Showing 48001 words to 51000 words out of 57328 words

Chapter 17 - Anya Baiwa Ce 1 Complete Hausa Novels.txt

30 Nov 2024

3908

ku kaɗai nake kalla naji daɗi, idan kuma wani abu ya faru da kai ya kake so nayi?" Goge hawayen idanunsa ya yi yace, "Na miki alƙawarin haka baza ta taɓa faruwa ba amma kema sai kin cire damuwar dake zuciyarki, kinsan fa ba ki kaɗai bace ko kina so ki jawa Jaririn da ke cikinki matsala, kina so ki haifo yarona yana tagumi?" murmushi tayi ta girgiza masa kai sannnan ya miƙe yace, "Amma ɗazu naga kamar bakya nan ina kika je" Ɗan duburburcewa ta yi ta ce, "Naje gurin Mirdad" ɗan canja fuska ya yi cikin damuwa yace, "Ki dinga hankali fa ina gudun kar su cutar da ke" Gyaɗa masa kai ta yi sannan ya fice daga cikin bukkar ya nufi bakin wutar da take ci kamar a maƙera. Zaune ya yi a bakin wutar ya ƙura mata ido yana kallo yana tunanin rayuwarsa ta baya da tushen mafarin shigar jikarsa cikin wannan matsala.


ASALIN LABARIN KYAUTA


Damina shine ainihin cikakken sunan Kaka asalinsa Maguzawa ne yana da Mata Dela dukkanninsu haifaffun garin Kano ne, iyayensu su Fatake ne wanda bincike bai tabbatar da asalin garin da suka fito ba, Mahaifin Damina dana Dele abokaine dan haka suka haɗa su aure. Damina ya taso da wata baiwa tun ranar da mahaifiyarsa ta fahimci tana ɗauke da cikinsa, a ranar da ta fahimci haka a ranar Bayan Mahaifinsa ya fita farauta Allah ya bashi nasara ya farauto wani ƙasurgumin Zaki wanda ya samu nasarar halakashi tun kafin ya kawo shi gida. Tun daga wannan ranar sai abubuwaa nasara ya dinga samunsa wanda basu taɓa tsammani ba, daga wannan lokacin sai suka fahimci Duk tinkiyar da shigo sashen Dela sai to babu jimawa zata samu ciki, kuma idan ta tashi haihuwa sai dai ta haifi ƴaƴa uku, huɗu har akwai wacce ta haifi ƴaƴa biyar. Lokaci ɗaya zance ya ƙaraɗe cikin ƙauyen Goron dutse cewar Dela na ɗauke da cikin Ɗan baiwa, tun daga wannan lokacin aka ɗinga ririta Dela hatta aikin gida bata yi akwai masu zuwa su yi mata, wannan magana ba iya nan kaɗai ta tsaya ba har sai da je kunnen Sarkin lokacin wato Sarkin Kano Rabo Juma Dogon gida, ba ƙaramin murna suka yi ba saboda a ganinsu sun samu Ɗan baiwa dan haka wasu al'amuran nasu zai zo da sauƙi. Akwana a tashi har Allah ya sauki Dela lafiya ranar da ta haifeshi kuwa aka wuni aka kwana ana tafka ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, dan a wannan lokacin tun da damina ta kama ba'a taɓa tafka ruwa mai yawa kamar na ranar ba, hakan ne yasa suka saka masa suna Damina, kuma tun da aka haifeshi yaƙi kama Mama duk yadda aka bashi ƙi ya yi, dan a lokacin har Nonon akuya dana Saniya aka taso aka bashi amma yaƙi karɓa, sai ruwa suke bashi haka ya ci gaba da rayuwa.Damina yana girma harkokin baiwarsa na ƙara bunƙasa har ya kai shekara goma sha takwas, tun daga wannan lokacin yan garin suka mayar da shi wani babban jigo daga rayuwarsu, dan a lokacin ba dan sun bada ƙarfi wajen bautar Rana ba wasu daga cikinsu da tuni sun fara bautawa Damina, lokacin da ya kai shekara goma sha takwas dai-dai Aljanu suka faa buɗe masa ido, har suna taimaka masa wajen bayar da magunguna da warkar da marasa lafiya. Hakan ne yasa ya fara killace kansa a wata bukka da Mahaifinsa ya tanadar masa, wacce a cikinta ne ake kai masa ziyara yake bada magunguna, tun tana bayar da magani har mata suka fara kawo masa tayin buƙatarsu dangane da kishiyoyinsu, sannu a hankali Damina ya rukiɗe ya koma Boka dan duk abin da kake buƙata kana zuwa gurinsa zai sanar da kai abin da yake tafe da kai, kuma bazaka bar gurin ba sai da biyan buƙatarka. Ana cikin haka wata mata tazo da ƴarta nemar mata maganin farin jini tun da Damina ya ƙyalla ido yaji ta kwanta masa, wani garin magani ya basu akan tayi wanka da shi tun daga ranar yarinyar me suna Laraba ta kamu da mutuwar sansa, lokacin da iyayenta suka fahimci haka sai suka shiga ɗimuwa saboda a tunaninsu ta ɗauko Dala ba gamo, amma wani abun mamaki ana tararsa da maganar sai ya yi na'am da ita. Ba'a ɗauki lokaci me tsayi ba aka sha bikinsu Laraba ta tare a gidan iyayen Damina, bayan wani lokacin Laraba ta haihu ta haifi Ɗanta kyakkyawa namiji wanda suka saka masa suna Nomau, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Damina babu wurin da labarinsa bai karaɗe ba, ba iya garin kano ba har sassan garuruwan da ke makwabtaka da garin na Kano sun san da zaman Damina. Shekara Nomau goma a duniya iyayen Damina suka rasu tare da wasu daga cikin mutanen dake kusa da su sakamakon ambaliyar ruwan da ta same su.


Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Nomau ya cika shekara Ashirin da biyar cif a lokacin girma ya fara kama, Damina kuma a wanann lokacin aka yi wa Nomau aure da matarsa Tani, bayan bikin Nomau da Tani babu jimawa Damina ya nemi alfarma gurun abokinsa Ɗan sarkin fararen Aljanun ƙarƙashin ƙasa, sai da Aljanin ya gama jin buƙatar Damina sannan yace. "Buƙatarka da ci gaban baiwarka ga sauran zuri'arka zata cika matsawar ka yarjewa tawa buƙatar, nikuma na yi maka alƙawarin wannan taimako da muke yi maka kana bada magunguna zamu ci gaba da buɗewa zuri'arka haska tun daga kan Ɗanka Nomau har zuwa ƙarshen zuri'arka, amma da sharaɗin zaka bawa Ɗana auren abin da yake cikin sirikarta Tani."


BARKA DA JUMA'A🤹🏻‍♀️


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[21/11/2021, 16:24] Ameera Adam🌚: 32...




Ban yi dogon tunani da nazarin abin da gaba zata haifar ba na amince da buƙatar Aljani Mardidas, ba ƙaramin daɗi Aljanin ya ji ba kuma tun daga ranar duk lokacin da zai ziyarce ni tare yake zuwa da Ɗansa me kimamin shekara goma a duniya wanda na yiwa alƙawarin jika ta, ni duk a tunanina hakan da na yi ne zai sa baiwar da nake da ita ta karkasu har zuwa kan zuri'ata ta ƙarshe, Sai dai wayo da dabarata sam basu tasirantu da abin da nayi tsammani ba, saboda lokacin da cikin Kyauta ya kai wata bakwai a lokacin ne Nomau ya kwanta wata gajeriyar jinya kuma be daɗe a kwance ba rai ya yi halinsa. A lokacin hankalina ba ƙaramin tashi ya yi ba saboda duk duniya Nomau kaɗai na mallaka a matsayin ɗana, ga shi sannu a hankali girma ya fara kamani. Fargaba ta ɗaya kada na tsufa na rasa madafar dafawa wannan hali da nake ciki yasa na nemi agajin abokina wato Mirdidas, lokacin da yaji bayanina ya tausaya mini matuƙa saboda duk kusan matsalarmu ɗaya da shi, shima Ɗansa ɗaya a duniya hakan ce ta sa ya kawo mini wata shawara wanda a lokaci nayi kasaƙe ina sauraronsa cikin yarensu na jinsin Jinnu, kasancewar idan na juya baki muna magana da shi sai ka rantse nima na fito daga cikin tsatsonsu ne.


