Showing 33001 words to 36000 words out of 57328 words
wuri haka zaku sauka na ɗauka sai zuwa azahar?" Farida ta miƙawa Fulani Maryama Jaririnta da bai fi watannin shida ba sannan ta ce. "Mama wallahi saukar wuri muka yi ina ta kewarku ina Salman?" Fulani Maryama jin ta ambaci Salman sai da gabanta ya faɗi tayi ta maza ta ce. "Ina jin yana cen sashensa. Ya Auwal ɗin?" Farida ta ce. "Lafiya ƙalau ya wuce gaishe da Mai martaba. Mama ya jikin Saif kuwa?" Fulani Maryama ta ce. "Da yake ƙanin Ubana ne ko? Sai inyi ta bibiyar lafiyarsa" Farida sauya fuska tayi dan jininta ba ƙaramin haɗuwa ya yi dana Saif ba, duk lokacin da zata zo gida hutu a sace take zuwa gurinsa su gaisa. Farida ta kuma cewa. "To ya su Ummansu Hidaya da Ummansu Yusra?" A daƙile Fulani Maryama ta ce. "Lafiya kalau. Zaki dameni da tambaye-tambayen jaraba ko gama gaisawa bamuyi ba" Farida tayi murmushi sannan ta sakowa musu wata hirar, suna nan zaune aka dinga shigo da akwatinta da kuma tsarabar da ta kawo musu.
Cikin tashin hankali Sarki Aminullah ya furta. "Subhanallah Yakubu." Da sauri wasu dogarawa suka ƙarasa gurinsa suna riƙe shi lokacin har ya fara fita daga hayyacinsa. Daga tsakiyar kanta taji yace. "Ba shi da laifi, a bakin aikinsa yake tun da kike zo a ƙarƙashin masarautarsu dole kibi umarninsu idan ya mutu ranki zai ɓaci" A hargitse Maryo ta furta. "Furzaan" Abu na ganin haka danne cinyar Maryo tana mata alamar da ta nutsu tasan a gaban wanda take, Miƙewa Maryo tayi ta fara kalle-kalle ta ce. "Kana ina ne Furzaan?" bin ta suka yi da kallo kowa na yi mata kallon ta fara samun taɓuw, ido ta zurawa Dogarin da ke cikin wani hali nan take ya fara jin komai yana lafa masa a hankali ya fara buɗe idonsa yana kallansu ɗaya bayan ɗaya a wahalce, Ajiyar zuciya Sarki Aminullah ya sauke ganin Dogarin ya fara dawowa dai-dai. Ɗan more ne ya taimaka musu aka ɗauke shi aka fice daga fadar. Har lokacin Maryo na tsaye tana waige-waige ragowar dogarawan tsoron taɓa ta suka ji musamman da suka ga abin da ya faru da Ɗan uwansu. Inna Habi ce ta kalli Maryo cikin tsawa ta ce. "Maryo nemi guri ɗaya ki zaune ko ranki ya ɓaci." Ba musu Maryo ta zauna kafin ta kai ga zama hawayen da take maƙalewa ya fara sharara a fuskarta, Sarki Aminullan ya yi mata kallan tsaf yana nazarinta sannan yace. "Me yake damunki?" Kamar jira take ta rushe da kuka, sai da tayi me isarta babu wanda ya tanka ta sannan ta ce. "Allah ya taimake ka Saif ne" Takawa ya gyaɗa mata kai alamar neman ƙarin bayani ta ci gaba da cewa. "Yanzun nan ya yi mini magana amma kuma ya guje ni" Galadima cikin tsawa yace. "Ke yarinya ki samu nutsuwa a gaban Mai martaba kike" Maryo ta watsa masa wani kallo da idanunta da suka rune jawur, tayi ƙwafa ta ɗauke kanta. Sarki Aminullah wani tunani ya yi sannan ya yi murmushi yace. "Yanzu ki bamu nutsuwarki daga baya sai muyi maganar Saif ɗin" Maryo goge hawayenta ta farayi ta tattara hankalinta waje ɗaya ta ce. "Ina jinka Ranka shi daɗe" Sarki Aminullah ya kalli Maleek yace. "Ki dubi girman Allah kiji tsoron Allah, ki sani zaki muti ki tarar da Ubangiji ki gaya mana gaskiyar abin da kike sani game da Maleek" Maryo kallon Maleek tayi da Mamaki saboda ita dai ta san tun da take ma