Showing 9001 words to 12000 words out of 57328 words

Chapter 4 - Anya Baiwa Ce 1 Complete Hausa Novels.txt

30 Nov 2024

3901

a fannin soyayya. Bayan sun fito daga wankan wani irin mayafi me walwali yasa ya rufe su sai da suka jima a haka sannan suka sanya waɗansu irin kaya masu tsananin kyau. Tsokanarta ya yi ya tafi da gudu sannan ta bishi suka fara wasan ƴar ɓuƴa idan ta kamoshi wannan karan wani karan shi zai kamo ta. Suna cikin haka bayan ya ɓuya ta fara nemansa ta rasa sai a cen nesa da ita ta hango wani namiji da bata ga fuskarsa ba ya saɓa shi a kafaɗa jini na zuba a jikinsa, wani irin kuka ta rushe da shi ta nufi gurin da gudun gaske kafin ta ƙarasa tuni sun ɓace daga gurin. Firgigit ta buɗe ido saboda yadda kanta ya sara mata nan take jini ya fara ɗiga daga hancinta, a fili ta furta. "Wai waye wannan da a duk lokacin nake cikin nishaɗi yake datse mini shi? Anya zancen Abu bazai zama gaskiya ba kuwa da tace ƙila asiri akayi masa." Miƙewa tayi tana lumshe ido saboda hasken ranar da ya haske idonta.


Kamar daga sama aka jefoshi haka ta ganshi jikin bishiyar ɗorawa yana sakar mata lallausan murmushi, duk yadda taso ɗaure bakinta abin ya gagara har sai da ta mayar masa da martani. Takawa ta fara yi a hankali kanta na ci gaba da sara mata a hankali take sa wani ɗan ƙyalle tana goge jinin da yake ɗiga daga hancinta, tana gabda ƙarasawa gurinta ya ware mata hannuwa alamun ta shiga jikinsa da sauri ta tsaya a gurin tana sunkuyar da kai. Tana nan tsaye ta tsinkayi muryarsa yace. "Me ya kawo ki gurin nan ke kaɗai keda kike da tsoron amma kike zuwa gurin nan ke kaɗai" Maryo ta ɗago da ta kalleshi nan take gabanta yayi wata mummunan faɗuwa. Kayan da ta gani sanye a jikinsa cikin mafarkinta shi ta gani a jikinta, kamar ya shiga ranta ya katse tunaninta da cewar. "Kina mamakin kayan jikina ne?" da sauri ta gyaɗa masa kai murmushi yayi yace. "Ki wuce gida Inna na cen tana neman ki" bata musa masa ba ta wuce zuciyarta fal farinciki tana tafe tana waiwayensa har tayi nisa sosai.


Shigowarta mararrabar da zata kaita sashen su ta hango Saif tafe da shi da wani Bafade har suna tafe wannan Bafaden na yi masa hira, abin da ya bata mamaki da ta ganshi da wani kaya daban ba wanda ta ganshi a jikin bishiyar ɗorawa ba, sai dai har lokacin da suka ƙaraso bai nuna ma yaga me yanayinta ba bare ya nuna ya santa. Bata wani damu ba sai tayi tsammanin dan yana tare da wani ne yasa ya yi mata haka, haka ta wuce cen sashensu gurin kiran da yace Inna Habi tana yi mata.


Da daddare suna zaune suna hira su Maryo sai sauraron labarin da ake basu na bikin al'ada wanda sauran bayin suke basu labarin suke, Fulani Zaliha ce ta aiko a kira Maryo Inna Habi sam bata so haka ba saboda tana gudun ƙananun maganganun gidan. Maryo kai tsaye ta wuce sashen Fulani Zaliha da sallama ta shiga sashen, kan mazauninta na alfarta hangota zaune cikin shiga ta alfarma, bayin da suke kula da ita suna tayi mata hidima. Cikin girmamawa ta rissina ta gaida Fulani Zaliha, da fara'a ɗauke a fuskarta ta amsa mata sannan ta miƙa mata wasu kaya masu kyau ta ce. "Idan Allah ya kaimu gobe bikin al'ada so nake kiyi kwalliya da wannan kayan ina san ki fi kowacce Baiwa kyau." Maryo ba ƙaramin jindaɗi tayi ba haka ta dinga zabga mata godiya da Addu'a babu adadi, miƙewa Maryo tayi zata tafi har ta je bakin ƙofa Fulani Zaliha ta ce. "Ungo wannan ki miƙawa Saif Alkakin nan yana nan zaune yana bitar karatu" russunawa Maryo tayi ta karɓa da sallama ta ƙarasa gurin Saif ta miƙa masa, karɓa kawai ya yi ya ajiye sannan Maryo ta fice daga sashen.


