Showing 30001 words to 33000 words out of 57328 words
iya baku satar amsa akan abubuwan da ya kamata ku kiyaye wataƙila zai taimaka muku wajen binnuwar wasu sirrika na ku. Ku kiyaye zaƙewa cikin lamarinsu gabaɗaya su ukun nan, Rayzuta, Furzaan da Zulik duk kuwa abin da zaku ga sun aikata a tsakaninsu. Duk irin gumurzun da zasu tafka kar wanda ya shiga tsakaninsu domin a lokacin idanuwansu a rufe yake, sai a asiri karku kuskura kuce sihiri zai yi tasiri a jikinsu ina me jaddada muku sai dai ku haɗa da kissa. Abu na ƙarshe da zan gaya muku ba mai daɗi bane wataƙila ya faru wataƙila ku riski akasin haka, akwai gagarumin tashin hankalin da yake tunkarar masarautar ku ni dama nasan tunda Kalimsiyat ta wanzu a doron ƙasa dole a zubda jini. Dan haka lokaci na zuwa da masarautarku take cikin barazanar zubar jini sai wanda Allah ya tsare. Amma fa ban tabbatar ba bincike ne ya nuna mini ina ƙara ankarar da ku ne saboda ni nan babu uwar da zan iya yi muku indai ba so nake tsibiri na ya kama da wuta ba." Wata gwauruwar ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke Jakadiya ta furta. "Tirƙashi" Fulani Maryama ta ce. "Marduska yanzu babu wani abin da zaka iya aiwatar mana?" a hassale Marduska yace. "Babu tun da nima ta kaina nake, bana taɓo tsuliyar dodo ba haka kawai tunda kinji dai ance kowa ya kwana lafiya shi ya so. Amma akwai mutane huɗu a cikin gidanku masu daraja waɗanda ko kaɗan baza'a taɓa cutar da su ba. Sai kuma wasu tsirarin bayin Allah da naga suna da riƙo da addini suma dai bance akwai wani abu mummuma da zai faru da su ba. Sannan meye tuƙwicin ziyarar mu tunda Rayzuta ta hana mu ɗaukan rayuwakan masarautarku" Jiki babu ƙwari Fulani Maryama ta ce. "Duk abin da ka faɗa" Marduska yace. "Yanzu ki ciro mini gashin sassan jikinku zanyi wani aiki da shi daga haka kun biya ni sai kuma wani jiƙon" Jakadiya ta hau raba idanu tana wuri-wuri Fulani Maryama ta ce. "Da me zamu yankar maka?" Marduska ya yi wani nazari yace. "Karku damu zan tura Murduss zai ɗebar mini da kansa" cikin halin ko'inkula suka yiwa Marduska sallama suka koma Masarautar Kano jiki a sanyaye saboda rashin nasara.
Sarki Aminullah kallanta yake yana jin yadda zuciyarsa ke yi masa wani iri musamman da ya ga yadda duk ta bi ta rame kamar wacce ta yi jinya, lokaci ɗaya kuma yaji yana jin kewar matarsa saboda ko babu komai yasan ita ɗin ta dabance a cikin mata. Ganin irin kallon da yake mata yasa ta ƙara tsuke fuska tana ƙara gyara zaman alkyabbarta tare da sunkuyar da kai ƙasa. Sarki Aminullah ya kalleta yace. "Zaliha yaushe Saif ya samu lafiya ban sani ba?" Wani ƙululun baƙin ciki ne ya turniƙe zuciyarta, ta ɗago tana kallonsa kamar bazata yi magana ba a daƙile ta ce. "Rannan" sai da ya ja shiru na ƴan sakanni sannan yace. "Me yasa baki sanar da ni ba?" Wannan karan bata ɗago ta kalleshi ba ta ce. "Saboda na ga kamar bai shafe ka ba" wani irin kallo ya wurga mata a ɗan fusace yace. "Saboda ba nine mahaifinsa ba ko" Ita ɗin ma a fusace ta kalleshi ta sauke a jiyar zuciya sannan ta ce. "Idan ma kaine wani abu kake masa da zai tabbatar da cewar kai mahaifinsa ne" Sarki Aminullah ya tamke fuska cikin tsawa ya ci gaba da magana. "Karki manta a gaban wanda kike magana idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci, banasan rashin kunya Saif dai Ɗana ne ko kina so ko bakya so dan haka na fiki iko da shi ace Ɗan cikina yana