Showing 45001 words to 48000 words out of 57328 words
A ɗan duburburce Abu ta ce. "Dama nazo na gaishe da Inna ta ne." Fulani Maryama ta taɓe baki ta ce. "Ba fa koyaushe na fiye san a dinga yi mini zarya a sashe ba, dan haka ki kiyaye idan ba haka ba zan sa a dakatar da zuwanki." Abu ta russuna ta ce. "Za'a kiyaye Allah ya taimake ki." Fulani Maryama kamar ba za ta amasa ba sai kuma ta ce. "Ki gaggauta zuwa kiyi abin da ya kawo ki dan ina da abin da zansa ta tayi mini" Abu ta russuna ta miƙe ta godiya. Abu na shiga ɗakin Inna Habi ko kyakkyawar gaisuwa basu yi ba, cikin raɗa tace. "Inna wallahi na yau a bakin kasuwa naga Maryo wai kafin na ƙarasa na neme ta na rasa" zaro idanu waje Inna Habi tayi cikin zumuɗi ta ce. "Me yasa baki mata magana ba?" Abu hawaye ta fara yi tana bawa Inna Habi labarin yadda sukayi, jiki a sanayaye Inna Habi ta ce. "Abu kuma kina ganin maganar Saif bata hanya kuwa? Gani nake Maryo zata zo amma taƙi ƙarasowa gidan nan? Idan Maryo bata Adamawa ai da tuni munji labari daga gurin Takawa. Ina ganin yawan tunaninta ne yasa kika fara ganin tana miki gizo." Motsi suka ji daga bakin ƙofar Fulani Maryama da sauri Abu ta ce. "Inna sai anjima ni zan wuce dama cewa nai bayi nazo na gaishe ki" Baiwar Fulani Maryama ce ta ce. "Inna Habi Fulani ta ce kije ki matsa mata ƙafa." Inna Habi jiki na rawa ta ce. "To muje" Abu cikin tausayi ta kalli Mahaifiyarta tana jin tausayinta dan tabbas tasan bata jin daɗin zaman gurin Fulani Maryama, ta so ace ita take zaune a ɓangarenta Mahaifiyarta na sashen Fulani Zaliha amma babu yadda ta iya, jiki babu ƙwari kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Zuciyarta babu daɗi ta koma sashen Fulani Zaliha, tana shiga ta wuce kan katifarta ta kwanta tana tunanin halin da ƴar uwarta take ciki.
Akan idanunta suka wuce suka tafi lokacin da take leƙensu tana daga wani ɗan lungu a ɓoye, lokacin da ta fito daga gurin da take ɓoye a dai-dai lokacin Saif ya juyo suna haɗa ido ya watsa mata harara hannunsa riƙe da na Abu, da sauri ta koma lungun ta ta jingina ta bango ƙirjinta na bugawa nan take taji wani abu na sukarta a zuciya, hawaye ne suka zubo mata saboda gabaɗaya rayuwar tayi mata zafi. Tana nan tsaye taji an dafa ta ta baya da sauri ta juya dan ganin wanda ya dafa ta, wata tsohuwa ta gani suna haɗa ido taji gabanta ya faɗi tsigar jikinta ta shi, ɗauke idanunta ta yi saboda bazata iya ci gaba da kallonta ba, tsohuwar ta katse mata tunani da cewar. "Ki ƙara haƙuri. A rayuwa dukkan tsanani yana tare da samu, da sannu ƙuncin rayuwa zai yaye miki ki dai karki cutar da kowa ki zauna da kowa lafiya, karki shiga haƙƙin wani ki riƙe Allah da manzansa indai kika riƙe wannan zaki ci ribar rayuwa." gyaɗa mata kai tayi ta sunkuyar da kai tana goge hawaye tana ɗago da kai ta nemi tsohuwar ta rasa, ba ƙaramin tsoro ta ji ba da sauri ta bar gurin jikinta har rawa yake saboda tashin hankali.