"Shawarar da nake ganin zata kawo maka mafita ba wata ce Damina illa ka tara mutanen garin nan tun da suna ɗaukar zancen fiye da tsammani, ka ce musu kayi harsashen za'a dinga samun hasara duk shekara dan haka bayan kowa ya yi noma, duk mutum ɗaya zai sauke maka buhun gero ɗaya, masara, da dawa ɗaya. Sannan ga waɗanda basa noma sai ka gindayawa muku su dinga kawo maka kayan sarrafawa, suma daga cikin ka zaɓi wani aiki da zasu dinga gudanar maka na ka,matarka da sirikarka. Sai dai ka gargaɗesu da cewar wannan kaya da zasu kawo maka zaka ajiye ne mu mutanenka mu dinga ɗauka saboda rabonmu ne, ga tabbatar musu da cewar ga duk wanda ya kuskurewa haka to tabbas annobar zata faɗa kansa. Haka zaka yi dan ka samu rayuwarka ta inganta cikin sauƙi, kuma ni nan zan taimaka maka akan duk mutumin da ya bijirewa umarninka." Ba ƙaramin jin daɗin jawabinsa na yi ba saboda ko kaɗan wannan dabarar bata zo mini ba, godiya nayi masa sannan muka yi sallama. Kamar yadda muka yi da Mirdidas haka na tara jama'ar gari na yi musu bayani dalla-dalla kamar gaske kuma duk cikinsu babu wanda ya misa mini, dan dama ko kaɗan ban kawo akwai wanda zai bijiremini ba duba da komai na faɗa musu yana faruwa kuma ina iya basu maganin warkar abun. Tun daga wannan lokacin abinci dai sai dai na bawa wani, dan abinci na wata shekara har tarar da na shekara baya yake yi, wannan shawara yasa na ƙara riƙe amini na hannu bibbiyu kuma amintakarmu ta ci gaba da tafiya lafiya kalau.


Ranar Juma'a aka haifi kyauta kuma a ranar ne aka yiwa Abokina Mardidas naɗin sarauta dan haka murnar ta haɗe mana, an naɗa sa a matsayin Sarkin fararen alijun ƙarƙashin ƙasa, wato kujerar mulkin da mahaifinsa ya yi murabus ya bar masa. Wannan dalili yasa ya nemi alfarmar saka mata suna Kyauta saɓanin Jummai da muka yi niyyar saka mata. Haka yarinya ta taso gwanin birgewa da ban sha'awa kuma tun da aka haifeta koyaushe Mirdad na tare da ita, shi yake yi mata wasa da duk wasu abubuwan ɗebe kewa shi yake mata, har ɗaukanta yake yana kaita cen duniyarsu domin ta saba da yanayinsu tun da alƙawarine cewar matarsa ce halak malak, Shiyasa ko da Kyauta ta fara wayo bata damuwa idan ya tafi ita dan sai ta shafe kwana biyu har zuwa uku a gurinsu, sai dai su ajiyewa Uwarta me siffarta a zuwan ita ce, Shekarar Kyauta bakwai annobar amai da gudawa ta sauka a nahiyarmu hatta ni bata kyale ba, dan ba ƙaramar wahala na sha ba. Ta wannan sanadin ne akayi asarar rayuka masu yawa ciki harda Mahaifiyar Kyauta da me ɗakina, wannan mutuwar ba ƙaramin taɓani ta yi ba dan ba ƙaramin so da ƙyauna nake yi wa Laraba ba, babu yadda muka iya haka muka haƙura.