fama da wannan lalurar har ya warke baki sanar da ni ba, wallahi da ace ƙaramin yaro ne babu abin da zai hana na ƙarɓe shi na bawa sauran matana riƙonsa. Sakarcin banza sakarcin wofi ko dan kinga nasa a kira ki ne har zaki nemi ki yi mini wulaƙanci?" Tun da ya fara zazzaga Faɗa idanunwanta suka fara zubda ƙwallah, tuna irin baƙar hawalar da ta sha akan Saif tayi da irin wulaƙancin da yake musu ita da shi har sauran matansa suka ara suka yafa, tun yana tsumma har ya yi wayo take wahala, tunowa tayi akwai ranar da Saif ya je fada gurinsa amma yasa aka dawo da shi gurinta wai zai yi baƙi kar su ganshi yaji kunya. Tana jin ya dire zancensa a zafafe ita ma ta ɗora da nata faɗan dan kamar wacce ta manta a gaban Sarki take, Sarkinma Sarkin Kano Sarkin da duk inda yaje aka ambaci masarautar da ya fito sai an bashi girma kuma an jinjina masa.
"Ni kaina da nasan maganar da zata kawo ni kenan da ban tako na zo turakarka ba, Wai me ka ɗauke ni ne ko dan kana matsayin Sarki? Kana tunanin a duniya bayan Ubangiji akwai wanda ya isa ya karɓe Saif daga hannuna? Wallahi idan zanyi yawo tsirara babu wani wanda ya isa ya rabani da Ɗana. Wato saboda yanzu ya warke ya koma cikakken mutum kamar kowa, babu nakasa a jikinsa shiyasa har zaka nuna shi wani mai muhimmanci ne a gurinka. Saif Ɗana ne nina ci wahalarsa ban ƙyamaci abuna ba, safe, rana, dare, sanyi zafi da damuwa ban taɓa jin kunyar wani ya ganni da shi ba saboda ni uwa ce a kowane yanayi Ɗana yake bazan guje shi ba, Dan Allah idan zakayi iko kayi da Ɗan lelenka wanda kasan ciwonsa baka jin kunyar nuna shi a idon duniya ba Saif da ya zame maka Alaƙaƙai ba. Na roƙe ka da girman Allah ka ƙyale mini Ɗana tun da na samu Allah ya bashi lafiya, karka jawo shi a jiki a nemi a salwantar mini da shi tunda ni shi kaɗai na mallaka."Tana kaiwa nan ta miƙe fuska ba walwala ta gyara alkyabbarta sannan ta juya ta ce. "Ranka ya daɗe na barka lafiya" ta yi ficewarta ba tare da ta ji daga bakinsa ba.
Sarki Aminullah ko kaɗan bai ji haushin maganganunta na ƙarshe ba domin ga duk wanda yake cikin gidan yasa Salman shine ɗan gaban goshinsa, sai dai wannan karan tsakaninsa da Allah yaji yana marmarin jan Ɗansa a jikinsa ba wai dan ya samu lafiya ba. A gefe ɗaya tunanin su Maryo ne ya faɗo masa maganganun da suka dinga furtawa ne suka shiga kai komo a ƙwaƙwalwarsa, a hankali ya furta.
"Wacece ita yarinyar nan? Meye ma asalinta ya akayi tazo gidan nan a matsayin baiwa." Shiru ya yi yana nazarin yadda yadda take furta kalamanta da yadda ta tako cikin fadarsa ba tare da tsoro ko shakka ba, a ɓangare ɗaya ya lura da rashin kwarjinin da ya yi mata uwa uba ga kalaman da take furtawa Salman kai tsaye. Salman da kowa a cikin gidan yake tsoron yi masa laifi ko da a cikin kuskure ne amma ace har Baiwa ta tsaya tana gasa mata maganganu haka. A fili ya furta. "Saif! To meye alaƙarta da Saif? Shi da ba wata isasshiyar lafiya ba" Lumshe idanunsa ya yi kamar wanda aka tsirawa allura a zabure haka ya buɗe su yana cewa. "Ita ce yarinyar da aka kama a turaka ta da wuƙa yanzu kuma ta dawo kan Ƴaƴana, ANYA BAIWA CE? Anya ba wani ne ya turo ta domin tayi masa aiki a kaina da iyalaina ba kuwa? Tabbas dole ayi mini binciken sirri domin na gano inda ta dosa." Yana rufe baki Wayarsa ta fara ringing yana dubawa ya ga sunan Sarki Abdallah Abdulmanaf, daidaita nutsuwarsa ya yi sannan ya ɗauka da sallama.
