Showing 18001 words to 21000 words out of 57328 words
mirzatu Zulik gurwatu bisanit kaljuwas fargista kalminfat wargas girbat?"
(Tuba muke ya shugaba amma bamu so kika ƙi bamu dama ba, yanzu haka zamu sa ido akan Zulik wannan karanma ya yi nasara akanmu?) miƙewa sukayi suna hawaye suka fara binta kusurwar bango suna wucewa.
TO FA MEYE HARSASHENKU NE KUNA KAN BAKARKU NA MARYO BAIWA CE? KU DUBA DAI DA KYAU ANYA BAIWA CE? 🤣🤣🤣🤣
YANZU FA SAI KUCE INA NEXT PAGE 🙄
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[02/11/2021, 18:30] Ameera Adam🌚: 20...
Fulani Zaliha a ɗan tsorace ta kalli Saif ta ce. "Wai duk a yaushe haka ta faru?" Saif cikin halin ko'inkula yace. "Ammi a mafarkin nan da nayi yanzu" Fulani Zaliha ta rasa abin cewa dan gabaɗaya bata fuskanci inda maganar Saif ta dosa ba, ya za'ace mutum daga dafe kai ko minti biyu baiyi ba amma har ya yi mafarki alhalin ba bacci yake ba, cikin zuciyarta take faɗin. "Allah ka dubeni ni da yaron nan bamu da gata bayan naka, Allah kasa ba wata matsalar bace take tunkaro yaron nan Allah ka jiɓanci lamarinmu" a fili ta kalli Saif ta ce. "Saif ka dage da Addu'a insha Allah babu abin da zai faru sai alheri." Gyaɗa mata kai ya yi sannan ya amsa mata da baki yana dafe kai har lokacin kansa bai daina juya masa ba.
Sarki Aminullah karɓar Jaririyar ya yi yana murmushj yana yabawa da wasannin da suke gudanarwa, ƙare mata kallo ya yi sannan ya karanta addu'a ya tofa mata tare da fatan Allah ya albarkaci rayuwarta, miƙawa Aminansa ya yi suma suka yi mata addu'a sannan aka miƙawa Dogarin ya ƙarasa ya miƙawa Sarkin Wanzamai ita, yana karɓarta ta buɗe cikin jakarsa ya zurata tare da riƙe hannun jakar ya kuma wulwulawa yana gamawa da ya ɗaga jakar ya zazzageta a idon mutane, ba ƙaramin mamakin wannan siddabarun nasa suka yi ba kuma abin ya ƙayatar matuƙa, Maƙera na fita sai maharba suka shigo suma suka gudanar da nasu wasannin gwanin birgewa kamar yadda yake bisa ga al'ada duk shekara, daga maharba sai Ƴan bori suma haka suka fito suka dinga wasanninsu da rawaye-rawayensu bayan fitar su babu jimawa mawaƙa da maroƙa suka shiga suka fara baje kolin tasu bajintar. Ana tsaka da shagali mutuwar Sarkin ƙira ta ƙarasa gurin wasan Al'ada ba ƙaramin kaɗuwa mutane sukayi ba saboda a yadda wasu suke faɗa ko awa guda basuyi ba da ganinsa a gefen fili ba amma ace ya mutu, wasu daga ciki muatane kuma musawa sukayi sai da aka hangi gawar Sarkin ƙira sannan suka yarda, ƴan uwansa Maƙera ba ƙaramin ƙaɗuwa sukayi da rasuwar shugabansu ba. A gurguje aka fara haramar tashi saboda mutuwar Sarkin ƙira ga kuma yamma ta fara yi, Gayyato Sabon Bawa aka ƙarayi domin a ji buƙatar da buƙata agurin Sarki Aminullah.
