Showing 54001 words to 57000 words out of 57328 words

Chapter 19 - Anya Baiwa Ce 1 Complete Hausa Novels.txt

30 Nov 2024

3910

ji sai dai bakinta na magana, haka ta yi ta jinyar jikinta har ta warware. Haka rayuwa ta ci gaba da gudana cikin azabtarwa da tsangwama, har Muhaibish ta cika goma da haihuwa.


Muhaibish ta taso kyakkyawa da ita gwanin birgewa, sai dai itama haka take rayuwarta koyaushe a jikin mahaifiyarta, sai a wannan lokacin ta tabbatar da maganar Mardid akan Muhaibish da yace mata sam ba jinsinta bace, dan ta ga ababuwan da take yi ne ta fahimci haka. Tun da dangin Mahaifinta suka fahimci ita ce Muhaibish ɗin wannan ƙarnin sai baƙin cikin duniya ya kama su, saboda a wannan lokacin da sun niyyar yi wa Kyauta, Mardid ko ita mugun abu tun kafin su aiwatar zai faru da su, a wannan lokacin haka suka dinga asarar rayuka saboda masu ayyana kashe Muhaibish su suka dinga mutuwa. Wanan yasa rayuwarsu ta ci gaba da tafiya cikin jindadi babu tsangwama bare fargabar azabtarwa. Wan Mahaifin Mardid satar jiki ya yi ya tafi cen ƙarshen duniya wurin wani tsohon Bokansu, nan take ya sanar masa buƙatarsa game da Muhaibish. Bokan numfawa ya yi yace, "Buƙata zata biya amma sai ka ziyarci kabarin Muhaibish ka ɗebo ƙasar kabarinta kana zuwa kar kayi magana da kowa ka watsawa ita wannan Muhaibish ɗin, idan ka yi haka duk wani kadarinta zai karye tana ji tana gani babu abinda zata iya aiwatarwa, wata ƙila tsinuwar Boka ta faɗa kanta. Amma akwai yuwar bayan wasu shekaru ruhinta ya wanzu a doron ƙasa, bana jin lokacin ma kana raye" Cikin jindaɗi ya amsa da cewar, "Zan aiwatar matuƙar buƙatata zata biya na ganin dukkansu sun wulaƙanta, ba damuwa ta bace dan sun dawo ko da har uwarta zasu dawo duniyar." Ya jima a wurin Boka suna tattaunawa sannan ya tashi ya nufi kabarin Muhaibish dake tsakiyar duniya a doron ƙasa.




Cikin nasara Kawun Mardid ya samu nasarar ɗebo ƙasar kabarin Muhaibish, kamar yadda Boka ya sanar masa haka shima ya aiwatar. Yana watsawa Muhaibish ƙasar ta faɗin gurin a sume sai bayan wani lokaci ta farko, tun daga wannan lokacin Muhaibish ta zama mai matuƙar hakuri duk wata baiwarta ta gushe, haka suka ci gaba da azabtar da su Kyauta da ayyukan wahala da tare da al'adatunsu na jinsin Jinnu, musamman Kyauta da bata daga ciki jinsin su. Shekarar Muhaibish ashirin a duniya Kakanta ya rasu nan suka fara taƙaddamar wanda za'a ɗora, dan sun san muddin Mardid ya hau karagar mulki watarana ita zata mulkesu, sai dai babban tashin hakalinsu sun san ko me zasu yi basu isa su ɗora wani akai ba, tun da sun san duk wanda aka ɗora indai bashi ya cancanta ba a ranar yake mutuwa.