Bayan sun gaisa Mahaifin Maleek yace. "Sirikina Ɗanka ya zo mini da wata magana" da yake sukanyi wasa a tsakaninsu kowannensu yana kiran kowa da Sirikina. Sarki Aminullah yace. "Sirikina wacce magana kenan" Babu ɓata lokaci Mahaifin Maleek ya zayyane masa duk abin da Maleek ya kira ya sanar da shi ya ɗora da cewa. "Ka san yaran zamani da ƙwallafa rai akan abin da suke so, yaron nan babu yadda bamu yi da shi akan ya yi haƙuri ya fauwalawa Allah lamuransa akan mutuwar matarsa amma ina abun ya faskara, yanzu dai na taso mutum biyu daga nan akan su zo su zama sheda akan ita ce ko ba ita ɗin bace." Sarki Aminullah ya fahimci wacce Maleek yake nufi jikinsa ba ƙaramin sanyi ya yi ba, mamaki haɗe da jimami ya kamashi. Sai da ya tattaro jarumta yace. "Shikenan Siriki Allah yasa muji alheri" daga cen ɓangaren ya amsa da Ameen sannan suka yi sallama. Sarki Aminullah ya jima a zaune yana nazari sannan ya tashi ya ɗauro alwala ya fara gabatar da sallar Nafila.
Inna Habi ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, da sauri ta nufi kan Maryo tasa aka ɗebo mata ruwa ta fara yayyafa mata, sun jima a tsaye a kanta sannan ta sauke ajiyar zuciya. Carko-carko mutanen gurin suka yi ana kallon abin da yake faruwa, ganin haka yasa Abu ta ce. "Dan Allah ku bamu guri ko ta sha iska" ba dan sun so ba suka marmatsa daga gurin ƙananan maganganu na tashi daga tsakar gidan. Inna Habi ce ta zurfafa cikin tunani ganin Maryo ta fara wahallalen bacci cikin zuciyarta take cewa. "Ya Allah ka kawo mini ɗauke a cikin baƙon yanayin da muke ciki, nikam dawowar mu cikin gidan nan sam bai amfanar da ni komai ba. Haƙiƙa akwai ɓoyayyen lamari saboda Maryo sam bata da waɗannan ɗabi'un, amma me yasa zata sauya haka me yasa zata yarda da hurewar kunnen ɗa namiji har ya kai ga cutar da rayuwarta. Allah kana gani nayi bakin ƙoƙarina akan tarbiyyar yaran nan, ya Allah ka kawo mana salama a cikin halin da muke ciki." hawaye ne ke gangarowa daga Idanun Inna Habi, Abu na ganin haka ta matsa kusa da ita ta ce. "Inna dan Allah ki daina kuka. Addu'a ita ce mafita." Inna Habi kamar jira take ta ci gaba da zubda ƙwalla cikin kuka ta ce. "Abu kina ganin halin da Maryo take ciki, yaushe rabon da ciwon ta na zuciya ya tashi? A ƙalla amfi shekara kusan biyar bai tashi ba, ki ga yadda yarinya ta lalace duk ta fita hayyacinta akan Ɗa namiji, Abu ki dubi fa Maryo ko abinci bata ci yarinya ta zama kamar taɓaɓɓiya sai dai tayi ta magana ita kaɗai tana kuka, da rana kuka da daddare kuka koyaushe kuka alhalin wanda take yi dominsa ma baisan tana yi ba. Yanzu ya kike so muyi idan abun ɓoye ya fito fili? Ina zan sa kaina da kunya Abu? Kinsan dai yadda gidan nan yake" Abu itama hawaye take ta ce. "In sha Allah, Allah zai kawo mana mafita amma har yanzu gani nake kamar mafarki ne Inna ace wai Maryo na da ciki." A daidai lokacin Maryo ta buɗe idonta tana yamutsa fuska saboda yadda cikinta yake hautsina mata da tsananin yunwa, a hankali ta ce. "Abu zan sha ruwa" da sauri Abu ta miƙa mata wani saurin ruwa kamar mayuwanciya haka take ɗaɗɗakar ruwa har sai da ta shaye duka, tana gama sha da sauri ta fice daga ɗakin tana yunƙurin amai. Daga Inna Habi har Abu bin Maryo suka yi da kallo da take ta kwara amai kamar zata amayo hanjin cikinta. Abu ta miƙe ta kai mata ruwa a buta sai da ta kuskure baki sannan ta taso suka shiga ɗaki, a wahalce ta zauna tana mayar da ajiyar zuciya.