Tana fita mararrabar matan sarki sabuwar Baiwar Fulani Maryama ta ƙwala mata kira tana zuwa ta ce. "Ki shiga ciki dama yanzu shugabata ta aika a kira ki" Maryo kanta tsaye ta shiga ta russuna da ladabi ta gaishe da Fulani Maryama. Bayan ta amsa ta miƙa mata wata ƴar doguwar wuƙa a cikin gidanta ta ce. "Ungo wannan ki je turakar Mai Martaba duk wanda ya tambayeki ki ce masa ni ce na aiko ki, idan kinje ki zaro ta daga gidanta ki ɗora aka adakarsa, ɗazu da naje yana bani tarihin shekarunta na manta na taho da ita yace tana da muhimmanci a gurinsa shiyasa bazan bari ta kwana a gurina ba, idan kin kai ki dawo zan baki saƙo ki kaiwa uwar bayi." Maryo kanta tsaye ta karɓi aiken Fulani Maryama bata tsaya ko ina ba sai turakar Sarki Aminullah.


Mamaki take sosai yadda ta ga gurin babu wani me gadi ko ɗaya kanta tsaye ta faɗa cikin turakar da yake da duhu haka ta fara laluben gurin da aka ce ta ajiye wuƙar. Wani uban itace aka buga mata a baya ana faɗin.


"Ƙarya kike makira ƴar talakawa" da sauri suka zagayeta aka haske turakar da fitilu sannan aka ɗaureta cikin wata irin murtukekiyar sarƙa.


YANZU BAKWA COMMENTS SOSAI BANSANI BA KO LABARIN NE BAYA MUKU DAƊI 😥😥😥😥




_LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[28/10/2021, 19:07] Ameera Adam🌚: 16...




Maryo cikin kiɗima da tashin hankali ta ce. "Dan Allah me nayi muku meye laifina?" Ɗaya daga cikin faɗawa ne ya kifeta da mari yace. "Tambayarmu ma kike yi me kikayi saboda tsabar rashin kunya?" Maryo shiru tayi tana jin jiri na ɗibanta da wani iri da kanta yake yi. A hankali Mai martaba ya ƙaraso gurin cikin ɓacin rai yace. "Ku wuce da ita gidan horo ɗaki na goma" tun bai rufe baki ba suka fisgi Maryo da ƙarfin tsiya suka fice da ita, Sarki Aminullah dafe kansa ya yi cikin damuwa ya furta. "Me na yi wa Zaliha take san hallakani me na aikata mata haka? Dama ƙiyayyar da take mini har ta kai haka? Ashe zata iya haɗa baki da wata a hallakani?" Ya jima a gurin yana zantuka kala-kala daga ƙarshe ya miƙe ya ɗauro alwala domin gabatar da sallar nafila.