Suna ji suna gani babu yadda suka iya haka suka ɗora Mardid akan karagar mulki tare da cin alwashin kawar da ita kafin mutuwarsa, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Muhaibish ta cika shekara ashirin da biyar ba tare ta yi aure ba, saboda gabaɗayansu babu wanda ya amince da haɗa iri da ita, kuma tun da Kyauta ta dawo rayuwar cikin jinsin jinnu bata ƙara hauro doron ƙasa ba, haka daga ɓangaren Muhaibish bata taɓa takowa doron ƙasa ba, tayi gabaɗaya rayuwarta ne a ƙarƙashin ƙasa. A wannan lokacin ne suka ƙara tsananta musu da iziya kala-kala har ta sanadin haka suka tsiyayewa Kyauta idanu ita kuma Muhaibish suka yanke mata hannuwa biyu, Mardid a wannan lokacin ne ya nemi ya yi musu bore amma sai suka nuna masa sam bazai yuwu ba, yana yunƙurin ɗaukan su Kyauta zuwa doron ƙasa suka kanainaye shi, su Muhaish da Kyauta suna tsaye haka suka dinga ciccire gaɓoɓin jikin Mardid gida-gida har yace ga garinku nan, Kyauta da lokacin girma ya fara kamata ban da kuka babu abin da take yi ita da Muhaibishi, saboda tun da taji ƴan uwansu sun fisgosu da ƙarfin tsiya sun fito da su jikinta ya bata akwai abinda zasu aikata musu mummuna, kuka take sosai da wannan ƙuncin rayuwar da suke fuska musamman da ta makance, tun da kafin makancewarta tana ganin abin da yake faruwa dan har maganar kurame suke da su Mardid, saɓanin yanzu da sai antaɓa jikinta take sanin yanayin da ake ciki, sai dai har zuwa wannan lokacin bakinta raɗau yake tana iya magana amma babu damar taji ko ta gani.


Kyauta ce ta fara lalubar hannun Muhaibish, sarƙar da Kaka ya bata ta damƙa mata sannan ta fara lalubar kunne ta tayi mata raɗa, jikinta ban da karkarwa babu abin da yake yi saboda firgici da kuma yanayin tsufa. Tana gama yi mata raɗa ta fara hankaɗata tana cewa, "Maza ki tafi dan karsu illata ki kema nasan tabbas bazasu barmu ba" Yayan Mahaifin Mardid da sauri ya fisgo Kyauta ganin haka yasa Muhaibish tabi umarnin mahaifiyarta, da gudu ta juya ta nufi sashensu da sauri ta fara haƙa ƙasar gurin cikin hannuwanta na jinnu masu kama da gatari, sai da tayi haƙa sosai sannan ta tura sarƙar ta rufe sai kuma ta rushe da matsanancin kuka saboda tasan yadda suka kashe Mahaifinta itama da Mahaifiyarta bazasu barsu ba, miƙewa tsaye tayi ta buga ramin ta ƙarfi ta ce, "Ya ke Mahaifiya na san a wanan lokacin bakya numfashi amma na tabbata sai kin dawo domin ki ɗau sarƙarki tare da fansar abin da waɗancen azzaluman suka yi mana" tana gama faɗa ta juyo ta fiti daga gurin anan ta yi cikiɓus da ƴan uwan mahifin na ta da ƙarfin tsiya suka ɗauke ta suka kaita wajen ta gawar iyayenta suke.


Tana zuwa ta sami Mahaifiyarta yashe a gefe kayan cikinta sun fito waye ga maƙogaronta shima sun fito da shi, a fusace ta juya gun Yayan mahaifinta da wasu jigajigai Biyar da suka fi tsananta musu ta fara kai musu duka cikin kuka, da ƙarfi suka fisgota suka danneta kallansu tayi tana huci ta ce, "Tabbas wannan abin da kuka aikata tamkar bashi ne na rantse da gawarwakin iyaye na sai na cimma buri da muradina akanku" Dariya suka bushe da ita sannan suka sa hannuwansu suka ɓara bakinta kamar yadda ake ɓare kan tinkiya bayan an yanka ta, wasu daga ciki kuma suka wara ƙafafuwanta suka raba ta gida biyu."


Ɗan Wanzam ya ɗago da kai ya kalli Sarki Abdallah cikin ladabi yace, "Allah ya taimake ka kaji ainihin labarinta, kuma maganar da nake maka bana tunanin akwai wani mai magani da zai iya ja da ita. Cimma buri da muradi ne ya dawo da ita banajin zata ƙyale me yunƙurin yi mata karan tsaye." Sarki Abdallah ya yi murmushi yace, "Lallai Wanzan ka iya bada tatsuniya me daɗi dan ko a cikin littafan tatsuniyoyi ban taɓa cin karo da labari me ban ta'ajibi kamar wannan ba"




Lamarin da ban tausayi😥 To fa mun dawo labari zamu ji yadda zata kasance mu kafta🤾🏻‍♀️


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[25/11/2021, 18:56] Ameera Adam🌚: 35...