Kamar wancen karon yana sanye da wandon ƙarfe haka ya shigo filin fuskarsa ɗauke da murmushi, yana shigowa cikin filin Salman da ke gefen Sarki Aminullah ya runtse idanu yana jin wani irin yaammm a jikinsa, kamar wancen karon nasa na farko da ya shiga filin gurin wannan karanma haka yaji, yana daga zaune yaji kamar ana fisgarsa duk yadda yaso ya dakatar da wannan yanayin ya faskara, daga cikin filin Dogarin ne ya fara tambayar Sabon bawan sunansa. Ɗagowa ya yi ya kalli sashen da Salman yake nan ya saki wani shu'umin murmushi sannan yace. "Suna nan Zulik" da sauri Dogarin ya kalleshi ganin yanayin kallon da Dogarin ya yi masa yasa ya fahimci suɓutar bakin da ya yi da sauri yace. "A garinmu sunan da ake kirana da shi kenan" Salman da ke gefe tun da ya kifa kansa a jikin kujera bai ƙara sanin abin da yake faruwa ba" Sabon Bawan ya saci kallan Sarki Aminullah ya ci gaba da cewa. "Amma sunana na ainihi Sulaiman" Dogari ya jinjina kai cin shela ya ce masa.
"Sarki ya ji ka yanzu sai faɗi buƙatarka" Zulik ya sunkuyar da kai ya yi yace. "Akwai wata yarinya da naji ta aikata laifi ita nake san Mai Martaba ya fito da ita kuma ya wanketa daga laifin da ake zarginta da shi, saboda tayi ƙanƙanta da a yanke mata hukunci amma ayi mini afuwa idan maganata tayi tsauri" Gabaɗaya ido aka zubawa Zulik, gurin shiru ya ɗauka kowa ya kasa kunne yana jiran jin maganar da zata fito daga bakin Sarki Aminullah, shi kansa Sarki sai da maganar ta ratsa sassan jikinsa saboda bai taɓa tsammanin akwai wani Bawa da zai taɓa tunkararasa da wannan maganar ba, cikin zuciyarsa yake faɗin. "Amma wannan koma waye zan nemeshi a sirrance dan jin abin da yasa shi neman wannan buƙatar, bayan kowa yasan gabaɗaya Bayin da ke shiga suna shiga gasar ne dan neman suna, dukiya ko sarauta." sai da ya saita nutsuwarsa sannan ya buɗe baki a hankali dan na nesa da su bazai taɓa fahimtar abin da ya faɗa ba. Dogarin da ke cen gefensa ya miƙe ya fara zuba banbaɗanci.
"Sikari bakai farin banza ba. Madafar bayi masu iyayenma kun gama musu komai, Allah ya taimakeka ya ƙara nisan kwana Hadari kake mai sauke dubun albarkai. Allah ya ja da zamaninka ɗan toron giwa sarkin Musulunci da Musulmai takawarka lafiya Madara mai farin gado..." Haka bafaden nan ya dinga bambaɗanci sannan daga ƙarshe yace. "Yaro ka kawo kuka gurin da za'a share maka hawayenka indai wannan ce damuwar duniya da lahira ta kau sai dai wata ba wannan Adalin Sarki Mai tausayin talakawansa ya amince da buƙatarka" Gabaɗaya gurin ya ɗau hanayaniya wasu daga ciki suna ganin sakarci da wawtarsa ace ka samu dama kamar wannan amma ace wai ka tsaya akan ceton wata Baiwa daban, wasu kuma na ganin taimako ya yi waɗanda suka yarda Maryo bazata iya aikata abin da ake zarginta ba, Har ila yau wasu daga cikin mutanen gani suke kamar da wata a ƙasa dan gani suke kamar bakinsu ɗaya tsakaninsa da Maryo. Zulik russunawa ya yi cikin girmamawa yace. "Godiya nake Allah ƙara girma da tsawoncin kwana" Bafaden da ya yi shela da farko yace. "Allah ya taimakeka yaro ya yi godiya ya daɗa ya yi godiya ga wannan karamcin da akayi masa." Sarki Aminullah da har lokacin idanunsa na kan Zulik ya gyaɗa kai. Bafaden yace. "Sarki ya amsa maka Yaro" Daga haka suka fice daga gurin. Bayan fitarsu babu daɗewa Salman ya buɗe idanunsa da suka rune jawur yana dafa kansa da yake sara masa, bin gurin da mutanen da ke zaune yake da kallo sannan ya fara jin waɗansu irin surutai a cikin kunnuwansa.
Daga haka Sarki Aminullah ya yi jawabi ga jama'ar gari da faɗakarwa sannan wasu daga cikin Manyan baƙi suma suka yi nasu ƙarin hasken sannan aka tashi daga wasan gwanin birgewa, bayan tafiyar Mai martaba da manyan baƙinsa gida matasa suka fara wasan tseren doki a tsakaninsu.
