Showing 6001 words to 9000 words out of 57328 words
wani yaji abin a suke faɗa, Abu ta ce. "Ke Maryo kiji tsoron Allah mutumin da yake fama da jinya" Maryo ta ce. "Wallahi da gaske nake kuma har magana munyi da shi kin ga ma zobenyar da ya bani, wallahi kamar yasan yadda nake ƙaunarsa." Abu ta ƙara ƙwalalo ido waje tana duba zoben da yake ta walwali a hannun Maryo.
_LITTAFIN ANYA BAIWA CE NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[26/10/2021, 19:44] Ameera Adam🌚: 14...
Maryo Fisge hannunta tayi ta ce. "Ke Abu wannan kallon har ina" Abu ta riƙe haɓa ta ce. "Maryo har yanzu ina mamakin abin da kika faɗa mini ne. Yanzu Ɗan Sarkin gidan nan guda shi ne zai faɗa soyayya da ke, anya Maryo ba yaudararki zai yi ba?" Maryo ta ce. "Wallahi nidai ina ƙaunarsa Abu kuma shima haka sannan kinsan me yace mini? Cewa yayi fa..." Maryo ta tsuke bakinta ta ci gaba da cewa. "Ke mu bar zancen dai" Abu cikin yanayin tsoro ta ce. "Maryo! Maryo anya kuwa? Ni fa ina guje miki wani abu ance fa akwai wani Ɗan sarki yadda kikasan bunsuru haka yake, kibi sannu fa wallahi kar dukiya ta ruɗeki ya kaiki ya baro mu shiga uku, saboda banza bata kai zomo kasuwa ta yaya yana Ɗan sarki zai ce ke yake so duk sauran Bayin gidan nan babu wacce ta kwanta masa sai ke da ko wata biyar bakiyi da zuwa ba" Maryo ta ce. "Ke wallahi sam ban fahimci haka daga gareshi ba, nifa wallahi ji nake ma kamar tsohon tsimin soyayya ya tado mini" Abu ta ƙara ware idanu tana kallan Maryo da take ta zubo kalamai. Cikin mamaki ta ce. "Wai nikam Maryo yaushe idanunki suka buɗe haka bansani ba, nifa tun da muka shigo gidan nan naga duk kin wani sauya kamar bake ba"
Maryo kafaɗar Abu ta dafa ta ce. "Ashe kin lura Abu wallahi ni kaina ji na nake wata iri musamman idan na tuna baiwa ce ni sai na dinga tunanin Anya baiwa ce? Ina jin girma da matsayi na ya wuce na kasance a matsayin Baiwa amma gabaɗaya na rasa amsar haka." Abu ta ce. "Maganar gaskiya Maryo muddin Inna ta san abin da yake faruwa hankalinta ba ƙaramin tashi zai yi ba, ni kaina yanzu haka a tsorace nake ina gudun abin da zai je yazo" Maryo ta ce. " Babu abin da zai faru sai alheri." Abu ta ce. "Allah yasa zan fi kowa murna" Maryo ta ce. "Wai ma kinsan wani abun farin ciki Abu" Abu ta girgiza kai"
Maryo ta ce. "Wallah Saif ya warke garau ke baki ji muryarsa ba raƙwai kamar me, kai amma gaskiya anyi kyakkyawa ajin farko" Abu ta ce. "Ke dama fa a wata majiya me tushe naji ana raɗe-raɗin wai asiri fa aka yi masa, wasu kuma suka ce mayu ne suka lashe shi tun a ciki wasu kuma suka ce aljanu ne ke zance dai da yawa amma fa anfi ƙarfafa asirin ne akayi masa." Maryo ta ce. "Aikuwa aniyarsu ta bisu." daga haka suka ci gaba da tafiya har sun kusa ƙarasawa sashen Bayi Maryo ta ce. "Yauwa Abu dan Allah ko Inna zata ga zoben nan zan ce tsintarsa nayi saura ki tona ni dan nasan halinki." Abu ta ce. "Kika ci gaba da yi mini rashin kunya a matsayina na yayarki wallahi babu abin da zai hanani tonawa." Maryo ta marairaice murya ta ce. "Wallahi na daina Yaya Abu" Abu tayi dariya ta ce. "Dole gyaɗa tayi mai in taƙi ta sha matsa" lokaci ɗaya suka kwashe da dariya.