Kyauta ta taso cikin gata da kulawa gaba da baya duk da kasancewarta marainiya amma tafi dubbanin masu iyaye gata, shekararta goma sha biyar aka sha bikinta da Mirdad. Sai dai dama tun kafin bikin take mini ƙorafin ƴan uwansa basa ƙaunarta, dan har akwai masu iƙirarin zasu kasheta, danma Mahaifin Mirdad wato Mardidas na tsaye tsayin daka yasa suke shakkun aikata mata wani abun, sai gori, tsangwama da wulaƙanci ba wanda bata sha. Dalilinsu na yin haka wai dan ta kasance jinsin bil'adam ce, kuma suna ganin irin fifikon da Mardidis yake yi akanta fiye da ƴaƴansu, saboda ba ƙaramin ƙaunarta yake yi ba sakamakon tsananin san da ɗansa yake yi mata. Kuma babban damuwarma so suke Mirdad ya auri ɗaya daga cikin ƴaƴansu saboda jikansu samu damar ɗane karagar mulkin da kowa yake fatan ace jininsa ne akai, da farko bansan da wannan matsalolin ba har sai da fa fara zama a cikinsu take sanar dani halin da ake ciki. Abokina Mardidas na samu da maganar cikin jin kunyata ya bani haƙuri tare da nuna mini kawo ƙarshen matsalar cikin kwanaki ƙalilan, haka na kawo ido na sa amma ƙasan zuciyata babu daɗi duba da yanayin waɗanda take rayuwa da su amma babu abin da zan iya dan na lura a duk duniya idan aka cire ni babu wanda Kyauta take ƙauna kamar Mirdad.


Mardidas ne ya tayarwa da ƴan uwansa da suke Uba ɗaya bore saboda dama shi kaɗai mahaifiyarsa ta haifa, ganin haka ya sa suka shirya masa zagon ƙasa da ƙulle-ƙullen makirci har ya kwanta wata irin jinya da ni kaina na kasa gano irinta, wannan dalili yasa shima ya yi murabus ya barwa Ɗansa Mirdad karagar mulkinsa wato mijin Kyauta, kuma anyi haka babu jimawa Kakan Mirdad mahaifin Mardidas ya mutu. Wannan ya ƙara wutar ƙiyayyarsu a zuciyar Kyauta dan dole ba dan ta so ba yasa ta haƙura da zaman cikin jinsun su saboda lamarin ya yi tsanani, sai dai wani abun ɗaure kai da ban mamaki kuma abin farinciki a gurina bayan na fahimci Kyauta na ɗauke da juna biyu, duk lokacin da wani daga cikinsu yayi niyyar cutar da ita, ko da bai aiwatar ba wannan abin da ya yi niyyar yi mata shi ba kuma sai abin ya faru da shi, wannan ne ya ɗan rage mini damuwa saboda na rage fargabar ko zasu cutar da ita, a gefe ɗaya kuma nake ƙara godewa Abokina Mardidas dan buƙatata ta biya tun da gashi jikata tana ɗauke da cikin ɗan baiwa kamar ni. Dalilin dawowarta gida gurina kuwa dan ta samu nutsuwa ne a matsayin da na me juna biyu, saboda ko da babu wani abu da zasu yi mata ya kamata ta samu hutu daga tarin baƙin cikin da suke ƙunsa mata. Daga ɓangaren abokina Mardidas tun ina samu na kai ziyara duba shi muna samu muyi magana da shi har ta kai ga ƴan uwansa na yi mini baraza da rayuwa ta, kuma a wannan lokacin hatta Ɗansa na cikinsa baya iya ganewa saboda zafin ciwo, wani abin farinciki da ko tunowa nayi da mutuwa ta bana jin fargaba yadda Mirdad yake tsananin ƙaunar Kyauta da bata kulawa nasan bana numfashi zai riƙe mini ita amana, tun da dai a duk duniya Kyauta bata da kowa sai ni sai kuma Mirdad, a gefe ɗaya kuma hankalina na matuƙar tashi idan na tuna kar ƴan uwan mahaifinsa su cutar da Mirdad kamar yadda suka cutar da Mahaifinsa, idan babu Mirdad babu niwace rayuwa Kyauta zata yi ita da abin da yake cikinta?"


Amsar da Kaka ya kasa bawa kansa kenan sai ƙwallar dake tsiyaya daga idanunsa, wasu ƙarare ya ɗiba ya ƙara watsawa cikin wutar sannan ya miƙe a hankali yana takawa har ya koma cikin wata bukka dake kallon wacce kyauta take ciki.