Inna Habi ita da Abu suna zaune sauran Bayi suka rinƙa shiga ɗaya bayan ɗaya, tun basu gama shiga ba akayi mata albishir da roƙon da Zulik ya yi, Inna Habi saboda murna har da kukanta, farin cikinta yaƙi musaltuwa, haka taci alwashin neman yaron da yayi wannan taimakon dan tayi masa godiya. Jakadiya baƙin ciki ƙunshe cikin zuciyarta ta wuce sashen Fulani Maryama, tana zuwa suka fara Jajantawa juna bisa amincewar da Sarki Aminullah ya yi.
Da daddare Dogarawan da ke tsaye a kan Maryo suna nan zaune suka ji bugun ƙofa suna buɗewa suka ga Uwar Bayi ce da wata baiwa biye da ita. Hamdala suka yi a fili saboda sun san ko ba komai Uwar Bayi zata fanshe su wannan zaman jigum-jigum ɗin da suke yi. Uwar bayi kallansu ta yi bayan sun gaisa ta ce. "Takawa ya turo mu akan mu ci gaba da kula da ita har zuwa lokacin da za'a sallameta." Babban Dogarin yace. "Gaskiya ba ƙaramin daɗi naji ba bari mu zo mu wuce sai ku ɗora daga inda muka tsaya" Uwar Bayi mugun kallo ta watsawa Maryo da ke kwance tana sauke numfashi sama-sama, lokaci-lokaci take jan guntun tsaki tana hararata.
Bayan tafiyar Dogarawan Sarki kamar daga sama aka jeho shi haka suka ga ya faɗo ɗakin ko wadatacciyar sallama babu a bakinsa, Uwar bayi a hassale ta kalleshi ta ce. "Kai yaro lafiyarka ka shigo mana saƙaƙa kamar wanda ya halarci taron kafirai?" Zulik bai bi ta kanta ba ya ƙarasa bakin gadon da Maryo take kwance ya tsugunna akan gwiwoyinsa fuskarsa saitin fuskarta ya fara shafawa. Uwar Bayi salati ta rafka tana tafa hannuwa tace. "Kai jama'a yau me nake gani a ido na garnaƙeƙen ƙato ya faɗo mana ɗaki zai aikata cin mutumci a kan yarinya" Wannan karanma bai tanka mata ba ya ci gaba da shafa fuskarta sannan ya kamo hannunta yana ƙoƙarin cire zobon hannunta, kamar wacce aka zubawa wuta haka ta buɗe idonta a gigice.
Uwar Bayi miƙewa tsaye tayi tana cewa. "Wallahi ba zan zauna ana alfasha a idanuna ba Allah ya kamani ba gwara na kira hukumar asibiti su san halin da ake ciki ba, dan wannan sai ya ja mana girgizar ƙasa..." ɗagowa ya yi a fusace cikin wata irin murya yace. "Idan na kuma jin bakinki sai na murɗe wuyanki fuskarki ta koma baya" Uwar Bayi har lokacin bakinta bai mutu ba ta ce. "Kai Yaro dube ni nan tun kafin a haifi uwar me sabulu balbela take da farinta babu wani buɗe ido da zaka nuna mini, bar ganin kaci gasar maƙera..." kafin ta ƙarasa magana taga ya ɗora hannuwansa biyu akansa ya fara wana kansa kamar yadda ake wana tayar keke, daga Uwar Bayi har baiwar da suke tare cen ƙuyar ɗakin suka maƙale tare da ƙanƙame juna, Uwar Bayi harda sakin fitsari daga gurin da take. Cikin muryarsa mara daɗin saurare yace.