Maryo ban da kuka babu abin da take yi damuwarta ɗaya da har lokacin batasan laifin da tayi ba, tun da ga shi har Mai Martaba da kansa yace akai gidan horo ta tabbata wannan ba ƙaramin laifi bane. Gidan horo wani gida ne mai ɗauke da manyan ɗakuna guda goma kowanne ɗaki akwai irin masu laifin da ake kaiwa ciki, lokacin da suka ƙarasa gidan baƙiƙƙirin yake sai aci bal-bal da Dogarawan suke tafe da ita kamar masu bautar wuta, tunda suka shiga ta ga ana lelleƙowa ta jikin windon ɗakin da ya kasance guda ɗai-ɗai a kowanne ɗaki, dukda duhun da ke mamaye a gurin bai hanasu san ganin wacce aka shigo da ita a cikin tsohon daren nan ba. Suna zuwa ɗaki na goma aka buɗe aka hankaɗa Maryo a ciki nan take suka rufo ƙofa suka fice daga gidan gabaɗaya. Yadda suka wurgar da Maryo a haka ta durƙushe a gurin tana wani irin gursheƙen kuka tana ambatar sunan Inna da kuma Abu, tana cikin wannan yanayin taji an zabga mata mari daga cen gefenta na hagu, ɗagowa tayi a gigice dan ganin wanda ya mareta amma duhun ɗakin ya hanata fuskantar wanda ya mareta. Wani abu ne ya tsaye mata a rai sai kawai ta ƙara rushewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Cikin wata irin murya shugabar ɗakin ta ce. "Zaki rufe mana baki ko sai na saɓa miki a gurin nan? Akanki aka fara shigowa gidan horo zaki hana mutane bacci da tsohon daren nan da alama ke ƙaramar ƴar iska ce." Maryo bata bi ta kan me maganar ba ta ci gaba da rera kuka me ban tausayi.


Batayi aune ba taji saukar duka ta ko'ina a jikinta, nan take kanta ya ci gaba da sara mata sai kuma jini ya ci gaba da zuba daga hancinta kamar wacce taji mugun rauni. Badariyya ita ce shugabar matan da suke cikin ɗakin kuma ita ta mari Maryo ta kuma jagoranci dukan da suke mata, daga jikin hannunta taji wani abu kamar jini, ta tsorata sosai sai dai babu damar ganin me yake faruwa saboda duhun da ke cikin ɗakin. Mutane huɗu ne suka rufawa Badariyya baya wajen dukan ta, dan haka Badariya jikinta ne yayi sanyi jin yarinyar da suke duka kamar bata motsi.


A hankali suka ji iska ta fara kaɗawa a cikin gabaɗaya gidan, sannu a hankali winduna ko ƙofofi suka amshi tayin da iskar take yi musu suma suka fara kaɗawa, tun suna yi a hankali har suka fara kaɗawa da ƙarfin gaske wata irin guguwa ce take tashi daga ko'ina, ba ƙaramin tsorata mutanen da ke cikin gidan suka yi ba hatta Dogarawan da ke tsaron bakin ƙofofin kowa ta kansa ya yi, dan ba ƙaramin tsorata suka yi da ganin irin iskar da take kaɗawa ba. Sai da iskar ta ɗauki lokaci me tsawo sannan komai ya fara lafawa kamar babu wani abu da ya taɓa faruwa.


Mutanen da suke cikin ɗakin su Maryo duk sunyi jigun-jigun kowa cikinsa ya ɗuru ruwa, duhun da ke cikin ɗakin shi ya hanasu ganin abin da yake faruwa.


Da Asubar fari ƴan ɗakin su Maryo suka tashi da mummunan tashin hankali sakamakon ganin gawarwaki a tsakar ɗakinsu kwance cikin jini, kafin wayewar gari tuni labari ya isa gurin dogarawa daga nan kuma labari isa zuwa fada.




A cikin daren bayan tafiyar da akayi da Maryo Mai Martaba ya jima a zaune sannan ya kira ɗaya daga cikin dogarawansa ya aika shi sashen Matansa akan ya kira masa Fulani Zaliha. Cikin girmamawa ya amsa tare da barin gurin.


Lokacin da Dogari yaje bakin sashen Fulani Zaliha baiwarta ya kira ya yi wa bayani, fuskarta ɗauke da damuwa ta ce. "Naji abin da ka faɗa sai dai ina tsoron sanarwa da uwar gijiyata saboda halin da take ciki, tun ɗazu jikin Mabiyin yarima ya rikice banda amai babu abin da yake yi, yanzu haka tana cen tsaye akansa sai suma yake yi." Dogarin yayi jim sannan yace. "Haka zaki yi ƙoƙarin sanar da ita saboda Mai Martaba ba abin wasa bane." Laraba ta juya jiki a sanyaye ta shiga sashen Fulani Zaliha a lokacin da ta shiga Saif na kwance ya samu jikin nasa ya lafa, Labara russunawa tayi cikin girmamawa ta ce. "Ranki shi daɗe Mai martaba ya aiko yana san ganin ki yanzu" da mamaki Fulani Zaliha ta kalli Laraba ta ce. "Ki je ki ce wa ɗan aiken ina zuwa." Laraba ta shi tayi ta wuce ta sanarwa da Dogarin sannan ta koma gurin zamanta ta zauna.