Inna habi kallan Maryo ta yi ta ce. "Me kike sha'awar ci" A kunyace Maryo ta saci kallan Inna Habi a hankali ta ce. "Kunun tsamiya kawai nake so" Inna Habi bata bata amsa ba ta miƙe ta fice daga ɗakin kai tsaye ta wace madafa domin nemowa Maryo kunu dan basa rasa kunun tsamiya da kunun kanwa a madafar.
Washegari tun asuba Jakadiya ta kasa zaune ta kasa tsaye sai kaiwa da kawowa take, Umma uwar soro ce ta leƙa ɗakin Jakadiya ta ce. "Jakadiya lafiya ke kaɗai sai ɓuruntu kike ko bakya jindaɗi ne?" Jakadiya ta kwaɓe fuska kamar zatayi kuka ta ce. "Cikina ne yake ɗan hautsina mini" Umma Uwar soro ta ce. "To sannu ko wani abun kika ci, kizo randar magani ki ɗiba kisha ko ya ɗaure miki ciki" Jakadiya daga ɗakinta ta amsa. "To bari sai zuwa wayewar gari" Jakadiya cen ƙuryar ɗaki ta shige ta tura kanta tana tura bakinta cikin zanin rufarta ta fashe da wani irin kuka, sai da tayi me isarta sannan ta kai hannunta ta ƙara shafa ƙwaryar molon da ta wayi gari da shi a kanta, kuka ta ƙara rushewa da shi ta zura hannunta cikin hammatarta nan ma taji siɗib kamar wacce aka sa wa aska aka aske. Duk wanda ya ga Jakadiya zai fahimci irin tashin hankalin da take ciki duk tayi zuru-zuru, tana ganin gari ya waye ko ta kan kayan kari bata bi ba kai tsaye ta wuce sashen Fulani Maryama. Bayin Fulani Maryama sunyi mamakin ganin Jakadiya dan haka sai da suka shiga suka sanar da ita sannan aka yiwa Jakadiya iso.
Jakadiya na shiga ta tsugunna gaban Fulani Maryama ta rushe da wani irin kuka, wanda dama jiran wannan sukunin take dan ta samu tayi kukanta san ranta, sai da tayi me isarta ta ce. "Maryama yau na wayi da tashin hankali abin da bokan ya yi mini ya shammace ni, dubi kaina yadda na wayi gari da shi da ƙwaryar molo" sai kuma ta fara tattare hannun riga tace. "Dan Allah leƙa hammata ta ki gani" kukan kura Fulani Maryama tayi cikin kuka ta ce. "Jakadiya kanki ko kaina yanzu me zan cewa Takawa? Dubi fa yadda kika san silba haka kaina ya koma ɗazu da na kalli mudubi har ɗauke kaina nayi, a haka Takawa zai dinga kallo na?" Jakadiya ta saki hanci da baki tana kallon rankwalelen kan Fulani Maryama ta ce. "Maryama dama haka kike da rafkeken kai kamar na jinjirin Jaki, wallahi idan Takawa ya ganki a haka idan bai nemi tsari da ke ba shegiya nake."