Maryo da Abu ba ƙaramin shaƙuwa sukayi ba Abu ita ce Babba amma idan ka gansu zaka ɗauka Maryo ce babba, saboda Maryo tafi Abu tsayi sosai suna san junansu sai dai idan faɗansu na sakuwa da sakuwa ya motsa zaka ɗauka basu taɓa zaman mutumci ba, sai dai dukda haka basa taɓa bari wani ya ci mutumcin ɗaya daga cikinsu.
Suna ƙarasawa gurin Inna Habi suka zauna Maryo ta bawa Inna Habi labarin kyautar da Fulani Zaliha tayi mata, sai da Inna Habi ta gama sauraronta sannan ta ce. "Maryo nikam ina jiye miki tsoro" Inna Habi sai da ta ɗaga kai ta lelleƙa ta ga kowa sabgarsa yake yi ta ci gaba da cewa. "Kinsan uwar gijiyarki alamu sun nuna ba mace ce me kirki ba, dan Allah kiyi taka tsantsan banasan kiyi abin da za'a azabtar mini da ke. Karki din ga shiga sashen Fulani Zaliha idan ba haka ba za'a kaɗa miki gangar munafurci, kuma bazaki ji daɗin zama da ita ba."
Maryo sai a lokacin ta tuno da abin da Fulani Maryama tayi mata amma bata sanarwa da Inna Habi ba saboda karta ɗaga mata hankali sai kawai ta ce. "Inna ai tama sallame ni ta ce kar na ƙara zuwa sai ta neme ni" Inna Habi ta zaro ido waje kamar maye ya ga jariri ta ce. "Maryo ince ba wani abin kika yi mata ba ko?" Maryo dariya take sosai ganin yadda Inna Habi ta firgice lokaci ɗaya sai da tayi me isarta sannan ta ce. "Inna wai dan Allah me yasa zuwan mu gidan nan kika zama matsoraciya" Inna Habi tayi murmushi ta ce. "Yaro man kaza. Ai dole na zama matsoraciya nan fa gidan sarauta ne kuma a ƙarƙashin wasu muke bamu da kowa sai su, al'adar gidan sarauta daban da ta sauran gidaje kuma akan kunnenku ake bamu labarin irin azabarwar da ake ganawa mutumin da aikatawa Sarki, Ƴayan sarki ko Matan sarki mummunan abu. To kuwa kun ga ai kowa ya kwana lafiya shi ya so." Gabaɗaya suka gyaɗa mata kai sannan Inna Habi ta ci gaba da yi musu nasiha akan zanantakewar rayuwar duniya.
Daren ranar gabaɗaya Maryo haka tayi shi cikin farin ciki har sai Inna Habi ta lura da walwalarta ta tambayeta amma ta ce babu komai.
Washegari da asubar fari Fulani Maryama ta aika kiran Jakadiya, Jakadiya ba ƙaramin haushin tashin da akayi mata taji ba tana tafe a zuciyarta tana mita. "Haka kawai mace da dameni ta addabeni ni kenan da zarya kamar nayiwa sarki ƙarya yasa a kamoni..." haka dai Jakadiya tayi ta mita har ta ƙarasa bayan ta gaida Fulani Maryama, ta ce. " Ranki shi daɗe lafiya kika aiko kira na da asubar fari?" Fulani Maryama da idanunta suka yi luhu-luhu saboda kuka da rashin bacci ta ce. "Jakadiya ko ban faɗa ba kinsan kwanciyar hankali yayi ƙaura akan fuskata da ilahirin jikina, Jakadiya harsashenki ya tabbata wallahi yarinyar nan ita ce dai da Boka ya gaya mini" Jakadiya na jin haka ta dafe ƙirji tana rafka salati Fulni Maryamm bata bi ta kanta ba ta ci gaba da cewa. "Wallahi jiya naga siddabaru a ɗakin nan kwana nayi banyi bacci ba, dubi hannuwa na" ta ƙarasa faɗa tana warawa Jakadiya Hannuwanta da duk suka kumbura sukayi taruwar jini. A tsorace Jakadiya ta ce. "Me nake gani haka ni jikar Sa'a meye haka a hannunki" Fulani Maryama ta ce. "Wallahi shaƙe yarinyar kawai nayi da hannuna shi ne yayi haka" Jakadiya ta ce. "To kuwa mun shiga uku wannan bala'in ai ba ke kaɗai zai shafa ba yanzu meye abin yi." Fulani Maryama ta ce. "Sannan wani babban tashin hankali cikin dare sai gani nayi yaron cen Saif ya ɓullo mini ta ƙarƙashin ƙasa yana yi mini kashedi kala-kala ke har zancen Salman ya yi mini wai yasan Salman ba Ɗan Takawa bane" Jakadiya najin haka ta zaro idanu haɗe da cewa. "Lallai kina cikin tashin hankali tashin alƙiyamarki yazo a gidan."
_LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[27/10/2021, 19:31] Ameera Adam🌚: 15...
Fulani Maryama da duk tayi zuru-zuru ta ce. "Kina nufin ni kaɗai bala'inta sai faɗawa kenan? Ai uban kuturu ya yi kaɗan bare na makaho. Jakadiya kin manta duk inda zan sa ƙafata tare muke zuwa ko kinmanta ke kike rakani wasu guraeren da bansani ba, ke tsohuwar banza kalleni da kyau kin tuna ke kika fara yi mini rakiya gurin boka kinga kuwa duk abinda ya same ni dole ya shefeki" Jakadiya tayi murmushin takaici ta ce. "Maryama ni kike kira da tsohuwar banza? Lallai na yarda ɗan adam butulu ne. Da kike iƙirarin nina fara yi miki rakiya gurin boka kinmanta bala'in da kike ciki a lokacin? Sai yanzu da kwaɓarki tayi ruwa zaki mayar da ni ƴar iska ko. Kar nake kallanki Maryama kuma wallahi da sannu sai na farke miki laya tun da ke ba ƴar arziki bace."Fulani Maryama cikinta ne ya ƙara ɗurar ruwa ganin Jakadiya na shirin yi mata bore, tunowa tayi da batun Boka Ɗan Duna sai kuma ta sheƙe da wata iriyar dariya har tana riƙe ciki.
Jakadiya zaro ido waje tayi saboda tafi kowa sanin wacece Fulani Maryama, tana shirin magana Fulani Maryama ta ce. "Kin makaro siyan kazar sayen baki ranar haihuwa, nasan kin fini sanin waye Boka Ɗan Duna tun da kece kika yi mini jagora gurinsa idan kinga dama zaki iya zuwa kice ya bincika miki naki matsayin agurin waccen yarinyar, saboda bazakiji mutuwar sarki a bakina ba dan waƙa a bakin me ita tafi daɗi, dama tuntuni na kwana da sanin duk daren daɗewa akwai ranar da zaki yi mini bore, dan haka idan kinje kinji daga bakinsa ganin damanki ne kizo mu haɗa kai mu yaƙeta ganin damanki ne ki ƙwaci kanki ke kaɗai."
Jakadiya ba ƙaramin sanyi gwiwoyinta sukayi ba kallan Fulani Maryama tayi ta ce. "Maryama anya ba yaudara ta kike yi ba? Idan haka ne me yasa tun tuni baki sanar da ni ba?" Fulani Maryama ta tsuke fuska ta ce." Saboda na kwana da sanin wannan ranar zata zo nasan kina nan cike da jin haushina kuma nasan har gobe mutuwar jikarki na tsaye a ranki duk ta dalilina, ba tun yau na lura da irin kallon ƙiyayyar da kike yi mini ba dama kawai kike jira ki ɗau mummunan mataki a kaina, shiyasa na barwa zuciyata har sai ranar da kwaɓarmu zatayi ruwa." Jakadiya ta ce. "Amma tsakanina da ke Allah ya isa Maryama kin cuceni yanzu me Bokan yace miki a kaina?" Fulani Maryama ta ƙara sunkuyo da kanta ta ce. "Yace akwai wani al'amari da zai haɗa ku da ita zata tona miki asiri akan marigayi Mahaifin Sarki Aminullah, sannan zata tona miki asiri akan kisan da aka yiwa Mahaifiyar Sarki Aminullah" Jakadiya a firgice ta miƙe tsaye jikinta na rawa ta ce. "Maryama ya akayi kika san wannan bayan ko aurenki da Aminullah ba'ayi ba lokacin" Wani irin shu'umin murmushi Fulani Maryama tayi ta ce. "Har yanzu baki gama sanin wacece ni ba Jakadiya shiyasa nace kibi sannu, kinsan har me ya gaya mini zata tona miki asiri akai? da sauri Jakadiya ta girgiza kai." Fulani Maryama ta ce. "Kawo kunnenki" Jakadiya har tuntuɓe take ta tsugunna saitin fuskar Fulani Maryama.