bata taɓa ganinsa ba sai a cikin Fada. Gyara zama tayi ta ce. "Allah ya taimake wallahi bansan shi ba hasalima ni bantaɓa ganinsa ba sai yau ko Inna" Inna Habi ta gyaɗa kai cikin gamsuwa da maganar Maryo, Maleek ya yi farat ya ce. "Shukra dan Allah karkiyi mini haka kinsan ko me ya faru ba laifina bane, ki tuna irin ƙaunar da na nuna miki da bakiki kike cewa duk rintsi duk wahaka bazaki gujeni ba amma me yasa kika mini..." Sarki Aminullah ya katse Maleek da cewar. "Maleek ɗan saurara mun" Shiru Maleek ya yi Takawa ya kalli Inna Habi yace. "Menene gaskiyar labarin yarinyar nan kinga wannan Ɗan ƙanwata ne yanzo yana iƙirarin Ƴarki Matarsa ce, ki gaya mini gaskiya tsakaninki da Allah" Inna Habi ta share gumin goshinta ta ce. "Allah ya taimakeka wallahi-wallahi Maryo dai ko auren fari bata taɓa yi na hasalima ko samari basa kulawa tunkafin mu shigo gidannan" Maleek ya karɓe zancen da. "Gaskiya akwai tuntuɓen harshe a maganarta, ku duba nan ku gani" ya faɗa yana lalubo salularsa mai kusan ƙirar rakani kashi wani hoto ya nuna musu da bai fito sosai ba, sai dai ga duk wanda ya san Maryo yana ganinta zai tabbatar da ita ce a jikin hotonsa duk kuwa da rashin kyawun camerar.Shiru fadar ta ɗauka kowa da abin da yake saƙawa a zuciyar shi. Baƙin da suka taho daga Masarautar Sarki Abdallah suma suna gani Maryo suka tabbatarwa da Sarki Aminullah cewar ita ce Shukran da Maleek yake faɗa.
Itama kuma Inna Habi ta tsaya kai da fata akan cewar Maryo ba Matar Maleek bace, dan ta ce ko kur'ani zata iya dafata akan haka ita kanta Maryo taci alwashin haka saboda ko a mafarki bata taɓa sanin ko da mai yanayin Maleek ba bare kuma a zahiri.Tun da aka fara maganar Salman ban da muzurai da harare-harare babu abin da yake yi, gani Sarki Aminullah ya fi karkata ga ɓangaren Maleek yasa Salman miƙewa tsaye cikin ƙaraji yace. "Ya isa haka! Kai Maleek wai me kake faɗa ne? Babu wata alaƙa da ke tsakaninka da ita, Ita ɗin tawa ce nine kaɗai zan mallaketa dan haka ka iya takunka tun kafin na ɗauki mataki a kanka" Maleek ya kalli Salman cikin nutsuwa yace. "Yaro man kaza. Matar tawa zaka dinga iƙirari da wacce zaka aura? Duk masarautarmu babu wanda bai san Shukra matata ce idan ma wani abun ka yi mata wanda yasa ta mance ni da ikon Allah sai komai ya warware, nina dogara da ikonsa kuma da sannu zai bayyana gaskiya." Wani kallo Salman ya watsa masa sannan ya saki wani malalacin murmushi ya fice daga fadar. Inna Habi da duk sauran mutanen gurin mamakin kalaman Salman suke idan aka cire Sarki Aminullah da Maryo da suka taɓa jin hakan daga bakinsa. Ganin haka yasa Sarki Aminullah ya umarci su Inna Habi da su koma sashensu bayan wani lokaci zai kuma nemansu idan buƙatar hakan ya taso, godiya suka yi masa sannan suka bar cikin fadar. Bayan fitar su idanun Maleek ya ciko da ƙwallah lokaci ɗaya ya fara zubda hawaye sanna ya kalli Takawa yace. "Allah ya taimakela dan Allah kayi wani abu kar na rasa Shukra dan Allah" Ba ƙaramin tausayi ya bawa Sarki Aminullah ba dafa kafaɗarsa yace. "Karka damu Son zan kira Sirikina muyi magana duk abin da ake ciki zaka ji, kai dai ka ci gaba da Addu'a Allah ya kawo mana mafita." Maleek ya gyaɗa kai sannan ya miƙe ta fice jiki babu ƙwari.