Wannan karan tsoro ne ƙarara ya bayyana akan fuskar Maleek yana san ya yi mata magana yana tsoron kar shima wani abun ya same shi, daga waje wani Dogari ne ya leƙo yace. "Allah ya taumaki Yarima labari ya ishewa Takawa akan tafiyar mai maganin, yanzu haka akwai wani Sarkin wanzamai yana bakin ƙofa idan ka bada umarni a shigo da shi yanzu, Mai martaba yace shima zai jarraba tashi basirar." Maleek yawu ya haɗiya mai ɗaci dan shi kansa ƙarfin halin zama ya yi a ɗakin da take, ajiyar zuciya ya sauke yace, "Ba damuwa a ce ya shigo" yana gama faɗa suka haɗa idanu da Maryo lokaci ɗaya ta sakar masa murmushi wanda ya sa cikinsa murɗawa ba tare da yasan dalili ba, dan ya yi imani da Allah wannan murmushi da take yi ba lallai ya zame musu alkairi ba. Yana nan tsaye Mai maganin ya shigo hannunsa rataye da jakar wanzancinsa, Dattijo ne dan da alama zai yi shekara hamsin zuwa hamsin da biyar. Cikin girmamawa ya russuna ya gaida Maleek sannan ya kai dubansa ga Maryo da ke zaune a gefe ta harɗe ƙafafuwanta, suna haɗa ido ta miƙe ƙafafuwanta sannan ta ce masa. "Idan zaka iya zan baka wani aiki, nima ba hurumi na bane da na aiwatar da shi tun tuni." Wanzamin kallanta ya yi yana ƙarewa yanayinta kallo ya ɗan tsorata da yadda ya kalli yanayinta, cikin ƙarfin hali yace. "Wane aiki ne? Idan bai gagara ba na aiwatar da shi" Maryo a hankali ta tako ta ƙarasa gabansa, Maleek dake ƙoƙarin zama yana kallonsu cikin mamaki, dan ya yi tsammanin shima wutar zata saka masa. Idanunta ne suka ciko da ƙwalla ta sa hannunta ta shafo hawayen idonta, hawayen ta dangwala a ƙasan tabarmin kaba. Nuna masa tayi ta ce, "Wannan abun nake son kaje ka tonr mini shi a fadar Daulatul Ujuran zan baka kyautar abubuwan da baka taɓa tsammani ba, zan baka sirrikan daga cikin irin ayyukanku, dan Allah wannan kaɗai zaka iya yi mini ka ceci rayuwata da ta Mijina." Maleek ido ya zuba musu dan shi dai babu abin da ya iya gani a gurin yana tabarmar gurin take haka yake kallanta, yana tsaka da tunani yaji Wanzamin yace, "Allah ya taimakeki wannan fa ba ƙaramin aiki bane, kuma maganar gaskiya nikam ina jin tsoro saboda kin ce kema ya gagareki, ina gudun halin da rayuwata da na iyalaina zamu shiga." Maryo ta share hawayenta ta ce, "Ba wai ya gagareni bane saboda ba zan iya ba, a'a kasan yadda ahalin Bidayatul jinn muke da kowanne irin rami. Da ace idan na shiga zan iya cimma burina babu yadda za'ayi na nemi agajin wata halitta, don Allah ka taimaka ka ceci muradin da aka jima ana ƙoƙarin cimma burinsa." Wanzamin sharce gumin kansa ya yi yace, "Gaskiya wannan aikin yafi ƙarfina haka zalika ni banma san ke zan yiwa magani ba, da babu abin da zai sa na zo gidan nan." Maryo ta miƙe ta koma gurin zamanta na farko ta ce, "Na baka lokaci kayi nazari dan na fahimci duk gidan nam babu wanda ya fahimci halin da nake ciki" Maleek idanu ya zura musu dan gabaɗaya kansa ya kulle, Wanzamin ya gyara zaman jakarsa sannan yace, "Ya kamata ki sanar da su dan su fita daga hurumin da ba nasu ba, wannan yaƙin naki ne ki daina tunanin wani zai iya taimaka miki idan ba haka ba bazaki taɓa nasara ba, ki bar tunanin zan iya yin wani abu akai domin kin fi kowa sani waye Zulik da mugun halinsa, matsawar yana raye bazai taɓa barin wani yaga wallensa ba. Ke kaɗai ce bazai iya cutarwa ba dan haka ke kike da yaƙin kuma kike da nasarar a hannunki." Maryo cikin gamsuwa da jawabinsa ta ce. "Alƙawari na ɗauka san raɗin kaina bazan waiwaye su ba, ba zan koma gurinsu ba har