciniyar ƙwace Waziri amma kamar ƙara turata suke, Galadima lura ya yi indai ƙarfi zasu sa bazai fisshesu ba, janye hannu Maleek ya yi ya kalleta ya ce. "Ƴata na haɗaki da girman Allah ki sake shi ki dubi girma da daraja ta" Maryo kamar wacce aka zarewa laka a jiki haka ta jiyo jiki babu ƙwari ta ce. "Na san dama bazaka taɓa bari ba, amma me yasa duk irin cutarwar da suka yi mana bazaka bari na aiwatar da muradin ruhina ba" Galadima da har lokacin bai fahimci inda zancen Maryo yake tafiya ba yace. "Eh naji nidai na ce ki sake shi." Maryo sakinsa ta yi ta zauna daɓar hawaye na bin idanunta, zamanta babu jimawa kanta ya ci gaba da sarawa jini ne ya fara ɗiga daga hancinta, hankali a tashe Maleek ya ƙarasa gurinta yana mata sannu, Galadima da sauran Dogaran gurin kan Waziri suka ƙarasa suna yi masa firfita da sannu. Sarki Abdallah shiru ya yi yana nazari ganin abun yake kamar al'amara saboda ko wata guda bai yi da yin makamancin mafarkin abin da ya faru ba, tsoronsa ɗaya kada mafarkin da yayi munana na bayan kwanakin su biyo baya, numfasawa ya ƙarayi yana kallan Maryo da take zaune tana share jinin hancinta da ƙyalle. Maleek lallaɓa Maryo ya yi da ƙyar ya samu ta tashi suka fice daga cikin Fadar tana tafe tana watsawa Waziri mugun kallo, a hanyar su ta kawawa sashensu ta ƙofar baya ya bi da ita saboda idanun mutane, suna wucewa ta sashen matan Sarki Maryo ta tirje a gurin.
Maleek ya waigo yace. "Muje mana Shukra" Maryo ta kalli sashen matan Sarki Abdallah ta nuna da ɗan yatsanta ta ce. "Nan zan shiga" Maleek yace. "Zaki je gaishe da Umma ne?" Maryo ta girgiza kai ta ce. "A'a wani abun ɓoye nake san tonowa" da mamaki yace. "Abun ɓoye kuma" bata kalleshi ba ta karkata akalarta zuwa sashen sannan ta ce. "Eh wanda ake cutar da bayin Allah, alƙawari na ɗaukarwa kaina wannann karan duk wani azzulumi da ke cikin daularmu dole ya gane kurensa." Har tayi gaba Maleek ya dafe kansa dan gabaɗaya ya rasa gane kanta, a sanin da ya yiwa Shukra mace ce da bata da hatsaniya bare tashin hankali, hasalima duk abin da zakayi mata na musgunawa sai dai ta zauna tayi ta kuka amma yau sai gashi ita ce take bankaɗo da tashe-tashen hankula, yana nan yana tunani bai yi aune ba sai jin ƙarar buɗe ƙofarta ya yi da sauri ya bita yana ƙoƙarin riƙe hannunta.
Hakimtacciyar matar sanye take da kayan alfarma, dukda kasancewarta mace ce mai cike da izza, ƙarfin hali, dakiya, jarumta, alfahari da nuna isa uwa uba kissa da kisisina. Amma hakan bai hana tashin