Bayan kwana biyu da faruwar wannan nazarin na Kaka ya fara wata irin rashin lafiya, a lokacin Hankalin kyauta ba ƙaramin tashi ya yi ba saboda tun da take bata taɓa ganin Kaka cikin wannan halin ba, ban da kuka babu abin da take yi. Danma Mardid na bata kulawa da yana ƙara kwantar mata da hankali akan damuwar da take ciki. Wata rana tana zaune a gefe Kaka yana fitar da numfashi da kyar gefe ɗaya Mardid ne yake kallansu cikin tausayawa, miƙa hannu ya yayi da sauri Kyauta ta miƙa hannuta cikin tafin nasa hannun. Miƙawa Mirdad ɗayan hannu ya yi shima ya miƙa masa nashi hannun, haɗa hannun Kyauta da na Mirdad ya yi yana runtse idonsa ya fara magana cikin ƙarfin hali, "Mirdad ga amanar Kyauta nan nikam tawa ta zo ƙarshe, ka kula min da ita amana da ita da abin da zaku haifa nan gaba, nasan da yadda ƴan uwanka suka ɗauki Kyauta sai dai nasan haɗuwarka da ita akwai wani ɓoyayyen al'amari, amma a kowanne hali kuke ka taimaka ka riƙe amanar dana baka, sannan ka isar yi mini da saƙo ga mahaifinka koda baya magana amma zai ji wannan wasiyyar da zan baka." wata sarƙa Kaka ya ciro daga wuyansa ya damƙawa Mirdad ya ci gaba da cewa.


"Wannan sarƙar Mahaifinka ne ya taɓa bani ita sama da shekara tamanin, shi kasan har yau ya kasa sanar dani inda ya samo wannan sarƙar. Idan kaje karka bari wani yaji wasiyya ta ku kaɗaice daga kai sai Kyauta sai Mahaifinka, ka ɗora masa a ƙirjinsa kace ya yafe mini idan har wani abu ya taɓa haɗa mu mara daɗi, sannan wannan sarƙa ka mallakawa Kyauta ita halak malak ita ce kaɗai abin da zata dinga gani tana tunawa da ni. Ina ji a jikina Kyauta zata fuskanci jarrawabawa kala-kala, sai dai har numfashi ya fita daga jikina a ƙasan zuciyata zan yi ta yi miki fatan ɗaukaka akanki da abin da yake cikinki, duk abin da zaki gani kiyi haƙuri domin rayuwa bata zuwar maka yadda kake son ta kasance maka..." maganar Kaka ce ta katse nan take ya fara kakari da tari kafin su miƙa masa ruwa yace ga garinki nan. Kyauta wani irin kuka ta fashe da shi mai tsuma zuciya nan take mara da bayanta ya amsa ta shiga murƙususu da alama naƙuda ce ta taso mata gadan-gadan. Kafin Mirdad ya yi wani yunƙuri sai jin kukan Jaririya ya yi ta faɗo, rasa yadda zai yi ya yi nan take wata dabara ta faɗo masa, shafe ganin gawar Kaka ya yi ga mutane yana gurgiza sai ga shi ya rikiɗa cikin siffar Kaka, da sauri ya fice ya nufi maƙotan bukkarsu ya sanar da wata tsohuwa halin da ake ciki, da murnarta ta ƙaraso tana yiwa Kaka barka duk a tunaninta Kaka ne, ta fara gyara Kyauta da ke tsugunne wanda har lokacin ban da kuka babu abin da take yi, musamman idan ta ɗaga ido ta kalli Mirdad dake cikin siffar Kaka wanda tasan ya yi haka ne dan ya kauda shakku a zuciyoyin mutanen da suke ma'amula da su Kaka.


Lokacin da aka kwantar da Kyakkyawar Jaririyarta a gefen makwancin Kaka, duk abin da yake faruwa tsohuwar bata lura da gawar Kaka dake gefe ba saboda Mirdad ya kauda ganinta, Mirginawa Jariryar tayi tana mutsu-mutsu hannunta ya hau kan Sarkar da Kaka ya bawa Mirdad ya ajiyeta lokacin da zai kira tsohuwar, Kyauta dake gefe tabi Jaririyar da kallo, Mardid ne ya ƙarasa ya ɗauki yarinyar yana jin ƙaunarta a zuciya sai dai gefe ɗaya yana tausayin Kyauta, ɗaga ta sama ya yi bayan tsohuwar ta fice yace, "Barka da zuwa Muhaibish, tabbas harsashen Kaka da alama bazai tashi a banza ba" Kallan Kyauta ya yi da tai zuru tana kallansa ya ci gaba da cewa, "Kyauta kiyi haƙuri! Na saka mata suna Muahaibish ne saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login