Fulani Maryama raɗa ta yi wa Jakadiya a kunne a firgice Jakadiya ta ɗago tana bin Fulani Maryama da wani irin kallo, sai kuma ta rushe da kuka tana dafa ƙafar Fulani Maryama ta ce."Maryama kiyi mini rai ki bani mafita wallahi muddin abubuwan nan suka fito kashina ya bushe nasan alƙiyamata ta tsaya dan ba makawa kasheni za'ayi, dan Allah ki ceceni" Fulani Maryama ta ce. "Mu ceci juna dai Jakadiya, kyace na ceceki ni idan kura na maganin zawo ta yi wa kanta mana. Ai ya zama wajibi mu haɗa kai mu yaƙi yarinyar nan tun bata fara yaƙarmu ba"
Jakadiya ta fara goge hawayenta ta ce. "Ta wace hanya kenen?" Fulani Maryama ta ce. "Na zauna nayi nazari asiri ko tsafi bazai kaimu ba, dole sai mun bi da dabara da makirci haɗe da zagon ƙasa. Dole mu shigo da Ɓoyayyiyar fuska cikin lamarin nan, idan ba haka ba muna ji muna gani wankin hula zai kaimu dare." Da mamaki Jakadiya ta ce."Waye kuma ɓoyayyar Fuska" Fulani Maryama ta ƙara yi mata raɗa a kunne wannan karan Jakadiya ta jima da baki a sake tana bin Fulani Maryama da kallon mamaki. Jiki a sanyaye ta ce. "Maryama kin wuce tunanin me tunani, amma ya akayi ya koma ɓoyayyar Fuska gaskiya lamarin Masarautar nan ya fara bani tsoro" Fulani Maryama ta ce. "Waɗanda kika sani kenan da zaki san sauran sai kin mutu a nan gurin saboda mamaki." Jakadiya da Fulani Maryama haka suka ci gaba da ƴan ƙulle-ƙullensu, sai da suka tattauna hanyoyin da zasu ɓullowa labarin sannan Jakadiya ta yi wa Fulani Maryama sallama ta koma sashen su jiki a sanyaye.
TARIHIN MASARAUTAR KANO
Masarautar Kano tana daga cikin manyan masarautu a kasar Hausa. Tarihi ya nuna cewar garin Kano ya kafu kimanin shekaru 400 kafin zuwan addinin musulunci. Ma'ana a yanzu garin ya kai shekara kusan 2000 da kafuwa.
Masarautar ta taimaka wajen bunkasar garin Kano da Arewa da ma Najeriya baki daya. Garin Kano ya kasance cibiyar kasuwanci a yankin arewacin Najeriya da Jamhuriyyar Nijar a tun kafin zuwan Larabawa da Turawa Kasar Hausa.
Asalin Kalmar 'Kano'
Mutanen da suka fara zama a Kano makera ne da suka tashi daga garin Gaya domin neman kasa mai arzikin tama, wacce za su sarrafa su yi karfe da ita.
Daga cikin mutanen da suka fi shahara cikin wadanda suka fara zama a yankin akwai wani jarumin mafarauci da ake cewa Kano, kuma sunansa ne aka sanya wa garin na Kano.
Mutanen sun yi dace da samun kasar mai kunshe da sinadarin tama, sannan kuma mai albarkar noma da ruwa da dazuzzuka da za a iya yin farauta. Wajen ya kasance mai matukar tsaro kasancewar akwai manyan duwatsu da tsaunuka, da mutane za su iya hawa su fake idan an kai musu hari.