"Wannan ƙaramin aikina ne na mayar da gabanki ya koma bayanki dan haka ki kiyaye..." Shima bai rufe bakinsa ba Maryo ta ɗauke shi da mari, kamar koyaushe duk lokacin da zata fuskanci wani yanayi yanzun ma hakance ta faru, jinin da ke ɗiga daga hancinta ya fara ɗiga a hankali. Sunkuyar da kansa ƙasa ya yi yana jiran yaji wani hukuncin nata da zai biyo baya amma sai ya ji shiru, idanunta ne suke ci gaba da rinewa ga wata irin ajiyar zuciya da take saukewa. Jin ta yi shiru ya sa ya ɗago yana kallonta hawaye ya gani kwance cikin idanuwanta yana shirin magana yaga tahowar hawayenta kafin ya ɗiga ya sa hannu, yana ɗiga ya kaishi bakinsa ya lashe. Runtse idanunta tayi ba tare da ta buɗe su ba ta ce. "Me ka yiwa Furzaaan" guntun tsaki ya ja yace. "Wato har yau bazaki daina zance wancen sakaran ba ko?" tun kafin ya ƙarasa maganarsa ta buɗe idanunta ta ɗorasu akanshi, da hannuwanta biyu ta shaƙo wuyansa tana jijjigashi ta ce. "Tambayarka nake me ka yiwa Furzaaan? Wallahi muddin wani abu ya faru da shi zaka yi mamakin hukuncin da ɗauka a kanka" Dariya ya farayi sama-sama sai kuma ya ci gaba da ƙyaƙyacewa da dariya sannan ya tsuke fuska yace. "Na ji na yarda duk abin da zakiyi ki aikata shi amma ki sani ke da Furzaaan har abada dan a yanzu kin yi gabas ya yi arewa, ammma idan kina ganin ƙarya ne bisimillah" Maryo runtse idonta tayi dan tabbas tasan Zulik ya faɗa ne amma Furzaaan bazai taɓa juya mata baya ba, kallansa tayi da idanunta da suka rine jawur ta ce. "Wani abun ka aikata masa?" Dariya ya yi ya kamo hannunta da sauri ta fusge tana tofa masa yawu a fuska, cikin rashin damuwa da abin da tayi masa yace. "Idan kina tantama ki cire zoben hannunki ki bani zan fayyace miki komai" Wani kallo ta wurga masa tace. "Kai ɗin? Kana tunanin akwai wata yarda da zan kuma baka kana tsammanin zan ƙara amincewa da ƙasƙantacce, makiri annamimi kuma azzalumi kamar kai? Sam har abada wannan kuskuren bazan ƙara aikatashi ba ka riƙe bayananka bana buƙata kuma ka fice mini dan bana ƙara muradin ganinka." tana zuwa nan a maganar ka ta rushe da wani irin matsanancin kuka, fuskar wani Dattijo ce take mata yawo a cikin ƙwayar idonta dan haka kukanta ya tsananta harda shassheka.
Uwar bayi ita da Baiwa suka gefe banda Idanu babu abin da suka zura musu kamar waɗanda suke kallon wata dirama ko wasan kwaikwayo. Zulik runtse idanunsa ya yi yace. "Banasan kina damuwa akan waccen mara amfanin babu wani abu da zai amfane ki da shi bansan wacce tsiyar ce a jikinsa ba, amma tun da haka kike ganin ya fi miki shikenan idan mutuwa zakiyi saboda kuka wallahi mutuwa ita zata rabamu, keda Furzaaan sai kallo dan babu ke a shafin rayuwarsa." Maganganunsa jinsu taje kamar saukar aradau kukanta ne ya tsananta gwanin ban tausayi.
Daga kusurwar bango ƴanmatan nan ne suka ƙara fitowa yanayinsu ɗauke da damuwa suna jifan Zulik da mugun kallo. Biyu daga cikinsu ne suka yo gaba ɗaya ta zagaya ta gefen hagunta ɗaya ta zagaya ta gefen damanta, dafata sukayi cikin lallashi suna lallashinta.
"Shugaba kukanki yana nuna masa alamaun gazawarki wanda haka sam baya mana daɗi, dan Allah ki bamu dama ko da sau ɗaya ne mu wanke wannan hawayen naki da yake kwaranya." suka faɗa lokacin da suma hawaye ke fita a idonsu.
Goge hawayenta Maryo tayi ta ce. "Baku san waye Zulik ba Fitya nina san wanene shi. Haka zalika wannan ba yaƙin ku bane dan babu tantama idan kuka saka kanku a ciki yana iya nakasta ku. Fitya idan na rasaku bayan Furzaaan da wa zanyi rayuwa?" Jinjina kai suka yi suna share mata hawaye sannan ta koma ta kwanta tana lumshe idonta.