Inna Habi suna tafe magana na cinta har ta kasa daurewa ta cewa Maryo. "Maryo wato shima wannan Ɗan sarkin sonki yake ko? Saboda ga ki sakarai ki bada kanki kare da doko kowa naki ne yanzu meye fa'idar haka? Muna neman mafita ga wata matsalar ta ƙara ɓullowa yanzu mecece mafita?" Maryo tayi shiru kamar bazatayi magana ba zuwan bayan ƴan sakanni ta ce. "Inna wallahi babu wata alaƙa a tsakaninmu da wancen mahaukacin, shi kuma wancen mutumin kece sheda ko a mafarki bantaɓa ganinsa ba" Inna Habi ta sauke ajiyar zuciya ta faɗa wani tunanin. Har sun kusa ƙarasaw ɓangaren bayi ta hango Saif a zaune a kan dadduma da sauri ta canja hanya ta nufi gurinsa, da sallama ta ƙarasa sannan ta tsugunna har ƙasa ta ce. "Ina wuni Yaya Saif" Bai ɗago ya kalleta ba yace. "Lafiya" a gefen ta zauna ta ce. "Ɗazu a fadar Takawa naji kana mini magan. Dan Allah me yasa kake guje mini ko tambayar abin da yake cikina bakayi, yanzu haka kake san na haihu baka kula da lamuranmu?" har lokacin bai tanka mata ba Maryo ta fara hawaye tana jin ƙaunarsa na ƙara nuƙurƙusar zuciyarta, ta kamo hannunsa tana ƙoƙarin kaiwa saitin ƙirjinta ta ce. "Ka tausaya mini kaji yadda zuciyata take harbawa saboda kai, ni ce wacce a kodayaushe bama rabuwa dare, rana, safiya, zafi, sanyi da damina..." Da sauri ya fisge hannunsa ya kifeta da mari. Yana ɗago kai yaga wasu bayi har sun fara taruwa suna kallonsu, ganin ya kallesu yasa suka yi maza suka bar gurin. Maryo kafeshi tayi da ido sai kuma hawaye ya fara zuba zuciyarta na bugawa akai-akai. Tamke fuska ya yi tamau ya nuna ta da ɗan yatsa yace. "Wannan ya zama shi ne kashi na ƙarshe da zan gargaɗe ki da karki ƙara shiga sabga ta idan ba haka ba zan ɗauki mummunan mataki akanki, ke wacce irin mayya ce ne? Ban da mace Karya wace mace ce take bim namiji yake yakice ta. Uban waye ya yi miki cikin da zaki haifa? Wallahi idan na kuma jin waɗannan kalmomin naki sai na sa ankaiki gidan turu" yana gama faɗa miƙe ya wuce har yana hankaɗeta ta faɗi a gefe. Kuka ta rushe da shi mai tsuma zuciya nan take kanta ya sara ta fara wani irin tari tana tofar da jini, tana waigawa ta hango Inna Habi a tsaye tana kallonta ga hawaye na zuba daga idanunta. Abu ce ta ƙaraso gurun ta kama hannunta ta miƙe suka nufi gurin Inna Hani, suna zuwa gurin Inna Habi saboda baƙin ciki ta ɗauke da mari sannan ta rushe da kuka cikin takaici ta rufeta da duka tana cewa. "Maryo yanzu a gabana namiji yake dukanki saboda kin bada kanki a banza anya kin yiwa kanki adalci kuwa Maryo abin da zakiyi mini kenan" nan da nan gurin ya fara taruwa da mutane. Abu ce ta janye Maryo da har lokacin aman jini take yi, Inna Habi ta wuce su tana share hawaye sannan suma suka bi bayanta. Kafin wani lokaci tuni maganar marin da Saif ya yi wa Maryo ya zaga cikin gidan masarautar, dan har da masu yaddawa su Inna Habi da baƙar magana babu abin da take ce musu saboda tasan duk me ma aka gaya mata Maryo ce ta janyo musu.