sai lokacin da suka fahimci cewar ni ba tasu bace, sai sun tabbatar da cewar kama da wane bata wane. Ina so su fahimci bambamcin dake tsakanin fari da fari-fari idan yaso dan kansu sai su yanke hukuncin da ya dace da kansu, amma ko da soyayyarsa zata kashe ni tabbas bazan taɓa kunyata baiwar Allah da ta taimaka mini a lokacin da bani da kowa ba, ta yi mini sutura a lokacin da nake tsirara ta maye mini gurbin uwa da uba a lokacin da nake marainiya gaba da baya." Wazamin ba ƙaramin tausayinta ya ji ba a hankali ya miƙe ya ɗauki jakarsa yace, "Zan yi ƙoƙarin na wayar da kansu akan su san halin da ake ciki har game da masu maganin da suke nema ido rufe, ina miki fatan nasara akan abin da kika sa a gaba." yana gaba faɗa ya zagaye ramin da ta nuna masa har ya kai bakin ƙofa ya juya ya ce mata, "Ki ƙoƙarin ɓatar da tasawirar ramin nan domin kinsan mugu bai da kama, bana fatana a ƙara miki wani ƙullin akan wani dan kinsan cikin gidannan ma maƙiyanki sunfi masoyanki yawa." ficewa ya yi daga ɗakin yana sauri kamar zai tashi sama. Maleek da ya jiƙu da mamaki ya kalli Maryo da ta ƙarasa bakin gurin da sa ɗigon hawayen tana shafe gurin da hannunta, bayan ta gama shafewa ta kai hannunta kan gashinta ta shafa akan gashinta ta ƙarasa yi tana girgiza kanta.
Wanzamin na fita bai zame ko ina ba sai fadar Sarki Abdallah, yana shiga ya nemi guri ya russuna cikin girmamawa ya ƙara gaida Sarki sannan ya ɗan jim dan yanasan sanar da shi abin da zai ɗaure musu kai, sai dai bai san ta siffar da zasu karɓi maganar ta shi ba. Sarki Abdallah ne ya kalli yanayinsa ya kalli wasu Dogarawa ya umarce su da su basu guri, fadar ta rage daga Ciroma, Galadima sai Ɗan more. Sarki Abdallah yace. "Ɗan Wanzam ya ake ciki ina fatan jin nasara daga bakinka" Wanzamin ya gyara zama yace. Allah ya taimakeka ka gafarceni amma labarin ba me daɗi bane, kuma ina fatan wannan jawabin nawa zai warware wasu wasin da kuke ciki dangane da abin da na sani zan sanar da ku. Maganar gaskiya wannan yarinyat duk wani Mai magani da zaku kira sai dai yaci kuɗinku dan babu wata nasara da zai samu a kanta, shekaru goma da suka wuce akwai wani abokina wanda ya kasance yana daga cikin jinsin aljanu, ya bani labarinta dan haka zan sanar da ku idan kuna da buƙata." Sarki Abdallah mamaki ne ya kama shi ya kallai Wanzami ya gyaɗa kai, Wanzamin ya ci gaba da cewa. "Wasu dubannin shekaru da suka wuce..."
Yanzu sai kuna hakuri wallahi sbd rashin wuta bana samun caji akai akai idan kun lura yawan typing ya ja baya ku karɓeshi yanda ya samu pls😥👏🏻
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[19/11/2021, 19:26] Ameera Adam🌚: 31...
SHEKARU DUBU ƊAYA
DA ƊARI BIYAR BAYA
Ƙorama ce mai cike da yalwar tsuntsaye da kala-kalar korayen ganyayyaki mabambamta, ban da kukan tsuntsaye babu abin da yake tashi a gurin sai tsirarin kukan hallitun dake cikin ƙarƙashin ruwa. Waɗannan kukan hallitu kaɗai sun isa zaburar ko tsoratar da duk wata hallitar bil'adama da tai gangancin halartar gurin, saboda tsari da yanayin gurin bai daidaitu da zubi da mazaunin hallitar da ta kasance Bil'adam ba. Ilahirin hankalinta ya tafi ga tunanin abin da yake faruwa dangane da makomar rayuwarta, a hankali take ɗaukan waɗansu irin duwatsu masu kama da ruwan zaiba tana jefawa a cikin ruwan, dukda a lokacin hawaye ne ke malala a saman fuskarta. A hankali ya tako ya ƙaraso gurinta cikin shauƙin so da ƙauna ya rungumota jikinsa ya fara yi mata magana cikin harshe yaren su na Jinnu.