Kamar wanda ya ga sabuwar hallita haka Ɗan Wanzam ya zubawa Sarki Abdallah Idanu sannan ya russunar da kai ƙasa, yana girgizawa kamar na ƙosasshen ƙadangare. Sauya fuska ya yi cikin damuwa yana ɗan jin haushin waɗannan kalamai na Sarki Aminullah, saboda yadda ya ɓata lokaci yana ta kwararo labarin kamar saukar ruwan sama. Amma ace wai duk wannan zantukan na shi sun tashi a banza, sake ɗago da kai ya yi yace, "Allah ya taimakeka ba zan tilasta amincewa da batu na ba, amma ina me bada shawara da abi lamarin yarinyar nan a sannu saboda gujewa hatsarin da baza'a yi saurin shawo kansa ba. Wani abu da na manta ban sanar da kai ba Ranka shi daɗe wannan masarautar da kake gani a cikinta ne Muhaibish suka yi rayuwa ita da iyayenta, ba wai ina nufin a doron ƙasa ba. A'a a dai-dai wannan gurin ta cikin ƙarƙashin ƙasa shuɗaɗɗiyar masarautarsu ta kasance. Allah ya baka yawan rai a wannan karan Muhaibish maganar mutum biyu kawai zata iya ji su dakatar da ita daga abin da tayi niyya, bansani ba suma ko sun ƙara dawowa ko kuma ita kaɗai ta dawo? Amma daga Mahaifiyarta Kyauta sai Mardid su kaɗai zasu iya dakatar da ita daga fitowar da tayi na cimma burinta, babban kuskuren da akayi kawo ta cikin masarautar nan, kuma bana tunanin akwai ƙaddarar da zata iya dakatar da ita. Allah ya taimake ka a dubi maganata da idanun basira, nan fada ce ban isa na faɗi abin da ba haka yake ba" Sarki Abdallah mutum ne me kafiya akan abin da yasa a gaba, dan haka ko da yaji wannan batu na Wanzam bai sa ko dai-dai da ƙwayar zarra yaji zuciyarsa ta sauya daga rashin gasgata Wanzan ɗin ba. Ɗan Wanzam ya gyara zaman Jakarsa sannan yace, "Allah ya baka yawan rai idan an sallame ni zan iya tafiya?" Sarki Abdallah ya bashi umarnin tafiya nan take kuma Wanzam ya maƙale jakarsa a hammata sannan ya yi godiya ga Takawa ya fice daga cikin fadar.


Bayan fitowar Wanzam Maleek na rakuɓe jikin bango, haka kawai yaji tausayinta ya kama shi duk da ya rasa dalilin haka. Kallanta ya yi ya ga tana zubda ƙwalla , kansa ya dafe ya rasa ma ta ina zai fara yi mata magana, mamaki yake a ransa ta yadda Shukransa duk ta birkice lokaci ɗaya. Karo na farko kenan da yaji tsoronta ya fara ɗarsuwa a zuciyarsa, jiki a sanyaye ya ƙarasa gurinta ya miƙa hannu yana san taɓata sai dai yana jin tsoro. Tattaro jarumta ya yi yasa hannu ya taɓa tana faɗin, "Shukra" Ɗagowa tayi tana kallansa da manyan idanuwanta da suka rune jawur kamar gauta, lokaci ɗaya yaji ya ƙara shiga taitayinsa. Cikin inda-inda yace, "Me yake damunki?" Hawayen idanuwanta ne suka ziraro ƙirjinta na bugawa da ƙarfi sannan ta ce, "Shima yace bazai iya ba. Yanzu haka zaku barni da tabon abin da yake damuna?" Lumshe idanunsa ya yi ya ware su akan kyakkyawar fuskarta yana kallonta da alamar neman ƙarin bayani, sunkuyar da kai ƙasa ta yi ta ce, "Babu damuwa zan aiwatar da kowane muradi da kaina bana neman taimakon kowa bare a nemi dakatar da ni a lokacin da nake tsaka da cimma burina." Tana gama ta miƙe tsaye ta fara takawa cikin izza da ƙasaita, bin ta ya yi da kallo baki a sake yana mamakin waɗannan bauɗaɗɗun kalamai na ta, daga kwanakin da tayi a cikin gidan yaci ace ya fara sabawa da waɗannan bauɗaɗɗun kalmomin nata, sai dai kodayaushe ta yi doguwar magana sai ya tsinci baƙin kalmomi, kamar wanda aka zarewa laka a jiki haka ya bi bayanta yana kiran sunanta, Maryo tafiya take kamar za ta tashi sama saboda sauri duk kiran da yake mata bata waiwayo ta kalleshi ba ballantana yasa ran zata bashi amsa.