Bayan kwana biyu gabaɗaya Maryo ta ƙara fita daga hayyacinta, ta rame ta lalace ko ruwan kirki bata iya sha, hatta makaranatar bokon data allon da suke zuwa gabaɗaya ta watsar bata da aiki sai kuka, idan abin duniya ya isheta sai dai ta wuce cikin daji ta nufi bakin bishiyar tsamiya ko kuka ta zauna, anan ne take samun nutsuwa wani lokacin har bacci take samu tayi.
Sati Biyu da zaman fadar su Maryo Sarki Aminullah ya tara su a lokacin wannan zaman harda Sarki Aminullah da da Mahaifiyar Maleek Hajiya Fahima, tun zamansu a fadar Sarki Abdallah da Hajiya Fahima suke bin Maryo da kallo, waɗansu hotuna Maleek ya ciro ya miƙawa Sarki Aminullah yace. "Waɗannan sheduna ne na farko" Sarki Aminullah ƙuri ya yi yana kallon hoton tabbas babu ko tantama wanna Maryo ce, miƙawa wani Dogari ya yi yace a miƙawa Inna Habi. Karɓa tayi tana kallo gabanta ya faɗi gani mace sak Maryo a kusa da Maleek sauran hotunan kuma tare da Sarki Abdallah ne da wasu mutane. Ta tsinkayi muryar Sarki Aminullah yace. "Me zaki ce game da wannan" kafin Inna Habi tayi magana Hajiya Fahima ta ce. "Nima ina da laifi a cikin wannan maganar saboda da ban musguna mata ba da bazata taɓa gujewa Maleek ba, ki sani nima nayi haka ne saboda wasu maganganu da aka gaya mini akanki" Sarki Aminullah ya dakatar da Hajiya Fahima ya kalli Inna Habi. Inna Habi ta ce. "A gafarce ni Allah ya taimakeka a baya na faɗi haka ne saboda banasan rabuwa da ita amma tabbas Maryo matar Maleek ce, hakan ne yasa na sauya mata suna zuwa Maryo a madadin Shukra" Ba Maryo ba hatta Abu a zabure suka kalli Inna Habi da ta sunkuyar da kai tana hawaye. Sarki Aminullah ya kalli Maryo yace. "Kinji me ta ce haka ne?" Maryo ta kalli Inna Habi nan take hawaye ya gangaro mata ta kalli Sarki Aminullah ta ce. "Eh haka ne amma ina nemar mata afuwa" Inna Habi ta ɗago da sauri ta kalli Maryo, Maryo ma ita take kallo tana hawaye. Sarki Aminullah yace. "Alhamdullah yanzu kin amince zaki bi mijinki" Abu tayi karaf ta ce. "Allah ya taimake ka yanzu bata da sha'awar zama da shi" Maryo ta sunkiyar da kai ta ce. "Eh ranka ya daɗe" Maleek ya ɗaga hannunsa yana godiya ga Ubangiji, Hajiya Fahima ta rungumo Maryo ta ce. "Matso ƴata Allah ya yi miki albarka" Sarki Abdallah yace. "Sirikina godiya muke Allah ya bar zumunci." Sarki Aminullah yace. "Akaita sashen Fulani Maryama a kintsata cikin shiga ta alfarma a yau za'a bashi matarsa ya wuce da ita" A firgice Inna Habi ta ɗago ta ce. "Ranka shi ɗaɗe amma..." Da sauri Maryo ta ce. "Amma barni yanzu ina san ƙeɓancewa da Inna" babu wanda ya hanata dan haka suka wuce cen sashen su na baya. Suna zuwa Inna Habi ta fisge hannunta daga cikin na Maryo ta ce. "Barni fada zan koma" Maryo ta ruƙo ta cikin kuka ta ce. "Me zaki ce?" Inna Habi ta ce. "Zan ce musu ƙarya nake bake bace" Maryo ta ce. "Inna gwara ki bari na tafi dan ko kin koma bazan fasa tafiya ba, dama tuni nayi niyyar nisa da gidan nan saboda soyayyarsa kasheni zata yi koda ban bi su ba zaku wayi gari da gawa ta ko kuma na gudu." Inna Habi ta fashe da kuka ta ce. "Amma me yasa baki ce musu ƙarya nake ba?" Maryo ta ce. "Ba zan iya ba Inna bazan taɓa kunya ta ki ba" Inna Habi ta ce. "Amma Maryo ya za'ayi ki zauna da mutum alhalin ba'a ɗaura muku aure da shi ba" Maryo ta ce. "Idam naje dole za'a ɗaura ku dai kuyi mini fatan alheri" suka rungumeta gabaɗaya suna kuka. Daga bakin ƙofa suka ji ana magana da Maryo da sauri ta yakice ta nufesu kai tsaye suka wuce sashen Fulani Maryama.