Daga cikin duwatsun da suka taras akwai dutsen Dala, Goron Dutse, Fanisau,Jigirya da Magwan.
Akwai kuma koguna daban-daban da suka kewaye yankin, da suka hada da kogin Jakara, da kogin Kano.
Hakan ya sa mutane da dama suka rinka yin kaura zuwa yankin domin zama.
KAFUWAR GARIN KANO
A lokacin da aka kafa garin Kano babu wani shugaba guda daya da ya hada kan jama'a a karkashin mulkinsa.
Jama'ar da suke zaune a kauyuka kamar Dala da Goron Dutse da Fanisau da Magwan da Jigirya duk suna karkashin shugabanci ne na mutanen da suke tare da su.
Daga baya ne da garuruwan suka fara bunkasa, sannan dangantaka tsakaninsu ke kara inganta a lokacin ne aka samu shugaba guda daya da ya hada kan mutanen wato Barbushe.
Masana tarihi na cewa Barbushe jika ne na kimanin 15 ga shahararren mafaraucin nan wanda aka bai wa birnin sunansa wato “Kano”. Barbushe shahararren mafarauci ne kuma shine mutum na farko da ya hada kauyukan a karkashin ikonsa a lokaci guda a bisa tsarin gudanarwan shugabanci da kuma addini. A lokacin sa ne addinin bautar Tsumburbura ya shahara. Barbushe shine babban bokan Tsumburbura.
Bayan zamanin Barbushe da kimanin shekara 200 aka samu wasu mutane daga yankin Daura da suka ci Kano da yaki suka kafa sarauta a karkashin Bagauda a shekarar 999.
Sarakunan Kano
Da akwai gidaje da dama da suka yi mulkin Kano tun daga 999 zuwa yanzu. Masana tarihi sun ce, tun daga kan Sarki Bagauda dan Bayajidda har kan sarkin Kano na karshe kafin fulani wato Sarki Alwali dukkaninsu daga jini daya suke.
Daga baya an ci gaba da samun sauye-sauye da kuma rungumar wasu sabbin abubuwa a tsarin shugabancin masarautar ta Kano.
Wannan kenan!
Maryo tun da gari ya waye ta kasa zaune ta kasa tsaye gabaɗaya zuciyarta so take tayi tozali da Saif ko taji daɗi, dabara ce ta faɗo mata dan haka ta saci jiki ta fice daga sashen su na bayi duk kuwa da kicimillin aikin da suke sha na shirin bikin al'ada, tana fita bata zame ko ina ba sai sashen matan sarki, tana gabda shiga ta hango shi zaune a wata ƴar inuwa, yana zaune ya jingina da bango idanunsa a rufe, ta jima a tsaye a gurin tana son tayi masa magana amma tana jin tsoro, kamar wanda aka tsikara haka ta ga ya buɗe idonsa karaf ƙwayar idonsu ta haɗu guri ɗaya, sunkuyar da kai tayi ta russuna tana murmushi ta ce. "Barka da hutawa Yaya Saif" ɗago ta idanunsa yayi a hankali ya gyaɗa mata kai.
Maryo ta shafi kanta ta ce. "Dama nazo wuce ne nace bari nazo mu gaisa" Wannan karanma gyaɗa mata kai yayi kamar dai zata ƙara maganan sai kuma ta ce. "Na barka lafiya" haɗa hannu biyu yayi alamun godiya sannan Maryo ta wuce. Tana tafe tana waigensa har ta yi nisa da shi.
Gabaɗaya sai taji babu daɗi saboda yadda ta ga Salf ya yi mata kamar ma bai santa ba, cen washen gari ta nufa bakin wata bishiyar tsamiya ta zauna isakar gurin me sanyi na ratsata nan da nan bacci yayi awon gaba da ita abinka da waɗanda bacci baya wadatarsu bacci take sosai harda minshari.
A cikin baccinta ne tayi mafarki ta hange su kwance a cikin wata ƙorama mai matuƙar kyau da daɗi, yanayin gurin ba ƙaramin kyau ya yi mata ba tana cikin ruwan suna wanka ita da Saif sai watsawa junansu ruwa suke, suna cikin nishaɗi sosai irin na masoyan da suka jima