"Har bis kilman dilfaskinbat miladu war kibtinga rautiku filsin yaytarku lilbaitu wurgas yaftis gurman?"
(Barka da hutawa Sarauniyar duniya shin akwai wani abu da bai yi miki daɗi ba dangane da zaman ki a gurin nan?"
(AI MUN ƊAN TAƁA YARENSU KO😂)
Hawayen idanuwanta ne suka ci gaba da malala kafin tayi wani yunƙuri yasa hannunda yana goge mata fuskarta yana cewa, "Zubar hawayenki dai-dai yake da zubar dalma a dandamalin zuciyata" a gaggauce ta ɗago tana kallonta dan ita kanta sheda ce dangane da abinda ya faɗa sai dai wannan jiginanniyar ƙaddarar ba lallai ta bar cikar burinsu ba, murya a sanyaye ta fara magana cikin irin yarensu na aljanu duk da kasancewarta cikin jinsin Bil'adam. "Ka mayar da ni gida kar su neme ni su rasa" hancin ta ya ja yace, "Idan sun tambayeki ai sai ki ce musu kina gurin mijinki" sunkuyar da kai ƙasa tayi ta ce, "Kasan Kaka ya hanani daɗewa a gurin nan sabo da yana tsoron abin da kaje yazo, kafi kowa sanin yadda ƴan uwanka suka ɗauke ni basa sona basa ƙunata, ina tsoronma wata rana karsu fara farautar rayuwata, amma na kasa haƙurƙurtar da zuciyata akan soyayyarka me yasa? Meyasa bazasu duba irin soyayyar da mukewa juna ba?" A wannan karan kukanta ne ya tsananta saboda yadda kalaman suke fitowa daga ƙasan zuciyarta, rungumota ya yi yana lallashinta yana jin kukan nata har cikin zuciyarsa. Sai da ya lura kukan nata ya fara tsagaitawa ya kalleta yace, "Dukkan tsanani yana tare da sauƙi. Ki daina kuka saboda hakan shi zai ƙara raunatar da tawa zuciyar, kin fi kowa sanin yadda nake ƙaunarki kuma bana tunanin ƙiyayyar da suke nuna miki zata iya tasiri a zamantakewar mu, kedai mu ci gaba da haƙuri wata rana sai labari." Da sauri ta fisge hannunta ta ce, "Har sai yaushe labarin zai zo ne sai yaushe zasu daina cin kashi a kaina yadda suka ga dama, dan Allah kayi wani abu mana me zai hana mu tafi wani gurin domin muyi rayuwarmu" sunkuyar da kai ya yi sannan ya ɗago da kai yana yi mata wani irin murmushi sannan yace, "Kinfi kowa sanin ni kaɗai Mahaifina ya mallaka kuma a yanzu yana cikin halin rashin lafiya, shin idan na tafi na barshi nayi masa adalci kenan?" Nine maganin masarauta Mahaifina yana da tarin ƴan uba kina ganin zasu kula da shi? A kan idonsa ma meye basa yi mana balle ace na tafi na barsu su biyu shi da Mahaifiyata." Cikin gamsuwa da kalamansa ta ce, "Tabbas hakane amma wannan shirun da kake yi a kodayaushe bazai fusshemu da komai ba." Murmushi ya yi mata yace, "Karki damu wata rana sai labari." gyaɗa masa kai tayi sannan ya sumbaci kumatunta, miƙewa ya yi yana riƙe da hannunta suka fara tafiya, suna gabda fita daga ƙoramara daga bayanta taji an fyaɗe ta tafi ta kifa ta faɗa kan cikinta, ƙara ta ƙwalla tana dafe baya cikin azaba, da sauri ya ƙarasa riƙeta Allah ya taimaka ma bata ji ciwo sosai ba, a hankali ta ɗago ta kalleshi suna haɗa ido ya wurga mata kallan tsana yana cewa. "Wannan cikin har abada bazaki haifeshi da sannu sai mun salwantar da ku gabaɗaya." Hawaye take yi a hankali ya ɗagata yana kaɗe mata kayan cikinta, faɗuwarta jinta ya yi har cikin jikinsa saindai babu yadda ya iya, hannunsa ya ɗora akan cikinta yace. "Ina fatan babu abin da ya shafi abin da yake cikinki" gyaɗa masa kai tayi tana sauke ajiyar zuciya. Ɗaukanta ya yi cak yace, "Rufe idonki" tun bai ƙarasa faɗa ba ta rufe saboda tasan gida zai mayar da ita.