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[11/11/2021, 18:02] Ameera Adam🌚: 26...
Inna Habi na ganin haka ta durƙushe a gurin tana rushewa da wani irin matsanancin kuka, Abu ma kifa kanta tayi jikin Inna Habi tana rusgar kuka kamar wacce aka yi wa bushara da mutuwa, Carko-carko mutane suka yi a bakin ƙofar daga cen ƙasa ƙananan maganganu suna tashi sama-sama, Umma uwar soro ce ta shiga ɗakin da sauri zaninta har yana neman faɗuwa, tana shiga ta dafa Inna Habi ta ce. "Habi labarin da nake ji ya riskeni shin da gaske ne wai Maryo tsohuwar matar Maleek ce Ɗan wajen Fulani Fahima?" Inna Habi bata bi ta kanta ba ta ci gaba da raira kuka, ganin ta wannan sigar bazai fisshe da uwar soro ba yasa ta fara lallashinta cikin nuna alamun tausayawa tana cewa. "Kiyo haƙuri Habi ummm ko ba daɗe ko ba jima kinsan wannan ranar tana tafe bare kuma dama kin saba da ita tun da abaya ma haka ta faru, oh ashe dai Maryo ba Baiwa ba ce da ƙimarta Habi nikam garin yaya haka ta kasance ne?" Inna Habi ta ɗago da kai ta ce. "Me yasa baki tambayi waɗanda suka kai miki labarin ba?" Umma uwar soro ta kyaɓe baki tana wurga mata harara ta ce. "Samun sarararin kuturu gaɗa a cikin rama, saboda kun taka wani matsayo har kika fara yiwa mutane wulaƙanci, aikin ɓur inji tusa." Tana gama faɗa ta fice fuuuu daga ɗakin dan haka ta so ba taso ace taji komai daga bakin Inna Habi yadda zata ji daɗin idar da labarin. Maryo suna tafe banda hawaye babu abin da take yi har sun kai gabda shiga ɓangaren Fulani Maryama ta ce wa Bayin da suke biye da ita. "Ku dakata a nan zan je wani uzuri yanzu." Kamar su tanka mata sai dai babu wannan damar, cikin girmamawa suka ce. "Hutawarki lafiya" Kamar wacce ake janta haka ta dinga bin hanyar daji tana tafe har sai da ta dangana da bakin murgujejiyar bishiyar kukar da ta saba zama, tun kafin ta ƙarasa ta farajin sautin shassheƙar kuka waigawa tayi taga babu kowa a gurin daga cen hanyar rafin ta hango shi tsaye da hawaye ɗauke akan fuskarsa yana miƙa mata hannu alamun ta taho gareshi, dukda kukan da takeyi hakan bai hanata sakar masa murmushi ba dan haka ta fara ɗaga ƙafarta da niyyar ƙarasawa gurinsa, daga bayanta taga wasu mutane suna janta da ƙarfi dan karta ƙarasa gurinsa, fisgewa ta fara ƙoƙarin yi amma babu hali saboda sun fi ta yawa cikin kuka ta juya ta ce. "Bulbiyat meyasa zaki ci amanar Mahaifina me yasa kika ha'ince mu ku barni naje gareshi kafin su tafi da ni" Wacce ta kira da Bulbiyat ta bushe da dariya ta ce. "Dama cen bana tare da Mahaifinki a fuska ne kawai na nuna masa goyon baya amma ni ta hannun daman Zulik ce ko Mahaifiyarsa bata kaini kusanci da shi ba" Duk yadda taso ƙwacewa daga gurinsu ta kasa har ta hango shi ya nutse a cikin rafin da karfi ta fisge ta rushe da wani irin kuka, tana tsaka da rusa kuka daga cen bayanta ta ji ance. "Ke lafiyarki me ya kawo ki nan?" Tana waigawa ta ga Saif a tsaye ya harɗe hannuwansa, sanya yake cikin kaya na alfarma irin na ƴaƴam sarakuna