Fulani Zaliha tayi mamaki sosai akan kiran da Sarki Aminullah ya yi mata saboda rabonda ya aika kiranta haka kawai har ta manta, alkyabbarta ta sa ta feshe jikinta da turare. Sai da ta ƙara leƙa Saif sannan ta kira su Laraba ta umarce su akan su zauna a bakin ƙofar saif su kula da shi, saboda ko da zai farka bata kusa. Tana fita kai tsaye ta wuce turakar Mai Martana, lokacin da ta ƙarasa ciki yana kwance ya lumshe idanunsa kamar me bacci. Bakinta ɗauke ta sallama ta shiga ciki tana shiga ta zame alkyabar jikinta, gefen kan shimfiɗarsa ta zauna ta ce. "Barka da hutawa Ranka shi daɗe uban mai marayu majidaɗin talakawa mai iyayenma suna Allah san barka, Ina zaune an aiko da..." bata ƙarasa magana ba Sarki Aminullah ya ɗauke fuskarta da wani irin azabtaccen mari, kafin ta dawo daga azabar raɗaɗin marin da ya yi mata ya ƙara ɗauke fuskarta da wani gigitaccen mari. Nan take ta kiɗime har wasu irin taurari take a idanuwanta saboda zafin marin da ya sakar mata, tana cikin wannan yanayin Sarki Aminullah ya damƙo wuyanta ya shaƙe idanuwanta suka firfito har tana kakarin tari saboda wahala, sai da ya ga ta galabaita sannan ya yi wurgi da ita cen jikin bango. A wahalce take sauke ajiyar zuciya saboda yadda ya shaƙe wuyanta ji tayi kamar zata mutu, ɗago da shayayyun idanuwanta tayi tana yi masa wani kallo murya na rawa ta ce."Ranka shi daɗe me nayi maka haka kake so ka kashe ni?"


Wata razananniyar tsawa ya buga mata wacce tayi sanadiyyar gutsire ragowar maganar da take shirin faɗa, ba ƙaramin tsorata tayi da yanayin da ta ganshi tayi ba, jikinta har karkarwa yake. Tana nan a takure ta ji yace. "Ashe ke makira ce annaimiya bansani ba? Wannan lumbu-lumbunnda kike yu mini ashe mugun hali ne fal a ranki? Sai anyi magana ki fara Allah yace Annabi yace ashe sheɗan da zuri'arsa ne a ƙasan zuciyarki. Kin bani mamaki Zaliha duk cikin matana babu wacce nake ƙauna kamar ce babu macen da na nunawa so miraran kamar ke amma da abin da zaki yi mini sakayya kenan, bazan sauwaƙe miki ba haka zalika bazan sa a hukuntaki ba ta yadda wani zai yi tsammani har zancen ya fita, saboda idan na wulaƙanta ki kaina na wulaƙanta ko ba komai ke uwar Ɗana ce kuma idan za'a bada labari za'a ce tsohuwar matar Sarki Aminullah ce ko a ce Mahaifiya Saif Ɗan gidan Sarki Aminullah, zaki ci gaba da zama a ƙarƙashina kuma daga yanzu duk abin da ya same ni kece saboda akwai wani ɓoyayyun aminai na da suka san komai, ni da kike kainuwa ne dashen Allah kuma na zama ƙadarangaren bakin tulu a karni a kar tulu a barni na ɓata ruwa, kije da halinki Allah ya ƙara tsareni daga kaidinki."