Tsaye yake da ita a cikin bukkar da babu komi a cikin sai gadon tabarmar kara da buzun damusa a shimfeɗe, kwantar da ita ya yi ta buɗe idonta, ya kai bakinsa ya sumbaci goshinta yace ina tare da kai babu abin da zasu iya yi miki da ke da abim da yake cikinki" murmushi ta yi tana gyaɗa kai motsi suka ji daga baya, nan take Yace. "Ina zuwa." Yana gama faɗa ya zama gizagizo ya bi ta jikin bango ya koma cikin ragar da ta kasance mazauninsa, Kaka ne ya shigo ƙugunsa ɗauke da tafka-tafkan ganye waɗanda suka zame masa kamar makari ne na rufe al'aurarsa.
Tsaye ya yi akanta yana ƙare mata kallo duk sai ya ji yanayinsa babu daɗi, dan gani yake duk wani abu da zai faru da ita kamar shine silar komai. Tsugunnawa ya yi yana kallon busassun hawayen idonta, a hankali ya fara yi mata magana cikin tausasawa, "Kyauta! Kiyi haƙuri" juyowa tayi idanunta na cikowa da ƙwalla bata tanka masa ba, ya russunar da kai ƙasa kamar me nazari ya ci gaba da cewa, har gobe bazan daina ganin kaina a matsayin mai laifi ba saboda ta silata ce kika faɗa cikin wannan halin da kika tsinci kanki, ka yafe mini dan na tabbata haƙƙinki bazai taɓa barina ba matasawar baki yafe mini ba" ɗagowa tayi tana kallonsa murya na rawa ta tashi zaune ta ce, "Kaka dan Allah ka daina faɗin haka kana sa ina jin babu daɗi a zuciyata. Na tabbata kayi haka ne ba dan komai ba sai dan ka sama mini gurbin da zan fi samun kwanciyar hankali, kasan duk duniya bani da kowa bayan kai. Kaine kaci kashi da fitsarina tun da ni da kai na saba bansan iyayena ba da kai na buɗi ido, na tabbata bazaka taba zaɓa mini abin da zai cutar da ni ba." Hawaye ya fara saboda ba ƙaramin daɗi yaji ba yadda Allah ya dasa mata tausayinta a zuciya, katse tunaninsa ta yi da cewar, "Kowanne abu da zai faru da bawa na tabbata yana daga cikin ƙaddararsa, ni wannan ita ce tawa ƙaddarar, ni kaina ina shiga cikin ɗimuwa da tashin hankali idan na tuna halin da jinina zai fuskanta idan babu ni" Tana zuwa nan a zancenta hawaye ya ci gaba da tsiyaya daga idanunta, Kaka shima hawayen yake cikin tausayawa a zuciyarsa yake jin inama a ce haka bata faru ba, me yasa ko kaɗam bai yi hangen abin da zai faru a gaba ba. Me yasa bai bari ta kai munzalin da zai yi shawara da ita ba? Waɗannan tambayoyin yake jerawa cikin zuciyarsa yana jin nadama da dana sani, kamar tasan abin da yake zuciyarsa ta ce, "Kaka banasan ka dinga jerawa zuciyarka tambayoyin da zasu saka cikin ɗimuwa da tashin hankali, Ka sani duk duniya bani da kowa sai kai" ta ɗan shiru tana jin zuciyarta na ƙara raunata sannan ta ci gaba da cewa, "Sai kuma Mirdad,