Tana shiga sashen su Bayi suka fara zubewa suna gaishe ta amma babu wacce ta kalla daga cikinsu, tana wucewa suka bi bayanta da kallo sannan suka fara yafitar junansu suna ƴan gulmammakinsu. Ƙarasowar Maleek ne yasa suka yi ɗif cikin yanayin rashin gaskiya suka fara yi masa barka da hutawa. Fuska a ɗaure ya kallesu ɗaya bayan ɗaya yace, "Ku fice daga sashen nan gabaɗaya bana buƙatarku har sai na neme ku..." tun bai ƙarasa maganar ba suka fara kama gabansu suna yi masa a fito lafiya. Lokacin da ya shiga ɗakin jiki a sanyaye ya fara kiran sunanta amma shiru yake ji kamar an aiki bawa garinsu, yana shiga uwar ɗakinsu ya sameta kwance a kan fado tayi ɗai-ɗai tana bacci har da minshari, ga wanda bai ga wucewar Maryo ba idan ya yi tozali da ita a yadda take baccin nan zai rantse da Allah ta shafe sama da awa guda tana bacci. Bacci take yi hankali kwance fuskarta tayi fayau sai dai rama da ya lura tayi, wuyanta ban da ƙashi babu komai ya lura ta yi haske amma gabaɗaya da alama bata cikin kwanciyar hankali, tausayinta ne ya kamashi ya ga jikinta duk ya wani ɗalli-ɗallin baƙi-baƙi, mayar da idanuwansa ya yi kan tafin hannuwansa da har wannan lokacin da taruwar jini a jikinsu, lokaci ɗaya damuwa ta mamaye zuciyarsa saboda sabuwar lalaurar da ke tattare da matarsa hasalima tunowa ya yi da irin wasannin da suke yi na soyayya shi da ita, amma sai ga shi yanzu ya taɓa mata hannu ma fargaba yake saboda gudun tsattsafowar jinin da ke fita daga jikinta, a ɓangaren sa kuma raɗaɗin ne yake damunsa daga baya kuma wurin ya yi taruwar jini. Gefenta ya koma ya kwanta babu jimawa shima bacci ya yi awon gaba da shi.