Duk wannan budurin da ake yi uwar bayi da Baiwa Salma suna tsaye suna kallon ikon Allah, tsoro da mamaki ne ya kamasu ganin yadda Maryo ke ta magangu ita kaɗai tana ambatar Fitya dan sun lura kamar da wata take magana ba Sabon bawa ba.
Zulik taɓe baki ya yi ya kalli Maryo yace. "Rayzuta tun ina binki ta lallami kar mu kaiga yadda mukayi a wancen karan, abin da baki sani ba wallahi Furzaaan ba naki bane kuma akan idonki zai nemi matar aure ya aura gwarama ki samawa ranki salama." Yana gama faɗa ya juya ya fice ko waiwayenta baya yi. A firgice ta ɗago tana kallon bayansa gabaɗaya tsoro yake bata saboda tasan waye Zulik, tasan wannan iƙirarin da yake ba a banza ba" hawaye ne suka ci gaba da kwarara a idonta. Kamar wacce ta tuna wani abu ta juya ta kalli ɗaya daga cikin ƴanmatan tace.
"Hikbiyat Maza kije gurin Abu ko Inna Habi inasan sanin abinda yake faruwa game da Furzaaan, ki hanzarta banasan a samu matsala." Uwar bayi kallan juna suka yi da suka ga Maryo na aike alhalin ita kaɗai ce kwance akan gadon, dan su tsoron ƙarasawa gurinta suke yadda suka ji tana surutai ba fasali.
MU HAƊE A COMMENT💃🏻 BA NEXT PG WLH WUTAR TA LALACE
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_
_Ummou Aslam Bint Adam_😉
[03/11/2021, 16:02] Ameera Adam🌚: 21...
Maryo na ganin wucewar Hikbiyat ta kuma runtse idonta tana jin zuciyarta na wani irin suya. Daga gefenta ƴan matan ne suka russuna cikin girmamawa suka ce. Hutawarki lafiya Shugaba" bata buɗe idonta ba ta gyaɗa musu kai sannan suka bi ta gurin da suka fito suka wuce.
Uwar Bayi suna nan daskare jikin bango sai zare ido suke kamar shege a rabon gado, ganin kamar Maryo ta fara bacci yasa suka saki juna suna tafiya saɗaf-saɗaf a hankali suka buɗe ƙofar suka fice harabar asibitin. Uwar bayi ido duk ya yi zuru-zuru ta kalli Baiwa Salma ta ce. "Ke Salame lamarin yarinyar nan ya fara bani tsoro fa anya ciwon nan nata babu bugun iska a ciki kuwa?" Baiwa Salma ta riƙe haɓa ta ce. "Nikam waccen mutumin da ya fita shi yafi ɗaga mini hankali, Uwar bayi dubi yadda yake wana kansa kamar kan babyn roba gaskiya nikam na gama tsorata da shi ai dole dama yaci gasar ƙira." Uwar Bayi ta ce. "Ke siddabaru ne fa kawai ina ce a gabanki sarkin wanzamai ya fiddo jaririya daga cikin jaka, kinga zancen da ake yi ya tabbata ko dama ni nasan ruwa baya tsami banza, ashe kuwa budurwarsa ce shiyasa ya shiga wannan gasar dan ya fitar da ita. Amma kuma fa kamar bulayi ne kawai yake yi dan na lura kamar bata san shi.?" Baiwa Salma ta ce. "Uwar bayi mu bar maganar danni na gama tsorata da lamarin mutumin nan kar muje ko yana laɓe yana jinmu." Uwar bayi shiru ta yi dan ita kanta har zuwa lokacin a tsorace take da lamarin Sabon bawan.
Daga cen gidan Sarki abin ciccika kala-kala aka girgirka na al'ada gidan cike yake da mutane da sauran baƙin da ba a ranar zasu wuce ba. Inna Habi tun da aka sanar da ita hukuncin Sarki Aminullah taji ta garau sai ma ta saki jikinta ita da Abu aka ci gaba da shagalin bikin al'ada dasu a cikin gida.
Gabannin magriba Inna Habi da kanta ta taka gurin