Sarki Aminullah zaune a cikin fada cikin ƙasaitacciyar shigarsa ta alfarma irin ta ƙasaitattun sarakuna, Maleek ne a gefensa na dama sai Salman dake gefensa na hagu, wani bafade ne ya shigo ya russuna yace. "Allah ya taimakeka suna tafe ita da Mahaifiyarta da ƴar uwarta." Jinjina kai Sarki Aminullah ya yi sannan Bafaden ya fita, daga cen gefe baƙin Sarki Abdallah ne sai Waziri da Galadima daga cen bakin ƙofa Ɗan more ne sai dogarawan ƙofa.
Inna Habi ce a gaba Maryo da Abu suna rufa mata baya har suka ƙarasa cikin fadar, cikin girmamawa suka russuna suka gaida Mai martaba. Maleek da tun shigowarsa ya kafe Maryo da kallo ba ƙiftawa, Inna Habi kana kallan ta zaka fahimci tana cikin tashin hankali ta russuna ta ce. "Allah ya taimakeka ance kuna buƙatarmu a fada" Sarki Aminullah ya gyaɗa kai a hankali ya fara motsa baki yace. "Hakane! Munaso mu ji sunayenku" Inna Habi ce ta fara gabatar da kanta sai Abu daga ƙarshe Maryo ta gabatar da kanta tana watsawa Salman harara." Sarki Aminullah yace. "Maryo kinsan wannan" Maryo kallan Maleek da aka nuna mata tayi tun daga ƙasa har sama sannan ta ce. "Bansan shi ba Allah ya taimakeka" Sarki Aminullah ya kalli Maleek da ya dafe kai da hannu biyu jin kalaman Maryo yace. "Kaji abin da ta ce, dama na gaya maka ba lallai ita bace saboda wannan Baiwa ce" Maryo kallan Sarki Aminullah tayi cikin rashin jin daɗin kalamansa ta ce. "Allah ya taimake ka ni ba Baiwa bace..." tun bata rufe baki ba wani Bafade ya zabga mata doruna yana cewa. "Ƙarya kike ƴar talakawa..." bai rufe baki ba yaji andamƙi wuyansa nan take ya fara wani irin kakari....
JAMA'A WAI BA ME TAMBAYAR ASALIN TARIHIN SARKI AMINULLAH DA IYALANSA NE🤣
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[10/11/2021, 18:26] Ameera Adam🌚: 25...
Fulani Maryama ta murtike fuska ta ce. "Jakadiya ki iya bakinki bar ganin na sake miki fuska ki nemi ganin makwancina." Jakadiya har wannan lokacin bakin buɗe tana ƙarewa hallitar kai da fuskar Fulani Maryama, ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Yooo ƙarya nayi wallahi Maryama tun wuri ki nemar mana mafita idan ba haka ba wallahi sai kin fi Bora ƙanƙanshi agun Takawa, to wai ma me zaki ce masa idan ya ga kan a haka ko bari zakiyi sai ya kai hannu yaji mulmulallan kai?" Fulani Maryama shiru tayi tana nazarin maganganun Jakadiya dan a duniya babu abin da tafi tsana ace Takawa zai juya mata baya, murya a raunace ta ce. "Jakadiya wallahi bansan ya zanyi ba. Gaskiya Marduska ya cuceni ya taƙauceni" Jakadiya ta keɓr baki ta ce. "Ya cuce ki ko ya cucemu?" Fulani Maryama ta ce. "Jakadiya ba gwara ke ba. Yanzu saboda Allah duk ranar da Takawa ya ganni a haka wacce irin kunya zanji? Danma babu wani kataɓus da yake aikatawa yanzu amma duk da haka ai da kunya." Jakadiya ta ce. "Mu koma gurin Marduska ba sai asan abin yi ba" Fulani Maryama na shirin magana daga tsakar gida taji ana yi wa Farida barka da zuwa, da sauri ta janyo Ɗan kwalinta ta ɗaura ta cewa Jakadiya. "Maza ɗaure kanki naji muryar Farida zata shigo" Jakadiya ɗaure kai tayi ta miƙe ta ce. "To na barki lafiya" A dai-dai wannan lokacin Farida tayi sallama cikin murna ta ƙarasa ta rungume mahaifiyarta, barka da zuwa Jakadiya ta yi mata sannan tayi musu sallama ta fice.
Fulani Maryama ta dubi Farida ta ce. "Wai dama da