Fulani Zaliha aikawa tayi a kira mata Abu saboda tun bayan dawowarsu bata ƙara saka ta a idanunta ba, da sallama ta shigo ɗakin cen ƙasa kusa da Fulani Zaliha ta zaune tana ƙaƙalo murmushi ta ce, "Barka da hutawa ranki shi daɗe" Fulani Zaliha kallan tsaf ta yi mata ta ce, "Zainab lafiya na ga baki fito ba, kin manta kayanki a wurina ko akwai abin da yake damunki?" Kamar ta soso mata inda yake mata ƙaiƙaiyi hawaye ya fara zubowa daga idanuwanta, dafa ta Fulani Zaliha ta yi tana kallonta don dama tun shigowarta ta fahimci tana cikim damuwa. Sai da tayi me isarta sannnan ta ɗago da kai ta ce, "Maryo na gani a bakin kasuwa kafin naje wurinta ta ɓace mini, na duba wurare amma babu ita babu alamunta." Fulani Zaliha cikin tausayawa ta ce, "Wace ce Maryo ɗin kuma a ina take?" Abu ta goge ƙwallar idonta ta ce, "Ƴar uwata ce da Ɗan ƙanwar Takawa ya tafi da ita a zuwan matarsa ce, ya tafi Adamawa da ita amma ɗazun nan na ganta. Kuma wallahi ba Matarsa bace hasalima Maryo bata taɓa aure ba tare muka taso a wurin Innarmu." Tana zuwa nan a zancen ta rushe da matsanancin kuka. Fulani Zaliha cikin rashin fahimta ta ce, "Bangane ba matarsa ba ce kuma ya tafi da ita? Kina nufin Maleek ɗan wajen Fulani Fahima da suka koma Adamawa?" Abu da sauri ta gyaɗa kai ta ci gaba da cewa, "Ni tsoro ma nake ji wallahi karta faɗa wani wurin, dan nasan kafiyar Maryo bazata taɓa dawowa gidan nan dan ra'ayin kanta ba, na tsaya zan nemo ta Yaya Saif ya janyo ni muka dawo wataƙila da na gano ta" Fulani Zaliha ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "To Takawa yasan ba matarsa bace kuma ya barsu suka tafi da ita, wanne irin lamari ne wannan kamar ba a ƙasar musulmai ba" Cikin Abu ne ya kaɗa sai a lokacin ta lura da irin sakin bakin da tayi, tsoro ne ya kamata musamman da taji Fulani Zaliha ta fara faɗa tana cewa zata samu Takawa da maganar, a tsure Abu ta kalli Fulani Zaliha ta ce, "Allah ya taimake ki dan Allah karki cewa Takawa a bakina kika ji, ina jin tsoron hukuncin da zai yi mini. Amma wallahi ko Inna ta zaki kira ki tambaya zata gaya miki Maryo ba matarsa bace, ko aure ma ba'a taɓa yi mata ba" Jikin Fulani Zaliha sanyi ya yi haɗe da tausayinta, cikin zuciyarta take faɗin, "Wai Mai martaba me yake so ya zama ne, bayan rashin adalcin da yake nunawa har kuma da shiga haƙƙin aure da musulunci. Anya ya cancanci ci gaba da mulkar dubbanin al'umma da.." Abu ce ta katse mata tunani da cewa, "Dan Allah Ranki shi daɗe ki..." Ƙaƙalo murmushi Fulani Zaliha ta yi ta katse ta da cewa, "Karki damu Zainab babu abin da zai faru bazan sanar masa ba, kawai ina mamakin yadda lamarin ya kasance. Kiyi ta yi mata addu'a in sha Allah babu abin da zai faru da ita sai alheri." Abu ta amsa da, "Ameen" Fulani Zaliha sallame ta sannan ta faɗa duniyar tunani da cin alwashin dole ta tunkari Sarki Aminullah da wannan maganar.


Yamutse fuska take kamar wacce tayi ta ci kashi, duk wanda ya kalli fuskar Jakadiya zai tabbatar tana cikin matsananciyar damuwa. Tana gabda shiga sashen Fulani Maryama suka yi karo da wata baiwa, da sauri ta dafe goshi tana zabga ruwan masifa, "Kai waɗannan yara dai tir da halinku jarababbu kuna tafe da kawuna a sama kamar raƙuma." Dije da take mulmula goshi ta ce, "Allah ya baki haƙuri Jakadiya ban san kin taho ba" A zafafe Jakadiya ta ce, "Ina zaki sane kina fama da ido yana karuwar akuya, wacce uwar kika ƙunso kike sauri kamar sabon kwarto" Ƙunshe dariyarta Dije tayi dan sun lura kwana biyu Jakadiya acikin masifa take, tana shirin bata amsa Jakadiya ta ce, "Ba magana nake yi miki ba Dije? Idan Uwarki Laraba ce zaki yi banza da ita" Dije ta tsuke fuska ta ce, "Ke dai wayon zagi ne kawai ban da haka me na yi miki da zaki zageni, yanzu ka rama cibi ya zama ƙari, ƙari ya zama ƙababa. Haka kawai tsohuwa sai jaraba" tana gama faɗa ta bi ta gefen Jakadiya fuuuu ta wuce. Baki a sake Jakadiya ta bi ta da kallo tana tafa hannu ta ce, "Biri ya yi kama da mutum. Wallahi ba banza ba wannan yarinyar sai mun binkiceta dan naji har wari-warin maza take, ban da haka har ni zata gayawa haka bari na shiga na fito dole mu zauna da Laraba mu lalube ta tass." tana gama faɗa ta shige ciki. Zaune ta samu Fulani Maryama da alama itama tana cikin damuwa, bayan sun gaisa Jakadiya ta saluɓe ɗankwalin kanta ta ce, "Maryama anya Marduska ba aljabu yake turowa suna kankarar naman kaina ba, dubi ki ga wani ɓamɓori kullin ta Allah idan na cire ɗankwalina sai na karkaɗe wannan farin garin, ina gudin a wayi gari aga kaina ya marmashe tass" Jakadiya ta faɗa cikin damuwa. Fulani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login