Fulani Zaliha ban da hawaye babu abin da take yi saboda irin maganganun da ya gasa mata har ta fi jin zafinsu akan zafin marin da ya yi mata. Murya a sanyaye ta kalleshi ta ce. "Ba tun yau na kwana da sanin ka jima da yakiceni daga zuciyarka ba, duk irin wulaƙancin da ƙasƙancin da aka nuna mini ban taɓa buɗe baki nayi magana ba, ni da Ɗana ka juya mana baya babu wanda nake gani a cikin gidan nan naji daɗi bayan Saif a koyaushe a kyara muke a gurinka, babu tausayi ko tausasawa a tsakaninmu saboda kawai na haifo maka yaro nasakasasshe, na janye yarona da ni kaina daga gareka wannan ma ban tsira ba har sai ka kirani ka tozartani ka ci mini mutumci, bansan laifin da kake tuhumata da shi ba da har kake alaƙantani da annamimiya."


Kuka ne ya ci ƙarfinta sai da tayi me isarta sannan ta ci gaba da cewa. "A wannan ƙadamin da ake ciki tura ta kai bango ko da sakina ka saka aka wulaƙanta ni bazan yi kaico ba domin na lura ba mu ne a gabanka ba, abu ɗaya ne zai dameni wato Saif zanyi ta tunanin halin da makomarsa zata kasance tun da dama ni yake gani yaji daɗi a zuciyarsa. Bansan abin da nayi maka ba kuma bazan tilasta ka da ka gaya mini ba, nidai a kullin kuma a kodayaushe nasan Allah ba azzalumin bawansa bane sai bawan da ya zalinci kansa, tabbas Allah shi yake sanmu kuma shi ya kafamu a cikin gidan dan haka saniyar da bata da jela Allah shi yake kore mata ƙuda." Fulani zaliha daga haka ta miƙe tana hawaye sannan ta zira alkyabbarta ta fice daga turakar ko waiwayen Sarki Aminullah bata yi ba.


Sarki Aminullah jim ya yi maganganun Fulani Zaliha na niyyar tasiri a zuciyarsa, a ɓangare guda kuma maganganun Fulani Maryama da kama yarinyar da akayi na ƙoƙarin danne zantukan da Fulani Zaliha tayi masa, kansa ba ƙaramin zafi ya ɗauka ba saboda abubuwa na neman rikita shi lokaci guda. A baya dai yasan ya yarda da Zaliha ɗari bisa ɗari amma me yasa zata aikata haka agareshi? Tashi ya yi ya fara kaiwa yana komawa dan ganin matakin da ya kamata ya ɗauka, wani tsagi na daga zuciyarsa yana san aminta da Fulani Zaliha ya yinda wani tsagin yake ƙaryata ta da kalamanta.


Fulani Maryama na cikin rumfarta tana ta zarya kamar wacce ta yi wa sarki ƙarya, da wata mai sanye da kayan bayi ta shigo fuskarta a naɗe ta yadda babu wanda zai gane ta. Tana zuwa ta russuna cikin girmamawa ta ce. "Allah ya taimakeki aiki ya tafi yadda ake so si jiran sakamako. Babban albishir da zan sanar da ke uwar gijiyata tuni Takawa ya sa anwuce da ita gidan horo" Fulani Maryama tayi murimushi mai sauti ta ce. "Kije zan neme ki zuwa safiya akwai tukwicin da zanyi miki" Me ɓoyayyiyar fuskar ta ƙara russunawa tana godiya sannan ta fice daga rumfar. Fulanj Maryama farinciki ne ya kamata dan tasan ko ba komai haƙanta zai cimma ruwa, tasan ba makawa sai an turata gidan horo daga nan tana da tabbacin Mai Martaba sawa zai yi a kashe su gabaɗaya, idan kuma ya musu da adalci ya sa a ɗaure su ɗaurin rai da rai.


Lokacin da Fulani Zaliha ta koma sashenta gari yayi shiru sai kukan tsuntsaye da ƙarananan dabbobi, tana zuwa ta sallami Bayinta suka wuce makwancinsu ita kuma ta wuce cikin ɗakinta, saboda ɓacin rai ko ɗakin Saif bata leƙa ba. Tana shiga ta faɗa kan gado ta fashe da wani irin matsanancin kuka, lokaci ɗaya taji zaman gidan gabaɗaya ya fice mata daga rai ji take a ranta ina ma ace Mai martaba ya saketa ko ta huta da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login